Muna bayan Tinubu a Zaɓen 2027 — Patience Jonathan
Published: 11th, May 2025 GMT
Uwargidan tsohon Shugaban Najeriya Dame Patience Jonathan, ta bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu za ta marawa baya a Zaɓen 2027.
Patience ta nanata cewa ba ta da burin komawa fadar shugaban ƙasa, amma ta ce a shirye take ta taimakawa uwargidan shugaban ƙasa na yanzu, Sanata Oluremi Tinubu wajen yaƙin zaɓen 2027.
Aminiya ta ruwaito Patience na bayyana haka ne a lokacin da take kiran sunan manyan baƙi ciki har da ’yar shugaban ƙasar, Folashade Tinubu-Ojo a wajen taron da aka karrama ta a matsayin jagora ta gari, wanda kamfanin Accolade Dynamics Limited ya shirya ranar Asabar a Abuja.
Ta ce, “ita ya kamata in fara kira amma sai na bari zuwa ƙarshe wato ’yar shugaban ƙasarmu wanda muka aminta da shi wato Shugaba Bola Tinubu.
“Iyajola ina miki godiya bisa yadda kike ƙarfafa gwiwar mata. Muna tare da ke a wannan aikin kuma za mu mara miki baya.
“Ina da yawan magana, idan ba na son abu ana ganewa, amma idan ina tare da abu, zan iya mutuwa a kansa.
“Kowa da lokacinsa a mulki, kuma idan lokacin mutum ne, ina goya masa baya ne.”
Ta ƙara da cewa a lokacin da suke mulki, Uwargidan shugaban ƙasa Oluremi Tinubu ta goya mata baya.
“Ina da hankali, don haka dole ne in mayar da biki. Na faɗa mata cewa zan taya ta yaƙin zaɓe, ba zan juya mata baya ba. Ni ba na sha’awar komawa fadar shugaban.”
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Zaɓen 2027
এছাড়াও পড়ুন:
Rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi ta bar babban gibi a Najeriya – Tinubu
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana kaduwa da rasuwar fitaccen malamin addinin Musulunci kuma jagoran Tijjaniyya, Sheikh Dahiru Usman Bauchi.
Fitaccen malamin ya rasu a Bauchi ranar Alhamis yana da shekaru 101.
Abubuwa 20 da ya kamata ku sani game da Sheikh Dahiru Bauchi Ɗan bindiga ya harbe sojoji 2 a fadar shugaban AmurkaA cikin wata sanarwa da Kakakin shugaban, Bayo Onanuga, ya fitar, Tinubu ya bayyana Sheikh Dahiru Bauchi a matsayin jagoran da ya sadaukar da rayuwarsa wajen koyarwa, wa’azi da jagorantar al’ummar Musulmi.
Tinubu ya ce rasuwar malamin ba wai asara ce ga iyalansa da almajiransa kawai ba, har ma ga ƙasa baki ɗaya.
“Sheikh Dahiru Bauchi malami ne, uba ne kuma murya ce ta daidaito da hikima. A matsayinsa na mai wa’azi kuma babban mai fassarar Alƙur’ani mai tsarki, ya kasance mai kira ga zaman lafiya da tsoron Allah. Rasuwarsa ta bar babban gibi,” in ji Shugaban Ƙasa.
Ya tuna da albarka da ya samu daga marigayin a lokacin shirye-shiryen zaɓen 2023.
Shugaban Ƙasa ya miƙa ta’aziyya ga almajiran malamin a faɗin Najeriya da wajen ƙasar, yana mai kira da su dawwamar da sunansa ta hanyar bin koyarwarsa ta zaman lafiya, tsoron Allah da kyautatawa ɗan adam.