Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp.

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Ta’aziyyar Rasuwar Jarumin Kannywood, Malam Nata’ala

 

Sunana Abdulhamid Ado (Danbayaro):

Inna lillahi wa inna ilaihirraju’un. Na ji ba dadi na ji komai sai da ya tsaya min har tsahon lokaci, abun ba zai musaltuba, sai dai kawai mu ce Allah ya ji kan Mal. Nata’ala. Mutum ne mai barkwanci, ga zumunci na gaske, ba a yin gulma da shi, baya boye wa mutum gaskiya, kuma baya cin hakkin mutum, kuma abun hannusa baya rufe masa ido. Kuma indai ya samu abun duniya ko baka sani ba sai ya kira ka an ci da kai, harkar sa ba bakin ciki yana da hali mai kyan gaske. Wata rigar san yi da ya kawo mana ‘location’ ya raba mana dukkan ‘crew’ sai da ya bamu, ina ganin rigar yake fado min tun da ya fara jinya har zuwa yanzun nan da kuma sauran abun alkairai da yayi mana muna tare. Mun yi rashi matuka da gaske, Allah yayi masa rahama, Allah ya kula da bayan sa.

 

Sunana Sarah Aloysius (Edecutibe Producer, Dadin Kowa):

Gaskiya Mun yi babban rashi, ba Dadin kowa kadai ba, Kannywood bakidaya. Malam Nata’ala yana daya daga cikin jigajigan jaruman da masana’antar kannywood ta dogara dasu da fuskar rike aikinsu da muhimmanci. Yana da hakuri da juriya wajen aiki, yana da girmama mutane komai girma ko kankantar mutum, yana da kyauta, abun hannunsa baya rufe masa ido. Malam Nata’ala yana da rike alkawari sosai, ga kyakkawar mu’amala da mutane da kuma barkwanci. Akwai wani lokaci da muka samu matsalar ‘schedule’ na aikin shirin Dadin Kowa, muka kira shi cikin dare cewa, za mu yi aiki da shi washegari, a lokacin bai ma fada mana baya kasar ba, amma haka muka tarar da shi washegari a ‘location’. Haka kuma a lokuta da dama, sai ka ganshi ya zo ‘location’ da kayan tsaraba ya rabawa ‘crew members’. Kawai sai dai muce Allah yayi masa rahma, ya haskaka kabarinsa.

 

Sunana Fati Al’amin wacce aka fi sani da Maman Badaru:

Inna lillahi wa inna ilaihirraji’un, wallahi na girgiza da jin rasuwar Malam Nata’ala sosai. Hakika mun yi babban rashin mutumin kirki wanda abin duniya bai rufe masa ido ba. A duk lokacin da muka fita wajan wani aiki ko wata gaiyata da aka yi mana wallahi shi ne yake shugabantar tafiyar. Amma abin da zai baki sha’awa da rayuwarsa duk wani alkhairi da aka samo to, fa baya bari a wajansa. Ni yake bawa ya ce, na ajjiye har sai mungama samun abin da aka bamu, sannan ya ce Fati na yarda da amanarki ki raba ki bawa kowa hakkinsa [Kuka]. Ni kuma sai na raba na bawa kowa, sannan na fitar masa da na sa dan shi ne ya kawo harkar. Wani lokacin har nakan yi bakin jini a wajan wasu su ce na cika masa, ni kuma sai na ce da bai kawo aikin ba fa?. Allah ya ji kansa da rahma ya sa aljanna makomar sa. Wallahi ina tuna shi ta son kawo wa al’umma alkhairi, ba tare da bakin ciki ba, ga son ciyarwa ga al’umma, Allah yayi masa rahma.

 

Sunana Alh. Dauda Adakawa, wanda aka fi sani da Malam Barau na Dadin Kowa:

Rasuwar malam Nata’ala ta girgiza ni da kyau, kasancewar ni ne kamar sa’ansa kuma aboki wanda ko harkar rashin lafiyarsa, da ni muke yawan magana da yan’uwansa, musamman Sadi Potiskum. Malam yana da karamci, jin kai, da son abokan aikin sa, sannan mai son kowa ya samu alkhairi ne. Gaskiya akwai abubuwan da za mu kare rayuwar mu muna tuna Malam Nata’ala da shi, kamar; Kyauta, gaskiya, da son jama’a.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Nishadi Babban Burina Zama Fitacciyar Jaruma A Duniya —Aisha Umar November 1, 2025 Manyan Labarai Gwarzon Mawaƙin Shekarar 2025, Skales October 25, 2025 Nishadi Neman Kudi Ne Ya Kawo Ni Masana’antar Kannywood Ba Fadakarwa Ba – Khadija Muhammad  October 11, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kasashen Afirka Bakwai Da Sojojin Amurka Suka Shiga
  • Ta’aziyyar Rasuwar Jarumin Kannywood, Malam Nata’ala
  • Matsalar Tsaro: Mun samu gagarumin ci gaba a shekaru biyu – Tinubu
  • Matsalar Tsaro: Mun sami gagarumin ci gaba a shekaru biyu – Tinubu
  • GORON JUMA’A
  • Shugaban Najeriya Bola Tinubu Ya yi Alwashin Kawo Karshen Ta’addanci A Kasar
  • Ta’addanci Ba Zai Yi Nasara Ba A Ƙasarmu — Tinubu
  • Ɓarayi Sun Shiga Ofishin Shugaban Karama Hukuma A Kano, Sun Tafka Sata
  • Gwamnatin Tarayya ta fara shirin sayar da matatun manta ga ’yan kasuwa
  • Hafsan sojin sama ya umarci a yawaita yi wa ’yan ta’adda ruwan bama-bamai