Shugaban Putin Ya Gana Da Sisi Don Karfafa Harkokin Kasuwanci Tsakanin Kasashen Biyu
Published: 11th, May 2025 GMT
Shugaban kasar Rasha Vladimir Puttin Ya gana da tokwaransa na kasar Masar Abdul alfattah Asisi bayan halattar bikin cika shekaru 80 da nasarar da kasar Rasah ta samu kan sojojin Nazi a yakin duniya na biyu wanda aka gudanar a birnin Mosco.
Shafin yanar gizo na labarai ya bayyana cewa harkokin kasuwanci a tsakanin kasashen biyu tana bunkasa inda a shekarar da ta gabata ya kai dalar Amurka biliyon $9.
Har’ila yau kowa ya san yadda kasar Masar ta zama sansanin sojojin kasar Rasha a lokacin yakin duniya na biyu. Da kuma yadda kasar ta taimakawa kasar Rasha a yakin da ta fafata da sojojin Nazi na kasar Jamus.
Har’ila yau shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya godewa shugaban kasar Brazil Lula de Silva a kan ziyarar da ya kawo kasar Rasha, ya kuma kara da cewa danganta tsakanin kasashen biyu yana kara karfi a hankali a hankalai.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: kasar Rasha
এছাড়াও পড়ুন:
Shugaban Kasar Iran Ya Ce Kungiyar ECO Ta Yi Tir Da Hare-Haren HKI Kan Kasarsa
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiya ya bayyana cewa dukkan kasashe mambobia a kungiyar ECO ta raya tattalin arziki na kasashen yankin sun yi tir da HKI a taron kungiyar wanda aka gudanar a birnin Khankendi. Na kasar Azerbaijan. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto shugaban yana fadar haka bayan tawowarsa daga taron a daren jumma’a a kuma shafinsa na X. Shugaban ya kuma kara da cewa Tehran a shirye take ta hada kai da wadannan kasashe makobta don taimakawwa juna a dukkan bangarorin rayuwa wadanda suka hada da kyautata tattalin arzikin yankin da al-adu da sauransu.
Shugaban ya bayyana cewa yana godiya ga dukkan kasashen kungiyar ECO da kuma sauran kasashen yankin da sauran kasashen duniya wadanda suka nuna goyon bayansu ga kasarsa bayan yakin kwanaki 12 da HKI da kuma Amurka.
Daga karshe yace yana fatan kasar da sauran kasashen kungiyar ECO zasu kai ga gurunsu na bunkasar tattalin arziki ta shekara ta 2035.
A ranar jumma’a 13 ga watan Yuni ne jiragen yakin HKI suka kai hare-hare a kan Iran inda suka kashe manya-manyan jami’an sojojin kasar da masana fasahar Nukliya da kuma fararen hula wadanda basu san hawa ko sauka ba. Sannan Amurka ta kai hare-hare kan cibiyoyin makamashin nukliya na kasar da suke fordo Natanz da kuma Esfahan.