2025-11-02@19:46:02 GMT
إجمالي نتائج البحث: 11044
«kasar Amurka»:
Fitaccen Malamin Addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Gumi, ya shawarci Shugaba Bola Tinubu da ya ɗauki mataki mai tsauri a kan Shugaban Amurka, Donald Trump, game da barazanar da ya yi na amfani da ƙarfin soja a kan Najeriya. Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Lahadi, malamin ya bayyana cewa irin wannan magana ta Trump cin mutunci ce ga ’yancin Najeriya. Tsaro: Taimakonmu Amurka ya kamata ta yi maimakon barazana — Kwankwaso Kisan Kiristoci: Ba zan yaƙi ƙasar iyayena kan labaran ƙarya ba — Sojan Amurka Don haka malamin ya yi kira da a ɗauki matakin diflomasiyya cikin gaggawa. “Trump ya yi barazana ga ƙasa mai cin gashin kanta da harin soja, wannan girmamawa ne...
A 2022, kasashe shida ne suka daina yanke hukuncin kisa, ko dai gaba daya ko kuma wani bangare. Hudu daga cikinsu; Kazakhstan, Papua New Guinea, Saliyo, Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, sun jingine shi kwatakwata. Ekuatorial Guinea da Zambia sun ce za a rika amfani da shi ne kawai kan laifuka mafiya kololuwar muni. A watan Afrilun 2023, majalisar dokokin Malaysia ta kada kuri’ar daina amfani da shi a matsayin tilas kan laifuka 11, ciki har da kisa da kuma ta’addanci. Majalisar dokokin Ghana ma ta kada kuri’ar soke hukuncin kisa a watan Yulin 2023. Wadanne kasashe ne suka fi yanke hukuncin kisa? Kasashe 20 ne suka zartar da hukunbcin kisa a 2022, idan aka kwatanta da 18 da suka...
Ga yadda ake hada Fab biskit (wani irin biskit mai dandanon madara da sukari, mai taushi da dan kamshi kamar na “shortbread”). Da farko za ki samu roba haka sai ki zuba sukari da Bota, ki cakuda su da cokali ko maburkaki har sai sun hade jikinsu kuma sun yi laushi. Sannan ki fasa kwai a ciki, ki zuba filaibo, ki ci gaba da cakudawa. A wani kwano ko robar daban, ki hada fulawa, bakin fauda, madara, da dan gishiri. Sai ki zuba wannan hadin a cikin wancan kayan da kika fara hadawa. Ki gauraya su sosai har sai ya zama kullu mai laushi, ba mai taurin gaske ba. Idan ya yi tauri, ki kara dan madarar ruwa ko dan...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Wasanni Wolves Ta Kori Da Kocinta Vitor Pereira Sakamakon Rashin Nasara November 2, 2025 Wasanni Shin Mene Ne Matsalar Liverpool A Wannan Kakar? November 2, 2025 Wasanni Waye Zai Lashe Ƙyautar Gwarzon Ɗan Wasan Afrika Na 2025? November 1, 2025
Da yake kaddamar da shirin, Darakta Janar na IRM, Alhaji Anas Muhammad, ya ce an kirkiro da shirin ne domin karfafa zaman lafiya da hadin kai ta hanyar tallafa wa Musulmai da Kiristoci ta bangaren samar da kiwon lafiya da bayar da tallafin kayan abinci da jari. Ya ce: “Kalubalen lafiya ba sa bambance addini ko kabila, don haka bama bambantawa wajen bayar da tallafin. in sha Allah zamu ci gaba da aiwatar da irin wannan shiri a fadin jihar Kaduna baki daya.” A nasa jawabin, Shugaban hukumar KADCHMA, Malam Abubakar Hassan, ya bayyana cewa wannan hadin gwiwa tana nuna muhimmancin dangantaka tsakanin gwamnati da kungiyoyi masu zaman kansu wajen cimma dorewar tsarin inshorar lafiya ga kowa. ...
Taron APEC Na 2026 Da Za A Shirya A Kasar Sin Zai Bude Sabon Babin Na Gina Al’ummar Bai Daya Ta Asiya-Pasifik
Bayan an mika damar karbar bakuncin taron kungiyar APEC, kasashen duniya sun soma zura ido kan kasar Sin. Ana sa ran cewa, taron APEC da za a gudanar a Shenzhen, zai kara habaka hadin gwiwa, da samun ci gaba, da wadata tare a shiyyar, kana zai shaida yadda kasar Sin ke kara samar da sabbin damammaki ga yankin Asiya da Pasifik, bisa ga sabbin nasarorin da take samu ta hanyar zamanantarwa irin ta kasar Sin. (Mai fassara Bilkisu Xin) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin An Bude Sabon Babin Huldar Sin Da Koriya Ta Kudu November 2, 2025 Daga Birnin Sin Sin: Katsalandan Cikin Harkokin Kamfani Da Netherlands Ta Yi Ya Kawo Tsaiko Ga Tsarin Masana’antu Da...
Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana damuwarsa kan kalaman da Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi game da Najeriya. Kwankwaso, ya yi wannan magana ne bayan Trump ya yi barazanar ɗaukar matakin yaƙi game da zargin kisan kiyashi da ake yi wa Kiristoci. Kisan Kiristoci: Ba zan yaƙi ƙasar iyayena kan labaran ƙarya ba — Sojan Amurka Kisan Kiristoci: Lauyoyi sun nemi Gwamnatin Tarayya ta tattauna da Amurka A cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Kwankwaso, ya ce Najeriya ƙasa ce mai cikakken ’yanci, wadda ke fama da matsalar tsaro daga miyagu a sassa daban-daban na ƙasar. “Matsalar tsaron da muke fuskanta ba ta bambanta tsakanin addini, ƙabila ko ra’ayin siyasa,” in ji...
Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana damuwarsa kan kalaman da Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi game da Najeriya. Kwankwaso, ya yi wannan magana ne bayan Trump ya yi barazanar ɗaukar matakin yaƙi game da zargin kisan kiyashi da ake yi wa Kiristoci. Kisan Kiristoci: Ba zan yaƙi ƙasar iyayena kan labaran ƙarya ba — Sojan Amurka Kisan Kiristoci: Lauyoyi sun nemi Gwamnatin Tarayya ta tattauna da Amurka A cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Kwankwaso, ya ce Najeriya ƙasa ce mai cikakken ’yanci, wadda ke fama da matsalar tsaro daga miyagu a sassa daban-daban na ƙasar. “Matsalar tsaron da muke fuskanta ba ta bambanta tsakanin addini, ƙabila ko ra’ayin siyasa,” in ji...
Imam Ali shi ne halifan Annabi Muhammad na hudu a mahangar Ahlussunnan, amma mabiya mazhabar Shi’a na daukar sa a matsayin na farko daga cikin imamansu 12. Wannan ya sanya akasarin mabiya Shi’a na Iraki kan bukaci a binne su a makabartar, kuma sanadiyyar saukin sufuri a zamunnan baya-bayan nan, wasu mabiya Shi’a daga kasashen duniya kan so a binne su a makabartar. Tsarin makabartar ya kasance cakuduwa ce ta gine-ginen hubbarai irin na zamanin baya, da hanyoyi masu tsuku da suka ratsa ta cikinta da kuma wasu wurare da ake yi wa kallon masu tsarki. Me ya sa ake kiran makabartar Wadi al-Salam? Ana kiran makabartar da sunan Wadi al-Salam, wato ‘kwarin aminci’ ne saboda dalilai na tarihi...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Sin: Katsalandan Cikin Harkokin Kamfani Da Netherlands Ta Yi Ya Kawo Tsaiko Ga Tsarin Masana’antu Da Samar Da Kayayyaki Na Duniya November 1, 2025 Daga Birnin Sin An Gudanar Da Taron Tattaunawa Na Duniya Kan Kirkire-Kirkire Da Bude Kofa Da Ci Gaba Na Bai Daya A Nijeriya November 1, 2025 Daga Birnin Sin Sabbin ‘Yan Saman Jannatin Kasar Sin Sun Shiga Tashar Sararin Samaniya Ta Kasar November 1, 2025
Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Faɗaɗa masana’antar makamashin nukiliyar Iran don inganta rayuwar mutanen kasar ne, ba don makamai ba Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya gana da manyan jami’ai a masana’antar makamashin nukiliya ta ƙasar a lokacin ziyarar da ya kai Hukumar Makamashin Nukiliya ta Iran (AEOI). Shugaban Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Masoud Pezeshkian, ya ziyarci AEOI a ranar Asabar da yamma, inda ya gana da wasu manyan jami’ai a masana’antar makamashin nukiliyar. A yayin taron, Shugaba Pezeshkian ya jaddada cewa: Abin takaici, farfagandar son zuciya ta sanya ra’ayin “Makamashin nukiliya” ya zama daidai da samar da makaman nukiliya. Ya ce, “Samar da bama-bamai na nukiliya ƙaramin ɓangare ne kawai na sakamakon da ba su dace ba da...
Ministan harkokin wajen Iran ya jaddada cewa: Isra’ila ba za ta kai hari kan Iran ba sai da goyon bayan Amurka Ministan harkokin wajen Iran Seyyed Abbas Araqchi ya bayyana cewa: Gwamnatin ‘yan sahayoniyya ba za ta kaddamar da yaki kan Jamhuriyar Musulunci ba tare da samun wata kariya daga Amurka ba. Ya kara da cewa, Iran ta gudanar da yakin kwanaki goma sha biyu da wannan gwamnati mai wuce gona da iri, kuma ta hana ta ci gaba da mummunar manufarta ta mamaya a yankin. A wata hira da ya yi da gidan talabijin na Al- Jazeera, Araqchi ya yi nuni da cewa: Gwamnatin masu wuce gona da iri ta yi kokarin fadada yakin zuwa yankin ta hanyar kai...
