2025-10-28@18:09:36 GMT
إجمالي نتائج البحث: 10822

«Muhammadu Buhari»:

    An bude taron ministocin cikin gida na kasashen kungiyar hadin kan tattalin arziki ta ECO a birnin Tehran. Shugaban Jamhuriyar Musulunci ta Iran Massoud Pezeshkian ne ya jagoranci bude taron wanda shi ne karo na hudu. Ministoci da manyan jami’ai daga Pakistan, Tajikistan, Turkmenistan, Jamhuriyar Azerbaijan, Afghanistan, Kazakhstan, Kyrgyzstan, Turkiyya, Uzbekistan, da Jamhuriyar Musulunci ta...
    Sojojin Isra’ila sun kashe akalla Falasdinawa uku yayin da suke fadada hare-haren da suke kai wa a Yammacin Kogin Jordan da aka mamaye. Kamfanin dillancin labarai na Falasdinawa WAFA, wanda ya ambato majiyoyin yankin, ya ruwaito cewa sojojin mamayar sun mamaye kauyen Kafr Qud da karfin soja a ranar Talata. Ma’aikatar Lafiya ta Falasdinawa ta...
    Kungiyar ƙwallon ƙafa ta Juventus ta kori kocinta, Igor Tudor, bayan da ta sha kashi da ci 1-0 a hannun Lazio, lamarin da ya ba ta damar haɗa maki biyar kacal a wasanni biyar da ta buga a baya-bayan nan. A cewar wata sanarwar da kulob ɗin ya fitar a ranar Litinin, Massimiliano Brambilla, wanda...
    Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas, ta bayyana cewa duk da jajircewar kungiyar na mutunta yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma da ita, firaministan gwamnatin Isra’ila yana kokarin karya sharuddanta. Hazem Qassem, kakakin kungiyar, ya ce “Mun yi wa masu shiga tsakani bayani kan cikas din da ke hana neman gawarwakin fursunonin Isra’ila kuma mun nemi...
    Kasar Rasha ta gargadi Faransa game da tura sojoji zuwa Ukraine don taimakawa Kyiv. Hukumar leken asiri ta Rasha (SVR) ta bankado cewa Faransa ta shirya aika Sojoji 2,000 zuwa Ukraine. Ma’aikatar Harkokin Wajen Rasha ta kira wannan yiwuwar “abin da ba za a yarda da shi ba,” tana mai gargadin hadarin dake tattare da...
      Idan muka kwatanta da kasar Sin, sabanin yawan albarkatun da Afrika ke da su kamar na kasar noma, ita Sin kasa da kaso 9 kadai take da shi, amma kuma tana bayar da gagagrumar gudunmawa a duniya, inda take tsaye da kafarta wajen ciyar da al’ummarta, har ma ta bayar da gudunmawa ga kasashe...
    Shugaba Tinubu, a cikin wasikarsa, ya ce, an yi nadin ne bisa tanadin Sashe na 18(1) na Dokar Sojojin Kasa, Cap A20, ta Dokokin Tarayyar Nijeriya, 2004.   Ya bukaci Majalisar Dattawa da ta yi la’akari da wannan bukatar don gaggawa kan tabbatar da daidaito mai inganci a cikin tsarin tsaron kasar. ShareTweetSendShare MASU ALAKA...
    Rundunar ’yan sandan Jigawa ta raba tallafin Naira miliyan 31 ga iyalan jami’ai 59 da suka rasa rayukansu a bakin aiki. Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, SP Lawan Shiisu Adam, ya fitar, inda ya bayyana cewa wannan mataki na nuna irin ɗawainiyar da rundunar ‘yan sandan...
    Bugu da kari, an shata wasu manyan manufofi game da shirin shekaru biyar-biyar na 15 da suka hada da gagarumar zurfafawa wajen samun ci gaba mai inganci, da ingantacciyar habaka dogaro da kai da karfin ci gaban kimiyya da fasaha, da cimma sabbin nasarori a cikin kara zurfafa gyare-gyare a gida gaba daya, da samun...
    Majalisar Dattawa za ta gudanar da zaman tantance manyan hafsoshin tsaron ƙasar a gobe Laraba waɗanda Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya naɗa kwanan nan. Shugaba Tinubu ya aike da sunayen sabbin hafsoshin zuwa majalisar ne domin tantancewa da amincewa da su, kamar yadda kundin tsarin mulkin ƙasar ya tanada. Rikicin adawa da cin zaben Shugaba...
