2025-05-12@18:26:56 GMT
إجمالي نتائج البحث: 45
«Jihar Kwara»:
Rukunin farko na maniyyata dari biyar da sittin (560) daga jihar Kwara tare da jami’an hukumar aikin hajji ta kasa NAHCON su biyu, sun tashi daga Filin Jirgin Sama na na Babatunde Idiagbon da ke Ilori zuwa Saudiyya domin gudanar da aikin hajjin shekarar 2025. Yayin da yake jawabi ga maniyyatan kafin tafiyarsu, Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya bukace su da su kasance masu kamun kai da kuma wakiltar jihar da kasa Najeriya. Gwamna AbdulRazaq, wanda mai ba shi shawara ta musamman, Alhaji Saadu Salaudeen, ya wakilta, ya yi kira ga dukkan maniyyata 2,174 daga jihar da su yi addu’a domin zaman lafiya da hadin kai a jihar da kuma kasa baki daya. Gwamnan ya kuma gargadi maniyyatan da...
Manistan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya gana da tokwaransa na kasar Saudiya Faisal Bin Farhan a birnin Jeddah inda bangarorin biyu suka tattauna kan al-amuran da suka shafi yankin, musamman batun Falasdinawa da kuma halin da suke ciki musamman a yankin gaza. Inda HKI take kashesu da yuwan, sannan tana ci gaba da rusa gidajensu a yankin yamma da kogin Jordan. Har’ila yau, kasashen biyu a matsayin manya-manyan kasashen a yankin yammacin Asiya sun yi kokarin kyautata dangantaka a tsakaninsu. Kuma Aragchi ya je kasar ta saudiya ne don kyautata dangantaka tsakanin kasashen biyu da kuma zurgaga al-adu da al-amura da suka hada kasashen biyu daga ciki har da kasancewarsu kasashe musulmi. A wani bangare Aragchi ya fadawa...

Bisa Rokon Bangaren Amurka Ne Manyan Jami’In Kasar Sin Zai Tattauna Da Takwaransa Na Gwamnatin Amurka Kan Batun Ciniki Da Tattalin Arziki
Yau Alhamis, kakakin ofishin jakadancin Sin dake Amurka ya amsa tambayoyi game da taron koli na tattaunawa kan batun ciniki da tattalin arziki tsakanin Sin da Amurka. A cewar kakakin, bangaren Amurka ta aikewa kasar Sin sakwanni da dama ta hanyoyi daban-daban don bayyana fatanta na tattaunawa da Sin kan batun harajin kwastam da sauransu. Kuma Sin ta yanke shawarar amincewa da shawarwarin ne bayan ta nazarci sakwannin da Amurka ta aika mata, kuma bisa rokon bangaren Amurka ne za a gudanar da shawarwarin. Ya ce Sin na nacewa ga matsayin kin yarda da matakin Amurka na yi gaban kanta wajen kakkabawa sauran sassan duniya harajin kwastam, kuma za ta ci gaba da kiyaye muradunta mai dacewa da kiyaye...
Bishop Joseph Osifuwa, Bishop na jihar Kwara, ya ce Nijeriya za ta iya magance matsalar rashin tsaro da ake fama da ita a sassan kasar nan idan har ta dauki matakin magance masu tada kayar baya. Bishop Osifuwa ya bayyana haka yayin da yake zantawa da manema labarai a gefen babban taron cocin karo na 35 a Ilorin. A cewarsa, magance rashin tsaro bai kamata ya zama matsala ga kasar da ta hada karfi da karfe a ayyukan wanzar da zaman lafiya na kasa da kasa domin murkushe ‘yan tawaye ba. Ya kuma shawarci gwamnati da kada ta rinka yi masu tada kayar baya ta hanyar yi musu afuwa, ya kara da cewa kada gwamnati ta tausayawa...
Dakta Abdulmalik ya ce, a halin yanzu gwamnatin jihar na da likitoci 99 kadai ne, wadanda ke kan tsarin albashi, ya kara da cewa; adadin da ake bukata kuma sun kai kimanin 180 zuwa 200. “Likitoci ukun da suka bar aiki, sun dawo bayan karin albashin likitocin da gwamnan ya yi a baya-bayan nan. Don haka, a da muna da likitoci 96, amma bayan karin albashin da gwamnan ya yi, uku da suka bar aikin sun dawo. Saboda haka, a halin yanzu muna da likitoci 99. Kazalika, muna da bukatar kari, domin kuwa kimanin likitoci 180 zuwa 200 muke bukata.” Saboda haka, hukumar ta ce; tana kokarin samar da wata manhaja da za ta bai wa marasa lafiya,...
Gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq ya ce gwamnatinsa ta himmatu wajen gina jihar da ma’aikata za su bunkasa, samar da ayyukan yi masu nagarta, da baiwa kowane bangare damar bayar da gudunmawa mai ma’ana ga ci gaban jihar. Gwamna AbdulRazaq a cikin sakonsa na bikin ranar ma’aikata ta duniya na shekarar 2025, a Ilorin, ya mika sakon gaisuwa ga maza da mata da jama’a da kungiyoyi masu zaman kansu wadanda kokarinsu ke karfafa tattalin arziki da samar da makomar al’ummarmu. Ya yaba da gagarumar gudunmawar da ma’aikata ke bayarwa a kowane fanni na sadaukarwa, juriya, da fasaha wanda ya sa su zama ginshiƙan girma da ci gaba. Gwamnan ya jaddada kudirin gwamnatin na aiwatar da manufofin da...
“Gwamnati ta amince da hada hannu da shugabannin al’umma na cikin gida domin tabbatar da tsaro. “Muna gode muku kan abin da kuke yi. Amma muna bukatar Sarakuna su yi magana da mutanenmu kan kokarin da dukkanmu muke yi don kare al’ummominmu daga masu kutse.” Gwamnan ya yi kira da a inganta hadin gwiwa a tsakanin al’umma da hukumomin tsaro domin kare rayuka da dukiyoyi. Mataimakin Shugaban Majalisar Sarakunan Jihar Kwara, Alhaji Ibrahim Bologi II, wanda shi ne Etsu Patigi, ya yaba wa gwamnan bisa hada gwiwa da su domin tabbatar da tsaro a jihar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin...
Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kwara ta fara yi wa maniyyata rigakafin cututtuka kafin gudanar da aikin Hajji na shekarar 2025. Da yake jawabi a wajen kaddamar da shirin rigakafin da aka gudanar a harabar hukumar da ke Ilori, shugaban hukumar, Alhaji Abdulsalam Abdulkadir, ya bayyana rigakafin a matsayin wani sharadi da ya zamto wajibi ga dukkan Alhazai bisa umarnin gwamnatin Saudiyya. Ya ce yin rigakafin yana da matuƙar muhimmanci wajen tabbatar da lafiyar Alhazai a lokacin gudanar da aikin Hajji. A cewarsa, an shirya shirin rigakafin ne domin hana yaduwar cututtuka da kuma tabbatar da cewa Alhazai sun samu lafiya da kwanciyar hankali yayin aikin Hajjin. Alhaji Abdulkadir ya bayyana cewa za a fara jigilar rukuni na...
A cewarsa, tuni aka shirya wuraren kwana da abinci ga maniyyatan a kasar Saudiyya. Abdulkadir ya tabbatar da cewa, ana shirye-shirye, inda za a yi alluran rigakafi a ranar 28 ga Afrilu, za a raba tufafi a 30 ga Afrilu, sannan kuma za a raba jakunkuna a ranar 1 ga Mayu. Ya kara da cewa maniyyatan da suka biya sama da Naira miliyan 8.4 na kudin aikin Hajji, za a biya su bayan sun dawo daga Saudiyya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na...
Ƴan fashi sun sace fasinjoji guda bakwai a cikin motocin haya biyu a ƙauyen Eleyin da ke cikin ƙaramar hukumar Isin a Jihar Kwara. A cewar rahoton LEADERSHIP, lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 5:45 na yamma a ranar Juma’ar da ta gabata, lokacin da wasu ƴan fashi su biyar suka toshe hanya, suka tsayar da motoci biyu, sannan suka tilasta ɗaukar dukkanin fasinjojin zuwa wani wuri da ba a sani ba. Uwargidan Shugaban Kasar Sin Ta Tattauna Da Takwararta Ta Kasar Kenya Ra’ayin Matasa Kan Kungiyar ‘Yan Ta’adda Mai Suna Lakurawa Da Ta Fito A Kebbi Wasu majiyoyi sun bayyana cewa, daga cikin fasinjojin motar ɗaya, akwai shugaban sashin shari’a na ƙaramar hukumar Oke Ero, Barr. Elizabeth Arinde,...
Babban hafsan sojin kasa, Laftanar Janar Olufemi Oluyede, ya ba da umarnin ga rundunar sojin Najeriya da ta fatattaki ‘yan bindigar da ke addabar al’ummar kananan hukumomin Baruten da Kaiama na jihar kwara da Borgu da ke dajin Kainji a jihar Neja cikin wata guda. A jawabin da ya yi wa dakarun rundunar soji bataliya ta 22 a Sobi Ilorin, Oluyede ya ce sojojin Najeriya ba za su bari tashin hankalin yankin arewa maso gabas ya rikide zuwa arewa ta tsakiya ba. A cewarsa nauyi ne da ya rataya a wuyan sojojin Najeriya su kare martabar yankunan kasar. Shugaban hafsan sojin ya ce dole ne a fatattaki ‘yan bindigar daga yankin Najeriya nan da wata guda. ...