Sakataren Majalisar Tsaron kasar Iran ya jaddada cewa: Ba suna cewa ba za su gudanar da tattaunawa ba ne, amma tattaunawar dole ta kasance ta gaskiya Sakataren Majalisar Tsaron Kasa ta Iran, Ali Larijani, ya tabbatar da cewa: Ba za a iya kwantar da hankalin makiya ta hanyar yin sassauci da rashin gindaya sharaɗi ba. Da yake jawabi a wani taron masana ilimin bil’adama a birnin Tehran fadar mulkin kasar Iran ‘yan kwanaki da suka gabata, Larijani ya bayyana cewa: “Hanya madaidaiciya ta gyara halayen makiyansu tana cikin ƙarfafa haɗin kan ƙasa, kuma tushenta shine gyare-gyaren tattalin arziki da dawo da kwanciyar hankali ga rayuwar mutane.” Sakataren Majalisar Tsaron kasar Iran ya jaddada cewa: Ba za a iya kwantar da...
Gwamnatin mamayar Isra’ila ta yanke hukuncin kisa kan masu fama da cutar kansa da kuma waɗanda suke fama da matsalar koda na mutuwa a Gaza domin hana fitar da su wata kasa don neman magani Cibiyar Kare Hakkin Dan Adam ta Gaza ta bayyana matukar damuwarta game da tabarbarewar lafiyar marasa lafiya da ke fama da cutar kansa da kuma cutar koda a Zirin Gaza. Wadannan cututtuka sun kara ta’azzara ne sakamakon hare-haren sojojin mamayar Isra’ila kan Gaza da kuma ci gaba da killace yankin bayan tsagaita bude wuta, gami da hana shigar dq magunguna da kayayyakin ayyukan likitanci masu muhimmanci cikin yankin. Cibiyar ta kuma yi nuni da tsauraran matakan fitar da marasa lafiya zuwa ƙasashen waje don neman...
Qatar ta bayar da tallafin gaggawa ga mutanen da suka rasa matsugunansu a Sudan Gwamnatin Qatar ta aika da agajin gaggawa da tallafin jin kai zuwa birnin Ad-Dabba da ke Jihar Arewacin Sudan domin rage wa dubban mutanen da suka rasa matsuguninsu da ke tserewa daga El Fasher, babban birnin Jihar Arewacin Darfur. Ma’aikatar Harkokin Waje ta Qatar ta bayyana cewa: “Wannan tallafin ya zo ne a cikin tsarin jajircewar Qatar na tallafawa ‘yan uwantaka na Sudan, musamman idan aka yi la’akari da mawuyacin halin jin kai da fararen hula ke ciki, ciki har da karancin abinci mai tsanani da kuma karuwar bukatar matsugunai da kayan masarufi.” Sanarwar ta kara da cewa wannan tallafin wani bangare ne na kokarin da...
Wani sojan Ƙasar Amurka ɗan asalin Jihar Kano, Suleiman Isah, wanda yake aiki a rundunar sojin Amurka, ya ce ba zai yaƙi da ƙasarsa ta haihuwa ba saboda yaɗa labaran ƙarya game da yi wa Kiristoci kisan gilla a Najeriya. Isah, wanda ya shiga rundunar sojin Amurka shekaru biyu da suka gabata, yana aiki ne da rundunar California Army National Guard, mai dakaru sama da 18,000. Kisan Kiristoci: Lauyoyi sun nemi Gwamnatin Tarayya ta tattauna da Amurka Muna shirin kai farmaki a Nijeriya — Ma’aikatar Yaƙin Amurka A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook wanda Aminiya ta tabbatar, Isah ya mayar da martani kan jita-jitar cewa Amurka za ta ɗauki matakin yaƙi a kan Najeriya saboda zargin...
Shi ma wasan da ta yi nasara a kan kungiyar Sifaniya a daf da za a tashi ta ci kwallon a gasar Zakarun Turai da na Newcastle United a Premier League. Tun daga nan alamomi suka fara bayyana cewar akwai tarin matsaloli a Liberpool, wadda kowanne wasa kwallo ke shiga ragarta in ban da wanda ta yi nasara a kan Arsenal 1-0 a Premier League cikin Agusta da wanda ta ci Burnley 1-0 a cikin watan Satumba a Premier League. Sababbnin ‘Yanwasan da Liberpool ta saya a kakar banamages Giorgi Mamardashbili daga Balencia Jeremie Frimpong daga Bayern Leberkusen, Florian Wirtz daga Bayern Leberkusen, Milos Kerkez daga Bournemouth, Hugo Ekitike daga Eintracht Frankfurt, Aledander Isak daga Newcastle United, Armin Pecsi daga...