    Messi, wanda ya lashe kyautar Ballon d’Or sau takwas, zai cika shekaru 39 a watan Yuni mai zuwa. Ya ce yana jin daɗin zama a Miami bayan shekaru masu yawa da ya shafe a Barcelona da kuma lokacin da ya yi a Paris Saint-Germain. Messi ya buga wasanni 195 tare da Argentina, inda ya zura...
    Rikici na kara bazuwa a Jamhuriyar Kamaru kwana guda bayan Kotun Kolin  ta tabbatar da Shugaba Paul Biya a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa mai cike da takaddama. Dan takarar jam’iyyar adawa, Issa Tchiroma Bakary, ta sake bayyana cewa ba zai amince da sakamakon zaben ba, yana mai cewa “zaben ba sahihi ba...
    Ya ba da shawarar a mayar da wajen ayyukan al’umma kamar filin motsa jiki ko ɗakin taro maimakon a sayar shi. Kiru, ya buƙaci gwamnan jihar da ya ɗauki alhakin kura-kuran da aka tafka a wajen wannan aikin, tare da tabbatar da cewa irin wannan kuskure ba zai sake faruwa ba a nan gaba, musamman...
    Mazauna ƙauyukan Bazar da makwabtansu a Karamar Hukumar Yabo ta Jihar Sakkwato, sun koka cewa ’yan bindiga sun kakaba musu harajin Naira miliyan 15 tare da barazanar kai sabbin hare-hare idan ba a biya ba. Wadannan ƙauyuka suna yankin Mazabar Sanatan Kudu ta Kudu, inda tsohon gwamnan jihar, Sanata Aminu Waziri Tambuwal, ke wakilta. Wani...
    Al’ummar Unguwar Filin Samji da ke garin Katsina sun buƙaci hukumomi su tabbatar da adalci, bisan zargin da ake wa jami’an Hisbah da na Rundunar Tsaron Al’umma na gwamnatin jihar (C-Watch) da harbin mutane da kuma lakaɗa musu duka ba tare da dalili ba. Wata matar aure mai suna Khadija Hamisu Wada ta samu raunuka...
    Hukumar Yaƙi da Masu Karya Tattalin Arziki (EFCC) ta bayyana damuwa kan yadda wasu ’yan kasuwar duwatsu masu tsada a Najeriya ke cikin wadanda ake zargin suna taimakawa wajen daukar nauyin ta’addanci a sassan Najeriya. Hukumar ta gargaɗe su da masu hakar ma’adinai da su guji zama hanyar safarar kuɗaɗen haram ko tallafa wa ƙungiyoyin...
    Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Haɗin kai a tsakanin kasashen yankin Gabas ta Tsakiya ba zaɓi ba ne, amma dole ne Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya jaddada cewa: Hadin kai da hadin gwiwar kasashen yankin Gabas ta Tsakiya a cikin tsarin Kungiyar Hadin Kan Tattalin Arziki (ECO) ba wani zaɓi ne na siyasa...
    Hukumar Yaƙi da Masu Karya Tattalin Arziki (EFCC) ta bayyana damuwa kan yadda wasu ’yan kasuwar duwatsu masu tsada a Najeriya ke cikin wadanda ake zargin suna taimakawa wajen daukar nauyin ta’addanci a sassan kasar. Hukumar ta gargaɗe su da masu hakar ma’adinai da su guji zama hanyar safarar kuɗaɗen haram ko tallafa wa ƙungiyoyin...
    Mataimakin Ministan Harkokin Waje kan Harkokin Siyasa na Iran ya bayyana cewa: Iran ta yi imani da diflomasiyya amma ta yi watsi da duk wata tattaunawar dole da aka tilasta mata Mataimakin Ministan Harkokin Waje na Harkokin Siyasa na Iran ya jaddada cewa: Iran ta yi imani da diflomasiyya, amma ta yi watsi da duk...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Tushen haɗin gwiwar Iran da Hukumar Kula da Makamashin Nukiliya shine dokar da Majalisar Dokoki ta zartar Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Isma’il Baqa’i ya jaddada cewa: Tushen hadin gwiwar Jamhuriyar Musulunci ta Iran da Hukumar Makamashin Nukiliya ta Duniya (IAEA) shine dokar da Majalisar Shawarar Musulunci...
