2025-08-01@15:14:00 GMT
إجمالي نتائج البحث: 11
«Haɗari»:
Wani mutum ya rasu yayin da yake ƙoƙarin raba wani mutum da matarsa da fada a yankin Babban Birnin Tarayya. Da farko mutumin ya faɗi ne a sume kafin daga bisani rai ya yi halinsa a yankin Dogon-Ruwa da ke Ƙaramar Hukumar Abaji. Wani ganau, Barnabas Yakubu, ya ce lamarin ya faru ne a ranar...
Kimanin mutum 16 sun rasa rayukansu a ranar Litinin bayan wani jirgin rundunar sojin sama ta Bangladesh ya fadi a cikin harabar wata makaranta a Dhaka, babban birnin kasar. Haɗarin jirgin saman yaƙin ya kuma yi sanadin jikkatar gommai, wanda ya kasance guda daga cikin haɗɗura masu muni da ƙasar ta gani a baya-bayan nan...
A ɗaya ɓangaren kuma Fita zuwa wani yanki daban da ba naka a halin yanzu, yana da nasa fa’idar. Domin kuwa, na ziyarci wasu jihohi uku kwanan nan; waxanda labarai a kansu babu daxin ji. Jihohin su ne, Delta, Inugu da kuma Zamfara, waxanda galibi labaransu marasa daxi ne ta fuskar siyasa, ta’addanci da sauran...
Wani haɗarin mota da ya faru a yau Lahadi a hanyar Lokoja-Obajana ya yi sanadiyar mutuwar mutane 19, yayin da wasu 8 suka jikkata. Sakataren FRSC na jihar, Kumar Tsukwam, ya tabbatar da cewa haɗarin ya faru ne sakamakon gudun da ya wuce ƙima. Mota bas da wata babbar mota sun yi karo da juna...
Fastan nan mai suna Rev. Azzaman David, shugaban majami’ar The King Worship Chapel da ke Kaduna, ya rasu a wani hatsarin mota a ranar Asabar yayin dawowarsa daga Makurdi, jihar Benue zuwa Kaduna. Shugaban ƙungiyar Kiristoci ta Nijeriya (CAN) na Jihohin Arewa 19 da FCT, Rev. John Joseph Hayab, ya tabbatar da mutuwar fastan, inda...
Rayukan al’umma gami da dukiya musamman na ababen hawa na ci gaba da salwanta a Mahadar hanya ta yankin Tipper-garage da ke Dutse-Baupma, da ke kan titin da ya tashi daga garin Dutsen-Alhaji ya nufi garin Bwari, a yankin Birnin Tarayya Abuja. Titin da ke mastayin tagwaye ya haɗa yankin da garin Jere da ke...
A wani hatsarin mota da ya faru a hanyar Malumfashi-Kafur a Jihar Katsina, mutane tara sun rasu yayin da wasu 11 suka jikkata. Hatsarin dai ya shafi wata babbar motar bas da ke ɗauke da fasinjoji 20. Aliyu Ma’aji, Kwamandan Hukumar Kiyaye Haɗɗura ta ƙasa (FRSC) a jihar, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata...
Aƙalla mutum 12 — ciki har da mata huɗu da maza takwas — sun riga mu gidan gaskiya a sanadiyyar wani mummunan haɗarin mota da ya auku a kan hanyar Lapai zuwa Agaie da ke Jihar Neja. Wani da lamarin na safiyar wannan Asabar ɗin ya faru a kan idonsa, ya shaida wa Aminiya cewa...
Hukumomin Jami’ar Tarayya da ke Lokoja a Jihar Kogi, sun rufe jami’ar har zuwa wani lokaci domin daƙile ci gaba da asarar rayuka da dukiya. Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun magatakarda kuma sakatariyar majalisar Jami’ar, Dokta Rebecca Aimiohu Okojie, a ranar Alhamis kuma ta bayyanawa manema labarai...
Hukumar kiyaye haɗɗura ta ƙasa (FRSC) reshen Jihar Kano ta tabbatar da wani mummunan haɗarin mota da ya yi sanadin mutuwar mutane 23 tare da jikkata wasu 48. Mummunan haɗarin wanda ya faru a ranar 13 ga Fabrairu, 2025, da misalin ƙarfe 9:50 na dare a ƙarƙashin gadar Muhammadu Buhari da ke kan hanyar Kano...
Shugaban kungiyar dalibai ta makarantar (SUG), Comrade Haruna Umar, ya bayyana cewa marigayiya tana cikin shirye-shiryen kammala rajistar ta a makaranta ne ma kafin rasuwarta, kana ya roƙi ɗalibai da su kasance cikin hakuri da lumana, yana mai tabbatar da cewa hukumar makaranta da ta tsaro suna iya ƙoƙarinsu na ɗaukar matakan da suka dace...