An samu rahoton cewa, Fursunoni tara a gidan yari na Oko Erin a jihar Kwara a ranar 19 ga watan Afrilu, sun tsere. Majiyoyin leken asiri sun shaida wa Zagazola Makama cewa, da misalin karfe 10:00 na dare, wani ma’aikaci a gidan, mai suna Joseph Issa, ya sanar da faruwar lamarin. Rugujewar Gini A Legas: Adadin wadanda Suka Mutu Ya Kai Biyar, An Ceto 20 Wang Yi Ya Yi Bayani Kan Ziyarar Shugaba Xi Jinping A Vietnam Da Malaysia Da Cambodia Ba tare da bata lokaci ba, ‘yansanda suka yi gaggawar isa wurin, inda suka sake kama daya daga cikin wadanda suka tsere, mai suna Abdul Raman Misa mai shekaru 15. An mayar da Misa gidan yarin, yayin da ake...
Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kwara ta kammala shirye-shirye domin fara taron bita ga maniyyata aikin Hajjin bana. Shugaban Hukumar, Alhaji Abdulsalam Abdulkadir ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai a Ilori. Ya shawarci dukkan maniyyata da su halarci wannan muhimmin shiri, yana mai cewa za a tattauna muhimman batutuwa da suka shafi yadda ake gudanar da ibadar Hajji. Alhaji Abdulkadir ya bayyana cewa za a fara gudanar da taron bitar ne a harabar Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar daga ranar Lahadi, 20 ga watan Afirilun 2025. Shugaban ya ƙara da cewa babban limamin masallacin Juma’a na Ilori, Sheikh Imam Mohammed Bashir, tare da wasu malaman addini daga sassa daban-daban na jihar za su jagoranci...
A zantawarsa ta wayar tarho da tokwaransa na kasar Kuwait, ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya ce tattaunawarsa da Abdullah Ali Al-Yahya ya fi bada karfi kan al-amuran yankin Asiya ta kudu musamman tattaunawa tsakanin Iran da Amurka kan shirinta na makamshin nukliya da kuma dagewa kasar takunkuman tattalin arzikin da aka dora mata. A cikin tattaunawar dai ministan harkokin wajen kasar Kuwai y ace, kasashen yankin da dama sun ji dadin ganin cewa Iran da Amurka suna tattaunawa a tsakaninsu, kuma fatansu shi ne ya zama daga karshe kasashen biyu sun cimma dai-dato don warware matsalolin da ke tsakaninsu ta hanyar tattaunawa. Aragchi ya bayyana cewa a halin yanzu ba zamu iya fadar menen sakamakon tattaunawar ba,...
Rundunar ‘yan sandan jihar Kwara, ta ce an shirya shirye-shirye domin karfafa tsaro a jihar da kuma tabbatar da mazauna yankin suna rayuwa cikin yanayi na zaman lafiya da tsaro. Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Adekimi Ojo ne ya bayyana haka da yake zantawa da manema labarai a hedikwatar ‘yan sanda da ke Ilorin. Ya ce gwamnatinsa ba za ta amince da rashin da’a, take hakkin bil’adama, yana mai cewa ma’aikatan da suka yi kuskure za su fuskanci tsauraran mataki. Ojo ya yi alkawarin samarwa jihar tsaro ta hanyar magance miyagun laifuffuka da kuma kiyaye da’a da kwarewa a cikin rundunar ‘yan sanda. Ya bayyana cewa rundunar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen yakar...
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Arakchi ya tattauna ta wayar tarho da takwaransa na Masar Badr Abdelatty, inda suka tattauna batutuwan da suka shafi yankin. Manyan jami’an diflomasiyyar Iran da Masar sun yi magana ta wayar tarho da yammacin ranar Laraba, a cewar shafin Telegram na kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran. Araqchi ya jaddada muhimmancin daukar matakin hadin gwiwa da kasashen yankin domin gaggauta dakatar da laifukan da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ke aikatawa, da kuma tsagaita bude wuta a zirin Gaza, lamarin da ya ce yana da matukar muhimmanci wajen warware wasu rikice-rikice a yankin yammacin Asiya. Jami’an biyu sun bayyana matukar damuwarsu kan yadda ake ci gaba da samun tashe-tashen hankula a yankin, sakamakon ci gaba da kai...
Akalla malaman makarantun firamare 1,800, a fadin kananan hukumomi goma sha shida na jihar Kwara, aaka horar da su kan kara kuzari kan ilimin zamani, hanyoyin amfani da kayan zamani wajen koyarwa. Da yake bayyana taron bitar na kwanaki goma da aka bude a makarantar sakandire ta Queen Elizabeth da ke Ilorin wanda KwaraLEARN tare da hadin gwiwar hukumar kula da ilimin bai daya ta jihar Kwara (KWSUBEB) ta shirya, kwamishinan ilimi da ci gaban bil’adama na jihar, Dokta Lawal Olohungbebe ya ce shirin na daya daga cikin manyan dabarun da jihar ta bullo da shi na bunkasa harkar ilimi domin ya dace da ka’idojin karni na 21. Ya kuma bukaci malaman da su ci gaba da jajircewa...
Hukumar Kula da Jin DDaɗin Alhazai ta Jihar Kwara ta ayyana ranar Juma’a 11 ga Afirilun 2025 a matsayin ranar ƙarshe da za a kammala biyan kuɗin aikin hajjin bana ga dukkan maniyyatan jihar. Shugaban hukumar, Alhaji Abdulkadir Abdulsalam ne ya bayyana hakan a yayin wata hira da manema labarai a Ilori. Alhaji Abdulkadir ya bayyana cewa jimillar kuɗin aikin hajjin bana ya kai naira miliyan 8,459,000. Ya yi kira ga dukkan maniyyatan da suka fara biyan kuɗi da su tabbatar sun kammala ragowar kuɗin kafin ranar ƙarshe, wato 11 ga Afrilu, domin ba za a ƙara lokaci ba. Alhaji Abdulsalam ya kuma buƙaci maniyyatan da su gaggauta miƙa fasfo ɗin su na tafiya ƙasashen waje ga jami’ansu domin fara...
A wani labarin makamancin wannan, kimanin kananan masu kiwo 100 ne a Jihar Kwara, suka amfana da tallafin kiwon Awaki na kashin farko. Wannan tallafi, na daga cikin dabarun gwamnatin jihar na son kara bunkasa fannin da kuma samar da kudaden shiga ga masu kiwon, domin samun riba. A jawabinta a garin Ilorin, wajen kaddamar da kashin rabon Awakin, kashi na farko; wato a karkashin shirin jin kan iyali na L-PRES, Kwamishin Bunkasa Kiwo, Oloruntoyosi Thomas ya sanar da cewa, masu ruwa da tsaki a fannin ne, suka bayar da tallafin Awakin Thomas ya sanar da cewa, kwalliya na biyan kudin sabulu dangane da shirin L-PRES a jihar ta Kwara. Ta sanar da cewa, Gwamnan Jihar Kwara, Abdulrahman Abdulrazak, ba...
Gwamnatin jihar Kwara ta kaddamar da wani shiri na sauya fasalin noma domin habbaka kiwon dabbobi da bunƙasa yankunan karkara a fadin jihar. Jami’in shiri na musamman kan harkar noma wato Special Agro Industrial Processing Zone (SAPZ) a turance, Dr. Busari Isiaka ne ya bayyana hakan ga manema labarai. Ya ce wannan shiri ne da aka samar ta hanyar haɗin gwiwa tsakanin gwamnatin jihar da Bankin Raya Musulunci (IsDB) na Saudiyya domin kafa ingantattun abubuwan more rayuwa ga masu zuba jari da manoma a fannin sarrafa nama da madara. Dakta Isiaka, wanda ya jaddada muhimmancin wannan aiki, ya bayyana cewa wannan ne karon farko da wani gwamna mai ci ke jagorantar kwamitin da ke kula da irin wannan babban shiri....
Yau Alhamis, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya gana da ministan kasar Faransa mai kula da harkokin Turai da sauran kasashen waje, Jean Noel Barrot a birnin Beijing. Yayin ganawar, Wang Yi ya ce a lokacin da duniya take fama da yanayi mai cike da sauye-sauye da hargitsi, ya kamata kasashen biyu su nuna sanin ya kamata a matsayinsu na manyan kasashe tare da karfafa hadin gwiwa. Ya kara da cewa, kasar Sin na daukar Faransa a matsayin babbar abokiyar huldar cimma ci gaba mai inganci. A nasa bangare, Jean Noel Barrot ya ce Faransa ta kuduri niyyar raya dangantaka mai karko da dorewa da kyakkyawar makoma da kasar Sin. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana...
Gwamnatin jihar Kwara ta gargadi mazauna jihar kan yin gine-gine a kan bututun ruwa a fadin jihar. Kwamishinan Albarkatun Ruwa na Jihar, Usman Yunusa Lade, ya yi wannan gargadin a lokacin da ya kai ziyarar duba aikin gyaran babban bututun ruwa dake Flower Garden, a Ilorin. Kwamishinan, wanda ya samu wakilcin Sakatariyar Dindindin, Misis Christiana Asonibare, ta ce “kamar gine-gine, masallatai, coci-coci da shaguna a kan bututun ruwa da jama’a ke yi yana da illa ga samar da isasshen ruwa a fadin jihar.” Yunusa -Lade ya yi kira ga daukacin mazauna yankin da su kara kaimi ga kokarin gwamnati ta hanyar yin la’akari da bututun ruwa kafin a gina wani gini domin kaucewa lalata bututun ruwa da...
Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Ilorin, karkashin jagorancin Mai shari’a Abimbola Awogboro ta yanke wa Musa Buba hukuncin daurin sa’o’i 300 da hidimar al’umma, bisa samunsa da laifin gudanar da harkokin kasuwanci na canji ba tare da wani cikakken lasisi ba. Hakazalika, alkalin ya kuma yanke hukuncin daure wani Akinwale Olamilekan daga Owena Ijesha a karamar hukumar Oriade ta jihar Osun, daurin sa’o’i 300 (dari uku) da yiwa al’ummar hidima na tsawon sa’o’i biyar a kowace rana ba tare da zabin biyan tara ba, bayan da ya same shi da laifin aikata laifukan da suka shafi yanar gizo wato walawala ko yahoo boyi. Hukumar dake yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC...
An yi kira ga gwamnati a dukkan matakai da su hada kai da sauran masu ruwa da tsaki a harkar rage karuwar amfani da magungunan ba bias ka’ida ba a tsakanin matasa. Babban Daraktan Kula da Lafiya (CMD,) a Babban Asibitin Neuro-Psychiatric na Tarayya, Budo Egba, Jihar Kwara, Dokta Issa Awoye, ya yi wannan kiran ne a cikin jawabinsa mai taken, Sakamakon Neuropsychiatric na Maganganun Magani: Ra’ayin Clinical a taron masu ruwa da tsaki na Kwara na biyu kan Kariya da Sarrafa miyagun kwayoyi, wanda aka gudanar a Ilorin. A cewarsa an samu karuwar noma da fataucin miyagun kwayoyi a kasar, musamman a tsakanin matasa. Ya jera magungunan da aka saba amfani da su sun hada da...
Wata gobara da ta tashi da sanyin safiya ta kone wani shago a wani gini mai daki 13 da ke rukunin gidajen Ile-Lodo a cikin garin Etan a karamar hukumar Ekiti a jihar Kwara. A cikin wata sanarwa da kakakin hukumar kashe gobara ta jihar Kwara, Hassan Adekunle ya fitar, ya ce bayan an samu tashin gobarar ta kira motar kashe gobara da ma’aikatanta sun isa wurin da gaggawa domin shawo kan gobarar, wadda ta kone wani shago a gaban wani gini mai daki 13. A cewarsa duk da tsananin gobarar, jami’an kashe gobara sun yi taka-tsan-tsan, inda suka dakile tare da kashe wutar kafin ta bazu zuwa wasu gine-ginen da ke kusa. Sanarwar ta bayyana cewa...
A yau Talata ce ake saran shugaban kasar Rasha Vladimir Putin zai zanta ta wayar tarho da tokwaransa na kasar Amurka Donal Trump, kuma wannan shine zantawar shuwagabannin kasashen biyu tun shekaru masu yawa. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ya nakalto kakakin Fadar Krimlin Dmitry Peskov yana fadar haka a jiya Litinin, ya kuma kara da cewa a halin yanzu ana shirye-shiryen zantawar shuwagabnnin biyu. Peskov ya kara da cewa tattaunawar tasu zai maida hankali ne kan yakin Ukraine da matsalolin da suke kewaye da yakin. Yau ita ce ranar da kasar Rasha ta hade yankin Cremear ga kasar Rasha, a shekara ta 2014. Kwace yankin dai ya jawo matsaloli da dama tsakanin Amurka da Rasha a lokacin.
Sama da mutane 100 ne mazauna garin Ijagbo da ke karamar hukumar Oyun ta jihar Kwara suka rasa matsugunansu sakamakon ruwan sama ya yi barna a cikin al’umma. Gidan Rediyon Najeriya ya tattaro cewa an lalata cibiyoyin ilimi da gidajen zama da rumfunan kasuwa tare da lalata dukiyoyi. Guguwar ruwan sama ta yi barna a kwalejin Ansar Deen da ke Ijagbo yayin da ajujuwa sama da 10 suka yi lalace, inda dalibai da malamai suka makale. An gano cewa guguwar ta afku ne da misalin karfe 4 na yamma. a ranar Litinin, tare da yaga rufin ajujuwan tare da lalata muhimman kayan koyo da kuma kawo cikas ga ayyukan ilimi. Da suke Magana game da wannan...
Shugaban kwamatin duba rabon abincin azumi na majalisar dokokin jihar Jigawa a shiyyar Dutse kuma mataimakin Shugaban Majalisar, Alhaji Sani Isiyaku Abubakar ya bukaci masu aikin dafa abincin a karamar hukumar Gwaram da su dauki wannan aiki a matsayin turbar samun lada daga Allah Madaukakin Sarki ba wai hanyar neman riba kadai ba. Alhaji Sani Isayku Abubakar ya yi wannan kiran ne lokacin da ya jagoranci Yan kwamatin domin duba aikin dafawa da kuma rabon abincin azumi a unguwar Sabon Layi da ke karamar hukumar Gwaram. Ya ce rangadin duba rabon abincin azumi na daga aikin majalisa na duba ayyuka da shirye-shiryen gwamnati domin tabbatar da inganci da kuma shugabanci nagari. Alhaji Sani Isayku Abubakar tare da Yan kwamatin sun...
Rundunar ‘Yan sanda a jihar Kwara ta ce ta fara bincike kan kisan da aka yi wa Alhaji Idris Abubakar, shugaban kungiyar Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria (MACBAN) na jihar. A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Adetoun Ejire-Adeyemi ya fitar, ya ce an harbe shugaban ne a ranar 8 ga Maris, 2025 a kofar gidansa da ke Oke-Ose, a unguwar Ilorin. A cewar sanarwar Jami’an ‘yan sanda sun garzaya inda lamarin ya faru nan take, inda suka gano kwamson harsashi guda biyar da aka yi amfani da su wajen yin harbin. Ya bayyana cewa Hukumar Binciken Laifukan Jiha (SCID) ta fara gudanar da cikakken bincike kan lamarin. Ta kuma bada...
Wasu ’yan bindiga sun harbe shugaban ƙungiyar makiyaya Fulani ta Miyetti Allah reshen Jihar Kwara, Alhaji Idris Abubakar Sakaina. Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 10 na daren ranar Asabar yayin da maharan suka biyo sawunsa suka harbe shi a ƙofar gidansa da ke yankin Oke Ose na birnin Ilorin. Malaman Tsangaya Sun Bai wa Gwamna Inuwa Lambar Yabo Ta ‘Khadimul Qur’an’ Ta’addancin yankin Sahel ya ninka na sauran sassan duniya — Rahoto Muhammad Abdullahi, wani hadimin Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq kan hulɗa da al’umma da harkokin Fulani, ya tabbatar da faruwar lamarin. “Eh, an kashe shi jiya da daddare. Wasu ’yan bindiga ne suka harbe shi. “A yanzu haka ana shirin yi masa jana’iza, amma tun a jiya ’yan...
Ministan ya bayar da jerin sabbin jami’o’in da suka hada da jami’ar New City, Ayetoro, a Jihar Ogun, jami’ar Fortune, Igbotako, a Jihar Ondo, jami’ar Eranoba, Mabushi, jami’ar Minaret, Ikirun, Osun Anned, jami’ar Abubakar Toyin, Oke-Agba, a Jihar Kwara da kuma jami’ar Southern Atlantic, Uyo, a Jihar Akwa Ibom. Sauran su ne jami’ar Lens, Ilemona a Jihar Kwara, jami’ar Monarch, Iyesi-Ota, Jihar Ogun, jami’ar Tonnie Iredia da za ta koyar da ilimin sadarwa a birnin Benin, jami’ar Isaac Balami Aeronautics and Management, a Jihar Lagos da kuma jami’ar Kebin Eze Mgbowo, ta Jihar Inugu. A cewar Alausa, Shugaban kasa Bola Tinubu ya himmatu wajen kyautata harkokin ilimi da kyautata gine-gine a bangaren ilimi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna...
LEADERSHIP tana da mabiya kusan miliyan 3.7 a shafukan sada zumunta daban-daban, ciki har da dandalinta na Hausa. Tun daga ranar Lahadi, da yawa daga cikin masu bibiyar wadannan manhajoji ko dai suna ba da alamar dangwale, ko kuma taya murna kan labaran da suka shafi bikin karramawar da ke tafe. A makon da ya gabata, jaridar ta ce ta kara samun wani matsayi na musamman a bikin na bana, wanda kuma ke bikin cika shekaru 20 da kafa kamfanin, ta hanyar baje kolin abin da ke tafe a jaridar Financial Times, babbar jaridar kasuwanci da hada-hadar kudi ta duniya. Gangamin wanda aka fara a makon farko na watan Fabrairu, zai ci gaba da kasancewa har zuwa watan Maris, wanda...
Sama da litattafai 73,000 na koyarwa da kayan wasanni, gwamnatin jihar Kwara ta raba wa daliban makarantun firamare da kananan sakandare a fadin jihar. Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq da yake jawabi a wajen taron raba kayayyakin a Ilorin, ya ce sauran kayayyakin da za a raba sun hada da dakunan karatu na firamare 12,780; guda 100 na kayan ilimi na musamman; 260 na Kula da Yara da sauransu. Gwamna AbdulRazaq wanda ya samu wakilcin kwamishiniyar ilimi da ci gaban jama’a ta jihar, Hajiya Sa’adatu Modibbo Kawu, ta ce wannan wani shiri ne a cikin jerin shirye-shiryen da gwamnatin ke yi wanda ke nuni da fifikon da take da shi na samar da ilimin boko a jihar. A cewarsa...
Gwamnatin jihar Kwara ta kaddamar da shirin horas da makarantun firamare da kananan makarantun gwamnati 50 a fadin jihar domin su iya amfani da fasahar ziyyana shafin internet. Da yake gabatar da shirin a madadin Gwamna Abdulrahman AbdulRazaq a Makarantar Sakandare ta Bishop’s Smith Junior Ilorin, babban mai ba gwamna shawara na musamman, Alhaji Sa’adu Salau, ya ce shirin na dijital ya kasance don ƙarfafa fannin ilimi. A cewarsa shirin ya shafi sama da dalibai 150 a kowace makarantu 50 na gwamnati a matakin gwaji. Ya ce idan aka kafa harsashin tsarin zamani, yaran jihar Kwara ba za su koma baya a tsakanin takwarorinsu na duniya ba.” Gwamna AbdulRazaq yace sauran makarantun gwamnati da za su...
Mutane huɗu sun rasa rayukansu, wasu 10 kuma sun samu raunuka bayan wata motar bas ƙirar Hummer ta kama da wuta a garin Gwaram da ke Jihar Jigawa. Lamarin ya faru da misalin ƙarfe 4 na yammacin ranar Asabar, a kusa da makarantar sakandaren gwamnati ta Government Girls Unity Secondary School da ke Gwaram. Gobara ta ƙone gidaje, amfanin gona da dabbobi a Borno Za a kafa ƙarin makarantu a Zariya — Abbas Tajudeen Kakakin ’yan sandan Jihar Jigawa, SP Lawan Adam, ya tabbatar da faruwar hatsarin cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi. Ya ce motar ta taso daga Ƙaramar Hukumar Zaki daga Jihar Bauchi zuwa ƙauyen Ribadi da ke Ƙaramar Hukumar Gwaram. Sanarwar ta bayyana cewa...
Mai Martaba Sarkin Ilori, Alhaji Ibrahim Sulu-Gambari, ya buƙaci a riƙa tona asirin malaman tsubbu a duk inda suke. Sarkin wanda shi ne shugaban Majalisar Sarakunan Jihar Kwara, ya buƙaci malaman Musulunci da su riƙa fallasa duk masu fakewa da rigar malumta suna ayyukan tsubbu. Basaraken ya buƙaci malaman addini da “su tsaftace harkar tasu, tare da tona asirin ɓata-garin cikinsu ga jami’an tsaro kafin miyagun su kai ga aikata munanan ayyukansu ko halaka jama’a.” Ya yi wannan kira ne bayan kisan gillar da wani mai iƙirarin malumta mai suna Abdurrahman Bello, ya yi wa wata ɗaliba ’yar ajin ƙarshe a Kwalejin Ilimi ta Jihar Kwara da ake Ilori, mai suna Hafsah Lawal. A cikin sanarwar da basaraken ya...
Gwamnatin jihar Kwara ta ware naira biliyan 5 domin inganta cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko guda 70 a kananan hukumomin uku na jihar. Babban Sakatariyar Hukumar Kula da Lafiya a matakin farko ta Jihar Kwara (KWHCDA), Farfesa Nusirat Elelu ce ta bayyana haka a lokacin rattaba hannu kan kwangilolin da aka yi a hedikwatar Hukumar da ke Ilorin. Ta ce matakin zai hada da inganta ababen more rayuwa, samar da lantarki ta amafani da hasken rana, da samar da wuraren zama na ma’aikata, da samar da ruwan sha da samar da kayan aikin asibiti na zamani a duk wuraren da ke amfana da cibiyoyin kiwon lafiya na farko. Farfesa Elelu ya bayyana cewa shiga tsakani na...
Masu zanga-zangar wadanda ke dauke da alluna da rubuce-rubuce daban-daban sun ce, dole ne kamfanin ya samar da mafita mai dorewa tare da maido da wutar lantarki a tashar wutar lantarki ta ‘Kwara Poly feeder’ da ke rarraba wutar ga al’ummomin yankin.
Akalla manoma da ma’aikatan gona 1,000 ne gwamnatin jihar Kwara ta horas da su akan aikin gona da sarrafa ragowar amfanin gona don inganta amfanin gonakin da makiyaya ke amfani da su. Da yake jawabi a karshen horon, a Ilorin, wanda Synergy Impact Limited ya shirya, tare da tallafin gwamnatin tarayya, bankin duniya da kuma shirin gwamnatin jihar Kwara akan kiyo da noma (L-PRES) kakakin majalisar dokokin jihar Kwara, Yakubu Danladi ya bayyana cewa shirin yana da karfin inganta ayyukan noma a jihar. Kakakin majalisar wanda ya samu wakilcin shugaban kwamitin noma na majalisar, Issa Gideon, ya bayyana cewa shirin ya kara wa dimbin matasa kwarin gwiwa da jami’an noma da manoma wajen samar da kananan manaoma da...
Rundunar ƴansanda ta jihar Kwara ta daƙile yunƙurin sace mutane biyu tare da cafke mutum huɗu da ake zargi da hannu a lamarin a ƙananan hukumomin Ifelodun da Baruten. Kakakin rundunar, Toun Ejire-Adeyemi, ya bayyana cewa jami’an tsaro sun cafke su ne bayan bin diddigin kiran wayar barazana da wasu mutane suka samu a Ifelodun da Ilesha-Baruba, inda aka buƙace su biya kuɗin fansa har Naira miliyan tara. Yadda Ficewar Kwararrun Ma’aikata Daga Nijeriya Ke Barazana Ga Tattalin Arzikin Kasa Ɗalibin Jami’a Ya Hallaka Kansa Saboda Matsin Rayuwa A Jihar Kwara Bincike ya kai ga cafke Umar Sanni daga jihar Neja da Dairu Isiaku daga Ifelodun, da kuma Tukur Muhammad da Yahaya Abdullahi, waɗanda suka amsa laifin yin barazana da...