    Sojojin mamayar Isra’ila sun kai hare-haren bama-bamai da dama a gabashin Zirin Gaza Sojojin mamayar Isra’ila sun yi rusa bama-bamai kan gidaje da dama a gabashin Zirin Gaza da safiyar yau Talata, tare da harba manyan bindigogi a yankuna daban-daban, a matsayin ci gaba da keta yarjejeniyar tsagaita wuta. Cibiyar Bayanai ta Falasdinawa ta ruwaito...
    Babban hafsan hafsoshin Sojin Sudan kuma shugaban majalisar gudanar da mulkin kasar ya bayyana cewa; Rundunar sojin kasar ta bar birnin El Fasher ne domin gujewa “kisan fararen hula” da dakarun kai daukin gaggawa ke yi Shugaban Majalisar Gudanar da Mulkin Soja ta Sudan, Abdel Fattah al-Burhan, ya ce: shugabannin sojoji sun yanke shawarar barin...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Zargin Almundahana: An Ɗage Shari’ar  Ganduje Da Matarsa Saboda Rashin Miƙa Takardu October 28, 2025 Manyan Labarai Sojoji Sun Kashe Masu Yi Wa ISWAP 4 Safarar Makamai A Borno October 28, 2025 Manyan Labarai APC Ta Yi Barazanar Dakatar Duk Kwamishinan Da Bai Sanya Irin Hular Tinubu Ba...
    Jami’an tsaron hadin gwiwar sun kashe fiye da ’yan bindiga 80 da suka yi yunƙurin kutsawa Jihar Kebbi ta iyakarta da Zamfara. Rahotanni sun bayyana cewa, sojojin sama da na ƙasa sun gudanar da sumame a dajin Makuku, inda suka yi ruwan wuta kan sansanonin ’yan ta’adda, suka kuma kashe da dama daga cikinsu. Dakarun...
    An ɗage sauraron shari’ar tsohon Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, matarsa Hafsat, da wasu mutum shida a ranar Litinin bayan sun kasa miƙa takardun da ake buƙata a kotu. Gwamnatin Jihar Kano ta gurfanar da su bisa tuhume-tuhume 11 da suka shafi cin hanci, haɗa baki wajen yin laifi, da karkatar da kuɗaɗen gwamnati...
    Iran, a matsayinta na ƙasa mai wayewa da wayewa, ta kasance mai himma wajen haɓaka zaman lafiya da tsaro a duniya, in ji Kakakin Ma’aikatar Harkokin Waje Esmail Baqaei a ranar Litinin a gefen wani biki na cika shekaru 80 da kafa Majalisar Dinkin Duniya a Tehran. A cewar Pars Today, Baqaei ya ƙara da...
    Cibiyar dake kula da ilimin kasa ta kasar Jamus ( GFZ) ta sanar da cewa, girgizar kasar da ta faru a Turkiya ta kai daraja 6.1 a ma’aunin motsin karkashin kasa. Girgizar dai ta faru ne da misalin 10;48 na daren jiya a nisan kilo mita 10 karkashin kasa. An yi karar girgizar kasar a...
    Sakamakon da aka fitar a jiya Litinin ya bayyana cewa, Alassan Outara dan shekaru 83  ya lashe zaben a kaso 89.77 na jumillar shugaban. Mutum na biyu wanda yake bin Outara a baya shi ne tsohon ministan kasuwanci Jean-Lous Billon da kaso 3%, sai kuma mai dakin tsohon shugaban kasar Simone Gbango da ta sami...
    Kungiyar Dakarun Kai Daukin Gaggawa ( RSF) ta kasar Sudan ta sanar da kwace iko da birnin El-Fashar, da nan ne tungarta ta karshe a yankin Darfur. Hakan dai ya haddasa matsalar dangane da ayyukan jin kai da ceto saboda yadda aka rutsa da dudun mutane a cikin birnin. A jiya Litinin ne dai rundunar...
    Mai bai wa jagoran juyin musulunci na Iran shawara akan harkokin siyasar kasa da kasa Dr.  Ali Akbar Wilayati ya ce; Da akwai kasashe uku a cikin Asiya wadanda suke da ‘yanci da su ne Iran, China da Rasha, kuma suna taka rawa domin samar da sabon tsarin tafiyar da duniya. Dr. Wilayati ya bayyana...
