A cewar sa, wannan bita tana da nufin tantance yadda aka samu cigaba a aiki, da kuma tabbatar da cewa hukumomin da ke ƙarƙashin ma’aikatar suna tafiya daidai da abin da aka ɗora masu a matsayin nauyi.

 

Ya ce: “Muna nan ne don sauraron shugabannin hukumomi domin mu ga yadda suka aiwatar da muhimman abubuwan da muka rattaba hannu a kai.

Idan akwai ƙalubale, za mu tattauna su. Idan akwai cikas, za mu duba abin da za mu iya yi domin shawo kansu.”

 

Ministan ya bayyana wannan taro a matsayin hanyar tantance kai kafin a kai tsakiyar wa’adin gwamnatin yanzu.

 

Ya ce: “Ku tuna cewa wannan gwamnati ta fara aiki kusan shekaru biyu da suka gabata. Cikin ƙasa da wata guda daga yanzu, wannan gwamnati za ta kai rabin wa’adin ta a ranar 29 ga Mayu.

 

“Saboda haka, lokaci ya yi – kamar yadda Ofishin Shugaban Ƙasa ya nema – da kowace ma’aikata za ta fidda sakamakon aikin ta kan abubuwan da ta tsara kuma aka amince da su ta hannun ofishin CDCU da ke Ofishin Shugaban Ƙasa.”

 

Idris ya kuma jaddada cewa ma’aikatar sa na jajircewa wajen samar wa ‘yan Nijeriya da sahihan bayanai game da nasarorin gwamnati da kuma ƙalubalen da take fuskanta.

 

Ya ce: “Abin da wannan ma’aikatar ke yi shi ne tabbatar da cewa ba wai kawai muna wayar da kan ‘yan Nijeriya kan abubuwan da ke cikin hangen nesa na Shugaban Ƙasa ba, har ma muna bayyana ƙalubalen da ke akwai cikin gaskiya da riƙon amana? Tabbas, wannan ne abin da muka ɗauka tun farko kuma za mu ci gaba da bin wannan hanya.”

 

Ya ƙara da cewa babban aikin ma’aikatar shi ne tsarawa da aiwatar da dabarun sadarwa masu ma’ana domin inganta gaskiya da rarraba bayanai game da manufofi da shirye-shiryen gwamnati, yaƙi da yaɗa ƙarya, da kuma ƙarfafa wayar da kan ‘yan ƙasa bisa fifikon gwamnatin Tinubu.

 

Taron ya samu halartar shugabannin hukumomi kamar haka: Darakta Janar na Hukumar Talabijin ta Nijeriya (NTA), Kwamared Abdulhamid Dembos; Darakta Janar na Hukumar Rediyon Tarayyar Nijeriya (FRCN), Dakta Mohammed Bulama; Darakta Janar na Hukumar Wayar da Kai ta Ƙasa (NOA), Mista Lanre Issa Onilu; Darakta Janar na Hukumar Kula da Gidajen Rediyo da Talbijin ta Ƙasa (NBC), Mista Charles Ebuebu; Darakta Janar na Muryar Nijeriya (VON), Malam Jibrin Baba Ndace; Darakta Janar na Hukumar Kula da Tallace-tallace (ARCON), Dakta Olalekan Fadolapo; da Manajan Darakta na Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN), Malam Ali M. Ali.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Darakta Janar na Hukumar

এছাড়াও পড়ুন:

Ka-ce-na-cen da ya biyo bayan ziyarar Tinubu a Katsina

Gwamnan Jihar Katsina Umaru Dikko Raɗɗa, ya ce ba shi da masaniyar wani allo da aka kafa mai ɗauke da saƙon ce wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu babu ƙorafi a Katsina ba kamar yadda ake ta muhawara a kai a ƙasar.

Hakan na ƙunshe cikin wani saƙon murya ta gwamnan da aka fitar da ke martani a kan ce-ce-ku-cen da ya kaure a Nijeriya kan wani allon saƙo da aka kakkafa a Katsina lokacin da Shugaba Tinubu ya halarci auren ‘yar gwamnan.

DAGA LARABA: Ɓoyayyun Dalilan Da ke Sa Faɗuwa Jarabawa A Najeriya Yaƙi ya ɓarke tsakanin Indiya da Pakistan

Gwamna Raɗɗa ya ce yana da kyau a riƙa bincike kafin yanke hukunci kan abubuwa.

