2025-05-08@11:33:14 GMT
إجمالي نتائج البحث: 3560
«kudaden waje»:
Dakarun Birget na 6 na Sojin Najeriya da ke Jalingo Jihar Taraba sun cafke wasu mutane huɗu da ake zargin cewa ’yan ta’adda ne. Kama waɗanda ake zargin ya biyo bayan wani samame da sojojin suka gudanar a ranar 7 ga Mayu, 2025 a Ƙaramar Hukumar Arɗo-Kola da ke jihar. Kakakin Rundunar, Kyaftin Oni Olubodunde, ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a garin Jalingo. Ya bayyana cewa rundunar ta sami kiran gaggawa dangane da shigowar wasu mutane ɗauke da makamai a yankin. ’Yan sanda sun kama harsasai 500 a Filato Jami’an tsaro na ba da gudunmawar aikata miyagun laifuka a Nijeriya — Zulum Kyaftin Oni ya ƙara da cewa dakarun sun yi gaggawar...
Amurka ta matsa wa gwamnatocin wasu ƙasashe da Shugaba Donald Trump ya ƙaƙaba musu haraji su amince da kamfanin intanet na Starlink mallakin Elon Musk a ƙasashensu. Elon Musk shi ne mai kuɗin duniya kuma babban makusanci ne ga Shugaba Donald Trump. Jaridar Washington Post ce ta ruwaito hakan a ranar Laraba, tana mai ambaton sakonnin waya na Ma’aikatar Harkokin Waje. Sakonnin sun nuna yadda ofishin Jakadancin Amurka da ma’aikatar suka matsa wa ƙasashe don su kawar da duk wata cikas ga kamfanonin tauraron dan Adam, yana mai ambaton kamfanin Starlink da sunanta, kamar yadda jaridar Post ta ruwaito. Takardun ba su nuna cewa gwamnatin Trump ta buƙaci a ba da fifiko ga Starlink a musayar rage haraji ba, kamar...
Shugaban kasar Sin, Xi Jinping ya aike da wasikar taya murna ga taron musayar al’adu da cudanyar al’umma da aka shirya domin murnar cika shekaru 80 da samun nasarar yakin turjiya da jama’ar kasar Sin suka yi a kan zaluncin Japan da kuma kazamin yakin ceton kasa na tsohuwar tarayyar Soviet. A cikin sakon nasa, Xi ya yi nuni da cewa, shekaru 80 da suka gabata, al’ummomin kasar Sin da na kasar Rasha sun bayar da gudummawa mai tarihi da ba za a taba mantawa da ita ba wajen samun nasarar yaki da zaluncin danniya a duniya, tare da kulla kakkarfar alaka da ba za a iya kassarawa ba ta hanyar sadaukar da jini, wadda ta kafa tubulin raya dangantakar...
’Yan sanda sun gano harsasai guda 500 a wata maɓoyar masu aikata laifuka da ke kusa da hanyar Bauchi a Ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa a Jihar Filato. Kwamishinan ’yan sandan jihar, Emmanuel Adesina, ya ce an gano harsasan ne ta hanyar rahotannin sirri, inda ya bayyana hakan a matsayin babbar nasara a yaƙi da aikata laifuka a jihar. Kwamishinan ya ci gaba da bayanin cewa an gano harsasan ne bayan wani kisan kai da ya faru a yankin, inda aka kashe wani da ba a gane ko wanene ba. “Bayan samun rahoton faruwar lamarin, nan take muka fara gudanar da bincike domin gano yanayin da ya kai ga mutuwar wanda aka kashe. An kwantar da kishiyoyi a asibiti bayan...
An kwantar da wasu matan aure kishiyoyin juna a asibiti bayan da suka sha maganin kara sha’awa domin burge mijinsu bayan ya auro mata ta uku. Kishiyoyin biyu da ke yankin Dakwa a Abuja sun sha maganin gargajiyan, wanda aka fi sani da kayan mata ne, kwana uku bayan amaryar da mijinsu ya auro ta tare. Da take tabbatar da faruwar lamarin, mijin nasu ya ce bayan kai su asibiti ne aka yi musu gwaji aka gano cewa wasu gaɓoɓinsu sun samu matsala, wanda ake zargin maganin da suka sha ne ya haddasa. Ya ce, “ina gidan amarya aka kira ni cewa matana ba su da lafiya, inda na je na samu suna birgima cewa cikinsu na ciwo. Sai na...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
An kuma yi kira ga jama’a da su ci gaba da ba da bayanai masu aminci don taimakawa wajen inganta tsaro a jihar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp

Iran Ta Yi Tsokaci Kan Jita-Jitar Da Ake Yadawa Cewa: Shugaban Kasar Iran Zai Gana Da Shugaban Amurka
Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta yi tsokaci kan jita-jitar cewa: Shugaban kasar Iran zai gana da shugaban kasar Amurka Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Isma’il Baqa’i ya yi watsi da jita-jitar da ake yadawa game da batun cewa shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian zai yi wata ganawa da shugaban Amurka Donald Trump a mako mai zuwa, da rashin gamsuwar bangaren Amurka da Iran da shiga tsakanin masarautar Oman, da kuma cewa Iran ta gabatar da shawarar gudanar da shawarwari kai tsaye da Amurka, da sauran da’awar karya a matsayin batutuwa na jita-jita maras asali da tushe. Dangane da wata tambaya game da jerin jita-jita da ake yadawa a kafafen yada labarai game da matsayin tattaunawar da ake yi tsakanin Iran...
Kakakin gwamnatin kasar Iran ta bayyana cewa: Duk wanda ya canza sunan Tekun Fasha, tabbas ya jahilci tarihin dubban shekaru na Iran Mai magana da yawun gwamnatin Iran Fatimah Mohajerani ta yi tsokaci kan rahotannin da suke cewa: Shugaban Amurka Donald Trump na yunkurin sauya sunan yankin tekun Fasha. Ta jaddada cewa “wadanda ke neman canza sunan Tekun Fasha ba su fahimci tarihin dubban shekaru na Iran ba.” Malama Mohajerani ta rubuta a dandalin na X cewa: Tekun Fasha bai takaita da kasancewa sunan yanki kadai ba, a’a ya zama wani muhimmin bangare na tarihin al’ummar Iran. Ta kara da cewa: “Wadanda ke neman canza sunan ‘Tekun Fasha’ ba su fahimci tarihin Iran na dubban shekaru ba. Wannan yunkuri na...

Yemen Ta Jaddada Cewa: Idan Amurka Ta Kai Mata Hari, Tabbas Yarjejeniyar Kawo Karshen Bude Wuta Tsakaninsu Zata Ruguje
Kasar Yemen ta jaddada cewa: Ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen kai munanan hare-hare kan Amurka idan ta dawo da kai hari a kan kasarta Sojojin Yemen sun sanar da aiwatar da hare-haren soji guda uku kan tashar jiragen sama na Ramon, wani muhimmin wuri ne na makiya yahudawan sahayoniyya, da a wurin akwai jirgin ruwan Amurka Truman mai dauke da dauke da jiragen saman yakin Amurka da kuma wasu kayayyakin yakinta. Majiyar sojojin Yemen ta bayyana a cikin wata sanarwa da ta fitar cewa, sojojin samanta sun gudanar da ayyukan soji guda biyu, na farko a kan filin jirgin saman “Ramon” na haramtacciyar kasar Isra’ila da ke yankin Umm al-Rashrash a kudancin kasar Falasdinu da aka...

Falasdinawa Sun Yi Shahada A Hare-Haren Da Sojojin Isra’il Suka Kai Gidan Cin Abinci Da Kasuwa A Gaza
Falasdinawa da dama ne suka yi shahada tare da jikkata sakamakon hare-haren bama-bamai da sojojin mamayar Isra’ila suka kai kan wani gidan abinci da wata shahararriyar kasuwa a Gaza Akalla Falasdinawa 20 ne aka kashe tare da raunata wasu da dama a jiya Laraba a wani sabon kisan kiyashi da jiragen saman yakin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila suka kai a wani gidan cin abinci na kasar Thailand da wata shahararriyar kasuwa a yammacin birnin Gaza. Sannan suka ci gaba da kai wasu hare-haren wuce gona da iri kan yankunan zirin Gaza a rana ta 213 a jere. Majiyoyi watsa labarai a Gaza sun rawaito cewa: Jiragen saman yakin mamayar Isra’ila sun kai wani hari kai tsaye kan gidan cin abinci...
Fira ministan kasar Siriya ya bayyana cewa: Kasar Siriya zata gudanar da tattaunawa ba na kai tsaye ba da haramtacciyar kasar Isra’ila! Shugaban gwamnatin rikon kwarya na kasar Siriya Abu Mohammed al-Julani ya sanar a jiya Laraba cewa: Kasar Siriya zata gudanar da zaman tattaunawa ba na kai tsaye ba da gwamnatin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila ta hanyar masu shiga tsakani domin kwantar da hankulan al’amura da kuma hana bullar rashin kwanciyar hankali a yankin. Al-Julani ya yi nuni da cewa: “Shisshigin da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ke yi ba bisa ka’ida ba ne, kuma sun bayyana cewa: Siriya ta amince da yarjejeniyar kawo karshen rikici ta shekara ta 1974,” yana mai cewa “Tsarin mulkin kasar Siriya zai tantance ‘yancin...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Duk wanda ya shekara arba’in zuwa sama ya san irin tarbiyyar da ya samu daga wurin iyayensa a da, da irin mu’amalar da ke tsakaninsa da iyaye da kuma irin shaƙuwar da ke tsakanin ’ya’ya da iyaye. A yanzu kuwa, abubuwa sun canza daga yadda aka san su, inda abubuwa suka rincaɓe suka yi wa iyaye yawa. Ɗaya daga cikin manyan sauyin da aka samu shi ne aikin gwamnati ko aikin wata da iyaye mata suke yi a wannan zamani wanda a wasu lokuta ke barazana ga irin kulawar da ’ya’ya suke samu. NAJERIYA A YAU: Me Ya Sa ‘Yan Gwagwarmaya Ke Shiga Tasku A Najeriya? DAGA LARABA: Ɓoyayyun Dalilan Da ke Sa...