    Rikicin Jam’iyyar ADC na Jihar Kaduna ya ɗauki sabon salo, bayan da uwar jam’iyyar ta nada tsohuwar Ministar Kuɗi, Sanata Nenadi Usman, a matsayin Shugabar Hadakar Jam’iyyar a jihar. Haka kuma jam’iyyar ta nada tsohon Kwamishinan Kudi na Jihar Kaduna, Bashir Sa’idu, na hannun daman tsohon gwamnan jihar, Mallam Nasir El-Rufa’i, a matsayin Mataimakin Shugaban...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Gwamnan Bauchi Ya Tabbatar Da Burgediya Janar Yake a Matsayin Sarkin Ƙabilar Sayawa October 27, 2025 Manyan Labarai Shugaba Tinubu Ya Gana Da Sabbin Hafsoshin Tsaro October 27, 2025 Manyan Labarai Sojoji Sun Kashe ‘Yan ta’adda 10, Sun Ƙwato Makamai A Borno October 27, 2025
    An kira wani taron musamman a Amurka na tattaunawa tsakanin kasa da kasa mai taken “Kirkire-kirkire da budadden kasuwanci, da more damammakin ci gaba” a birnin Washington na Amurka. Babban rukunin gidan rediyo da talibijin na kasar Sin wato CMG da ofishin jakadancin Sin dake Amurka ne suka gabatar da taron cikin hadin gwiwa. Kusan...
    Shugaba Alassane Ouattara, ya sake lashe zaɓen shugabancin ƙasar Ivory Coast wanda ya ba shi sabon wa’adin mulki a karo na huɗu. Ouattara mai shekaru 83, ya samu kashi 89.77 cikin 100 na ƙuri’un da aka kaɗa, kamar yadda hukumar zaɓe ta ƙasa ta tabbatar a ranar Litinin. Tinubu ya gana da sabbin hafsoshin tsaro...
    Wani rahoto da hukumar kula da kididdiga ta kasar Sin (NBS) ta fitar a yau Litinin ya nuna cewa, ribar da manyan masana’antun kasar Sin suka samu cikin watanni tara na farkon shekarar 2025 da muke ciki, ta karu da kashi 3.2 cikin dari. A cewar hukumar ta NBS, masana’antun da ke samun kudaden shiga...
    Da yake miƙa takardar naɗin, Sakataren Gwamnatin Jihar Bauchi, Alhaji Aminu Hammayo, ya taya sabon Sarkin murna, tare da kira gare shi da ya bi dokokin gwamnati da na ƙasa wajen gudanar da mulkinsa. Ya ce gwamnatin jihar ta tabbatar da naɗin ne bayan ta binciki cancanta, da halayya, da tarihin mulki na sabon Gung...
    Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi wata ganawar sirri da sabbin hafsoshin tsaron Najeriya a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja. Sai dai babu wani cikakken bayani kan dalilin ko maudu’in wannan taron, wanda shi ne karo na farko bayan sauya manyan hafsoshin tsaron Najeriya da shugaban ƙasar ya yi. An kashe wasu makiyaya 10...
    A yau Litinin 27 ga Oktoba, kungiyar jigilar kayayyaki da sayayya ta kasar Sin ta ba da rahoton bayanan ayyukan jigilar kayayyakin dake bukatar kankara a watannin Yuni da Yuli da Agustan bana. Bayanan na nuna cewa, a karkashin jagorar manufofi da bukatun kasuwa, aikin jigilar kayayyakin dake bukatar kankara ya nuna samun ci gaba...
    A Ivory Coast sakamakon wucin gadi na zaben shugaban ya nuna cewa  Shugaba Alassane Ouattara, wanda ke jagorantar kasar tun 2011, na kan lashe zaben shugaban kasa na ranar 25 ga Oktoba, 2025 da gagarumin rinjaye. Rahotanni sun ce Ouatara ya samu kashi 89.77% na ƙuri’un da aka kaɗa, bisa ga sakamakon wucin gadi da...
    Aƙalla makiyaya goma aka kashe a wani hari da aka kai wa Fulani makiyaya a wata ruga da ke yankin Tilli a ƙaramar hukumar Bunza ta Jihar Kebbi. Majiyarmu ta ce harin wanda ya yi kama da na ramuwar gayya na zuwa ne bayan kashe wani ɗan sa-kai a yankin. An rufe makarantu saboda ƙarancin...
