Minista Tuggar ya bayyana cewa, kasar Cuba ta taka mihimmiyar rawa wajen samar da ‘yancin kai ga wasu kasashen Afrika a lokacin da ake gwagwarmaryar kwato ‘yanci daga ‘yan mulkin mallaka a shekkarun 60s, 70s, 80s da 90s.

“Cuba da Nijeriya sun yi aiki tare wajen yaki da ‘yan mulkin mallaka a kasashen Angola, Namibia, Afrika ta Kudu da Zimbabwe” in ji shi, ya kara da cewa, wannan sabon yarjejeniyar za ta karfafa hadin kai a bangarorin kimiyya da fasaha, bincike da kuma samar da ci gaba mai dorewa.

A nasa tsokacin, Ministan harkokin waje na Cuba, ya ce, dangantakar da ke tsakanin Cuba da Afrika mai karfi ne, ya kuma gode wa Nijeriya a kan goyon bayan da ta bata a lokacin da Amurka ta sanya wa kasar takunkumin karya tattalin arziki.

Amma kuma yana da muhimmanci a fahimci cewa, fiye da shekara daya kenan Nijeriya bata nada cikakken ambasada ko wani wakili a kasar ta Cuba, hakan kuma yana matukar shafar harkokin huldar diflomasiya dana kasuwanci a tsakanin kasashen biyu.

A taron manema labarai na shekara-shekara (2025), da ma’aikatar harkokin kasashen waje ta yi kwananan, Minista Tuggar ya bayyana wa Duniya yadda ya tafiyar da harkokin ma’aikatar hulda da kasashen duniya, ya bayyana cewa, gwamnatin tarayya ta yi nisa wajen nada ambasadoji a kasashen duniya domin tuni sunayen wadanda za a nada yake a gaban majalisar dattawa domin amincewa.

Tuggar, wanda ya yi jawabi mai taken “Nasarori da kalubalen hulda da kasashen waje a karkashin mulkin Shugaba Bola Ahmed Tinubu”, ya kuma bayyana cewa, Nijeriya na aiki tukuru wajen gudanar da harkoki da kasahen waje ta hanyar la’akari da mutunci da kuma jin dadin ‘yan Nieriya a kasashe waje da kuma dawo da mutumcin Fasfot din Nijeriya a sassan duniya.

A wani bangaren kuma, kokarin Nijeriya na bunkasa tattalin arzikin kasa, ma’aikatar harkokin kasashen waje ta samo wa Nijeriya jarin Dala Biliyan 14 daga kasar Indiya, za a zuba jarin ne a bangarori da daban-daban na rayuwa da tattalin arzikin kasa haka kuma kasar Netherlands ta zuba jarin Fam miliyan 250 a bangarori daban-daban na tattalin arzikin Nijeriya.

A nasa tsokacin, tsohon Ambasadan kasar Jamus a Nijeriya, ya bayyana cewa, “An samu fiye da kashi 300 na wadanda suka yanki hannun jarin Nijeriya ‘Eurobond’. Wannan kuma alama ce na yadda duniya ta amince tare da rungumar Nijeriya domin gudanar da harkokin kasuwanci, tuni Nijeriya ta sanya hannu a yarjejeniya kasuwanci a tsakaninta da kasashen Jamus, Saudi Arabia, China, Ekuatorial Guinea, Faransa, Cuba, Katar, Birtaniya India, da kuma Brazil wanda hakan ya karfafa bangaren samar da wutar lantatrki, man fetur aikin gona da kuma samar da ayyukan yi ga dinbin matasan mu.”

Haka kuma masana sun bayyana cewa, tattaunawa da kasa Sin ya bude kofofin kasuwanci a tsakanin kasashen biyu ya kuma katse dukkan tarnakin da yake kawo cikas a harkokin kasashe biyu a baya. A halin yanzu an fara wata gaggarumar kasuwancin Kashu a tsakanin kasashen biyu an kuma kafa wata kwamiti domin samar da kyakyawar kalkibla domin samun nasarar hulda da juna a tsakanin kasashen. Haka kuma an samar da wata yarjejeniya a tsakanin kasar Ekuatorial Guinea, yarjejeniya nada nufin samar da butun gas tare da bunkasa yankin kahon Guinea gaba daya.

Duk da muhimmanci kasuwanci da zuba jari ga rayuwar kasa, a ‘yan shekarun baya an bata sunan Nijeriya saboda ayyukan rashin gaskiya da wasu ‘yan Nijeriya ke aikatawa a kasashe waje.

Amma a halin yanzu, Minista Tuggar ya bayar da tabbacin cewa, wannan gwamnatin za ta yi dukkan mai yiyuwa don farfado da mutumcin kasar nan tare da kuma kare mutumcin ‘yan Nijeriya a kasashe waje. Ya ce, ‘’muna fatan samun kasar da dukkan ‘yan Nijeriya za su shiga kowacce ofishin jakadanci ko filin jiragen sama ko kuma shiga wata yarjejeniyar kasuwanci ba tare da wani tsoron barazana ba.

“Ka sawwala Nijeriyar da farfot dinta ke bude wa ‘yan kasa kofofin kasuwanci a dukkan fadin duniya kuma a cikin mutuntawa.”

Duk da muhimmancin wadannan matakai da ake kokarin dauka da kuma wadanda aka dauka, ba za su yi wani tasiri ba har sai matakan sun kai ga bunkasa rayuwar al’ummar kasa, kasar da ke fama da dimbin marasa aikin yi da kuma hauhawar farashin kayan abinci dana makamashi.

Masu lura da al’amurran yau da kullum sun jinjina wa Ministan harkokin kasashen wajen Nijeriya a kan yadda ya tsayu wajen daukaka suna da mutuncin Nijeriya a idanun duniya.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Nijeriya Tugar harkokin kasashe kasashen waje bayyana cewa kasuwanci a

এছাড়াও পড়ুন:

Za A Gudanar Da Taron Davos Na Yanayin Zafi Na Bana A Birnin Tianjin

Yanzu haka ana shirye-shiryen gudanar da taron kasa da kasa na tattauna batutuwan raya tattalin arziki na Davos na yanayin zafi karo na 16, taron da aka fi sani da dandalin Davos. A bana za a gudanar da taron ne tsakanin ranakun Talata 24 zuwa Alhamis 26 ga watan nan na Yuni, a birnin Tianjin dake arewacin kasar Sin, bisa taken “sana’o’i a sabon zamani.”

A bana taron zai mayar da hankali ne ga muhimman fannoni biyar, wadanda suka hada da warware batu game da tattalin arzikin duniya, da hange game da kasar Sin, da halin da masana’antun duniya suka fuskanta na taka musu birki, da zuba jari kan al’umma da duniyar bil’adama da batun sabbin makamashi da hajoji.

Game da hakan, jami’i a hukumar tsara manufofin ci gaba da aiwatar da sauye-sauye ta kasar Sin Chen Shuai, ya ce Sin za ta yi amfani da taron na Davos na bana, wajen jaddada aniyarta, ta ci gaba da kwazo don cimma nasarar bude kofa bisa matsayin koli, da rarraba damammakinta na ci gaba da ta samu tare da sauran sassan kasa da kasa.

A nata bangare kuwa, Gim Huay Neo, babbar daraktar dandalin tattalin arziki na duniya, ta shaidawa wani taron menema labarai da ya gudana a baya bayan nan cewa, daya daga cikin yankunan duniya mafiya samun sauye-sauye a duniya shi ne nahiyar Asiya, nahiyar da ke kunshe da kaso 60 bisa dari na ci gaban tattalin arzikin duniya, kuma cikin wannan adadi kasar Sin ita kadai na bayar da gudummawar rabin kason ci gaban nahiyar. Jami’ar ta kara da cewa, dandalin Davos na bana zai samar da zarafi ga mahalartansa, na zurfafa fahimtarsu ga salon ci gaban Sin da sauran sassan Asiya. (Saminu Alhassan)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamnati Ta Bayar Da Tabbaci Akwai Tsaro A Abuja Duk da Gargaɗin Da Ofishin Jakadancin Amurka Ya Yi
  • Akwai ƙasashen da ke shirin bai wa Iran makaman nukiliya — Rasha
  • Sin Na Fatan Kwamitin Sulhun MDD Zai Goyi Bayan Kuduri Game Da Halin Da Iran Ke Ciki
  • Amurka ta roƙi China ta sa baki kada Iran ta rufe mashigar tekun Hormuz
  • Nijeriya Da Brazil Sun Ƙulla Yarjejeniyar Horar Da Matasa Kiwon Dabbobi
  • Za A Gudanar Da Taron Davos Na Yanayin Zafi Na Bana A Birnin Tianjin
  • Hikimar Yunƙurin Sake Farfaɗo Da Noman Filanten A Jihar Nasarawa
  • Sin A Shirye Take Ta Yi Aiki Da Rasha Don Daukaka Amincewar Juna Ta Fuskar Siyasa Da Karfafa Muradun Juna
  • Ministan Harkokin Wajen Iran ya isa taron Kungiyar OIC a Turkiyya
  • Iran Ta Bayyana Sharaɗin Sasantawa Da Isra’ila – Ministan Harkokin Waje