2025-05-05@21:50:42 GMT
إجمالي نتائج البحث: 11
«tarayyar turai»:
Jami’ar siyasar waje ta tarayyar turai Kaja Kallas ta bayyana cikakken goyon baya ga warware batun makamashin Nukiliyar Iran ta hanyar diplomasiyya. Jami’ar ta wallafa a shafinta na X cewa: Na tattauna da ministan harkokin wajen Iran Abbas Arakci domin tabbatar da goyon bayan kungiyar tarayyar turai akan aiki da hanyar diplomasiyya domin warware batun Nukiliyar Iran da kuma rage rikice-rikice a cikin wannan yankin.” Haka nan kuma Kallas ta jaddada abinda a baya tarayyar turai din ta rika riyawa da ba shi da tushe na cewa, Iran tana bai wa Rasha taimakon soja tana mai cewa: ” Na kuma yi kira ga Iran da ta dakatar da bai wa Rasha taimakon soja.” Iran dai ta sha yin watsi da...
Kasashen kungiyar Tarayyar Turai sun amince da cewa kungiyar za ta kaddamar da matakan yaki da harajin da shugaban Amurka Donald Trump ya dora mata. Kungiyar mai kasashe mambobi 27 tana fuskantar kashi 25% na harajin shigo da kayayyaki kan karafa, aluminium, da motoci, da kuma karin harajin kashi 20% akan kusan duk wasu kayayyaki karkashin manufofin Trump. Domin mayar da martani, Tarayyar Turai za ta aiwatar da ayyuka, galibi an saita su a kashi 25%, kan nau’oin kayayyakin da ake shigo da su daga Amurka, wanda zai fara daga ranar Talata mai zuwa a matsayin martani na musamman ga harajin karafa na Amurka. Kungiyar har yanzu tana kimanta tsarinta na magance tasirin karin haraji. Kayayyakin na Amurka da tsarin...

Tarayyar Turai Ta Yi Maraba Da Tattaunawa Tsakanin IRAN da Amurka Kan Shirinta Na Makamashin Nukliya
Kungiyar tarayyar Turai ta yi maraba da tattaunawa tsakanin Amurka da JMI dangane da shirinta na makamashin Nukliya, tare da kara jaddada cewa hanyar diblomasiyya kadai ta rage don warware wannan matsalar. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa a halin yanzu dai kungiyar tarayyar ta Turai ta na ci gaba da takurawa JMI da takunkuman tattalin arziki, masu tsanani, a lokaci guda tana fadar cewa hanyar Diblomasiyya ce kadai ta rage wajen warware matsalar shirin makamashin nukliya na kasar Iran, wanda ya tabbatar da fuska biyu na kasashen na Turai. Labarin ya kara da cewa, wani mai magana da yawun kungiyar ta EU wanda kuma baya son a bayyana sunansa, ya fadawa kamfanin dillancin labaran IRNA...
An kori jakadan Isra’ila a Habasha Avraham Neguise daga taron kungiyar Tarayyar Afirka da aka gudanar a wannan Talata a Addis Ababa domin tunawa da kisan kiyashin da aka yi a Rwanda. An fitar da Neguise daga dakin taro na Mandela da ke hedikwatar Tarayyar Afirka bayan da kasashe da dama suka nuna rashin amincewarsu da halartarsa a taron shekara-shekara kan kisan kiyashin da aka yi a kasar Rwanda. Jakadan na Isra’ila ya shiga wurin taron ne ba zato ba tsammani, ba tare da an gayyace shi ba, a cewar majiyoyin diflomasiyyar da suka halarci taron. Majiyar ta kara da cewa tawagogin kasashen Afirka da dama sun nuna rashin amincewa da zuwansa, lamarin da ya sa aka dakatar da taron...
Jami’ar kula da manufofin ketare ta Tarayyar Turai, Kaya Kalas, ta tabbatar da cewa, EU za ta iya sake kakaba takunkumi kan kasar Syria, idan aka samu tabarbarewar lamurra, tana mai nuni da yadda ake cin zarafin fararen hula a gabar tekun Syria. Kaya Kalas ta shaidawa kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya cewa, “Muna shirye-shiryen mayar da takunkumi kan Syria, idan muka ga tabarbarewar lamurra na ci gaba, inda ta jaddada cewa, dole ne mika mulki ya kasance cikin lumana da kuma hadin kai, kuma dole ne a kare fararen hula a kowane hali.” Ta bukaci dukkan masu ruwa da tsaki na waje da su mutunta hadin kan Syria, da kuma iko da iyakokinta.”