    Firaministan kasar Sin Li Qiang, ya ce kasar Sin a shirye take ta yi aiki wajen kare tsarin cinikayya tsakanin mabanbantan sassa bisa matukar himma, tare da kasancewa cikin shirin aiki tare da dukkanin sassa, don kare martabar cudanyar mabanbantan sassa bisa gaskiya. Li, ya yi tsokacin ne cikin jawabinsa a yau Litinin, yayin taron...
    A yau Litinin shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya halarci nune-nune da aka gudanar a babban gidan adana kayan tarihi na “Palace Museum”, albarkacin cika shekaru 100 da kafuwar gidan tarihin. Xi, wanda shi ne babban sakataren kwamitin kolin JKS, kana shugaban hukumar zartarwar rundunar sojojin kasar Sin, ya yi kira da a kara babbar...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Sojoji Sun Kashe ‘Yan ta’adda 10, Sun Ƙwato Makamai A Borno October 27, 2025 Manyan Labarai Matatar Dangote Za Ta Faɗaɗa Ƙarfin Aiki Zuwa Ganga Miliyan 1.4 Kullum October 26, 2025 Labarai “Ba Gudu Ba Ja Da Baya Game Da Tsarin “Call-up system” A NPA” October 26,...
    Wata hukumar shige da fice da kwastam ta Amurka (ICE) ta tsare wani dan jarida mai sharhi kan harkokin siyasa, Sami Hamdi, a filin jirgin sama na San Francisco saboda sukar da ya yi wa Isra’ila a yayin wani rangadin jawabai da ya yi a Amurka. A wata sanarwa da ta fitar, kungiyar CAIR ta...
    Wata kuri’ar jin ra’ayin jama’a ta Ifopa faransa, ta nuna cewa kasha 84 cikin dari na ‘yan kasar basu gamsu ba da Emmanuel Macron a matsayin shugaban kasa. A cewar kuma wannan binciken da aka yi aka kuma wallafa a jaridar le Journal du Dimanche, kashi 16% ne kawai na mutanen Faransa suka “gamsu” da...
    Jamhuriyar Musulinci ta Iran, ta bukaci Majalisar Dinkin Duniya da ta nisanci nuna bangaranci a cikin ayyukanta musamman game da yadda Amurka da Isra’ila ke keta dokokin kasa da kasa. Da yake bayyana hakan mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Iran Esmail Baghai ya yi kira ga Majalisar Dinkin Duniya da ta zama wakiliya...
    Majalisar tsarin mulki a jamhuriyar Kamaru ta sanar da Paul Biya mai shekara 92 a matsayin wanda ya lashe zaben shugabancin kasar da aka gudanar a ranar 12 ga wata. Mista Biya ya lashe zaben da kashi 53.66% na kuri’un da aka kada, wanda hakan ya ba shi damar shugabancin kasar a wa’adin mulki na...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Ra'ayi Riga Me Ya Sa Kasar Sin Ke Son Ganin Ci Gaban Kasashen Afirka? October 27, 2025 Labarai Ba Za A Samu Ƙarancin Man Fetur A Lokutan Bukukuwan Ƙarshen Shekara Ba – Dangote  October 27, 2025 Labarai An Zaɓi Birgediya Janar Yake A Matsayin Sarkin Sayawa Na Farko Duk...
    Sa’an nan matakin da kasar Sin ke dauka yanzu, shi ne jagorantar manyan gyare-gyare kan tsare-tsaren samar da kayayyaki na duniya, ta yadda ita da dukkan kasashe masu tasowa za su samu damar inganta tsare-tsarensu na tattalin arziki, musamman ma a bangaren masana’antu. Dangane da batun, babbar darektar hukumar kasuwanci ta duniya (WTO) Ngozi Okonjo-Iweala,...
    An kammala bikin bayar da Kyautar Jaruman Indomie karo na 17, inda aka karrama matasan da suka nuna hazaƙa da jarumtaka, kuma suka zama jakadun Najeriya a fannoni daban-daban. Wannan gagarumin biki ya gudana a birnin Legas a ranar 16 ga Oktoba, 2025, ƙarƙashin shirye-shiryen kamfanin Dufil Prima Foods, masu samar da Indomie Instant Noodles,...