“Na saurari muryar da aka turo aka ce daga Alhaji Garba Dangida ne da kuma Janar Tsiga, kuma na yi godiya sosai da wannan voice da na ji, kuma ina fatan Allah Ya saka musu da alheri.

“Amma abin da nake so na ce shi ne ya kamata a riƙa bincike idan an ji labari a soshiyal midiya ko a zahiri kuma a riƙa tambaya,” in ji gwamnan.

Lamarin dai ya jawo zazzafar muhawara da ce-ce-ku-ce daga ko ina a faɗin Nijeriya, inda masu sharhi ke cewa jihar da ke fama da ƙalubalen tsaro bai kamata ta nuna wa Shugaban Ƙasa cewa ba ta da wani ƙorafi ba.

Sai dai Gwamna Raɗɗa ya ce sun tattauna matsaloli uku da ke damun Jihar Katsina da Shugaban Ƙasar da suka haɗa da matsalar rashin tsaro da aikin samar da lantarki daga iska na Rimi da ayyukan filin jiragen sama da aka tsaida.

“Maganar hanyoyi kuwa da kansa (Shugaban Ƙasa) dama ya yi kuma hanyoyin an ba da aikinsu kuma mun shaida wa Shugaban Ƙasa wannan.

Amma a kan batun allon talla da aka rubuta Katsina babu ƙorafi gwamnan ya ce “Maganar billboard da wani ya buga na cewa ‘Katsina Ba Ƙorafi’ ni a matsayina na gwamna ban ma san an buga shi ba sai da na gani a soshiyal midiya nake tunanin yaya aka buga shi, wa ya buga shi.”

Raɗɗa ya koka cewa kuskure ne idan aka dinga jam’i ana zargin mutane a kan abin da a zahirance sun tabbatar ba su yi ba.

“Amma ku manyanmu ne iyayenmu ne idan kun ga wani abu na kuskure kuna iya mana magana muna iya gyarawa, mu kuma mutane ne muma kamar kowa muna iya yin kuskure muna iya yin ba daidai ba.

“Amma dai don Allah a matsayin manya da iyaye idan kun ji abu a soshiyal midiya ku dinga kiranmu ku ji yaya abin ya kasance ba wai a tafi soshiyal midiya a dinga irin wadannan maganganun ba.

“Ina ga ba za su taimake mu ko kawo mana ci gaban da muke buƙata ba a Katsina,” a cewar gwamnan.

A ƙarshen saƙon muryar na ranar Talata mai tsawon minti 2.48, Raɗɗa ya ce “shugabancin nan idan Allah Ya ba ka shi kowa na iya kuskure yana iya daidai.

“Muna fatan Allah ya dora mu bisa daidan. Amma dai a wannan labarin da aka ba da ba haka yake ba.

Ka-ce-na-cen da ya biyo baya

Gwamna Raɗɗa ya fitar da wannan jawabin ne bayan ka-ce-na-cen da ya kaure game da ziyarar kwana biyu ta Shugaba Tinubu a Katsina, ɗaya daga jihohin Arewa maso Yamma da ke cikin masifar rikicin ‘yan fashin daji.

Ka-ce-na-ce ya ɓarke ne har a shafukan sada zumunta tun lokacin da aka fara ganin wasu manyan allunan da aka kakkafa ɗauke da saƙon ‘Katsina Ba Ƙorafi’, a yayin ziyarar Tinubu.

Saƙon “Katsina Ba Ƙorafi” ga alama ya jefa ɗimbin mutane cikin mamaki, inda suke neman sanin hikimar nuna wa Tinubu cewa jihar ba ta da wani ƙorafi.

Mutane masu yawa ba kawai a Katsina ba, har ma a Arewacin Najeriya na ganin ziyarar wata gagarumar dama ce ta yi wa Tinubu gamsasshen bayani kan matsalolin tsaro da na tattalin arziƙi da suka fi addabar jihar.

Da dama a yanzu na cike da wasu-wasi. Suna tunanin ko saƙon “Katsina Ba Ƙorafi” ne ainihin jawaban da manyan ’yan siyasar jihar suka yi wa Tinubu a tsawon kwana biyu da ya kwashe a can.

Yayin da wasu ke kallon saƙon a matsayin tumasanci, ba-ni-na-iya da bambaɗancin ’yan siyasa da ke son burge Tinubu, duk da al’ummominsu na ci gaba da shan azabar tsananin talauci da yunwa da kuma hare-haren ’yan fashin daji.

BBC ya ruwaito yadda mutane da yawa sun yi ta bayyana ra’ayoyi mabambanta a shafukan sada zumunta game da batun.

