Aminiya:
2025-09-20@13:44:52 GMT

DAGA LARABA: Ɓoyayyun Dalilan Da ke Sa Faɗuwa Jarabawa A Najeriya

Published: 7th, May 2025 GMT

More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba

Duk shekara, dalibai kan rubuta jarabawa a matakai daban-daban na makarantu daban-daban.

Ɗaya daga cikin nau’ukan jarabawa da ɗaliban Najeriya suke yi ita ce Jarabawar Neman Shiga Manyan Makarantu, wato UTME.

Kamar kowace shekara, a bana ma ɗalibai sun rubuta wannan jarabawa kuma a cewar Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Manyan Makarantu (JAMB), kashi 78.

5 cikin 100 na waɗanda suka rubuta jarabawar sun samu ƙasa da maki 200.

Ko waɗanne dalilai ne suke kawo faɗuwa jarabawa a Najeriya?

NAJERIYA A YAU: Me Ya Sa ‘Yan Gwagwarmaya Ke Shiga Tasku A Najeriya? DAGA LARABA: Asarar Da Hausawa Ke Tafkawa Sakamakon Bacewar Tatsuniya

Wannan shi ne batun da shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi ƙoƙarin amsawa.

Domin sauke shirin, latsa nan

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Faɗuwar ɗalibai jarabawa

এছাড়াও পড়ুন:

Amurka ta hau kujerar-na-ƙi kan buƙatar MDD ta tsagaita wuta a Gaza

Ƙasar Amurka ta hau kujerar-na-ƙi kan wani ƙudurin Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da ke neman a dakatar da yaki a Gaza nan take kuma ba tare da sharaɗi ba.

Daftarin kudurin na majalisar ya kuma buƙaci Isra’ila ta cire duk wani takunkumi kan kai agaji ga yankin na Falasɗinawa.

Wani ya sace munduwar Fir’auna a gidan tarihin Masar Kasar Albania ta nada mutum-mutumi a matsayin minista

Kudurin, wanda ƙasashe 10 da aka zaɓa daga cikin mambobi 15 na majalisar suka tsara, ya kuma buƙaci a saki dukkan fursunonin aka yi garkuwa da su daga hannun Hamas da sauran kungiyoyi ba tare da sharadi ba, cikin mutunci da girmamawa.

Kudurin dai ya samu goyon bayan ƙasashe 14, sai dai Amurka ta yi amfani da karfin tuwo wajen kin amincewa da shi.

Wannan shi ne karo na shida da Amurka ke hawa kujerar-na-ki kan batun yaki tsakanin Isra’ila da Hamas tun kusan shekaru biyu da suka gabata.

Jakadiyar Denmark a Majalisar Dinkin Duniya, Christina Markus Lassen, kafin ta kada kuri’arta, ta ce, “An tabbatar da yunwa a Gaza, ba hasashe ba ne, ba jita-jita ba, an tabbatar da ita.”

Ta ƙara da cewa: “Isra’ila ta faɗaɗa hare-haren soji a birnin Gaza, lamarin da ke ƙara jefa fararen hula cikin wahala. Wannan mummunan yanayi da gazawar jin kai ne ya tilasta mu daukar mataki a yau.”

Wani rahoto daga hukumar da ke sa ido kan yunwa a duniya ya tabbatar da cewa birnin Gaza da kewaye na fama da yunwa, kuma akwai yiwuwar ta yadu.

Amurka na da al’adar kare Isra’ila a Majalisar Dinkin Duniya. Sai dai a makon da ya gabata, a wani mataki da ba kasafai ake gani ba, ta goyi bayan wata sanarwa daga majalisar da ke sukar hare-haren da aka kai Qatar, duk da cewa ba a ambaci Isra’ila a cikin rubutun ba.

Wannan mataki ya nuna goyon bayan Shugaban Amurka Donald Trump ga umarnin da Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya bayar.

Sai dai hawa kujerar-na-kin da Amurka ta yi a ranar Alhamis ya sake tabbatar da cewa Washington na ci gaba da ba Isra’ila kariya ta diflomasiyya.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Makarantun Da Ba Ƙwararrun Malamai Za Su Rasa Zama Cibiyar Rubuta Jarrabawar NECO
  • Takari: Rayuwar baƙin haure ’yan Najeriya mazauna Saudiyya
  • Matasan Nijeriya sun koma yin ci-rani a Nijar da Chadi
  • NAJERIYA A YAU: Ayyukan Da Fasahar AI Za Ta Raba Mutane Da Su Nan Ba Da Jimawa Ba
  • Akasarin masu kai mana hare-hare daga jihohin da suka kewaye mu suke – Gwamnatin Filato
  • Najeriya Ta Shirya Karɓar Wasannin Kungiyar Kasashen Renon Ingila A 2030– Tinubu
  • Amurka ta hau kujerar-na-ƙi kan buƙatar MDD ta tsagaita wuta a Gaza
  • Karamar Hukumar Malam Madori Ta Horar Da Mata Kare Kai Daga Cututtukan Mahaifa
  • Kuri’ar Jin Ra’ayin Jama’a Ta CGTN: Baje Kolin Sin Da ASEAN Ya Fadada Matsayar Bai Daya Ta Cudanyar Sassa Daban Daban
  • An Bude Dandalin Tattauna Batutuwan Tsaro Na Xiangshan Karo Na 12 A Beijing