2025-09-20@15:32:35 GMT
إجمالي نتائج البحث: 9132

«Farfesa Shehu Abdullahi Ma aji»:

    Wasu ’yan bindiga da ake zargin Lakurawa ne, sun kai hari ƙauyen Sayinna, da ke Ƙaramar Hukumar Tangaza a Jihar Sakkwato. Sun kashe Hakimin ƙauyen, Malam Murtala Sa’adu, tare da wani mutum mai suna Ibrahim Mai-Kuɗi. Yadda za ka dawo da kuɗinka da ka yi kuskuren turawa wa wani An tsinci gawar kwamandan hukumar NDLEA...
    Wasu mazauna ƙauyen Zalla Bango a ƙaramar hukumar Sabon Birni, Jihar Sokoto, sun rasa rayukansu a wani haɗarin jirgin ruwa yayin da suke tserewa daga harin ƴan bindiga. Lamarin ya faru ne da yammacin Alhamis, 18 ga Satumba, lokacin da Kwale-Kwalen da ke ɗauke da jama’a yayi karo da dirkar gadar ruwa da ta rushe...
    Daga nan ya wuce gidan tsohon shugaban ƙasa Marigayi Muhammadu Buhari domin yi wa matar sa Aisha da sauran ‘yan uwa ta’aziyya. Tinubu a gidan marigayi tsohon shugaban kasa, Buhari Ya bayyana Buhari a matsayin “shugaba mai kishin ƙasa da sadaukarwa, wanda gudunmawarsa ga haɗin kan Najeriya da ci gabanta ba za a manta da...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Gundumar Bakori ta jihar Katsina ta kaddamar da shirin dashen itatuwa domin rage zaizayar kasa a yankin. A cikin wata sanarwa da shugaban kwamitin aikin gona, Cigarin Bakori Alhaji Shehu Ishiye ya fitar, ya bayyana cewa Hakimin Bakori, Makaman Katsina Alhaji Garba Tukur Idris, ya yi kira ga jama’a da su daina sare itatuwa ba...
    Tashar talabijin din al-mayadin ta bayar da labarin cewa, rundunar kai daukin gaggawar ta kai hari akan masallacin unguwar “Abu Shauk” dake birnin Al-fasha a lokacin sallar asuba. Da safiyar jiya juma’a ne dai mayakan rundunar ta r.s.f su ka kai wa masallacin na Abu Shauka hari a birnin al-fasha da shi ne babban birnin...
    Ministan tsaron kasar Pakitsan Khaje Asif ya fada a jiya Juma’a cewa, makaman Nukiliyar da kasarsa take da su, wani sashe ne na yarjejeniyar tsaro da su ka kulla da kasar Saudiyya. Haka nan kuma ya kara da cewa; Yarjejeniyar ta tsaro ce tsagwaronsa, kuma manufarta ita ce aiki tare a tsakanin kasashen biyu a...
    Kididdigar da aka fitar akan adadin Falasdinawan da su ka yi shahada da kuma jikkata sun haura 230,000,wanda ya faro tun daga watan oktoba 2023. Ma’aikatar kiwon lafiya a Gaza ce ta fitar da wannan kididdigar a jiya Juma’a, sannan kuma ta bayyana cewa an kara samin wani adadi mai yawa na shahidai a cikin...
    Sheikh Na’im Kassima wanda ya gabatar da jawabi a jiya  juma’a ya kuma kara da cewa; A halin yanzu kungiyar gwagwarmaya tana fuskantar matsanancin yanayi mai hatsari,tare da jaddada cewa; Wanzuwar HKI, manufarsa ita ce a samar da wani yanki na turai da Amurka a cikin wannan yankin domin hana al’ummar yankin ci gaba da...
    Duk da cewa, Nijeriya ce kan gaba wajen kiwon dabbobi a nahiyar Afirka, amma har yanzu, mahukunta a ƙasar sun gaza gudanar da wani kyakkyawan tsari da kuma samar da kayan aiki wajen samar da kashin na dabbobi, inda rashin hakan ke ci gaba da haifar da damuwa ga waɗanda ke fannin a faɗin ƙasar....
    Tsarin ya ƙunshi na “ kwas na ƙwarewa kan lamarin koyarwa na gajeren lokaci wanda akan yi wata uku zuwa shida ne,  bayan haka ne waɗanda suka yi kwas ɗin ne za su cancanci yin rajista da hukumar , har su samu Lasin na amincewa da sun cancanta  su yi aikin koyarwa.” Tsarin na ma’aikatar...
    An tsinci gawar Igbonna Uzoma, kwamandan hukumar da ke yaƙi da fataucin miyagun ƙwayoyi (NDLEA) a otel da ke birnin Kalaba, Jihar Kuros Riba, a ranar Juma’a. Rahotanni sun ce Uzoma, wanda aka dawo da shi aiki daga wata jiha zuwa Kuros Riba a kwanan nan, bai daɗe da kama aiki a sabon ofishin ba...
    Ukraine ta ce Rasha ta kai sabbin hare-haren makamai masu linzami da na jirage marasa matuka wasu yankuna da dama na kasar cikin dare. A gabashin birnin Dnipro, an kai hari kan wani gini kuma an ji ƙarar fashewar wasu abubuwa a Zaporizhzhia kusa da tungar da ke zaman iyakar dakarun Rasha da na Ukraine...
    A ci gaba da kokarin da take yi na tsaftace harkar ilimi, wata kotu a Kano ta bayar da umarnin rufe wasu makarantu masu zaman kansu nan da nan, 6 saboda saba ka’idojin jihar da suka hada da kara kudin makaranta da kuma tilasta iyayen yara sayan litattafai na dole da sauran tsarabe-tsarabe da suka...
    An shawarci Musulmi da su yi koyi da kyawawan halaye na tawali’u kamar yadda Annabi Muhammadu ya yi misali da su don yin rayuwa mai inganci.   Babban Limamin Masallacin Darul Khair Imam Abdulmumini Abdulrafiu-Onilaru ya bada nasihar ne a cikin hudubar Juma’a da ya gabatar a garin Ilorin na jihar Kwara.   Ya ce...
    An bukaci gwamnatin jihar Kwara da ta gaggauta shiga tsakani kan rufe kasuwar Kara da ke yankin Kwara ta Kudu da shugaban karamar hukumar ya yi domin ceto harkokin kasuwanci daga durkushewa.   Shugaban kungiyar Miyetti Allah reshen jihar Kwara, Alhaji Shehu Garba ne ya yi wannan roko a wata sanarwa da ya rabawa manema...
    Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya amince da sauya sunan ma’aikatar harkokin mata, yara da nakasassu a hukumance zuwa “Ma’aikatar harkokin mata, yara da masu bukata ta musamman.”   Wannan dabarar yanke shawara, ga kwamishiniyar harkokin mata Ambasada Hajiya Amina Sani Abdullahi, ta nuna irin kwakkwaran kudurin gwamnati na inganta mutunci, hada kai,...
    Ma’aikatar kasafin kudi da tsare-tsare ta jihar Jigawa, ta shirya taron yini daya a birnin tarayya tare da hadin gwiwar ELIP kungiyar farar hula ta musamman, domin tattara kayan aiki na kasafin kudin 2026.   A nasa jawabin kwamishinan kasafin kudi da tsare-tsare na jihar Alhaji Ibrahim Babangida Umar Gantsa ya bayyana mahimmancin taron, inda...
    Kwamitin bincike na Majalisar Dinkin Duniya (MƊD) ya ƙasar samu Isra’ila da laifin aikata kisan ƙare dangi kan Falasɗinawa a zirin Gaza. Wani sabon rahoton kwamitin binciken ya ce akwai ƙwararan hujjoji da za a iya cewa Isra’ila ta aikata huɗu daga cikin nau’ika biyar na kisan ƙare dangi a ƙarƙashin dokokin ƙasa da...
    Da yake magana game da taron, Maiha ya ce sadarwa ita ce jigon ciyar da harkar kiwon dabbobi gaba, “Bayan wannan taron, muna sa ran za ku yi amfani da dabarun ku don ƙara faɗaɗa labarin fannin kiwo. “Muna yaba wa ƴ an jarida bisa aikinku na ƙwarewa da muke sa ran za ku ci...
    Dubban ’yan Nijeriya ne ke zaune a ƙasar Saudiyya ba tare da takardun izinin zama ba, musamman a biranen Makkah da Madina. Rayuwarsu cike take da fargaba da rashin tabbas, a yayin da suke yin ayyukan hannu ko ƙananan sana’o’i ba tare da wata kariya ta doka ba. A yayin aiki Hajjin shekarar nan...
    A ɓangaren al’umma an samu halartar shugaban ƙaramar hukumar Faskari Hon. Surajo Aliyu Daudawa da Ɗan Majalisa dokokin mai wakiltar ƙaramar hukumar Faskari injiniya Sama’ila Mu’azu Bawa. Sauran sun haɗa da Hakimin Faskari da kuma na Mai Ruwa da wakilan al’umma da masu riƙe da masarautar gargajiya da sauran al’umma. Sai kuma ɓangaren ɓarayin daji...
    Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Iran ba ta yarda da duk wani aiki na siyasa ko matsin lamba na rashin adalci ba Rafael Grossi, babban darektan hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA, ya gana da ministan harkokin wajen Iran Seyyed Abbas Araqchi ta wayar tarho. Kamfanin dillancin labaran Tasnim ya bayar...
    Jakadan Iran a Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa: Kwamitin sulhun Majalisar ya rasa damar tattaunawa da fahimtar juna a yau Jakadan kasar Iran kuma wakilin din-din-din a Majalisar Dinkin Duniya Amir Sa’ed Irawani, ya yi tsokaci kan rashin amincewa da daftarin kudiri na ci gaba da dage takunkumin da aka kakabawa Iran a taron...
    Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta jaddada cewa: Iran tana da ‘yancin mayar da martani ga duk wani mataki da ya sabawa doka Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta fitar da wata sanarwa a jiya Juma’a dangane da haramtaccen matakin da kungiyar Tarayyar Turai Troika ta dauka na mayar da takunkumin Majalisar Dinkin Duniya kan Iran...
    Mataimakin ministan harkokin wajen Iran mai kula da harkokin shari’a da na kasa da kasa ya mayar da martani kan zargin shugaban Faransa Emmanuel Macron Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran mai kula da harkokin shari’a da na kasa da kasa, Kazem Gharibabadi, ya musanta zargin da shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya yi a...
    Shugaban kasar Faransa ya jaddada cewa; Zai amince da kafa kasar Falasdinu a ranar Litinin mai zuwa a birnin New York Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya tabbatar a yammacin jiya Juma’a cewa: Zai amince da kafa kasar Falasdinu a ranar Litinin mai zuwa a birnin New York. Macron ya bayyana cewa: Amincewa da kasar...
    Daga baya an ƙara nata wani nauyin kula da Tashoshin Warri, Koko, Burutu da kuma ta Sapele, waɗanda kamfanonin ƴ an kasuwa masu zaman kansu ne, ke tafiyar da su, amma har zuwa yau, mahukunta a NPA ne, ke tafiyar da duk wata ragamar hukumar baki ɗaya. A shekaru da dama da suka gabata, matsaloli...
    Kamfanin man fetur na kasar Sin (CNPC), ya mika wasu kayayyakin agaji ga dubban mutanen da ambaliya ta raba da matsugunansu a jihar Unity mai arzikin man fetur dake arewacin kasar Sudan ta Kudu. Daraktan sashen hulda da jama’a na reshen kamfanin CNPC a Afrika Ren Yongsheng, ya ce gudunmuwar ta kunshi tantuna, da barguna,...
    1- Musayar yawu ta hanyar sumbatar juna- Ma’ana, ta hanyar sumbatar juna a tsakanin ma’aurata, idan guda daga cikinsu na ɗauke da cutar, nan da nan ɗayan shi ma zai kamu da cutar. 2- Gaurayewar jini ko haɗuwar jini- Haɗuwar jini, misali; idan wani ya yi amfani da reza ya yanke, ɗayan ya yi amfani...
    A yau Juma’a ne aka rufe taron dandalin tattauna batun tsaro na Xiangshan karo na 12 a birnin Beijing, bayan mahalartansa sun zurfafa tattaunawa karkashin jigon “Mara baya ga odar kasa da kasa da ingiza ci gaba cikin lumana.” An bude taron ne a ranar Laraba, ya kuma hallara sama da wakilai 1,800, ciki har...
    Firaministan kasar Sin Li Qiang, zai halarci babban taron mahawara na MDD karo na 80 a birnin New York na kasar Amurka, tsakanin ranakun 22 zuwa 26 ga watan Satumban nan. A cewar kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, firaminista Li, zai kuma halarci wasu ayyuka da Sin za ta shirya, ciki har da taron...
    Wata matar aure ta shiga hannu kan zargin ƙone fuskar ’yar mijinta, Fatima Talba mai shekara 17 da tafasasshen man girki, a unguwar Jiddari Polo da ke Jihar Borno. Wata majiya ta tabbatar da cewa lamarin ya faru a ranar Asabar da ta gabata, bayan wata taƙaddama da kaure tsakanin Fatima da matar ubanta. Sauya...
    A yau Juma’a shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya zanta ta wayar tarho da takwaransa na Amurka Donald Trump. (Saminu Alhassan)   Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki...
    Tawagar gwamnatin jihar Jigawa ta shiga sahun sauran kasashe da suka halarci taron kasa da kasa na Halal da ke gudana a Malaysia (MIHAS), domin neman jari da kuma ƙarfafa haɗin gwiwa na tattalin arziki. Tawagar karkashin jagorancin Kwamishinan Harkokin Kiwo, Farfesa Abdurrahman Salim Lawal, ta hada da Dr. Saifullahi Umar, Darakta-Janar na Hukumar Zamanantar...
    Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NNPP a zaɓen 2023, Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce jam’iyyarsa a shirye ta ke, ta haɗa kai da APC, idan an shirye karɓar sharuɗansu. Kwankwaso, ya faɗi haka ne a gidansa da ke Miller Road a Kano, lokacin da ya karɓi baƙuncin tsohon jigon APC a jihar, Buhari Bakwana,...
    Muhawara game da sanya doka a kan makarantu masu zaman kansu yana ta ci gaba a  ciki da wajen jihar Kaduna saboda ƙaruwar makarantun masu zaman kansu a cikin ƴ an shekarun nan musamman a cikin sabbin unguwanni da ke cikin ƙwaryar Kaduna. Abubuwan da jama’a ke magana a kai sun haɗa da tabbatar da...
    Rundunar ’yan sandan Jihar Yobe, ta ƙaryata rahotannin da ke nuna cewar an kai hari sakatariyar ƙungiyar ’yan jarida ta Najeriya (NUJ) da ke Damaturu. Wannan na cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar a ranar Juma’a. An cafke mutum 6 kan tono gawa a kabari don yin asiri a Gombe Wata mata ta ƙona...
    Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya ziyarci iyalan tsohon Shugaban Ƙasa, marigayi Muhammadu Buhari a Jihar Kaduna bayan halartar ɗaurin auren ɗan tsohon gwamnan Jihar Zamfara, Abdulaziz Yari. Da zuwansa, Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umar Radda, da ɗan marigayin, Yusuf Buhari, tare da wasu suka tarbe shi. Sin Ta Fitar Da Takardar Bayani Game Da...
    Majalissar gudanarwar kasar Sin ta fitar da takardar bayani, game da bunkasa ci gaban mata mai taken “Nasarorin Sin a fannin bunkasa ci gaban mata a dukkanin fannoni a sabon zamani”. Takardar bayanin da aka fitar a Juma’ar nan, na zuwa ne gabanin bude babban taron shugabanni na kasa da kasa na 2025, game da...
    Hukumar Sibil Difens (NSCDC) a Jihar Gombe, ta kama mutum shida bisa zargin tono gawar wani mutum a kabari tare da cire sassan jikinta domin yin asiri. Ɗaya daga cikin waɗanda aka kama, Kawuji Sarki, mai shekaru 39, ya amsa laifin. Wata mata ta ƙona al’aurar ’yarta da wuta kan zargin maita a Bauchi Janye...
    Albarkacin bikin murnar cika shekaru 100 na kafuwar Jam’iyyar Zhigong ta Sin, shugaban kwamitin kolin Jam’iyyar Kwaminis ta Sin, JKS, kana shugaban kasar Xi Jinping ya aika wasikar taya murna, kuma a madadin kwamitin tsakiyar JKS, ya taya dukkan ’yan Jam’iyyar Zhigong murna tare da nuna musu gaisuwa. Xi Jinping ya jaddada cewa, a kan...
    Wata mata mazauniyar garin Magama Gumau a Ƙaramar Hukumar Toro, Jihar Bauchi, ta shiga hannun ’yan sanda biyo bayan ƙona al’aurar ’yarta mai shekaru 10 kacal a duniya, kan zargin maita. Rahotanni sun nuna cewa matar ta yi amfani da cokali ta hanyar sanya shi a wuta ya yi zafi sannan ta umarci ’ya’yanta biyu...
    Ya ce ma’aikatar ta tsaya a kan tabbatar da ladabi da bin doka don haka babu wani shugaban makaranta da za a bari yana sabawa doka ko karbar kudade a hannun dalibai da iyaye ba tare da an hukunta shi ba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun...
    Wata mata mazauniyar garin Magama Gumau a Ƙaramar Hukumar Toro, Jihar Bauchi, ta shiga hannun ’yan sanda biyo bayan ƙona farjin ’yarta mai shekaru 10 kacal a duniya, kan zargin maita. Rahotanni sun nuna cewa matar ta yi amfani da cokali ta hanyar sanya shi a wuta ya yi zafi sannan ta umarci ’ya’yanta biyu...
    Rundunar ƴansanda a Jihar Bauchi ta tabbatar da kama wata mata, wadda ake zargi da yi wa wata yarinya ‘yar shekara bakwai mummunan rauni ta hanyar ƙona mata al’aura da wuka mai zafi a garin Magama Gumau, ƙaramar hukumar Toro. Rahotanni sun ce matar ta zargi yarinyar da maita, lamarin da ya sa ta yi...
    Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara, ya dawo bayan shafe tsawon lokaci baya jihar biyo bayan sanya dokar ta-ɓaci da  Shugaba Tinubu ya yi. A ranar Laraba ne Shugaba Tinubu ya janye dokar ta-ɓaci, wadda tsohon Hafsan sojan ruwa, Vice Admiral Ibok-Ekwe Ibas (rtd), ya jagoranta. ’Yan bindiga sun kai hari sakatariyar ’yan jarida ta jihar...
    Wasu ’yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun kai hari a sakatariyar Ƙungiyar ’Yan Jarida ta Najeriya (NUJ) da ke Damaturu, babban birnin jihar Yobe, da sanyin safiyar Juma’a. Rahotanni sun ce yayin harin, maharan sun harbi wani jami’in ɗan sanda da ke gadin sakatariyar suka ji masa rauni ƙafa. An...
    Gwamnatin jihar Sakkwato ta dakatar da wasu shugabannin makarantun sakandare guda shida kan zargin karbar kudi daga hanun dalibai na bisa ka’ida ba. Kwamishinan Ilimin Firamare da Sakandare na jihar, Farfesa Ahmad Ladan Ala ne ya amince da dakatarwar. Matasan Nijeriya sun koma yin ci-rani a Nijar da Chadi Akasarin masu kai mana hare-hare daga...
    A yau a Nijeriya, kalmar “Japa” ta zama gamagari wajen bayyana yadda matasa da dama ke barin ƙasar domin neman ingantacciyar rayuwa a wasu ƙasashe. Abin da ya bambanta shi yanzu shi ne inda suke nufa: ba kawai Turai da Amurka ba kawai, har ma da ƙasashen Afirka maƙwabta. Yawaitar tsadar rayuwa da ƙarancin ayyukan...