“Duk da cewa, ba zan iya yin cikakken bayani dangane da sabbin dabarun da muka dauka ba. Amma mutanen Yobe su kwantar da hankalinsu kuma abubuwa za su inganta.” Har ila yau, ya yi karin haske dangane da wasu muhimman matakan da za a dauka don magance rashin tsaro a jihar, ciki har da tura karin sojoji tare da kayan aikin tsaro. A nasa bangaren, Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya yaba wa COAS kan daukar matakan gaggawa wajen mayar da martani kan hare-haren kwanan nan, sannan ya yi wa sojojin da suka rasu addu’a. Ya jaddada muhimmancin hadin gwiwa tsakanin farar hula da sojoji, inda ya bukaci karfafa hadin gwiwa wajen bayar da bayanan sirri...
Burin Arsenal na lashe gasar UEFA a karon farko a tarihinta ba zai cika a wannan shekarar ba, sakamakon rashin nasarar da ta yi a hannun PSG a wasan zagayen na kusa da na karshe, Arsenal ta buga wasan karshe a UEFA sau daya a shekarar 2006 tsakaninta da Barcelona. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A jiya ne jakadan Sin a Najeriya Yu Dunhai ya gana da ministan harkokin wajen Najeriya Yusuf Tuggar. Jakada Yu ya bayyana cewa, ganawar da ta gudana tsakanin ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi da mista Tuggar a kasar Brazil a baya-bayan nan, ta aike da sako mai karfi cewa, Sin da Najeriya na tsayawa tsayin daka kan bin ra’ayin bangarori daban-daban, da tabbatar da adalci da daidaici. A nasa bangare, minista Tuggar, ya yi kyakkyawan nazari kan yadda huldar dake tsakanin kasashen biyu ke gudana, ya kuma jaddada cewa, Najeriya na fatan karfafa hadin gwiwa da kasar Sin a fannonin cinikayya, zuba jari, da hada-hadar kudi da dai sauransu, da zurfafa tuntubar juna da hadin gwiwa a harkokin...
Bayanai na baya-bayan nan da hukumar kula da harkokin musayar kudaden waje ta kasar Sin ta fitar sun nuna cewa, ya zuwa karshen watan Afrilu, asusun ajiyar kudaden waje na kasar Sin ya kai dalar Amurka biliyan 3281.7, wanda ya karu da dalar Amurka biliyan 41 ko kashi 1.27 bisa dari daga karshen watan Mayu. Kazalika, ma’aunin asusun ajiyar kudaden waje na kasar Sin ya kasance cikin daidaito da sama da dalar Amurka tiriliyan 3.2 na tsawon watanni 17 a jere. Wani jami’in hukumar musayar kudaden waje ta kasar Sin ya bayyana cewa, tattalin arzikin kasar Sin yana cikin kyakkyawan yanayi, tare da nuna juriya da karfi a ci gaban tattalin arziki, wanda hakan zai taimaka wajen tabbatar da...
A cewar sa, wannan bita tana da nufin tantance yadda aka samu cigaba a aiki, da kuma tabbatar da cewa hukumomin da ke ƙarƙashin ma’aikatar suna tafiya daidai da abin da aka ɗora masu a matsayin nauyi. Ya ce: “Muna nan ne don sauraron shugabannin hukumomi domin mu ga yadda suka aiwatar da muhimman abubuwan da muka rattaba hannu a kai. Idan akwai ƙalubale, za mu tattauna su. Idan akwai cikas, za mu duba abin da za mu iya yi domin shawo kansu.” Ministan ya bayyana wannan taro a matsayin hanyar tantance kai kafin a kai tsakiyar wa’adin gwamnatin yanzu. Ya ce: “Ku tuna cewa wannan gwamnati ta fara aiki kusan shekaru biyu da suka gabata. Cikin...
Sumaila, tsohon mataimaki na musamman ga shugaban kasa Muhammadu Buhari kan harkokin majalisar dokokin kasar, ya bayyana jam’iyyar NNPP a matsayin “jam’iyyar da ke da rabe-rabe da tabarbarewar al’amura, inda ya ce, rikicin da ya dabaibaye Jam’iyyar a fili yake babu mai musantawa, wadanda suka hada da shari’o’i a kotuna da dama da kuma gwagwarmayar shugabancin jam’iyyar.” A karshe, Sumaila ya kafa uzuri a karkashin doka ta 42, inda ya bayyana godiyarsa ga takwarorinsa da jama’ar mazabarsa, inda ya yi alkawarin kara zage damtse wajen gudanar da ayyukansa na ‘yan majalisu domin yi wa kasa hidima. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku....
Ayatullah Sayyid Ali Khamnei wanda ya aike da sako zuwa wurin taron tunawa da cikar shekara 100 daga kafuwar cibiyar koyar da addinin musulunci ta “Hauza” wanda aka yi a yau a birnin Kum, anan Iran, ya bayyana cewa: Aiki mafi muhimmanci na makarantar addini shi ne isar da sakon addinin musulunci domin gina sabon ci gaba na addinin musulunci. Jagoran juyin musuluncin na Iran ya kuma bayyana cewa da akwai ayyuka masu yawa da suke na cibiyar koyar da addinin musulunci ta Hauza ne da sun kunshi bayar da jawabi akan sabbin batutuwa na zamani da suke bijirowa, ruhin ci gaba, tsarkake zukata, da kuma siffa ta juyin juya hali.” Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya kuma bayyana cewa daga...
Rundunar sojan Ruwan Amurka ta sanar da cewa; Jirgin sama samfurin F-18 wanda kudinsa ya kai dalar Amurka miliyan 67 ya fadi akan jirgin dakon jiragen ruwa na ” USS Harry Truman” a tekun “Red Sea”. Jaridar ” Washington Post” ta buga labarin dake cewa; Jirgin ta fado ne a lokacin da yake kokarin sauka akan doron jirgin ruwan dakon jiragen saman na ” USS Harry Trauman”. Sanarwar ta kuma kara da cewa; Matuka jirgin sun fice daga cikinsa ta hanar lema, kuma an tserato da su daga cikin ruwa ta hanyar jirgi mai saukar angulu. Matukan, kamar yadda sanarwar ta sojojin na Amurka, sun ji rauni. Wani jami’in soja wanda ya bukaci a sakaya sunansa ya fada wata kafar...
Wani rahoto na musamman da HKI ta gudanar akan asarar da ta fuskanta sanadiyyar yaki da Hizbullah, ya bayyana cewa, a fagen aikin gona kawai sun yi asarar dalar Amurka miliyan 108 wacce ta fara daga 8 ga watan Oktoba 2023. Kungiyar ReGrow Israel” ta ce, yakin da aka yi da Hizbullah ya yi barna gagaruma a fagen aikin gona da asarar da ta kai ta dala miliyan 108 a kan iyaka da Lebanon. Nazarin wannan kungiyar ya kuma kara da cewa; Tun daga ranar 8 ga watan Oktoba 2023 har zuwa lokacin tsagaita wutar yaki a karshen 2024, hare-haren Hizbullah sun lalata muhimmacin cibiyoyi a “Isra’ila” da kuma haddasa gobara mai girma, da hakan ya tilastawa mazaunan yankin, musamman...
119-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin al-kur’ani mai girma ko cikin wasu littafan wadanda suka hada da littafin Dastane Rastan na Aya. Shahid Murtadha Muttari, ko kuma cikin littafin Mathnawi na maulana Jalaluddin rumi, ko cikin cikin wasu littafan da fatan masu sauraro zasu kasance tare da a cikin shirimmu na yau. ///…Madalla, Masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata a kuma cikin sirar Imam Al-Hassan al-Mujataba (a) da muke kawo maku, mun ji yadda aka yiwa Amirul muminina Aliyu dan Abitalib (a) bai’a bayana kashe khalifa na uku Uthman bin Affan, munji...

Sharhin bayan Labarai: Mahangar Iran Dangane Da Tattaunawa Kan Shirinta na Makamashin Nukliya Na Zaman lafiya
Assalamu alaikum masu sauraro sharhin bayana labarummu na yau zai yi magana dangane da ‘Mahangar Jumhuriyar Musulunci na Iran ta yadda za’a kai ga fahintar juna a tattaunawanta da kasar Amurka da suke yi wanda ni tahir amin zan karanta. Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi a wata tattaunawa ta wayar tarho da tokwaransa na kungiyar tarayyar turai wato Kaja Kallas, ya bayyana mata yadda bangarorin Amurka da Iran za su kai ga cimma yarjeniya dangane da shirin makamashin nukliya na kasarsa. Ministan ya kara da cewa tun kimani shekaru 20 da suka gabata ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran bangaren tattaunawa dangane da shirin nukliyar kasar ta zaman lafiya. Kuma batun shirin nukliyar kasar Iran tana daga cikin ayyuka...
“Dole ne mu daina tallata miyagun ayyukan ‘yan ta’adda. Dole ne mu cire su daga jerin shafukan manyan labarai na jaridunmu, mu rahoto ayyukansu a matsayin masu aikata laifuka, sannan mu kore labaran karya.” Ministan ya jaddada cewa, kungiyoyin ta’addanci da masu aikata laifuka sukan yi amfani da kafafen yada labarai da shafukan sada zumunta don yada tsoro, yada labaran karya, domin samun sabbin mabiya. A saboda haka, ya bukaci ‘yan jarida da editoci da su rungumi dabi’ar kishin kasa wajen bayar da rahoto ta hanyar guje wa kanun labarai masu daukar hankali ga farfagandar ta’addanci. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin...
Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum, ya yi zargin cewa sojoji da sauran jami’an tsaro na bayar da gudunmawar aikata miyagun laifuka da cin zarafin jama’a a Nijeriya. Zulum ya faɗi hakan ne yayin da yake haramta sayar da barasa a birnin Maiduguri da kewaye. Ka-ce-na-cen da ya biyo bayan ziyarar Tinubu a Katsina DAGA LARABA: Ɓoyayyun Dalilan Da ke Sa Faɗuwa Jarabawa A Najeriya Gwamnan ya bayyana haka ne a ranar Talata a wajen ƙaddamar da wani kwamitin da aka kafa don “ƙwace haramtattun otal-otal da gidajen karuwai da gidajen kwana da maɓoyar miyagun laifuka da kuma daƙile illolin munanan ɗabi’u. Gwamnan ya ce tsofaffin jami’an tsaron Nijeriya da na yanzu da suke aiki sun taka rawa wajen jawo...
Ya ce, “Na koma jam’iyyar APC ne domin in ci gaba da samun ribar kujerar kakakin majalisar domin ci gaban mazaba ta. “A gare ni, sauya sheka ba batun jam’iyya ba ne, illa don ci gaban mazaba ta, a matsayina na mai wakiltar mutane na, idan na jefar da wannan matsayi saboda jam’iyya, matsayin da zai bunkasa ci gaban yankina, hakan na nufin ban shirya yi wa jama’a aiki ba. “’Yan uwana na majalisa, ina so in sanar da wannan majalisa a hukumance cewa, kakakin majalisar, Rt. Hon. Blessing Agbebaku, ya koma APC,” inji shi. Agbebaku ya bayyana cewa ‘yan mazabar sa na goyon bayan matakin da ya dauka, inda ya ce “akwai ayyukan ci gaba...
Malam Bala Dutse, wanda ɗansa Amadu yana cikin waɗanda aka kashe, ya bayyana cewa gwamnati na ƙoƙarin mantawa da al’amarin. “An ce an kama wasu, amma har yau ba mu ji komai ba. Na rasa ɗana, kuma rayuwata ta shiga taka mai wuya. Mafi ƙaranci, gwamnati ta fito ta faɗa mana abin da ke faruwa,” in ji shi cikin hawaye. Hauwa’u Isa, matar ɗaya daga cikin waɗanda aka kashe, ta ce tana wahala da ’ya’yanta uku. “Sun ce za su taimaka mana da adalci, amma har yau babu wani taimako. Ba zan daina fatan samun adalci ba, amma har yaushe za mu jira?” in ji ta. Idan ba a manta ba gwamnonin Kano da Edo, Abba Kabir Yusuf da Monday...
Gwamnan Jihar Katsina Umaru Dikko Raɗɗa, ya ce ba shi da masaniyar wani allo da aka kafa mai ɗauke da saƙon ce wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu babu ƙorafi a Katsina ba kamar yadda ake ta muhawara a kai a ƙasar. Hakan na ƙunshe cikin wani saƙon murya ta gwamnan da aka fitar da ke martani a kan ce-ce-ku-cen da ya kaure a Nijeriya kan wani allon saƙo da aka kakkafa a Katsina lokacin da Shugaba Tinubu ya halarci auren ‘yar gwamnan. DAGA LARABA: Ɓoyayyun Dalilan Da ke Sa Faɗuwa Jarabawa A Najeriya Yaƙi ya ɓarke tsakanin Indiya da Pakistan Gwamna Raɗɗa ya ce yana da kyau a riƙa bincike kafin yanke hukunci kan abubuwa. “Na saurari muryar da...
Kungiyar gwagwarmaya ta Ansarullah ta bayyana cewa yarjejeniyar tsagaiat wutar da ta cimma da Amurka, ba ta sauya matsayin kasar ba na kai wa Isra’ila hari. Kakakin kungiyar Ansarullah Mohammed Abdul-Salam ya jaddada cewa Dakarun Yeman za su ci gaba da kai hare-hare kan Isra’ila domin goyan bayan Falasdinawa a zirin Gaza. Yarjejeniyar da Amurka ba ta da alaka da matsayinmu na goyan bayan Gaza, inji Abdul-Salam. A jiya ne masarautar Oman ta sanar cewa Amurka da kungiyar Ansarullah da aka fi sani da ta ‘yan Houtshis a Yeman suka cimma yarjejeniyar tsagaita wuta. Ma’aikatar harkokin wajen kasar Oman ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ta fitar cewa: Bayan tattaunawa da tuntubar juna da aka yi a baya-bayan...
Jihar Kaduna na ɗaya daga cikin jihohin Nijeriya da ke fama da matsalar samun tsaftataccen ruwan sha, musamman a karkara, inda mutane da dama ke fuskantar wahala wajen samun ruwan da zai ishe su sha da amfani. Sai dai gwamnatin ta ce ta ƙudiri aniyar magance wannan matsala domin inganta rayuwar al’umma da kare lafiyar jama’a. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Sai dai, rikice-rikicen cikin gida da matsalolin tsaro da tattalin arziƙi sun sa gwamnatin ke ci gaba da yin gyare-gyare don samar da hanyoyin da za su ba ta kariya da cikakken iko kan harkokin leƙen asiri da tsaro. Wannan mataki yana iya nuni da cewa Nijar na ƙoƙarin zama mai dogaro da kai a fannin tsaro, ko kuma tana neman ƙawancen da zai fi dacewa da manufofinta na cikin gida da waje. Duk da haka, ƙwararru na ganin cewa hakan na iya janyo sabon matsin lamba daga ƙasashen duniya da ƙungiyoyin yanki kamar ECOWAS. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu...
Majalisar Dokokin Jihar Kaduna ta amince da wani kudirin doka da ya soke Dokar Kwalejin Kimiyya da Fasaha na Jihar Kaduna ta shekarar 1989, tare da maye gurbin ta da dokar Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Nuhu Bamalli. Kudirin, mai taken “Kudirin Soke Dokar Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kaduna na Shekarar 1989 (Dokokin Jihar Kaduna na Shekarar 1991) da kuma Kafa Dokar Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Nuhu Bamalli, 2025,” an amince da shi ne yayin zaman majalisar wanda Shugaban Majalisar, Rt. Hon. Yusuf Dahiru Liman, ya jagoranta. Yusuf Liman ya bayyana cewa sabuwar dokar za ta bai wa kwalejin damar yin gogayya da sauran manyan cibiyoyin ilimi a fadin kasar nan, tare da dacewa da tsarin...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Duk shekara, dalibai kan rubuta jarabawa a matakai daban-daban na makarantu daban-daban. Ɗaya daga cikin nau’ukan jarabawa da ɗaliban Najeriya suke yi ita ce Jarabawar Neman Shiga Manyan Makarantu, wato UTME. Kamar kowace shekara, a bana ma ɗalibai sun rubuta wannan jarabawa kuma a cewar Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Manyan Makarantu (JAMB), kashi 78.5 cikin 100 na waɗanda suka rubuta jarabawar sun samu ƙasa da maki 200. Ko waɗanne dalilai ne suke kawo faɗuwa jarabawa a Najeriya? NAJERIYA A YAU: Me Ya Sa ‘Yan Gwagwarmaya Ke Shiga Tasku A Najeriya? DAGA LARABA: Asarar Da Hausawa Ke Tafkawa Sakamakon Bacewar Tatsuniya Wannan shi ne batun da shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi...
A ranar Litinin ne hukumar JAMB ta bayyana cewa daga cikin ɗalibai miliyan 1.95 da suka zauna jarabawar bana, kusan miliyan 1.53 — wato kashi 78 cikin 100 — ba su samu maki 200 ba. Sai dai ɗalibai 12,414 kacal suka samu maki 300 ko sama da haka. Ministan ya jaddada cewa wannan mataki na hana satar amsa zai taimaka wajen samar da ƙaimi na ɗalibai masu ƙwazo da amana, tare da ƙarfafa ingancin ilimi a Nijeriya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp

Iran Ta Ce Ana Yin Nazari Kan Lokacin Gudanar Da Zagaye Na Hudu Na Shawarwari Tsakanin Iran Da Amurka
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya bayyana cewa; Ana nazarin lokacin gudanar da zagaye na huɗu na shawarwari tsakanin Iran da Amurka Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Isma’il Baqa’i ya sanar da cewa: Ana nazari kan lokacin gudanar da zagaye na gaba na tattaunawar Iran da Amurka wand aba na kai tsaye ba, kuma mai shiga tsakani na Oman zai sanar da karin bayani da zarar an tantance lokaci da wurin da za a yi. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Isma’il Baqa’i ya shaidawa kamfanin dillancin labaran kasar Iran cewa: Ana duban lokacin da za’a gudanar da zagaye na gaba na tattaunawa tsakanin Iran da Amurka. Baqa’i ya kara da cewa: Mai shiga tsakani na Oman zai sanar da bayanai...
Kungiyar Ansarullahi ta kasar Yemen ta mabiya Al-Houthi ta sanar da cewa: Sanarwar da shugaban Amurka ta fitar kan Yemen gazawa ce ga Netanyahu Kungiyar Ansarullahi ta kasar Yemen ta sanar a jiya Talata cewa: Sanarwar da shugaban Amurka Donald Trump ya yi dangane da kasar Yemen gazawa ce ga Fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu. Mohammed Ali al-Houthi mamba a majalisar koli ta siyasa ta kungiyar Ansarullahi ya bayyana cewa: Sanarwar Trump gazawa ce ga Netanyahu, kuma dole ne fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ya yi murabus daga kan mukaminsa. Ya kara da cewa: “Za su fara tantance sanarwar da Trump ya bayar na dakatar da hare-haren wuce gona da iri kan kasar Yemen,” bisa la’akari...
