Wasu yan jaridu masu bincike a kasar Amurka sun gano sunan sojan HKI wanda ya bindige yar rahoton tashar Aljazeera ta kasar Qatar a shekara ta 2022 a lokacinda take Shirin bada rahoton hare-harenn da sojojin yahudawan suke kaiwa kan wata unguwa ta Falasdinawa a birnin Jenin na yankin yamma da Kogin Jordan.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto wadanda suka shirya film na tattara bayanai yadda aka kashe Shirin Abu Akela wato ‘ Zeteo’ dake da cibiya a birnin Washington na kasar Amurka na cewa sunan sojan HKI ta ya kashe Shirin shi ne Alon Skajio, wanda shima daga baya an kashe shi a birnin na Jenin daga bayan a wani farmakin da sojojin yahudawan suka kai cinin birnin.

Majigin mai tsaron mintuna 40 ya bayyana yadda gwamnatin Amurka ta shugaba Biden ta yi kokarin boye sunan wanda ya kashe yar jaridar da kuma wanke HKI kan wannan laifin da ta aikata na kashe yan jaridu.

Alon ya kashe Shirin yar shekara 51 a duniya da bindiga wanda ake cillawa daga nesa wato Sniper al-hali a fili yake tana sanye da kayakin yan jaridu wadanda aka rubuta Press a kansa a ranar 26 ga watan Mayun shekara ta 2022. Banda haka sojojin sun kai farmaki kan gawarta a lokacin jana’izata.

An haifi Abu Akleh a birnin al-Quds a shekara 1971 sannan tana da dijiri kan aikin jarida daga jami’ar Yarmouk ta kasar Jordan sannan ta fara aikin da tashar talabijin ta Al Jazeera a shekara ta 1977.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Karuwar Tafiye-Tafiye Yayin Hutun Ranar Ma’aikata A Kasar Sin Ya Bayyana Kuzarin Masu Kashe Kudi

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An zaɓi Robert Prevost sabon fafaroma
  • An kwantar da kishiyoyi a asibiti bayan sun sha ‘Kayan Mata’
  • An gabatar da sabbin shaidu kan Nnamdi Kanu
  • Duniya Ta Gano Damammaki Masu Kyau Daga Kasuwar Kasar Sin A Yayin Hutun Ranar Ma’aikata Ta Duniya
  • DAGA LARABA: Ɓoyayyun Dalilan Da ke Sa Faɗuwa Jarabawa A Najeriya
  • Karuwar Tafiye-Tafiye Yayin Hutun Ranar Ma’aikata A Kasar Sin Ya Bayyana Kuzarin Masu Kashe Kudi
  • Jiragen Yaken HKI Sun Kai Hare-Hare A Kan Tashar Jiragen Sama Na Birnin San’aa Na Kasar Yemen
  • Matashi ya kashe mahaifinsa da adda a Jigawa
  • AU, ta yi tir da harin baya bayan nan a tashar ruwan Sudan