2025-05-05@10:50:03 GMT
إجمالي نتائج البحث: 32

«Lakurawa sun»:

    Tawagar haɗin gwiwar jami’an tsaro na aikin gano gawarwakin wasu mafarauta da mayaƙan Lakurawa suka kashe a yankin Ƙaramar Hukumar Tangaza da ke Jihar Sakkwato. Ana fargabar Lakurawa sun yi garkuwa da wasu daga cikin mafarautan da suka fito daga ƙananan hukumomin Tangaza da Gwadabawa, bayan sun faɗa tarkon ’yan ta’addan Aminiya ta ruwaito cewa mayaƙan Lakurawa sun kashe mafarauta 13 a wani harin kwanton ɓauna tare da tayar da bom a wani turken sadarwa a Jihar Sakkwato. ’Yan ta’addan sun kai wa mafarautan farmaki ne a yayin a yayin da suka fita farautar shekara-shekara a Dajin Hurumi da ke Ƙaramar Hukumar Ta gama, wanda ya samu halartar mafarauta daga sassa daban-daban. Aminiya ta samu labarin cewa mafarautan sun yi...
    Wasu ’yan bindiga da ake fargabar mayaƙan Lakurawa ne sun kashe wasu ’yan bijilanti da ke aikin sintiri a Jihar Sakkwato. Aminiya ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne a ranar Juma’ar da ta gabata bayan musayar wuta da mayaƙan suka yi da ’yan sintiri a Ƙaramar Hukumar Tangaza a jihar ta Sakkwato. Ya kamata a zuba jari a harkar noman rani — Zulum Wa zai cire wa Real Madrid kitse a wuta? Bayanai sun ce kawo yanzu akwai ragowar gawawwakin ’yan bijilantin da ke hannun Lakurawan a dajin da suka yi sansani. Sai dai wakilinmu ya ruwaito cewa rundunar soji na ƙoƙarin ƙwato gawawwakin a dajin Binji da Raka. Shaidu sun ce tun da farko lamarin ya faru ne...
    Yayin da ake ci gaba da bincike, hukumomi na ƙoƙarin gano waɗanda suka ɓace da kuma gano sauran gawarwakin waɗanda abin ya shafa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa gwamnatin JMI ba zata amince da tattaunawa tare da kara tsuge takunkuman tattalin arziki na koli da aka dorawa kasar ba. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto ministan yana fadar haka a yau Jumma’a ya kuma kara da cewa yin haka sabawa dokokin kasa da kasa ne. Har\ila yau take hakkin mutanen kasar Iran ne da kuma shigar da shakku a cikin tattaunawar da Amurka take yi da kasar. Kafin haka dai gwamnatin kasar Amurka ta bada sanarwan kakabawa mutanen da kamfanoni 7 wadanda suke mu’amala da kasar Iran a kasashen UAE da Turkiya saboda sayan danyen man kasar Iran da kuma sinadaran manfetur na kasar. Har’ila...
    An fara kasuwar baje koli na kayakin kasuwancin da ake samarwa a cikin Iran ko IRAN EXPO 2025, karo na 3 a nan Tehran. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa kasuwar baje koli na Iran EXPO 2025 zai jawa masu zuna jari daga kasashen Afirka. Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya fadawa kamfanin dillancin labaran IP kan cewa Kasuwar ta bana dai, za ta tara kamfanonin  masu samar da kayaki daga yankuna daban daban na kasar Iran da dama, kuma akwai fatan cewa wannan kasuwar ta zama mabudi ga kyautatuwan tattalin arzikin kasar. EXPO dai ita ce kasuwar baje koli na kayakin kasar Iran mafi girma wanda ake gudanarwa a ko wace shekara, sannan...
    Ƙasashen Nijar da Mali da Burkina Faso, ƙarƙashin inuwar Ƙungiyar Ƙasashen Sahel (AES), sun sanar da shirinsu na ƙaddamar da gidan rediyo na haɗin gwiwa. Ƙasashen guda uku, waɗanda duk a halin yanzu suke ƙarƙashin mulkin soja, sun jaddada cewa sun kafa gidan rediyon ne da nufin daƙile farfagandar ƙasashen waje da kuma isar da “ingantattun bayanai na gaskiya” ga ’yan ƙasarsu. Sanarwar tasu ta kasance bayan ƙaddamar da gidan talabijin ɗinsu na intanet na haɗin gwiwa da suka yi a watan Disamba na 2024, wanda suka bayyana a matsayin dandamali da aka samar domin “yaƙi da yaɗa labaran ƙarya.” Baya ga waɗannan ayyukan watsa labarai, a baya ƙungiyar ta nuna sha’awarta ta kafa kamfanin jiragen sama na yankin da...
    Fadar shugaban kasa ta musanta rahotannin da ke nuni da cewa an hana mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, GCON shiga fadar shugaban kasa, inda ta bayyana ikirarin a matsayin shirme, kage da kuma karya gaba daya.   Wata sanarwa da babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai da sadarwa na ofishin mataimakin shugaban kasa Stanley Nkwocha ya sanyawa hannu, ta ce rahoton da wasu shafukan da ba su da tushe suka yada shi, na cikin jerin labaran karya da aka kitsa domin haifar da rashin jituwa tsakanin shugaban kasa da mataimakinsa.   Sanarwar ta kara da cewa, “Wannan wani yunkuri ne mai rauni na cin mutuncin mutum da ofishin Mai Girma, Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima....
    Lamarin ya ƙara tayar da hankali a Jihar Kebbi, duba da yadda hare-haren ’yan ta’adda ke ƙaruwa a yankunan Arewacin Nijeriya. A baya, wata kotu a Nijeriya ta ayyana Lakurawa a matsayin ƙungiyar ’yan ta’adda domin bai wa hukumomin tsaro damar amfani da ƙarfi wajen yaƙar su. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ana fargabar cewa kimanin ’yan sa-kai 13 ne suka rasa rayukansu a wasu hare-hare da wasu ’yan bindiga da ake zargin mayaƙan Lakurawa ne suka kai Jihar Kebbi a jiya Lahadi. Lamarin ya faru ne a yankin Morai na Ƙaramar Hukumar Augie — ɗaya daga cikin yankunan da ake cewa mayaƙan Lakurawa na da sansani. HOTUNA: Zanga-zangar adawa da gwamnatin Tinubu ta ɓarke a Abuja da Legas Mutanen da Sanƙarau ta kashe sun kai 151 — NCDC Wani mazauni, Malam Ibrahim Augue, ya ce maharan sun kashe mutum shida ne, suka kwashe shanu, sai ’yan sa-kai suka bi su. “A nan suka yi wa ’yan sa-kan kwanton ɓauna, suka buɗe musu wuta, inda suka kashe guda 13 daga cikinsu.” Ƙoƙarin...
    Shahararren masanin tarihin nan na Jihar Kano, Ibrahim Ado Kurawa, ya bayyana cewa soke hawan Sallah da Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero ya yi tamkar wani wasan kwaikwayo ne. A makon jiya ne dai Sarki Aminu Ado ya sanar da janye hawan Sallar da ya ce zai jagoranta kan abin da ya kira gudun tayar da hargitsi a Jihar Kano. ’Yan sanda sun haramta hawan Sallah a Kano Yadda kisan ’yan Arewa 16 a Edo ya tayar da ƙura a faɗin Nijeriya Gabanin yanzu dai, Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II da shi kansa Sarki Aminu sun ɗaura azama ta gudanar da haye-hayen sallah bana. Sai dai da yake magana da manema labarai a ranar Alhamis, Kurawa...
    Wasu ’yan bindiga da ake zargin Lakurawa ne, sun kai har iyakar Bachaka da ke Ƙaramar Hukumar Argungu a Jihar Kebbi, inda suka kashe jami’an Kwastam biyu da wani mazaunin garin. Harin ya faru ne kwana guda bayan da dakarun tsaro suka kashe wasu dakarun Lakurawa a yankin. Ban sani ba ko zan tsaya takara a 2027 — Atiku Mutum 2,000 za su riƙa kamuwa da cutar HIV duk rana a duniya — MDD Rundunar ’yan sandan Jihar Kebbi, ta tabbatar da faruwar harin, inda ta ce ba a tantance sunayen jami’an Kwastam da aka kashe ba. “Eh, an kai hari, kuma ya yi sanadiyyar mutuwar jami’an Kwastam biyu da wani mazaunin Bachaka,” in ji kakakin rundunar, Nafiu Abubakar. Bayan...
    A ranar 19 ga watan Maris na ko wace shekara ne mutanen Iran suke gudanar da bukukuwan tunawa da ranar da mutanen kasar tare da taimakon gwamnatin lokacin suka sami nasarar kwace kamfanin haka da sarrafa man fetur na kasar, daga hannun wani kamfanin mai na kasar Burtaniya suka maida shin a kasa. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya ce , wannan rana abin alfakhari ne ga mutanen kasar, don bayan haka ne kasar ta sami ikon kawo ci gaban tattalin arzikin kasar da kuma shimfida harsashen samun yencin kasar daga hannun kasashen yamma wadanda suka mamaye bangarori da dama a cikin al-amuran kasar. A ranar 19 ga watan Maris na shekara ta 1951 ne, wato shekaru 78...
    An shiga wata 11 da Gwamnatin Jihar Sakkwato ƙarƙashin Gwamna Ahmad Aliyu ta tuɓe rawanin wasu sarakuna da take ganin sun yi abin da bai dace ba na shiga siyasa. Tun bayan cire sarakunan, mutane sun yi tsammanin gwamnati za ta nada wadanda take muradi ne kai-tsaye domin su maye gurbin tubabbun sarakunan, amma shiru kamar ba wasu da ke jiran hukunci da sakayyar gwamnati mai ci. Kofin Duniya: ’Yan wasan cikin gida 8 da Super Eagles ta gayyata Tsofaffin furodusoshin Kannywood da aka daina jin ɗuriyarsu Har yanzu gwamnati ba ta fito ta fadi dalilin rashin sake nada sababbin sarakunan ba domin ci gaba da wakilcin jama’a, ganin an bar garin kufai ba cikakken basarake. A baya da ma...
    Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya ce Tehran a shirye take ta shiga tattaunawa da kasashen Turai bisa mutunta juna. A wata tattaunawa ta wayar tarho, Araghchi da Ministan Harkokin Wajen Netherlands Caspar Veldkamp sun tattauna hanyoyin inganta alakar juna da sabbin abubuwa dake faruwa a yankin da na kasa da kasa. Babban jami’in diflomasiyyar na Iran ya nanata tsarin kasar na kulla kyakkyawar alaka ta diflomasiyya da kasashen. Iran da kasashen Turai dai na tattaunawar ba-zata kai a kai tun shekara ta 2021, shekaru uku bayan da Amurka ta fice daga yarjejeniyar nukiliyar iran – tare da maido da takunkumin da Washington ta kakaba wa Jamhuriyar Musulunci ta Iran. bangarorin kasashen Turai da suka shiga yarjejeniyar nukiliya –...
    Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya buƙaci Gwamnatin Tarayya da ta kafa sansanin soji a Ƙaramar Hukumar Arewa domin inganta tsaro. Ya yi wannan roƙo ne bayan ziyarar da ya kai sansanin ‘yan gudun hijira a Kangiwa, bayan harin da wasu da ake zargin Lakurawa ne suka kai musu. Cutar sanƙarau ta kashe sama da mutum 50 a Sakkwato da Kebbi ’Yan bindiga sun kai hari ƙauyukan Kaduna, sun sace matasa 3 Harin da aka kai a ranar 9 ga watan Maris ya yi sanadin mutuwar mutum 11 tare da ƙone ƙauyuka bakwai. Yankunan da abin ya shafa sun haɗa da Dogon Daji, Danmarke, Yar Goru, Tambo, Birnin Debi, Garin Nagoro, da Garin Rugga. “Sansanin soji a yankin zai taimaka...
    Gwamnan Jihar Kebbi, Dakta Nasir Idris ya tabbatar wa mutanen da hare-haren Lakurawa a ƙaramar hukumar Arewa ya raba da muhallansu cewa gwamnatinsa za ta ɗauki matakan gaggawa domin mayar da su garuruwansu. Nasir Idris ya bayyana hakan ne lokacin da ya kai ziyarar jaje ga mutanen da hare-hare ya raba da garuruwansu a sananin ƴangudun hijira da ke Kangiwa a jihar ranar Laraba. Peter Obi na ganawar sirri da gwamnan Bauchi ’Yan bindiga sun sace gwarzon gasar karatun Alƙur’ani a Katsina Sansanin ya tanadi waɗanda suka rasa muhallansu daga garuruwan Birnin Debe da Dan Marke, da Tambo, ne ke samun mafaka a sansanin inda wasu mahara ɗauke da makamai suka kai hari a ranar Asabar ɗin da ta gabata,...
    Mayaƙan Lakurawa sun kashe mutum 13 a wani harin ramuwar gayya da suka kai yankin Birnin Debe da ke Ƙaramar Hukumar Arewa a Jihar Kebbi. Wani mazauni mai suna Musa Gado, ya ce maharan wanda suka kai harin a ranar Lahadi, sun kuma ƙone ƙauyuka takwas daga cikin tara da ke yankin. Tsohon shugaban Philippines ya faɗa komar ’yan sanda Jihohi 12 da za a fuskanci tsananin zafin rana — NiMet Shi ma wani mazaunin yankin, Suleiman Abubakar wanda ya rasa ɗan uwansa ɗaya a dalilin harin, ya ce maharan sun auka wa ƙauyukan ne da yammaci bayan sallar Magariba. “Abin ba a cewa komai domin mun ga tashin hankali. Sun kashe mutane da dama sun ƙone mana ƙauyuka kuma...
    Shugaban karamar hukumar Arewa ta jihar Kebbi, Alhaji Sani Aliyu, ya tabbatar da harin da ‘yan ta’addan Lakurawa suka kai a yankin, inda suka kashe mutane kimanin 15 tare da kona kauyuka 7. Da yake tabbatar da faruwar lamarin ga gidan rediyon Najeriya da ke jihar Kebbi, shugaban karamar hukumar ya ce an baza jami’an tsaro a yankin domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma. A cewar wata majiya mai tushe, Malam Umar, maharan sun kara kona akalla wasu kauyuka bakwai da ke kusa da Birnin Dede, duk a cikin karamar hukumar Arewa ta jihar Kebbin. A wata tattaunawa ta wayar tarho, Malam Umar ya bayyana cewa, an kai harin ne domin ramuwar gayya kan kisan da jami’an tsaro...
    Jami’an tsaro da ’yan sa-kai sun kashe shugaban ’yan ta’addan Lakurawa, Maigemu, a Jihar Kebbi. Daraktan Tsaro na Jihar Kebbi, AbdulRahman Usman Zagga ne, ya shaida wa manema labarai a ranar Juma’a cewa an kashe Maigemu a ranar Alhamis. PDP ta soki dakatar da Natasha, ta nemi a binciki Akpabio Fashewar tankar mai: Mutum 7 sun mutu, gonaki sun lalace a Neja Ya ce an kashe shi ne yayin musayar wuta da jami’an tsaro a garin Kuncin Baba da ke Ƙaramar Hukumar Arewa. Mutuwarsa ta zo ne mako guda bayan da Gwamna Nasir Idris ya kai ziyarar jaje ƙauyukan Bagiza da Rausa Kade, inda ’yan ta’adda suka kashe mutum shida. “Ƙoƙarin gwamna ya haifar da ɗa mai ido, domin yanzu...
    Rundunar hadaka ta jami’an tsaro da suka hada da ‘yan banga sun yi nasarar hallaka  wani kasurgumin jigon kungiyar Lakurawa da aka fi sani da  Maigemu a jihar Kebbi. Sanarwar da Daraktan Tsaron, Alhaji AbdulRahman Usman Zagga, ya fitar, ta ce an kashe Maigemu ne a ranar Alhamis a Kuncin Baba da ke karamar hukumar Arewa, bayan musayar wuta da jami’an tsoro. Sanarwar ta ce, wannan nasarar ta zo ne mako guda bayan da Gwamnan Jihar Kebbi, Kwamared Nasir Idris ya ziyarci al’ummar Bagiza da Rausa Kade a yankin karamar Hukumar Arewa, domin jajantawa al’ummar yankin bisa kashe wasu mutane shida da ake zargin barayin shanun Lakurawa ne suka yi. An bayyana cewa, matakin da gwamnan jihar ya dauka kan...
    Fitaccen Malamin Addinin Musuluncin nan, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya zayyana wasu muhimman abubuwan da ya kamata mai azumi ya lazimta a watan Ramadan. Yayin da al’ummar Musulmi ke gudanar da ibadar azumi, Sheikh Daurawa ya bayyana cewa akwai ɗimbin lada ga duk wanda ya aiwatar da waɗannan ayyuka: Kwamitin majalisa ya yi watsi da ƙorafin Natasha a kan Akpabio Ramadan: Abubuwa goma ga ma’aurata 1. Azumi: Mai azumi ya kula da azuminsa, ya san hukunce-hukuncensa, ya kiyaye su, tare da nisantar abin da zai rage lada ko karya azumi. 2. Sallah: Ya fi dacewa a dage da Sallar Taraweeh da Tahajjud, tare da yin sallolin farilla a cikin jam’i da nafiloli da ake yi kafin ko bayan su. 3....
    Mataimakin ministan harkokin wajen a kan al-amuran siyasa, dole ne Amurka ta daukewa kasarsa wadannan takunkuman tattalin arziki wanda suke cutar da mutanen kasar Iran da al-adunsa. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto TakhtaRawanchi yana fadar haka a shafinsa na X ko twitter a da, a kuma  jiya Talata, Mataimakin ministan ya kara da cewa, takunkuman tattalin arzikin da kasashen Amurka da Turai suka dorawa kasar Iran ya zuwa yanzu ya shafi rayuwar mutanen kasar da dama wanda kuma take hakkinsu ne. Labarin ya kara da cewa a shekaru fiye da 40 da suka gabata, gwamnatocin Amurka kadai sundorawa kasar Iran takunkuman tattalin arziki mafi muni, kuma nau’ii daban-daban. Haka ma ta dade tana wa kasar barazanar...
    A yau Talata, kasar Sin ta bakin ma’aikatar kula da harkokin kasuwanci ta kasar ta bayyana rashin jin dadinta game da karin harajin da Amurka ta yi ikirarin sanyawa kayayyakin kasar, bisa kafa hujja da maganin Fentanyl. Kamar yadda kakakin ma’aikatar ya bayyana, Sin tana daya daga cikin kasashe mafiya tsauraran matakan yaki da miyagun kwayoyi ko sarrafa su. Tabbas kasar Sin kasa ce mai sa ido da daukar tsauraran matakan dakilewa da yaki da tu’ammali da duk wani abu mai illa, musammam miyagun kwayoyi, kuma tana iyakar kokarinta kan wannan batu. Idan ba a manta ba, kasar Sin ce ta jagoranci duniya wajen tsara jerin rukunin kwayoyin Fentanyl da sauran abubuwan da suka jibance shi a watan Mayun 2019,...
    Gwamnatin kasar masar ta tabbatarwa gwamnatin Falasdinawa kan cewa tana goyon bayan falasdinawa a cikin dawo da hakkinsu, na kafa kasarsu mai cikekken yanci wacce take da gabacin birnin Qudus a matsayin babban birnin Kasar. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Mostafa Madbouly ministan harkokin wajen kasar Masar yana fadar haka a lokacin ganawarsa da tokwaransa na gwamnatin Falasdinawa a Ramallah Mohammada Mustafa a birnin Alkahira. Madbouly ya kara da cewa gwamnatin kasar Masar tana son ganin an gaggauta sake ginza Gaza da kuma maida rayuwa kamar yadda take a gaza da gaggawa. Ya ce kasashen larabawa ba zasu taba yarda da kasar Falasdina kasa da yarjeniyar 4 ga watan Yunin shekara ta 1967. A ranar Talata...
    Shugaban kasar Rasha Vladmir Putin ya bayanna cewa, Turawa za su iya shiga cikin shirin warware rikicin Ukraine, yayin da kungiyar EU ke fargabar cewa za a mayar da ita saniyar ware tun bayan fara tattaunawar kai tsaye tsakanin Moscow da Washington. “Turawa, amma har da sauran kasashe, suna da hakki kuma suna da damar shiga, Kuma zamu mutunta hakan, ”in ji Vladimir Putin a wata hira da aka yi da shi ta talabijin. Ya nanata cewa kasashen Turai ne suka yanke alaka da Rasha bayan da ta fara kai hari kan Ukraine shekaru uku da suka gabata, Don haka “Shigowarsu a cikin tsarin tattaunawar ya zama dole. Vladimir Putin ya dage kan cewa tattaunawar da Rasha da Amurka suka...
    Jam’iyyar NNPP reshen jihar Kano ta dakatar da ‘yan majalisar tarayya huɗu bisa zargin aikata abubuwan da suka saɓa wa manufofin jam’iyya. Shugaban jam’iyyar a jihar, Alhaji Hashimu Dungurawa, ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai a Kano a ranar Litinin. Waɗanda aka dakatar sun hada da Kawu Sumaila (Sanatan Kano ta Kudu), Ali Madakin Gini (Dala), Sani Rogo (Rogo/Karaye), da Kabiru Rurum (Rano/Kibiya). Dungurawa ya ce waɗannan ‘yan majalisa sun samu tikitin NNPP ne, amma daga baya suka fara aikata abubuwan da suka sabawa jam’iyyar. Nan Kusa Ƴan Majalisun NNPP Za Su Koma APC – Ganduje  Jam’iyyar NNPP Daya INEC Ta Amince Da Ita – Shugaban Jam’iyyar  Ya ce misali, Sanata Sumaila ya ƙaddamar da...
    Jaridar Wall Satreet Journal ta ambaci cewa kasashen Faransa da Birtaniya suna shirya yiyuwar aikewa da sojojin tabbatar da zaman lafiya a cikin kasar Ukiraniya idan an tsagaita wutar yaki. Jaridar ta Amurka ta kuma kara da cewa; Idan an kai ga cimma tsagaita wutar yaki to da akwai yiyuwar turawan za su aike da sojojin zaman lafiya da za su kai 30,000 daga cikin har da na kasar Switzerland. Sai dai kuma aiwatar da shirin na turai yana da alaka ne da yadda Donald Trump zai amince da kasarsa ta taka rawa, idan har Rasha ta kai wa turawan hari, ko ta keta yarjejeniyar tsagaita wuta, kamar yadda jaridar ta ambato wani jami’in turai din yana fada. Jaridar ta...
    Hukumar Hisbah ta rufe gidajen rawa da ke gudanar da harkokinsu a Jihar Katsina. Hukumar ta umarci ɗaukacin masu gidajen rawa da ke gudanar da harkokinsu a cikin dare a faɗin jihar da su rufe. Shugaban Hukumar, Dakta Aminu Usman ne ya bada umarnin tare da gargaɗin masu wuraren da matakin ya shafa. Ya bayyana cewa ɗaukar matakin ya zama dole domin kare tarbiyya da dokokin addinin Islama da kuma barazanar tsaro a jihar. Jami’an tsaron al’umma 6 sun mutu a artabu da ’yan bindiga a Sakkwato NAJERIYA A YAU: Tanadin Dokar Kasa Kan Kirkirar Gwamnatin Bibiya A Kano Sanarwar da ya fitar ranar Laraba ta bayyana cewa tabbatar da tarbiyya da kare dokokin Musulunci sun zama wajibi. Ya ci...
    Shugaban kasar Amurka Donal Trump ya bayyana cewa kasashen Turai basa cikin tattaunawar tsagaita wuta a Ukraine. Jaridar Daily Mail ya bayyana cewa hankalin shuwagabannin kasashen turai ya tashi a lokacin da JD Vance mataimakin shugaba Trump ya fada masu cewa ba wani shugaba daga cikin shuwagabannin kasashen Turai da zasu halarci taron tsagaita wuta na Ukraine. Wannan labarin ya Eu ta kira taron gaggawa don tattauna wannan batun. Sannan Sir Keir Starmer ya kuma hanya zuwa Amurka da gaggawa. Mataimakin shugaban kuma yakadansa na musamman a kan shirin tsagaita wuta a Ukraine ya bayyanawa Ukrain kan cewa batun shigar Ukraine kungiyar tsaro da NATO bai da wani muhimmanci a wajen shugaba Trump a yanzu. Mr Vances ya bayyana hakane...
    Kotun hukunta manya-manyan laifuka ta kasa da kasa ICC ta yi allawadai da takunkuman da gwamnatin Amurka ta dorawa kotun, ta kuma kara da cewa zata ci gaba da aikinta na tabbatar da adalci a duniya kamar yadda ta saba. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa kotun ICC kotu ce wacce take karban koke-koke na mutane da kasashe a duk fadin duniya, amma wacce gwamnatin Amurka ta ke son takaita ikonta don tallafawa HKI a yakin da take fafatawa da Falasdinawa wadanda ta mamaye kasarsu fiye da shekaru 76 da suka gabata. A ranar Alhamis da ta gabata ce shugaban kasar Amurka Donal Trump ya sanya hannu a kan wata doka wacce ta dorawa kotun ta...
    Mayaƙan Lakurawa sun kashe farar hula ɗaya tare da jikkata wasu shida a yankin Gulma da ke Karamar Hukumar Argungua Jihar Kebbi. Da misalin ƙarfe 11 na dare ne maharan suka suka wa yankin yayin da mazauna suke tsaka da barci a ranar Alhamis suna harbe harbe-harbe. Shugaban Ƙaramar Hukumar Argungu, Aliyu Sani Gulma, ya bayyana cewa waɗanda maharan suka yi raunin harbi suna samun kulawa a Asibitin Tarayya da ke Birnin Kebbi, babban birnin jihar.
    Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi, a lokacin da yake maida martani ga jawabin shugaban kasar Amurka Donal Trump a jiya Laraba, ya ce takurawa mai tsanani ya karya. Abbas Aragchi ya fadi haka a jiya Laraba , ya kuma kara da  cewa bayan takuarawa masu tsanani Amurka tana bukatar tattaunawa da Iran. Harma ya zauna da shugaban kasarta. A wani bangare na maida martanin Aragchi ya bayyana cewa dangane da fadinsa, ba zai taba amincewa Iran ta mallaki makaman Nukliya ba, yace Iran mamba ce a yarjeniyar NTP, a kuma hukumar makamashin nukliya ta IAEA. Zasu lamunce masa kan cewa Iran bata bukatar makaman nukliya. Amma duk da haka Iran ba zata taba sayar da hakkinta na mallakan...
۱