Ministan Ilimi a Nijeriya, Tunji Alausa ya ce hana satar amsa ne ya janyo faɗuwar ɗalibai a jarawabar shiga manyan makarantu da JAMB ke shiryawa a kowace shekara. Tunji ya bayyana haka ne yayin tattaunawa da gidan talabijin na Channels a ranar Talata. ‘Raini ne ya sa ake ƙalubalantar yunƙurin kafa ƙungiyar Hausawa zalla’ Majalisar Dattawa ta kafa kwamitin lura da gwamnan riƙo na Jihar Ribas Ya ce sakamakon bana da aka samu, ya nuna irin yadda aka ƙara inganta yanayin rubuta jarabawar yadda ya kamata. Ya bayyana cewa hakan kuma ya nuna yadda tsarin rubuta jarabawar ya daƙile satar amsa da ɗalibai ke yi. Alausa ya ƙara da cewa kada a ɗauki sakamakon na JAMB a matsayin koma-baya, maimakon...
Shugaban tawagar kasar Yemen, Mohammed Abdul Salam, ya sanar da cewa ayyukan Yemen na tallafawa Gaza ba zai tsayawa ba Shugaban tawagar shiga Tsakani na kasar Yemen Abdul Salam ya bayyana cewa: Yemen ta samu sakon bukatu daga Amurka ta hanyar masarautar Oman, kuma wanda ya sauya matsayinsa Amurka ce, ba Yemen ba. Ya kara da cewa ikirari da Amurka ta yi na mika wuya, yana nuni ne ga gazawa, saboda Amurka ba zata iya kare jiragen ruwan haramtaciyar kasar Isra’ila daga hare-haren Yemen ba. Abdul-Salam ya kara da cewa: Fahimtar farko da aka samu tsakanin Amurka da Yemen ba ta da wata alaka da matsayar Yemen kan goyon bayan Gaza, yana mai nuni da cewa za a samu ci...
Gwamnatin kasar Indiya ta yi luguden makamai masu linzami kan kasar Pakistan, yayin da Pakistan ta sha alwashin mayar da martani Gwamnatin Indiya ta kai hare-haren makamai masu linzami kan wasu wurare a kasar Pakistan da yammacin jiya Talata, kuma sojojin Pakistan sun sha alwashin mayar da martini, yayin da ake ci gaba da samun takun saka tsakanin kasashen biyu masu karfin nukiliya. Gwamnatin Indiya ta kai hare-hare da makamai masu linzami guda uku kan wasu wurare a yankin Kashmir da Punjab na kasar Pakistan, yayin da daya daga cikin makaman ya afkawa tsohon filin jirgin sama na Muzaffarabad a yankin Kashmir da Pakistan ke iko da shi. A nata bangaren, gwamnatin Indiya ta sanar da cewa ta kaddamar da...
Kasar Sudan ta yanke huldar jakadancinta da kasar Hadaddiyar Daulart Larabawa tana mai ayyana UAE a matsayin ‘kasa mai cin zali’ Kamfanin dillancin labaran Sudan (SUNA) ya watsa rahoton cewa: Kwamitin tsaro da kula da matakan tsaron kasar Sudan ya sanar a cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya Talata cewa: Sudan ta yanke huldar diflomasiyya da kasar Hadaddiyar Daular Larabawa da kuma kiran hanzarta dawowar ma’aikatan ofishin jakadancin Sudan gida daga Abu Dhabi. Kwamitin tsaro da kula da matakan tsaron Sudan ya bayyana cewa: Fiye da shekaru biyu, daukacin duniya take bibiyar laifuffukan wuce gona da iri kan kasar Sudan, da tabbatar da tsaron yankunanta, da tsaron ‘yan kasarta daga hadaddiyar daular Larabawa ta hanyar wakiliyarta na cikin...
Inter Milan ta samu nasarar tankaɗo Barcelona daga Gasar Zakarun Turai, lamarin da ya ba ta damar kaiwa zagayen ƙarshe na gasar ta bana. A daren wannan Talatar ce aka buga wasa falle na biyu a zagayen kusa da na ƙarshe a Gasar Zakarun Turai ta bana tsakanin ƙungiyoyin biyu. ‘Raini ne ya sa ake ƙalubalantar yunƙurin kafa ƙungiyar Hausawa zalla’ Majalisar Dattawa ta kafa kwamitin lura da gwamnan riƙo na Jihar Ribas Inter Milan ce ta yi nasarar doke Barcelona da ci 4-3 a filin wasanta na San Siro da ke Italiya, bayan a makon jiya sun yi kunnen doki 3-3 a Nou Camp da ke ƙasar Sifaniya. A wasan na yau da aka barje gumi har tsawon mintuna...
Inter Milan ta samu nasarar tankaɗo Barcelona daga Gasar Zakarun Turai, lamarin da ya ba ta damar kaiwa zagayen ƙarshe na gasar ta bana. A daren wannan Talatar ce aka buga wasa falle na biyu a zagayen kusa da na ƙarshe a Gasar Zakarun Turai ta bana tsakanin ƙungiyoyin biyu. ‘Raini ne ya sa ake ƙalubalantar yunƙurin kafa ƙungiyar Hausawa zalla’ Majalisar Dattawa ta kafa kwamitin lura da gwamnan riƙo na Jihar Ribas Inter Milan ce ta yi nasarar doke Barcelona da ci 4-3 a filin wasanta na San Siro da ke Italiya, bayan a makon jiya sun yi kunnen doki 3-3 a Nou Camp da ke ƙasar Sifaniya. A wasan na yau da aka barje gumi har tsawon mintuna...
Wannan nasara da Inter Milan ta samu ya sa ta kai wasan karshe na gasar Zakarun Turai a karo na biyu cikin shekaru 3, a shekarar 2023 Manchester City ta doke Inter Milan a wasan karshe na gasar, wannan rashin nasara da Barcelona ta yi ya bata mata burinta na lashe gasar a karon farko cikin shekaru 10. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Wannan nasara da Inter Milan ta samu ya sa ta kai wasan karshe na gasar Zakarun Turai a karo na biyu cikin shekaru 3, a shekarar 2023 Manchester City ta doke Inter Milan a wasan karshe na gasar, wannan rashin nasara da Barcelona ta yi ya bata mata burinta na lashe gasar a karon farko cikin shekaru 10. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp

Ya Kamata Amurka Ta Daina Yin Barazana Da Matsin Lamba Idan Tana Son A Tattauna Batun Harajin Kwastam
Bugu da kari, Lin Jian ya bayyana cewa, bangaren Sin ya nuna godiya da taya kasar Togo murna nasarar kammala mika mulki a siyasance da kuma zaben sabon shugaban kasar da shugaban majalisar ministocinta na farko.(Safiyah Ma) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Sanarwar mai dauke da sa hannun shugaban kungiyar ta ARD-FCTA, Dokta George Ebong, da babban sakataren kungiyar, Dr. Agbor Affiong, sun yi Allah wadai da matakin da gwamnati ta dauka na cire ma’aikatan da abin ya shafa daga cikin tsarin albashi ba tare da sanarwa ko tuntuba ba, inda kungiyar ta ya bayyana matakin a matsayin “rashin gaskiya da adalci”. A cewar kungiyar, ma’aikatan da aka kora da suka hada da likitoci, ma’aikatan jinya, masu kula da bangaren magunguna, da masana kimiyyar dakin gwaje-gwaje, an yi kuskure ne aka bayyana su a matsayin ma’aikatan bogi ko kuma wadanda basu zuwa aiki, duk kuwa da gudummawar da suke bayarwa wajen gudanar da ayyukan asibiti. Daga kanmu, magana ta ƙare....
Majalisar Dattawa ta kafa kwamiti mai mambobi 18 domin sanya idanu kan yadda gwamnan riƙo na Jihar Ribas Vice Admiral Ibok Ete Ibas mai ritaya ke tafi da aikinsa. Majalisar ta ce ta ɗauki matakin ne a wani yuƙuri na ƙarfafa shugabanci na gari ba tare da rufa-rufa ba a jihar da ke kudu maso kudancin Najeriya. Alƙaluman sakamakon jarabawar bana — JAMB Friedrich Merz ya zama sabon shugaban gwamnatin Jamus Shugaban Majalisar Dattawan, Godswill Akpabio ya sanar yayin zaman majalisar na yau Talata cewa kafa kwamitin na da matuƙar mahimmancin wajen sa ido kan abubuwan da ke faruwa a jihar. Shugaban masu rinjaye Opeyemi Bamidele ne shugaban kwamatin, yayin da mambobin kuma sun haɗa da Adamu Aliero, da Osita...
Trump ya bayyana cewa, waɗanda suka zabi barin ƙasar da kansu na iya samun dama ta hanyar doka don dawowa cikin Amurka nan gaba idan suka cika ka’idojin da suka dace. A cewar rahoton, an riga an sayo tikitin jirgi ga mutum na farko da ya karɓi wannan tayin — daga birnin Chicago zuwa ƙasar Honduras. Tun bayan da Trump ya sake komawa kan kujerar mulki a watan Janairu, ya gindaya sabbin matakai masu tsauri don hana baƙin haure shiga ƙasar. Wasu daga cikin waɗannan matakan na haifar da ce-ce-ku-ce, musamman ganin yadda ake amfani da tsofaffin dokokin wanda suke da alaka da zamanin yaƙi wajen aiwatar da su. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun...
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa hanyar deblomasiyya ce kadai zata warware matsakar shirin nukliyar kasar iran da kasashen yamma. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto ministan yana fadar haka a zantawa ta wayar tarho da jami’a mai kula da al-amuran harkokin waje na kungiyar tarayyar Turai Kaja Kallas. Labarin ya kara da cewa ministan yana ganin matsalolin shirin Nucliya da kuma tsaron kasar ba za’a iya warwaresu ba sai ta wannan hanyar. JMI ta dauki wannan hanya ce don ita ce kadai wacce zata kai da gamsuwar ko wani bangare a cikin al-amuran da suke sabani a cikinsu. Aragchi ya fadawa Kallas kan cewa da wannan dalilin ne JMI ta dauki hanyar...
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esmail Baghaaei ya bukaci kasashen turai da su shiga a dama da su kan tattaunawa dangane da shirin nukliyar kasar Iran na zaman lafiya. Ya kuma jaddada cewa Iran tana turjiya ga dukkan tunanin Amurka na wargaza shirin Nukliyar kasar Iran kwata-kwata. Baghaei ya kara da cewa duk da cewa Iran a shirye take a ci gaba da tattaunawa kan shirin makamashin nukliyar kasar, da sake farfado da yarjeniyar JCPOA ta shekara ta 2015 amma kuma ba zata taba barin hakkinta na mallakar fasahar nukliya da luma sarrafashi a hanyoyin da yarjeniyar NPT ta amince da su ba. Kuma da alamun tattaunawar tsakanin Amurka da Iran ya daki dutse, saboda sun sami sabani a...
Mamba a majalisar gudanarwa ta kungiyar Ansarulla ta kasar yemen Muhammad Bukhaiti ya bayyana cewa hare-haren da HKI da Amurka suka kai fararen hula a kasar yemen wuce jan layi, ko ketare haddi ne na kungiyar don haka su jira maida martani mai tsanani. Kamfanin dillancin labaran Iran ya nakalti yana fadawa tsahar talabijin ta Al-mayadeen ta kasar Lenamon a yau Talata. Ya kuma kara da cewa hare-haren da Amurka suke kaiwa ma’aikatu da wuraren fararen hula a kasar Yemen na baya-bayan nan duk sun nuna cewa an sami nasara a kansu. Albukhaiti ya kara da cewa sadaukarwa da mutanen kasar Yemen suke yi saboda Gaza, ba zai tsaya ba, sannan muna son fadawa kasashen Amurka da ingila da kuma...
A yau, rukunin farko na tawagar wanzar da zaman lafiya da martanin gaggawa na kasar Sin kashi na biyu wadda za ta je yankin Abyei, ya tashi daga birnin Zhengzhou na kasar Sin, da jirgin saman soja domin gudanar da aikin wanzar da zaman lafiya na tsawon watanni 12. Bugu da kari, ana shirin tura rukuni na biyu na tawagar a tsakiyar watan Mayu. Kasar Sin ta aike da tawagar wanzar da zaman lafiya da martanin gaggawa ta farko zuwa yankin Abyei a watan Mayun shekarar 2024. Tawagar tana dauke da bangarori da dama da suka hada da bangaren tuki, sadarwa, bincike, da kiwon lafiya, wadanda ke yin sintiri da makamai, da kula da wadanda suka jikkata, da kuma...
Kawamcen jam’iyyun siyasa na kasar Ivory Coast ya bukaci a sake lalen yadda aka tsara yadda ake ristar jam’iyyu a hukumar zaben kasar, ganin yadda ta hana rijistar wasu jam’iyyun saboda dalilai daban daban. Shafin yanar gizo na labarai Afirka news ya bayyana cewa an kafa kawancen ne wanda aka sanyawa suna CAP-CI a farkon wannan shekarar, don tunkarar zaben shugaban kasa wanda za’a gudanar a ranar 25 ga watan Octoban shekara ta 2025 da muke ciki. Kawancen CAP gamayyar jam’iyyun adawa da dama ne na kasar, in banda Jam’iyyar da Lauranta Bagbo a kafa don tunkarar zaben na watan Octoba. Har’ila yau kawancen na zargin hukumar zaben kasar da rashin adalci a yadda take amincewa da yan takara a...
Hukumar shirya jarabawar shiga manyan makarantu a Nijeriya (JAMB) ta fitar da alƙaluman sakamakon jarabawar UTME ta shekarar 2025, inda ta bayyana cewa yawancin daliban da suka zauna jarabawar sun gaza samun maki 200 daga cikin maki 400. Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar yayin wani taron manema labarai da ta gudanar a ranar Litinin. JAMB ta ce ɗalibai miliyan 1.95 ne suka rubuta jarabawar, amma cikin wannan adadi, miliyan 1,534,654 ne wanda ya kai kaso 78 cikin 100 suka samu maki ƙasa da 200. Alƙaluman sakamakon ya nuna cewa kashi 0.63 ne na ɗalibai ƙalilan da suka samu makin da ya haura 300, wanda a jimlace suka kai ɗalibai 12,414. A matakin maki tsakanin 250...
Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa ta kaddamar da manyan jami’an likitocin kasa a shirye-shiryen gudanar da aikin Hajjin shekarar 2025. Babban Daraktan Hukumar Alhaji Umar Ahmed Labbo ne ya bayyana haka a yayin bikin kaddamar da aikin da aka gudanar a Dutse babban birnin jihar. Ya bayyana cewa, hukumar ta kaddamar da tawagar likitocin guda 10, inda ya bukaci kungiyar da ta yi aiki da gaskiya, hakuri, da jajircewa wajen yi wa alhazan jihar hidima a kasar Saudiyya. Alhaji Ahmed Umar Labbo ya ce aikin amana ce da bai kamata kungiyar ta dauka da wasa ba. Ya yabawa Gwamna Umar Namadi bisa amincewa da wannan tawagar, inda ya nuna cewa, wannan shi ne karon farko da jihar...
A sanarwar da kakakinsa Mukhtar Gidado ya fitar, gwamnan ya miƙa saƙon jajantawa ga iyalan waɗanda suka rasa rayukansu, al’umman ƙaramar hukumar Alkaleri da ma mutanen jihar Bauchi baki ɗaya. Ya yi addu’ar Allah ya jiƙan jaruman da suka rasa rayukansu a ƙoƙarinsu na kare yankunansu. Gwamnan sai jaddada aniyar Gwamnatinsa na daƙile kowace irin nau’in barazanar tsaro a dukkanin faɗin jihar. Ya yi kira ga jama’a da su rika zama cikin haɗin kai da bayar da gudunmawarsu ga jami’an tsaro tare da samar musu da bayanan sirri a kan lokaci da zai bada damar daƙilewa ko magance matsalolin tsaro a kan lokaci. Yayin da ya ke tabbatar wa jama’a cewa gwamnati tana kan aikin haɗin...
Friedrich Merz na jam’iyyar CDU ya zama sabon shugaban gwamnatin Jamus. Majalisar Dokokin Jamus ta Bundestag ta zabi Merz a matsayin sabon shugaban gwamnati lokacin zaɓen zagaye na biyu, bayan ya gaza samun ƙuri’un da yake buƙata a zagayen farko na zaɓen. A zaɓen farko Merz ya samu ƙuri’u 325 na jam’iyyun ƙawance daga majalisar mai mambobi 630. Kafin zama shugaban gwamnati ana buƙatar kuri’u 316 kuma jam’iyyar CDU/CSU da kuma jam’iyyar SPD suna da kujerun majalisar 328, fiye da adadin da ake buƙata. Merz zai maye gurbin Olaf Scholz wanda ya faɗi zaɓen ƙasar da aka gudanar a watan Fabrairu Upon announcing the second vote, the head of the Union bloc in parliament, Jens Spahn, said, “The whole of...

Xi Da Shugaban Majalisar Turai Da Shugabar Kwamitin EU Sun Tayawa Juna Murnar Cika Shekaru 50 Da Kulla Hulda
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A bidiyon da wani mai suna Nawab Sheikh ya fitar na nuna yadda ya hau motarsa, wacce yake tuka ta a kan titunan birnin Murshidabad a cikin ƙasar Indiya, don nishaɗantar da mahaya babur, wanda ya sa bidiyon yake ta yaɗuwa a shafin sada zumunta na Instagram. Babu wani wuri mafi kyawun nuna bajintar kirkira don jan hankalin ɗan Adam kamar intanet. Matashi ya kashe mahaifinsa da adda a Jigawa ’Yan PDP 6 a Majalisar Tarayya sun koma APC Haka kuma idan aka zo fannin ƙirƙirar sabuwar fasaha, ba da yawa ba ne ke irin wannan a cikin Indiyawa. Na baya-bayan nan shi ne ƙirƙirar da wani mutumin West Bengal – “motar gado” inda ya mai da gadonsa ya koma...
Lamarin ya tayar da hankali a unguwar, inda wasu matasa suka yi yunƙurin kai farmakar Saudat. Amma jami’an tsaro sun isa wajen a kan lokaci, suka ceci amaryar tare da kai ta wajen hukuma. Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano ba ta fitar da wata sanarwa kan lamarin ba zuwa lokacin haɗa wannan rahoto. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Wani matashi dan shekarar 20 ya fada hannun hukuma kan zargin kashe mahaifinsa da adda a Jihar Jigawa. Rundunar ’yan sandan Jihar Jigawa ta kama wanda ake zargin kashe mahaifinsa mai shekara 57, da adda. Wanda aka kashe ya samu raunuka a kafadarsa da wuya da kirjinsa, kuma an kai shi Babban Asibitin Tarayya (FMC) da ke Birnin Kudu, inda aka tabbatar da mutuwarsa. Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne a ranar Litinin 5 ga Mayu, 2025, da misalin ƙarfe 10:00 na safe a unguwar Bakin Kasuwa, da ke Karamar hukumar Gwaram. Wata mata ta auri maza biyu a lokaci guda a Kano ’Yan PDP 6 a Majalisar Tarayya sun koma APC Daukar nauyin dalibai: Rikici ya barke a...
Mambobin Jam’iyyar PDP shida a Majlisar Wakilai daga Jihar Delta sun sauya sheka zuwa Jam’iyya APC. Kazalika wasu biyu daga Jihar Enugu sun sauya sheka daga Jam’iyyar adawa ta LP zuwa PDP. Shugaban Majalisar Wakiliai, Abbas Tajuddeen, ne ya sanar da hakan bayan dawowar majalisar daga hutu a ranar Talata. Shugaban Majalisar ya bayyana cewa ’yan majalisar sun yanke shawarar sauya sheka ne sakamakon rikicin cikin gida da ya dabaibaye jam’iyyun nasu a matakin jiha da kuma kasa. Wadanda sauka sauya sheka zuwa APC su ne: Victor Nwokolo, Julius Pondi, Thomas Ereyitomi, Nicholas Mutu, Okodiko Jonathan, da kuma Nnamdi Ezechi. Wadanda suka bar LP zuwa PPD su ne Mark Obetta da kuma Dennis Nnamdi. Idan ba ma manta ba a kwanakin baya...
Wani sabon rikici ya dabaibaye Hukumar Raya Yankin Arewa maso Yamma (NWDC) kan shirin daukar nauyin dalibai zuwa karatu a kasashen waje. Wannan dambarwar ta kunno kai ne bayan sanarwar da hukumar ta fitar na shirin daukar nauyin daliba domin karatun jami’a daga yankin. Majalisar Amintattun Hukumar ta ce ba a taba tattaunawa kan shirin a zamanta ba, a yayin da majalisar gudanarwar Huukumar ke ikirarin cewa ta sanar da su ta wata wasika da ta aike musu. Wasu mambobin Kwamitin Amintattun hukumar da wakilinmu ya zanta da su sun zargi hukumar gudanarwar da yin gaban kanta. Hajj 2025: Maniyyatan Kaduna za su fara tashi ranar 14 ga watan Mayu Wata mata ta auri maza biyu a lokaci guda a...
“Mun rufe dukkan sansanonin ‘yan gudun hijira da ke cikin Maiduguri. Yanzu haka saura biyu da ba na hukuma ba. Mun riga mun dawo da kashi 75 na ‘yan sansanin Muna gida, saura kashi 25 za su koma cikin kwanaki masu zuwa.” Kowane iyali sun samu tallafin abinci, kayan gini da kulawar lafiya. Haka kuma, kowane magidanci mace ko namiji za a ba shi Naira 100,000, yayin da matan gidan za su ƙara samun Naira 50,000 don taimaka musu da buƙatunsu na yau da kullum. Za a Ƙara Inganta Cibiyar Koyo Sana’o’i a Gidan Gyaran Hali Tun da safiyar ranar Litinin, Gwamna Zulum ya kai ziyara gidan gyaran hali na manyan laifuka da ke Maiduguri. Ya ce za a inganta...
Wanda ya ba su masauki a otal, gida, ko wani wurin zama shi ma zai fuskanci irin wannan hukunci. Duk wanda ya je aikin Hajji ba tare da izini ba ko dan ƙasa ne ko wanda ya daɗe fiye da lokacin zama za a kori mutum zuwa ƙasarsa tare da dakatar da shi daga shiga Saudiyya na tsawon shekaru 10. Hukumomin shari’a za su kuma karɓi motocin da aka yi amfani da su wajen safarar waɗanda ba su da izinin yin aikin Hajji, musamman idan motocin na masu laifin ne. A wani labari da ya shafi aikin Hajji, Hukumar Hajji ta Ka6sa (NAHCON) ta sanar da cewa jigilar mahajjatan Nijeriya na shekarar 2025 zai fara ne daga ranar 9 ga...
Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta bayyana cewa tattaunawar sulhu a Gaza ba ta da wani tasiri a wannan mataki. Ofishin kungiyar, ya yi kira ga kasashen duniya da su matsa lamba kan gwamnatin Netanyahu don kawo karshen laifukan yunwa, kishirwa da kisan kai a Gaza, in ji wani babban jami’in kungiyar. Halin da ake ciki a Gaza ya kai intaha inji kungiyoyin kasa da kasa. A wani rahoto data fitar a baya baya nan kungiyar agaji ta Red Crescent ta Falasdinu ta yi gargadi kan halin da ake ciki a zirin fiye da na watanni 19 da suka gabata.” kungiyar ta jaddada cewa “mafi yawan jama’a na yankin na fuskantar matsananciyar hadarin yunwa.” Sama da mutane miliyan daya...
Kungiyar Tarayyar Afrika (AU), ta yi tir da hari na baya-bayan nan da aka kai Port Sudan, muhimmin birni a kasar Sudan dake cikin ’yan kalilan da yakin da ake yi a kasar bai shafa ba. Port Sudan ya taka muhimmiyar rawa a matsayin cibiyar jigila da ayyukan agaji, yayin da ake ci gaba da gwabza fada a Sudan. Kungiyar AU mai mambobi 55 ta yi gargadin cewa, kai hari birnin zai kawo tsaiko ga kokarin da ake yi na wanzar da zaman lafiya a kasar. Rahotanni daga kafafen yada labarai na cewa, kungiyar RSF ta kai hari da jirgi mara matuki zuwa filin jirgin sama na sojoji, da sauran wuraren dake filin jirgin sama na kasa da kasa na...

Hannayen jarin kamfanonin fina-finan Amurka sun fadi sakamakon barazanar Trump na kakaba harajin kwastam
Bayanai daga Amurka na cewa Hannayen jari na kafofin watsa labaru da kamfanonin shirya fina-finai da harkokin nishadi na Amurka sun fadi kasa, bayan da shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da cewa, yana shirin kakaba harajin kwastam da kashi 100 bisa 100 a kan fina-finan da ake shiryawa a ketare. Hannayen jarin kamfanonin fina-finai irin su Netflix Inc. da Warner Bros. Discovery Inc. sun fadi da kusan kashi 3 cikin dari, inda na Paramount Global da Walt Disney Co. kuma suka fadi da kusan kashi 2 cikin dari yayin da aka bude kasuwa. A wani sakon da ya wallafa kan shafinsa na manhajar True Social, shugaban na Amurka ya ce yana umurtar ma’aikatar kasuwanci da wakilinsa na cinikayya da...
Hukumar Kula da Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kaduna za ta fara jigilar maniyyata zuwa kasar Saudiyya a ranar 14 ga watan Mayu, 2025. Shugaban hukumar, Malam Salihu S. Abubakar, ne ya bayyana hakan a wani shirin rediyo kai tsaye da aka watsa daga Kaduna, inda ya bayyana shirye-shiryen da jihar ta kammala domin aikin Hajjin bana. Ya bayyana cewa maniyyata 4,060 daga jihar Kaduna za su sauke farali a bana, kuma kamfanin jirgin sama na UMZA ne zai yi jigilarsu. Shugaban hukumar ya bayyana cewa domin kammala matakan da ake bi kafin tafiya, za a yi duk maniyya cikakken gwajin lafiya a sansanin alhazai da ke Mando. Wata mata ta auri maza biyu a lokaci guda a Kano NAJERIYA...
EFCC ta ce za ta gurfanar da shi a gaban kotu da zarar ta kammala bincike. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
An gurfanar da wata matar aure a gaban kotun Musulunci kan zargin ta da auren maza biyu a lokaci guda a Jihar Kano. Wannan lamari ya faru ne wata shida bayan auren matar mai suna Harira Muhammad Tudun Murtala da mijinta na farko mai suna Sagiru Shu’aibu Tudun Murtala. A yayin zaman Kotun Musulunci da ke zamanta a Post Office Malam Sagiru ya shaida wa alkali cewa kasncewar ba tare suke zaune da matar tasa ba, wata rana ya je gidanta sai kawai ya iske ta tare da wani mutum a gan gadon aurensu, lamarin da ya sa ya sanar da makwabta abin da ke faruwa. Bayan gurfana da ita a gaban kotu, Harira ta musanta cewa akwai aure tsakaninta...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Yin gwagwarmaya ko fafutuka wani abu ne da ke cikin jinin dan Adam, musamman idan yana kokarin ganin an samu sauyi ko cigaba a al’umma. Sai dai a Najeriya, sau da yawa ana danganta kalmar “gwagwarmaya” da rikici ko sabani da gwamnati. NAJERIYA A YAU: Abin da ke kai matasan Najeriya ci-rani wasu ƙasashen Afirka DAGA LARABA: Asarar Da Hausawa Ke Tafkawa Sakamakon Bacewar Tatsuniya Shirin Najeriya A Yau na wannan rana zai yi nazari ne kan yadda za a yi gwagwarmaya ba tare da an taka doka ba. Domin Sauke shirin, latsa nan
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Yin gwagwarmaya ko fafutuka wani abu ne da ke cikin jinin dan Adam, musamman idan yana kokarin ganin an samu sauyi ko cigaba a al’umma. Sai dai a Najeriya, sau da yawa ana danganta kalmar “gwagwarmaya” da rikici ko sabani da gwamnati. NAJERIYA A YAU: Abin da ke kai matasan Najeriya ci-rani wasu ƙasashen Afirka DAGA LARABA: Asarar Da Hausawa Ke Tafkawa Sakamakon Bacewar Tatsuniya Shirin Najeriya A Yau na wannan rana zai yi nazari ne kan yadda za a yi gwagwarmaya ba tare da an taka doka ba. Domin Sauke shirin, latsa nan
Shugaban kasar Iran ya jaddada cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana neman karfafa hadin kai da ‘yan uwantaka da kasashen makwabtanta Shugaban kasar Iran Mas’oud Pezeshkian ya jaddada cewa: “Babban burinsu shi ne neman karfafa hadin kai da ‘yan uwantaka da makwabtansu, kuma ba su dauke da kiyayya a kansu.” Shugaba Pezeshkian, a jawabin da ya gabatar a gaban taron majalisar kwararru masu zaben Jagoran juyin juya halin Musulunci a Iran a jiya litinin, ya jaddada wajabcin kiyaye hadin kai da hadin kai a cikin kasar da dukkan al’ummar musulmi. Yana mai cewa: “Tare da haɗin kan kasa, za su iya magance dukkan matsalolin cikin gida.” Sannan ya kuma yi kira da a kaucewa duk wani mataki da zai kawo...

Jamhuriyar Musulunci Ta Iran Ta Sha Alwashin Mayar Da Martani Cikin Gaggawa Kan Duk Wani Hari Kan Kasarta
Jamhuriayar Musulunci ta Iran ta sha alwashin mayar da martani cikin gaggawa ga duk wani kasadan ‘yan Sahayoniyya da Amurka kan kasarta Jakada kuma zaunannen wakilin Jamhuriyar Musulunci ta Iran a Majalisar Dinkin Duniya Amir Sa’ed Irawani ya jaddada cewa: Duk wani kasadan harin soji da Amurka ko wakilliyarta gwamnatin ‘yan sahayoniyya suke yi, ko da kuwa wani mataki ne da ya sabawa ‘yancin kai, ko cikakken amincin Iran ko kuma muhimman muradun kasa na Jamhuriyar Musulunci ta Iran, za a mayar da martani cikin gaggawa, da ya dace kuma halastacce. Wannan dai ya zo ne a cikin wata wasika da Amir Sa’ed Irawani, jakada kuma wakilin din-din-din na Jamhuriyar Musulunci ta Iran a Majalisar Dinkin Duniya, ya aikewa babban...
Tawagar jiragen saman yaki da dama ne suka kai munanan hare-hare kan sassa daban-daban na kasar Yemen a jiya Litinin Kafofin yada labaran kasar Yemen sun rawaito a jiya litinin cewa: Wata tawagar jiragen saman yakin Amurka da haramtacciyar kasar Isra’ila sun kai hare-hare kan yankuna daban-daban na kasar Yemen da suka hada da gundumar Bajil da wasu wurare a gundumar Al Hudaydah da ke yammacin kasar ta Yemen, da kuma gundumar Sinjan da ke birnin San’a. Ma’aikatar lafiya ta kasar Yemen ta sanar da cewa: Mutane 21 ne suka jikkata sakamakon hare-haren bama-bamai da aka kai kan masana’antar siminti na Bajel da ke gundumar Al Hudaydah. A nata bangaren, tashar talabijin ta 12 ta haramtacciyar kasar Isra’ila ta nakalto...
Falasdinawa fiye da 50 ne suka yi shahada yayin da wani adadi da dama suka jikkata a hare-haren da sojojin mamayar Isra’ila suka kai Gaza a jiya Litinin Rahotonni sun bayyana cewa: Fiye da Falasdinawa 50 ne aka suka yi shahada wasu adadi da dama kuma suka jikkata sakamakon hare-haren da sojojin mamayar Isra’ila ke ci gaba da kai kan yankin Zirin Gaza na Falasdinu. Daga cikin hare-haren har da hare-haren da jiragen mamayar Isra’ila suka kai kan wani gini mai yawan jama’a a unguwar Al-Karama da ke arewacin Gaza, wanda ya yi sanadin kisan kiyashi kan mutane ciki har da mata da kananan yara 20 da kuma fararen hula na daban. A wani labarin kuma, Falasdinawa a yankin Al-Karama...
A nasa jawabin, shugaban NAHCON ya bukaci tawagar da ta tunkari wannan aiki tare da himma da kwazo, tare da jaddada tsarkin aikin da ke gabansu. Wannan Tawagar ta musamman, ita ce ke da alhakin kafa harsashin gudanar da aikin Hajji baki daya, da suka hada da tsare-tsare na masaukai, ka’idojin karbar baki a filin jirgin sama na kasar Saudiyya, da hada kai da hukumomin Hajji na Saudiyya. Yunkurin nasu ya share fagen isowa da jin dadin alhazan Nijeriya, da ma’aikatan lafiya, da jami’a na jihohi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki...
Da yake karin haske game da abubuwan da aka tsara da kuma yadda hukumar za ta kasance, shugaban masu rinjaye na majalisar, Hon. Lawan Husseini ya shaidawa manema labarai cewa, sanya hannu kan dokar za ta kara samar da damarmakin wutar lantarki a jihohin uku. Husseini ya jaddada cewa, za ta kuma rage wahalhalu da kuma rage tsadar makamashi ga ‘yan jihohin, za ta kuma samar wa kananan masana’antu da manyan masana’antu isasshen makamashi don yin kasuwanci, tare da bai wa asibitoci da cibiyoyin kula da ruwa damar gudanar da ayyuka yadda ya kamata. Dangane da tsarin shugabancin hukumar da ake son yi, Husseini ya ce, za a samar da shugaba, manajan darakta da mataimakin manajan darakta wanda...
Da safiyar jiya Lahadi bisa agogon wurin, aka kammala horon hadin gwiwa tsakanin sojojin saman kasashen Sin da Masar mai suna “Shaho na wayewar kai-2025” cikin nasara, a wani sansanin sojojin saman Masar, wanda ya kwashe kwanaki guda 18. Wannan horon na hadin gwiwa shi ne karo na farko da rundunar sojin saman kasar Sin ta aike da dakaru zuwa kasashen Afirka domin ba da horon hadin gwiwa. A yayin horon na hadin gwiwa, sojojin saman kasashen Sin da Masar sun tattauna tare da yin musayar ra’ayi kan nau’o’in horarwa, da dabarun yaki da jiragen sama, da samar da man fetur a sama da dai sauransu, kuma sun samu nasarar kammala horarwa kan ayyukan sarrafa jiragen sama, da kiyaye...
Shugaban Ghana a wannan Litinin ɗin ya bayyana ɗaukar mataki kan ministoci da sauran masu riƙe da muƙaman siyasa fiye da 40 da suka gaza bayyana kadarorin da suka mallaka. Wannan na zuwa ne a yayin da Shugaba John Mahama ke ci gaba da zage dantse wajen yaƙi da cin hanci da rashawa a ƙasar da ke yammacin Afirka. ’Yan bindiga sun kashe matar aure bayan karɓar N10m kuɗin fansa ’Yan fashi sun kashe matashi a Kano A yayin karɓar rantsuwar kama aiki a watan Janairun bana ne Shugaban Ghana ya sha alwashin yaƙi da rashawa domin fitar da ƙasar daga ƙangin matsalar tattalin arziki A watan Afrilun da ya gabata ne mahukunta suka gurfanar da wani babban jami’in tsaro...
A wani bangare na wasikar na cewa, “An umurce ni da in isar da amincewar Gwamnati na fitar da jimillar kudi Naira miliyan 15,227,272.72 a asusun kowace karamar hukuma domin gyaran motoci biyu tare da siyo karin wasu guda hudu ga Majalisar masarautar Kano wanda kamfanin Sottom Synergy Resources Ltd zai dauki nauyin siyowa. Wasikar ta kuma umurci shugabannin kananan hukumomin da su tabbatar an bi tsarin da ya dace wajen aiwatar da wannan umarni. Duk da cewa, wannan umarnin ya janyo cece-ku-ce amma har zuwa rubuta wannan rahoto, gwamnatin jihar Kano ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance ba dangane da cece-ku-cen. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun...

Sharhin bayan Labarai: Ci Gaban Harkokin Kasuwanci Tsakanin Iran Da Kasashen Waje Duk Tare Da Takunkuman Kasashen Yamma
Assalamu alaikum masu sauraro sharhin bayan labarammu zai yi magana dangane da “Bankasar tattalin arzikin Iran duk tare da takunkuman tattalin arziki masu tsanani wadanda kasashen yamma musamman Amurka suka doramata, wanda ni tahir amin zan karanta. ////…A dai-dai lokacinda gwamnatin kasar Amurka take barazanar zata hana sayan danyen man fetur daga kasar Iran kwatakwata, sannan take barazanar zata farwa kasar da yaki saboda shirin na makamashin nukliya, sabbin rahotanni sun bayyana cewa iran tana gaba a fitar da kayaki kasuwanci zuwa kasar China sannan ita ce ta 9 a duniya wajen samar da kwan kaji da sauran tsuntsaye. Kamfanin dillancin labaran Parstoday na kasar Iran ya bayyana cewa, yawan danyen man fetur wanda kasar Iran take sayarwa kasar China...
’Yan bindiga sun kashe wata mata da suka sace tare da mijinta Yakubu Dada watanni bakwai da suka gabata a yankin Kontagora da ke Jihar Neja. Aminiya ta ruwaito cewa ’yan ta’addan sun halaka matar mai suna Lami bayan karɓar Naira miliyan 10 kuɗin fansa. ’Yan fashi sun kashe matashi a Kano Kwankwaso: Abba ya mayar wa Baffa Bichi martani Kazalika, ’yan bindigar sun kuma nemi ƙarin Naira miliyan 20 da baburan Bajaj huɗu, tare da yin barazanar kashe mijinta muddin aka gaza kai musu abubuwan da suka buƙata. Aminiya ta ruwaito cewa, tun a ranar 31 ga watan Oktoba na 2024 ne Yakubu Dada da mai ɗakinsa suka faɗa tarkon masu garkuwa yayin da suke kan hanyar zuwa Kontagora....
An labarto cewa harin ya wakana ne da safiyar ranar Lahadi kuma ‘yan bindigan sun yi awun gaba da shanu da sauran dabbobin al’umman yankin a yayin farmaƙin. Kazalika, wakilinmu ya gano cewa baya ga ‘yan bijilante da suka rasa rayukansu akwai wasu fararen hula mazauna ƙauyen Sabuwar Sara su ma sun gamu da ajalinsu yayin da suke ƙoƙarin gudun neman tsira bisa harbe-harben ‘yan bindigan. Sai dai bayanai sun tabbatar da cewa su ma ɓangaren ‘yan fashin dajin sun rasa mutanensu da dama da ake hasashen sun ma fi ‘yan Bangan mutuwa. Rundunar ‘yansandan jihar Bauchi ta tabbatar da faruwar lamarin, sai dai ba ta bayyana haƙiƙanin adadin mutanen da suka rasa rayukansu a ɓangaren ‘yan...
Ana fargabar cewa wasu da ake zargin ’yan fashi da makami ne sun kashe wani matashi a unguwar Ɗanbare da ke Ƙaramar Hukumar Kumbotso a Jihar Kano. Bayanai sun ce waɗanda ake zargin sun kashe matashin ne mai suna Shuaibu Muhammad da adda, bayan sun shiga gidan da yake zaune da nufin sata. Wani abokin kasuwancinsa, Haruna Nuhu Hussain, ya ce gungun ’yan fashin sun shigo gidan da suke zama a daidai lokacin da suke shirye-shiryen tafiya sallar Asuba. To sai dai mazauna unguwar sun bayyana wa Aminiya cewa sun samu nasarar kama wanda suke zargin shugaban ’yan fashin ne, sun kuma miƙa shi ofishin ’yan sanda na Ɗorayi. Kimanin mutum 10 sun bayyana cewa ko a kwanakin nan jagoran...
A cikin wata daya kadai sojojin HKI sun rushe gidajen Falasdinawa 152 a yammacin Kogin Jordan. Majiyar Falasdinawa ta ambaci cewa a kudancin garin Khalil ‘yan mamayar sun rushe gidaje 25 da kuma wasu cibiyoyi, da hakan ya sa adadin gidajen da su ka rushe zuwa 152 kamar yadda hukumar Falasdinu ta ambata. Bugu da kari, majiyar Falasdinawan ta ce, ‘yan mamayar sun kuma aike wa da wasu cibiyoyin da gidaje 46 gargadin cewa za su rushe su, da yin kira da su fice daga cikinsu. Wata cibiyar ta Falasdinawa ta ce fada wa kamfanin dillancin labarun “Anatoli’ cewa; ;yan mamayar sun rushe gidaje 96 da mutane suke rayuwa a cikinsu, sai kuma wasu gidaje 10 da babu mutane a...
Ana fargabar cewa wasu da ake zargin ’yan fashi ne sun kashe wani magidanci a unguwar Ɗanbare da ke Ƙaramar Hukumar Kumbotso a Jihar Kano. Bayanai sun ce waɗanda ake zargin sun kashe magidancin ne da adda, bayan sun shiga gidansa da yake zaune domin sata da asuba. To sai dai mazauna unguwar sun bayyana wa Aminiya cewa sun samu nasarar kama wanda suke zargin shugaban ’yan fashin ne, sun kuma miƙa shi ofishin ’yan sanda na Ɗorayi.
Jami’ar siyasar waje ta tarayyar turai Kaja Kallas ta bayyana cikakken goyon baya ga warware batun makamashin Nukiliyar Iran ta hanyar diplomasiyya. Jami’ar ta wallafa a shafinta na X cewa: Na tattauna da ministan harkokin wajen Iran Abbas Arakci domin tabbatar da goyon bayan kungiyar tarayyar turai akan aiki da hanyar diplomasiyya domin warware batun Nukiliyar Iran da kuma rage rikice-rikice a cikin wannan yankin.” Haka nan kuma Kallas ta jaddada abinda a baya tarayyar turai din ta rika riyawa da ba shi da tushe na cewa, Iran tana bai wa Rasha taimakon soja tana mai cewa: ” Na kuma yi kira ga Iran da ta dakatar da bai wa Rasha taimakon soja.” Iran dai ta sha yin watsi da...
Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta yi watsi da zarge-zargen da aka yi ma ta dangane da kasar Yemen. A wani bayani da ma’aikatar harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran din ta fitar ta bayyana cewa: Abinda mutanen Yemen suke yi domin taimakawa al’ummar Falasdinu, mataki ne na kashin kansu da su ka dauka cikin ‘yanci saboda lamirinsu na ‘yan adamtaka da kuma taimako na musulunci ga ‘yan’uwansu Falasdinawa.” Bayanin ya kuma ci gaba da cewa; Jinginawa jamhuriyar musulunci ta Iran abinda mutanen na Yemen suke yi, ba shi da tushe, kuma manufar hakan ita ce, rufe laifukan da ‘yan sahayoniya suke yi a Falasdinu.” Bayanin ya kuma ce; Jamhuriyar musulunci tana sake jaddada matsayarta akan wajabcin kiyaye da karrama kasashe...
Kotun duniya ta yi watsi da karar da Sudan ta kai Hadaddiyar Daular Larabawa tana mai zarginta da hannu a kisan kiyashin da aka yi wa al’ummar wannan kasa. A yau Litinin ne kotun duniyar ta yi watsi da karar ta Sudan, tana mai wanke Hadaddiyar Daular Larabawa. Ita dai Sudan ta zargi Hadaddiyar Daular Larabawar da cewa ta hada baki da dakarun kai daukin gaggaawa wajen yi wa mutanen yankin Darfur kisan kiyashi. A nata gefen Hadaddiyar Daular Larabawan ta ki amincewa da tuhumar da Sudan ta yi mata tana mai siffata ta da cewa; Farfaganda ce, kuma Sudan din ta yi hakan ne domin kawar da hankulan duniya daga kan laifukan da sojoji suke aikatawa.
“A ranar 2 ga Mayu, 2025, wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne dauke da makamai sun kai hari kan wani Abu Iro, wani matashi dan shekara 23 a karamar hukumar Faskari, inda suka Sara masa Adda a kokarinsu na tafiya da shi. “Bayan samun rahoton, cikin gaggawa tawagar jami’an ‘yansanda tare da kungiyar tsaro ta cikin al’umma ta jihar Katsina (KSCWC), karkashin jagorancin babban jami’in tsaro na Faskari, suka amsa kira, inda suka dakile yunkurin yin garkuwa da mutane, tare da samun nasarar kubutar da wanda aka sace.” In ji Sadiq Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na...
’Yan fashi sun harbe mafarauta da fararen hula kimanin 19 har lahira a Karamar Hukumar Alƙaleri ta Jihar Bauchi. A yayin ziyarar da ya kai wurin, Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Bauchi, Sani-Omolori Aliyu, ya ba da umarnin yin cikakken bincike da kuma tura karin jami’an tsaro yankin. Mazauna kauyen Mansur sun ce an kashe ’yan farauta guda tara da kuma fararen hula guda goma, kuma an yi jana’izar ’yan bangar a kauyen Mansur kamar yadda addinin Musulunci ya tanada. Amma ’yan sanad da jami’an Ƙaramar Hukumar Alƙaleri ba su ce komai ba kan adadin mamatan ba. Kakakin ’yan sanda na jihar, CSP Ahmed Mohammed Wakil, ya ce kwamishinan ya tattauna da masu ruwa da tsaki a yankin, inda ya buƙaci...
’Yan fashi sun harbe mafarauta da fararen hula kimanin 19 har lahira a Karamar Hukumar Alƙaleri ta Jihar Bauchi. A yayin ziyarar da ya kai wurin, Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Bauchi, Sani-Omolori Aliyu, ya ba da umarnin yin cikakken bincike da kuma tura karin jami’an tsaro yankin. Mazauna kauyen Mansur sun ce an kashe ’yan farauta guda tara da kuma fararen hula guda goma, kuma an yi jana’izar ’yan bangar a kauyen Mansur kamar yadda addinin Musulunci ya tanada. Amma ’yan sanad da jami’an Ƙaramar Hukumar Alƙaleri ba su ce komai ba kan adadin mamatan ba. Kakakin ’yan sanda na jihar, CSP Ahmed Mohammed Wakil, ya ce kwamishinan ya tattauna da masu ruwa da tsaki a yankin, inda ya buƙaci...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya caccaki tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, Abdullahi Baffa Bichi da cewa maƙaryaci ne da ba shi da “kunya”. Gwamnan ya bayyana haka ne a yayin wani taro da ya yi tare da ilahirin kansiloli 484 da ke fadin jihar a ranar Lahadi da maraice. Kotu za ta rataye matashi kan kisan karuwa Lakurawa: Yadda mafarauta 13 suka gamu da ajalinsu a Sakkwato Abba Kabir Yusuf ya ce gwamnatinsa ba wajen zaman ɓarayi ba ce sabo da jajircewa wajen yaƙi da cin hanci da rashawa. Da ya ke jawabi a wajen taron da kansilolin, Gwamna Yusuf ya ce gwamnatinsa ba za ta lamunci satar kudin al’umma ba. A cewarsa, yana jagorantar gwamnati mai tsafta da kaffa-kaffa...
Kotu ta yanke wa wani matashi hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan kan laifin kashe wata karuwa bayan ya yi lalata da ita. Babban Kotun Jihar Ekiti ce ta yanke masa hukuncin bayan an gurfanar da shi kan zargin haɗa baki da kuma garkuwa da matar da kuma amfani da maganin kashe ciyawa wajen halaka ta a ranar 18 ga Afrilun 2024. Tun da farko mai gabatar da ƙara, Ibironke Odetola, ya bayyana wa kotun a ranar 6 ga watan Fabrairu, cewa wanda ake zargin ya haɗa baki d da wani abokinsa wajen sace matar da ke sana’ar kasuwanci. Wanda ake zargin, David Isaiah, mai shekara 26, ya shaida wa kotun cewa bayan ya yi lalata da matar ne ya...
Hukumar Tsare-Tsaren Biyan Fansho PTAD ta nesanta jami’anta daga laifin jinkirin biyan hakkokin tsofaffin ma’aikata masu ritaya. A cikin wata sanarwa da ta fitar a Abuja, hukumar ta bayyana cewa Babban Bankin Najeriya (CBN) ne ke da alhakin kai tsaye wajen tura kudaden fansho zuwa asusun tsofaffin ’yan kasa. PTAD ta roƙi afuwa kan jinkirin da aka samu, tana mai kira ga masu karban gansho da su jira shigowar kudi daga CBN, tana mai jaddada cewa an kammala dukkan shirye shirye da suka wajaba tun da farko. Wasu daga cikin tsofaffin ma’aikatan FRCN da NTA Kaduna sun bayyana bacin ransu kan ci gaba da jinkirin biyan hakkokinsu, musamman ganin cewa tsofaffin sojoji sun riga sun karɓi nasu hakkokin tun...