Sin Na Fatan India Da Pakistan Za Su Kaucewa Kara Rura Wutar Tashin Hankali
Published: 11th, May 2025 GMT
Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya bayyana fatan ganin kasashen India da Pakistan sun kai zuciya nesa, tare da warware sabani ta hanyar shawarwari da tattaunawa, kana su gujewa sake rura wutar tashin hankali.
Wang ya bayyana hakan ne a jiya Asabar, yayin tattaunawa ta wayar tarho da mashawarcin gwamnatin India ta fuskar tsaro Ajit Doval, inda ya ce Sin na goyon baya, da fatan sassan biyu za su kai ga cimma cikakken yanayi mai dorewa na dakatar da bude wuta ta hanyar tattaunawa, wanda hakan muhimmiyar moriya ce ta kasashen biyu, kuma zai cika burin sassan kasa da kasa.
Wang ya kara da cewa, a yanayin duniya na sauye-sauye da tangal-tangal, samun zaman lafiya da daidaito a yankin Asiya abu ne mai kima da ya wajaba a martaba.
A wani ci gaban kuma, Wang Yi ya zanta ta wayar tarho da mataimakin firaminista, kuma ministan harkokin wajen Pakistan Mohammad Ishaq Dar, inda ya ce a matsayin Pakistan da India na kasashe makwaftanta, Sin ta damu matuka da kara ta’azzarar rikici tsakanin kasashen biyu. Ya ce Sin ta gamsu Pakistan za ta tunkari wannan lamari cikin lumana, da aiwatar da matakai daidai da babban burin cimma moriya mai dorewa. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Nijeriya Ta Horar Da Likitoci 360 Don Magance Mutuwar Mata Masu Juna Biyu
Shugaban tsangayar Kula da Lafiyar Mata Masu Juna Biyu A Kwalejin Likitanci Ta Ƙasa (NPMCN), Farfesa Ayodeji Oluwole, ya bayyana hanyoyin da shirin ke bi wajen aiwatar da aikin:
” Wannan horo ya samar wa likitocinmu da fasaha ta zamani, kuma a cikin shekaru biyar, muna sa ran raguwar mutuwar mata masu juna biyu.
“Babban abin da ake buƙata shi ne a rage yawan mace-macen mata masu ciki a Nijeriya da Afirka, mun horar da likitoci kusan 220 da masu ba da shawara 140 a duk yankuna shida na siyasa.
“A yanzu haka, likitocin suna samun horo a babban asibitin ƙasa dake Abuja; hakan na da matuƙar muhimmanci wajen cimma manufofin gwamnatin tarayya na kula da lafiyar mata masu juna biyu,” in ji shi.
Farfesa Sanusi Ibrahim na Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri ya bayyana cewa a Arewacin Nijeriya, mace-macen mata masu juna biyu na da matuƙar tayar da hankali.
“Wannan shirin ya ƙarfafa wa likitoci da ma’aikata, da dabarun ceton rai.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp