Za Mu Magance Matsalar Ruwan Sha Kafin Ƙarshen 2025 A Kaduna – Uba Sani
Published: 7th, May 2025 GMT
Jihar Kaduna na ɗaya daga cikin jihohin Nijeriya da ke fama da matsalar samun tsaftataccen ruwan sha, musamman a karkara, inda mutane da dama ke fuskantar wahala wajen samun ruwan da zai ishe su sha da amfani.
Sai dai gwamnatin ta ce ta ƙudiri aniyar magance wannan matsala domin inganta rayuwar al’umma da kare lafiyar jama’a.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Matsalar Ruwan Sha
এছাড়াও পড়ুন:
Ambaliya ta lalata kauyuka 3 a Sakkwato
Akalla magidanta 50 ne ambaliyar ruwa ta raba da muhallansu a kauyuka uku na karamar hukumar Tangaza da ke jihar Sakkwato, sakamakon wani mamakon ruwan sama da aka tafka a yankunan.
Ambaliyar da ta mamaye kauyukan na Tangaza ne da suka hada da Gidan Madi da Baidi da Madarare, kuma ta haifar da rushewar gidaje da lalacewar gonaki da rijiyoyi da sauran su.
Yadda ’yan bindiga suka sace Zamfarawa 150 a cikin kwana 4 Duk wanda ya haka rijiyar burtsatse a Lekki ruwan masai yake sha – Gwamnatin LegasMutanen da lamarin ya shafa sun ce suna bukatar agajin gaggawa na abinci da magani da tsaftataccen ruwan sha.
Shugaban karamar hukumar ta Tangaza, Isah Salihu Kalenjeni, ya jagoranci wata tawaga sun ziyarci wuraren da lamarin ya shafa don ganin barnar da ambakiyar ta yi tare da jajanta wa mutanen yankunan.
A yayin ziyarar, Shugaban karamar hukumar ya tabbatar wa mutanen zai sanar da duk wata hukuma da ta dace don kawo masu daukin gaggawa kan halin da suke ciki.
Hukumomi a karamar hukuma da masu bayar da agajin gaggawa sun kuma yi kira wadanda iftila’in ya shafa da su yi aiki tukuru don kare barkewar annobar ciwo ga sauran al’umma.
Aliyu Na Abba daya daga cikin mutanen da ambaliyar ta rusa wa gida da gonaki biyu ya ce yana bukatar hukuma ta tausaya masa halin damuwar da shi da iyalansa suka fada.
Umaima Dan Umaru da ta ke da marayu uku a tare da ita ta ce gonakinsu biyu da suka yi shuka sun lalace sabadiyyar ambaliyar, don haka suna neman agaji.
Ta ce akalla akwai kusan mutum 50 da suka tafka asara a yankin nasu.