Shuwagabannin Kasashen Kungiyar tarayyar Turai Sun Bukaci Karin Kudade A Bangaren Tsaro A Rigimarsu Da Amurka
Shuwagabannin kasashen Turai, sun amince da kara kudade mai yawa a bnaren tsaro da kuma tallafawa kasar Ukraine, a yakin da take yi da kasar Rasha, saboda janyewar Amurka dukkan taimakon da take bawa kasar ta Ukraine. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto majiyar taron shuwagabannin kasashen na Turai, sun zuba kudade dalar Amurka biliyon $860 (Euro 800bn) don karfafa kasashen Turai da kuma Ukrania. Shugaban kungiyar ta EU Ursula von de Leyen yace a karon farko tsaron kasashen yake komawa kansu bayan da Amurka ta dauki nauyin hakan tun bayan yakin duniya na II. A halin yanzu gwamnatin kasar Amurka tace ba zata ci gaba da kashewa wadannan kashe kudade don tsarunsu ta kungiyar tsaro ta...
Kungiyar Hamas ta jinjinawa kungiyar tarayyar Afrika ta AU kan yin Allah wadai da kisan kiyashin da Isra’ila ke yi a Gaza bayan da kungiyar ta soki Isra’ila da keta dokokin kasa da kasa a jawabin rufe taron da ta yi na kwanaki biyu a Addis Ababa. Hamas ta ce tana matukar godiya da matsayin da kasashen Afirka suka dauka a kan Isra’ila da “mummunan” ayyukanta a Gaza. A cikin sanarwar da ta fitar, kungiyar ta AU ta ce tana adawa da keta dokokin kasa da kasa da kuma “kai hari kan fararen hula da kayayyakin more rayuwa da Isra’ila ke yi”. Kungiyar dai ta yi Allah Wadai da duk wani Shirin tilastawa Falasdinawa gudun hijira daga muhallinsu Batun neman...
Kungiyar Tarayyar Afirka ta yi Allah Wadai da duk wani Shirin tilastawa Falasdinawa gudun hijira daga muhallinsu Batun neman tilastawa Falasdinawa gudun hijira daga kasarsu ta gado yana ci gaba da fuskantar tofin Allah da Allah wadai a duk fadin duniya da kuma a taruka daban-daban, kuma batun Falasdinu shi ne kan gaba a ajandar taron kolin Afirka karo na 38 da aka yi a birnin Addis Ababa fadar mulkin kasar Habasha. A yayin bude zaman taron kolin kungiyar tarayyar Afirka, shugaban hukumar Tarayyar Afirka, Moussa Faki, ya yi gargadi game da kiraye-kirayen da ake yi na tilastawa Faladinawa gudun hijira, yana mai jaddada cewa ci gaba da tauye wa Falasdinawa ‘yancinsu abin kunya ne ga bil’Adama, yana mai sukar...
Kungiyar Tarayyar Turai EU ta yaba wa ƙoƙarin Gwamna Babagana Umara Zulum wajen farfado da harkokin rayuwar al’ummar Jihar Borno bayan tashe-tashen hankulan ’yan ta’adda da jihar ta yi fama da shi. EU ta buga misali da cibiyar koyar da sana’o’i ta Muna da ke horar da matasa musamman waɗanda rikicin Boko Haram ya shafa na tsawon fiye da shekaru goma. Ya je Maiduguri daga Legas a kan keke Rikicin rusau ya yi ajalin mutum 4 a Kano Shugaban tawagar Tarayyar Turai a Borno, Ambasada Gautier Mignot ne ya yi wannan yabon a Maiduguri a lokacin da yake zantawa da manema labarai a cibiyar koyar da sana’o’i ta Muna. Ambasada Mignot ya ce tawagarsa ta yi matuƙar farin ciki da...

Majalisar Dokokin Tarayyar Turai Ta Amince Da Bukatar Kawo Karshen Rikicin Jin Kai Cikin Gaggawa A Gaza
Majalisar Dokokin Tarayyar Turai ta yi kira da a kawo karshen rikicin jin kai na Gaza cikin gaggawa Majalisar dokokin Tarayyar Turai ta amince da wata shawara a jiya Larabar da ta aka gabatar da ta bukaci kawo karshen rikicin jin kai na yara, mata da fursunoni a Zirin Gaza, sakamakon kisan kare dangi da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta yi a yankin sama da watanni 15. Cibiyar yada labarai ta Falasdinu ta watsa rahoton cewa: An tattauna shawarwarin da suka yi kira da a kawo karshen rikicin jin kai da ya shafi yara, mata da fursunoni a Gaza, a babban taron Majalisar Dokokin Tarayyar Turai. A kuri’ar da aka kada, an amince da kudurin da rinjayen kuri’u 90, inda...