Za mu ci gaba da aikin haƙo ɗanyen mai a Arewa —NNPCL
Published: 12th, May 2025 GMT
Kamfanin Mai na Kasa (NNPCL) ya bayyana cewa zai ci gaba da aikin haƙa danyen mai a Arewa da ke yankin Kolmani.
Shugaban NNPCL, Bayo Ojulari ne ya sanar da aniyar kamfanin na ci gaba da aikin haƙar mai a yankunan arewa da gwamnatin Buhari da ta gabata ta fara.
Bayo Ojulari ya kuma addada aniyar NNPCL na kammala aikin bututun iskar gas da ya taso daga Ajaokuta a Jihar Kogi ya bi ta Abuja da Kaduna zuwa Kano (AKK).
A zantawarsa da kafar yaɗa labarai ta BBC, Injiniya Bayo ya ce, Za mu ci gaba da aikin haƙo mai a Kolmani da sauran wurare. Bayan aikin haƙo man, za mu kuma tabbatar da cewa mun gama aikin bututun man gas daga Ajaokuta zuwa Kano,” in ji shi.
An kama ɗan daba mai yin fashi a cikin shigar mata a Kano Boko Haram ta ƙwace makaman sojoji na tiriliyoyin naira —MajalisaA cewarsa, ayyukan haƙar man da na bututun iskar gas ɗin AKK za su taimaka wajen farfaɗo da kamfanonin da aka rufe a baya domin su ci gaba da aiki sannan a buɗe wasu sababbi.
“Wannan zai amfanar da yankin Arewa ta yadda kowa zai ci moriyarsa saboda za a samu bunƙasar arziki,” a cewarsa.
Game da ce-ce-ku-ce da ya biyo bayan naɗa, inda ake zargin Shugaba Tinubu da fifita ’yan yankin Kudu wajen rabon mukamai a gwamnatinsa, shugaban na NNPC ya ce, shi ma ɗan Arewa ne, kuma ya yi maganganu a lokacin da aka sanar da naɗa shi.
Don haka ya buƙaci al’ummar Arewa da ma ƙasar baki ɗaya da su ba shi goyon baya, kuma su taimaka masa da addu’a domin ya samu nasarar ciyar da yankin da ma ƙasar gaba.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
An buɗe wasu makarantu domin ci gaba da jarawaba a Katsina
Hukumar kula da makarantun firamare da sakandare ta Jihar Katsina ta sanar da sake buɗe wasu makarantu domin ci gaba da jarabawar zangon farko na shekarar karatu.
A wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na hukumar, Sani Danjuma Suleman, ya fitar a madadin Shugaban hukumar, ta ce makarantun firamare, sakandiren je-ka-ka-dawo da kuma makarantu masu zaman kansu za su buɗe daga yau Talata domin ci gaba da jarabawar zangon farko.
Sanarwar ta ƙara da cewa, sauran makarantun kwana za su ci gaba da kasancewa a rufe har sai lokacin da hali ya ba da dama.
Aminiya ta ruwaito cewa, a bayan nan ne Gwamnatin Katsina ta rufe makarantun bayan ƙaruwar hare-haren sace ɗalibai da masu garkuwa da mutane suka sake farfaɗowa da su a wasu yankuna.
Gwamnatin ta ce ta ɗauki matakin ne da nufin daƙile matsalar tsaro da kuma sa ido a kan al’amura.
A ƙarshe, hukumar ta roƙi haɗin kan iyaye da masu kula da ɗalibai domin su ci gaba da ba wa shirin goyon baya tare da ƙarfafa ɗaliban su dage da karatu wajen rubuta jarabawar da suke yi.