Iran Zata Fara Aikin Nema Da Kuma Hakar Danyen Man Fetur A Cikin Ruwan Tekun Caspian
Published: 10th, May 2025 GMT
Kamfanin man fetur da gas na kasar Iran zai fara aikin nema da hakar man fetur a tekun Caspian da ke arewacin kasar, wanda mataki ne na ci gaba ga kamfanin musamman a halin da ake ciki.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto jami’an kamfanin na cewa tuni sun kai kayakin aiki zuwa wuraren da suke zata akwai danyen man fetur a cikin tekun, sannan a shirye suke su fara aiki don hakar man daga yanzun.
Ba wannan ne karon farko wanda gwamnatin kasar Iran take hakar danyen man fetur a cikin tekun Caspian ba, saboda a shekara ta 1997 ne ta dakatar da hakar mai daga gabar tekun, sannan ta dakatar da hakar man a tsakiyar tekun a shekara ta 2014.
Labarin ya kara da cewa ministan man fetur na kasar ne Mohsen Paknejad ya kaddamar da aikin hakar man a gefen kasuwar baje koli na Gas, tashewa, da sinadaran danyen mai karo 29 da ke gudana a nan tehran.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Sin Ta Yi Matukar Allah Wadai Da Hare-Haren Da Amurka Ta Kaiwa Iran
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, ya ce Sin ta yi matukar Allah wadai da hare-haren da Amurka ta kai kasar Iran, tare da jefa bama-bamai kan cibiyoyin sarrafa nukiliyar kasar, dake karkashin kulawar hukumar lura da makamashin nukiliya ta kasa da kasa ko IAEA a takaice.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ya bayyana hakan ne a Lahadin nan, lokacin da yake tsokaci kan sanarwar da shugaban Amurka Donald Trump ya gabatar, cewa Amurka ta kaddamar da hare-hare kan cibiyoyi uku na nukiliyar kasar Iran. Jami’in ya ce matakin Amurka ya yi matukar keta makasudi, da ka’idojin MDD da dokokin kasa da kasa, ya kuma ruruta yanayin rashin tabbas da ake ciki a yankin Gabas ta Tsakiya.
Daga nan sai jami’in ya ce Sin na kira ga sassa masu ruwa da tsaki a tashin hankalin dake wakana, musamman ma Isra’ila, da su gaggauta cimma matsayar dakatar da bude wuta, tare da tabbatar da tsaron rayukan fararen hula, da fara tattaunawa da shawarwari. Ya ce Sin a shirye take, ta yi aiki da sauran kasashe wajen aiwatar da matakan tabbatar da adalci, da aiki tukuru wajen dawo da yanayin zaman lafiya da daidaito a Gabas ta Tsakiya. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp