Majalisar Dokokin Jihar Kaduna ta amince da wani kudirin doka da ya soke Dokar Kwalejin Kimiyya da Fasaha na Jihar Kaduna ta shekarar 1989, tare da maye gurbin ta da dokar Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Nuhu Bamalli.

Kudirin, mai taken “Kudirin Soke Dokar Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kaduna na Shekarar 1989 (Dokokin Jihar Kaduna na Shekarar 1991) da kuma Kafa Dokar Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Nuhu Bamalli, 2025,” an amince da shi ne yayin zaman majalisar wanda Shugaban Majalisar, Rt.

Hon. Yusuf Dahiru Liman, ya jagoranta.

 

Yusuf Liman ya bayyana cewa sabuwar dokar za ta bai wa kwalejin damar yin gogayya da sauran manyan cibiyoyin ilimi a fadin kasar nan, tare da dacewa da tsarin karatu na zamani. Ya jaddada muhimmancin sabunta tsarin dokar duba da yadda kwalejin ke samar da kwararrun dalibai masu nagarta.

Tunda farko da Yake gabatar da rahoto akan Kudirin dokar, Shugaban Kwamitin Hadin Giwa na Ilimi da Shari’a na majalisar, Barr. Mahmud Lawal Isma’ila, ya ce sun gudanar da bincike mai zurfi tare da tuntubar masu ruwa da tsaki, kuma suka gano cewa tsohuwar dokar ba ta dace da tsarin zamani ba.

Barrister Isma’ila ya ce sabuwar dokar ta kunshi muhimman sauye-sauye kamar mayar da wa’adin shugabancin makarantar zuwa shekara biyar kacal ba tare da sabuntawa ba, maimakon tsohon tsarin wa’adin shekara biyu da za a iya sabunta.

Yace wannan doka ta dace da tsarin ilimin manyan makarantu na kasar nan musamman a bangaren fasaha da kere-kere don cigaba mai maana.

Shima da Yake tsokaci Bayan amincewa da kudirin ya zama doka, Barr. Emmanuel Kantiyok, wanda ya dauki nauyin gabatar kudirin, ya yaba da yadda majalisar ta amince da dokar, yana mai cewa sabuwar dokar za ta bayar da ginshikin doka mai karfi ga ci gaban kwalejin, tare da tabbatar da cewa za a aiwatar da sauye-sauyen da dokar ta tanadar sannu a hankali don inganta tsarin ilimi a Jihar Kaduna.

Ya ce, daga yanzu, duk wanda ke rike da takardar shaidar Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Nuhu Bamalli yana da cikakken kariya da amincewa karkashin tanadin doka.

Shamsuddeen Mannir Atiku

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: Kwaleji Majalisar Dokar Kwalejin Kimiyya da Fasaha dokar Kwalejin Kimiyya da Fasaha Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kaduna

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamnatin Kaduna Ta Amince Da Hutun Wata 6 Ga Mata Masu Shayarwa

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamnatin Kaduna Ta Amince Da Hutun Wata 6 Ga Mata Masu Shayarwa
  • ‘Yansanda Sun Kama Mutane 302, Sun Ceto Mutum 50 Da Aka Sace A Katsina
  • UEFA Ta Ci Tarar Lamine Yamal Da Lewandowski Kan Karya Dokar Shan Ƙwayar Ƙara Kuzari
  • PDP ta gargaɗi ’ya’yanta kan goyon bayan Tinubu a zaɓen 2027
  • Axios: Majalisar ministocin Isra’ila ta amince da sabon shiri na mamaye birnin Gaza
  • Majalisar Kaduna Ta Amince da Dokokin Yawon Buɗe Ido da Zartar da Shari’a
  • Majalisar Jigawa Ta Yi Karatu Na Biyu Kan Dokar Fansho Ga Tsofaffin Shugabanni
  • Gwamnatin Kwara Ta Horar Da Manoma Sama Da 500 Tare Da Basu Tallafi
  • An kama bama-baman da aka boye a cikin kayan gwangwan a Kaduna
  • Tinubu Ya Umurci A Bada Kulawar Lafiya Kyauta Ga Tsofaffin Ma’aikata Masu Karamin Fansho