Xi Jinping Ya Gana Da Shugabannin Kasashe Daban-Daban A Moscow
Published: 10th, May 2025 GMT
Jiya Juma’a, a birnin Moscow na kasar Rasha, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da takwarorinsa na kasashe daban daban, wadanda suka hada da shugaban kasar Serbia, Aleksandar Vucic, da mai jagorantar gwamnatin kasar Myanmar, Min Aung Hlaing, da babban sakataren kwamitin tsakiya na jam’iyyar Kwaminis ta kasar Cuba, kana shugaban kasar Cuba, Miguel Diaz-Canel Bermudez, da shugaban kasar Venezuela, Nicolas Maduro Moros, gami da firaministan kasar Slovak, Robert Fico.
Bayan haka, ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta sanar da cewa, bisa gayyatar da shugaba Xi Jinping ya yi, shugaban kasar Brazil, Luiz Inacio Lula da Silva, zai ziyarci kasar Sin, tsakanin ranar 10 zuwa 14, ga watan Mayun da muke ciki. (Bello Wang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: shugaban kasar
এছাড়াও পড়ুন:
Xi: Hadin Gwiwa Tsakanin Sin Da Rasha Na Samar Da Daidaito Ga Duniya Mai Cike Da Tashin Hankali
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana a yau Alhamis cewa, a yayin da ake fuskantar sauye-sauyen da ba a taba ganin irinsu ba a duniya, kasashen Sin da Rasha sun ci gaba da zurfafa amincewa da juna ta fuskar siyasa, da hadin kai bisa manyan tsare-tsare, da kiyaye daidaito da hadin gwiwa a harkokin kasa da kasa, da sanya kwanciyar hankali da kyakkyawan kuzari a duniyar mai fuskantar sauyi da tashe-tashen hankula.
Xi ya bayyana hakan ne a lokacin da yake tattaunawa da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin yayin ziyarar da ya kai kasar ta Rasha. Yana mai cewa, dangantakar dake tsakanin Sin da Rasha ta samu ci gaba mai dorewa, cikin koshin lafiya kuma a babban mataki, sakamakon kokarin hadin gwiwa daga bangarorin biyu. Ya kuma yaba da kyakkyawar makwaftaka da kawance na dogon lokaci, da hadin gwiwar moriyar juna a matsayin wani muhimmin yanayi na dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.
Xi ya kara da cewa, kasar Sin ta kasance babbar mai bayar da gudummawa da daidaita ci gaban tattalin arzikin duniya tsawon shekaru, kana kasar Sin a shirye take ta yi aiki tare da kasar Rasha wajen kiyaye tsarin cinikayyar duniya bisa ra’ayin bangarori daban daban, da kiyaye tsarin masana’antu da samar da kayayyaki cikin kwanciyar hankali ba tare da cikas ba. (Mai fassara: Mohammed Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp