Kasashen duniya sun damu da rikici tsakanin Indiya da Pakistan
Published: 7th, May 2025 GMT
Kasashen duniya na ci gaba da nuna matukar damuwa game da rikicin da ya barke tsakanin Pakistan da Indiya.
Iran na daga cikn jerin kasashen da a baya bayan nan suka nuna damuwa.
Sanarwar da ma’aikatar harkokin wajen Iran ta fitar ta ce “Jamhuriyar Musulunci ta bayyana matukar damuwarta kan yadda takun saka tsakanin Indiya da Pakistan ke ci gaba da ruruwa.
Iran ta ce a matsayinta na kasa mai iyaka da Pakistan wacce kuma ke da kyakkyawar alaka da Indiya, ta yi tayin shiga tsakani a rikicin tun cikin watan Maris.
Kasar Turkiyya ma ta yi gargadin game da rikicin.
Inda a wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen kasar ta fitar ta yi Allah wadai da hare-haren da ake kai wa fararen hula da kayayyakin more rayuwa.
A nata bangaren gwamnatin Jamus ta yi kira da a dakile duk wani tashin hankali da kuma kare fararen hula.
Moscow ta yi kira ga kasashen Indiya da Pakistan da su yi taka-tsan-tsan.
Inda ta bukaci bangarorin da su yi taka-tsantsan don kaucewa tabarbarewar lamarin.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Kotun Duniya Ta Wanke HDL Akan Zargin Kisan Kiyashi A Sudan
Kotun duniya ta yi watsi da karar da Sudan ta kai Hadaddiyar Daular Larabawa tana mai zarginta da hannu a kisan kiyashin da aka yi wa al’ummar wannan kasa.
A yau Litinin ne kotun duniyar ta yi watsi da karar ta Sudan, tana mai wanke Hadaddiyar Daular Larabawa.
Ita dai Sudan ta zargi Hadaddiyar Daular Larabawar da cewa ta hada baki da dakarun kai daukin gaggaawa wajen yi wa mutanen yankin Darfur kisan kiyashi.
A nata gefen Hadaddiyar Daular Larabawan ta ki amincewa da tuhumar da Sudan ta yi mata tana mai siffata ta da cewa; Farfaganda ce, kuma Sudan din ta yi hakan ne domin kawar da hankulan duniya daga kan laifukan da sojoji suke aikatawa.