Wani Abdullahi Mansir Gafai ya yi tambaya a shafinsa na Facebook cikin Ingilishi cike da kaɗuwa cewa ‘Katsina Ba Ƙorafi?’.

“Wane irin cin fuska ne wannan. Wannan wata zolayar rashin kunya ce ga mutanen da ke kwarma ihu a zuci da kuma a sarari yayin da suke dulmiya cikin tsoro da yunwa da kuma ƙaƙa-ni-ka-yin rayuwa.

“Don a sani, ban da masifar hare-haren ’yan fashin daji, Katsina na ɗaya daga cikin jihohi mafi talauci a Najeriya.”

Ya ƙara da cewa: “Yayin da Shugaba Tinubu ke sharɓar liyafar ƙasaita a Katsina rahotannin ”yan fashi sun auka wa garuruwa a Faskari da Bakori da Dutsin Ma da Ƙanƙara da Ɗan Musa, tuni sun cika gari.

“Wani zai cika da murna kan irin wannan dama wadda ba a cika samu ba da ta faɗo wa Gwamna Raɗɗa don ya zayyana ‘ƙorafe-ƙorafen’ al’ummarsa, amma maimakon haka sai ya zaɓi nuna ƙwambo da wadaƙa.

Haka zalika, wani mai suna Kabiru Garba ya wallafa cewa: “Amma fa wannan wulaƙanci ne na ƙarshe wallahi.

“Da a ce Jagaban (Shugaba Tinubu) yana jin Hausa, kuma ya ga wannan shirmen to tabbas sai ya ce mu wawaye ne ko da a ransa ne.”

Za a kai mu a baro — Dattawan Katsina

Ita dai muryar dattijan da aka ce saboda tsokacinta ne Gwamna Raɗɗa ya mai da martani ta zargin dattijan jihar Katsina da zuba ido kawai, ba tare da yunƙurin taka wa Dikko Raɗɗa burki ba.

Ɗaya daga cikin muryoyin ta nuna takaici kan yadda dattijan suka gaza haɗuwa su fito da matsalolin al’ummar jihar, don tunkarar Tinubu su yi masa jawabi.

“Mutane manya su sadu da shi, su yi masa magana. Ai zai je wajen sarki ko, sarki ma ya yi mishi magana.

“Ya ga cewa duk inda ya isa, ya ga gwamna ya yi mishi magana, elders (dattijai) sun mishi magana, dole ya samu abin da zai yi.”

Ya ƙara da cewa: “Mu akwai abin da yake damun mu irin…. rashin tsaro (insecurity) da talauci mai kassara al’umma?

Ya kuma ce kamata ya yi su iya ƙarfin hali da nuna dattakon da za su tunkari haƙiƙanin matsalolinsu na rayuwa.

Ɗaya muryar ta zargi Gwamna Raɗɗa da “sakarcin” shaida wa Tinubu cewa Katsina ba ta da ƙorafi, inda ya ce kamata ya yi dattijan jihar su kira taron manema labarai domin nisanta kansu da wannan iƙirari.

Ya ce da sun yi haka, gwamnan zai san idanun mutane na kansa, kuma zai shiga taitayinsa.

“Maganar gaskiya, wannan abin damuwa ne. In ba mu tashi ba tsaye, wallahi Katsina za a kai mu a baro mu.”

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An Fara Gabatar Da Shirin “Kalaman Magabata Dake Jan Hankalin Xi Jinping” A Rasha
  • Sharhin bayan Labarai: Mahangar Iran Dangane Da Tattaunawa Kan Shirinta na Makamashin Nukliya Na Zaman lafiya
  • Ka-ce-na-cen da ya biyo bayan ziyarar Tinubu a Katsina
  • Birnin Kudu Za Ta Samar Da Cibiyar Horas Da Maniyata
  • Jigawa Ta Kaddamar Da Kwamitin Likitocin Da Su Duba Lafiyar Mahajjatan Bana A Saudiyya
  • Daukar nauyin dalibai: Rikici ya barke a Hukumar Raya Arewa Maso Yamma
  • Hajj 2025: Maniyyatan Kaduna za su fara tashi ranar 14 ga watan Mayu
  • Sharhin bayan Labarai: Ci Gaban Harkokin Kasuwanci Tsakanin Iran Da Kasashen Waje Duk Tare Da Takunkuman Kasashen Yamma
  • Iran Ta Mayar Da Martani Akan Zarginta Dangane Da Yemen