Xi Da Putin Sun Gana Da Manema Labarai Tare
Published: 9th, May 2025 GMT
A yau, shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na Rasha Vladimir Putin sun gana tare da manema labarai bayan tattaunawa a fadar Kremlin dake birnin Moscow. Inda Xi ya jaddada cewa, a yayin da yanayin kasa da kasa ke fuskantar sauye-sauye da hargitsi, kamata ya yi kasashen Sin da Rasha su yi riko da ruhin kyakkyawar makwaftaka kuma na dindindin, da hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare daga dukkan fannoni, da hadin gwiwar samun moriyar juna da nasara tare, da habaka girma, fadi da juriyar dangantakar Sin da Rasha daga dukkan fannoni, da sanya karin kwanciyar hankali ga zaman lafiya da tsaro a duniya, da samar da kuzari ga ci gaban duniya da wadata.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Batun Ceto Wanda Ake Zargi Da Kwaya: Kwamishinan Kano Ya Yi Murabus
Kwamishinan Sufuri na Jihar Kano, Alhaji Ibrahim Ali Namadi, ya ajiye aikinsa bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf ya karɓi rahoton kwamitin bincike da ke duba rawar da ya taka a batun ceto wani da ake zargi da safarar miyagun kwayoyi, Sulaiman Aminu Danwawu.
Wannan matakin na murabus ana kallonsa a matsayin wani muhimmin cigaba da ke nuna jajircewar gwamnatin jihar wajen kare gaskiya, bayyana ta da kuma ɗaukar nauyin ayyukanta a bainar jama’a.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, Kwamishinan ya bayyana cewa ya yanke shawarar murabus ne duba da muhimmancin al’amuran da suka shafi jama’a da kuma halin da ake ciki.
Ya ce: “A matsayina na ɗaya daga cikin masu fada-a-ji a wannan gwamnati da ke yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi, ya dace na ɗauki wannan mataki, koda kuwa zai sosa zukata.
“Ko da yake ina ci gaba da musanta hannuna a lamarin, ba zan iya watsi da irin yadda jama’a ke kallon batun ba, da kuma bukatar kare ƙimar gwamnati da muka ginata tare.” In ji shi.
Alhaji Namadi ya nuna godiya ta musamman ga Gwamna Abba Kabir Yusuf saboda ba shi damar yi wa jiharsa hidima, tare da jaddada aniyarsa ta ci gaba da bin manufofin gwamnatin.
Ya ƙara da cewa: “A matsayina na ɗan ƙasa nagari, dole ne in ci gaba da kare amana da hangen nesan da muka haɗa kai wajen shimfiɗawa a jiharmu. Zan ci gaba da kasancewa mai biyayya ga akidun da suka kawo wannan gwamnati kan mulki.”
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya karɓi murabus ɗin cikin farin ciki, tare da yi masa fatan alheri a duk wani yunƙurinsa na gaba.
Gwamnan ya sake jaddada kudirin gwamnatinsa wajen tabbatar da adalci, ladabi, da kuma yaki da miyagun dabi’u da laifukan da suka shafi kwayoyi da sauran matsalolin da ke shafan matasa da al’umma baki ɗaya.
Ya kuma ja hankalin duk masu rike da mukaman siyasa da su kasance masu hikima da taka-tsantsan wajen hulɗa da al’amuran jama’a, tare da neman izini daga hukumomi mafi girma kafin su shiga cikin wani lamari da ke da tasiri a bainar jama’a.
Abdullahi Jalaluddeen