Rundunar ƴansanda ta jihar Kwara ta daƙile yunƙurin sace mutane biyu tare da cafke mutum huɗu da ake zargi da hannu a lamarin a ƙananan hukumomin Ifelodun da Baruten. Kakakin rundunar, Toun Ejire-Adeyemi, ya bayyana cewa jami’an tsaro sun cafke su ne bayan bin diddigin kiran wayar barazana da wasu mutane suka samu a Ifelodun da Ilesha-Baruba, inda aka buƙace su biya kuɗin fansa har Naira miliyan tara. Yadda Ficewar Kwararrun Ma’aikata Daga Nijeriya Ke Barazana Ga Tattalin Arzikin Kasa Ɗalibin Jami’a Ya Hallaka Kansa Saboda Matsin Rayuwa A Jihar Kwara Bincike ya kai ga cafke Umar Sanni daga jihar Neja da Dairu Isiaku daga Ifelodun, da kuma Tukur Muhammad da Yahaya Abdullahi, waɗanda suka amsa laifin yin barazana da...
A yau ne shugaba Bola Ahmed Tinubu zai tashi daga Abuja zuwa birnin Paris na kasar Faransa a wata ziyarar kashu kai, inda daga nan zai wuce Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha. A cikin wata sanarwa da mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai Bayo Onanuga ya fitar, ya ce a birnin Addis Ababa, shugaba Tinubu zai bi sahun shugabannin Afirka a zaman taron majalisar zartarwa karo na 46 da kuma zaman taro na 38 na shugabannin kasashen kungiyar tarayyar kasashen Afirka wato AU, wanda aka shirya daga ranar 12 zuwa 16 ga watan Fabarairun 2025. Shugaban zai isa Addis Ababa a farkon mako mai zuwa don halartar taron kungiyar ta AU. Yayin da yake...
An kuma samu labarin cewa ɗalibin ya rasa mahaifinsa a wasu shekarun baya, lamarin da ya mahaifiyarsa wadda tsohuwar malamar makaranta ce ta ci gaba da ɗaukar nauyin karatunsa tun daga lokacin. Rahotanni sun nuna cewa matsalarsa ta ƙara tsananta tun bayan dawowarsa makaranta a bara, inda abokan karatunsa suka tara kuɗi domin biya masa kuɗin makaranta da kuma siya masa kayan abinci. Duk da cewa jami’ar ba ta fitar da sanarwa a hukumance ba, amma wani babban jami’i a makarantar, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Talata, yana mai bayyana hakan a matsayin abin mamaki da ya jefa jami’ar cikin jimami.
Gwamnatin Jihar Kwara ta bayyana damuwarta kan ambaliyar rowa a gonakin shinkafa da dama a Shonga, da ke karamar hukumar Edu ta jihar. A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamna Rafiu Ajakaye ya fitar, ya ce Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq ya kafa kwamitin da zai binciki musabbabin ambaliyar. A cewarsa ana sa ran kwamitin zai ziyarci yankunan da lamarin ya shafa domin gudanar da bincike. Sanarwar ta ce kwamitin zai kai ziyarar jaje ga Sarkin Shonga Dr. Haliru Yahyah da wadanda abin ya shafa a cikin al’umma. Mambobin kwamitin da mataimakiyar shugaban ma’aikatan jihar, Gimbiya Bukola Babalola za ta jagoranta, sun hada da kwamishinan ayyukan gona, Mrs Oloruntoyosi Thomas, da kwamishinan muhalli, Hajiya Nafisat Musa Buge; da mai ba...
Gwamnatin jihar Kwara ta ce ta samar da matakan dakile yawaitar kauran likitocin daga jihar zuwa wasu kasashe, domin neman ingantacciyar rayuwa. Kwamishiniyar lafiya ta jihar, Dakta Amina El-Imam ta bayyana haka, a lokacin da ta karbi bakuncin shugabannin kungiyar likitoci ta kasa, a Ilorin. A cewarta gwamnatin ta amince da biyan Asusun Horar da Likita masu neman kwarewa da sauran abubuwan karawa likitoci gwarin gwiwa. Dokta El-Imam ta bayyana cewa gwamnatin jihar tana bakin kokarinta wajen ganin dukkan ma’aikatan jinya sun yi fice a aikin da suka zaba, domin dakile yawan barin kasan nan da likitoci ke yi zuwa kasashen waje. Kwamishinan, ya yi kira ga kungiyar da ta ziyarce ta, da ta fahimci...