Duk da cewa suna da karfi a fannin aikin soja, amma harinsu zai zama tamkar amfani da igwa ne wajen kashe sauro. Duk wani fifikon da suke da shi ba zai dore ba. Saboda haka, a zahiri wannan tambayar da wani mai amfani da yanar gizo ya yi, ta nuna rashin hankali cikin kalaman shugaban Amurka. Sai dai kalaman sun dace da halayya, da salon musamman na shugaba Donald Trump. Wani lokaci, da gangan ya kan yi amfani da kalmomi, da aikace-aikace marasa ma’ana wajen samar da yanayi na rashin tabbas, ta yadda zai samu damar matsawa wani lamba, don tilasta masa ya yi wani aiki. Wannan dabara ce da wasu masanan kasar Amurka ke kira da “ka’idar...
Yawan shafa man kade a wurin ma yana rage ta sosai. Daga karshe Ina kira ga mata da su daure da zarar sun haihu su fara neman hanyan magance wannan matsalar kuma ku sani cewa wannan hadin gargajiya ne babu Kemikal a cikinsa don haka yana daukar lokaci kafin a ga canji kamar, sati biyu idan ba ki ga canji ba sai ki dauki wani kuma. Allah shi ne masani. Allah yasa mu dace. Ga hanyoyi guda 5 da za’a iya magance su a saukake ba tare da amfani da mayuka masu illlata fata ba Hanya ta 1: Dankalin Hausa Dankali yana dauke da sinadarin sitaci da yake lausasa fata da kuma sinadarin da yake hana fata lalacewa wato antiodidant....
Manajar ofishin na NIWA, da ke a jihar ta Legas Injiniya Sarat Braimah ta bayyana cewa, tura ma’ikatan hukumar domin yin aikin, zai taimaka wajen gudanar da aikin a cikin inganci. Kazalika, ya sanar da cewa, hakan zai kuma bayar da damar yin safarar kaya a cikin sauki da kuma safarar matafiya da ke bin hanyar ruwa ta yankin na Ikorodu. “Mun yi nazari a cikin kwanciyar hankali kan yadda za a tabbatar da an cire fulawar da ke a cikin kasan ruwan ba tare da wata miskila ba tare da kuma bai wa jiragen ruwan damar yin zirga-zirgarsu a hanyoyin ruwan, ba tare da wata matsala ba, “ Inji Injiya Braimah. “ Aikin ya wuce batun fannin samar da...
A yayin da ake ci gaba da cece-kuce kan kalaman Shugaban Amurka Donald Trump da ke zargin gwamnatin Nijeriya da watsi da batun kisan Kiristoci a ƙasar, Ma’aikatar Yaƙin Amurka ta bayyana cewa ta fara shirin kai farmaki a Nijeriya. Sakataren Ma’aikatar, Pete Hegseth, ne ya tabbatar da hakan cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Asabar, yana mai cewa ma’aikatarsa “na shirye-shiryen ɗaukar mataki” bayan umarnin da Trump ya bayar. Jamus ta shiga sahun ƙasashen da ke neman kawo ƙarshen yaƙin Sudan Tinubu zai gana da Trump kan zargin kisan Kiristoci a Nijeriya “Muna shirye-shirye don ɗaukar mataki a Nijeriya. Idan gwamnatin Nijeriya ba ta kare Kiristoci ba, za mu kai hari, mu kawar...
Da yake mayar da martani ga wannan zargin na Amurka, Bwala ya ce gwamnatin Tinubu tana jajircewa wajen kare dukkan ‘yan Nijeriya ba tare da la’akari da addini ba, yana mai cewa Amurka da Nijeriya sun dade suna hadin gwiwa a yaki da ta’addanci. “Shugaba Bola Tinubu da Shugaba Donald Trump suna da kudiri iri ɗaya a yaƙi da ta’addanci da duk wani nau’in ta’addanci a kan bil’adama,” in ji Bwala. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai An Kashe Mutum 3 Yayin Da ‘Yan Bindiga Suka Kai Hari Kan Iyakokin Kano November 2, 2025 Manyan Labarai Yadda Ƴan Mata Ke Kashe Kuɗaɗe Wajen Yi Wa Samarinsu Hidima November 1, 2025 Manyan Labarai Tinubu Ya Kaddamar Da...
Babban dakaktan hukumar kula da makamashin nukiliya ta Duniya ya tabbatar da cewa Iran ba ta kera makaman nukiliya ba, yana mai jaddada cewa tana ci gaba da kasancewa cikin yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya (NPT). Rafael Grossi, ya shaida wa manema labarai a hedikwatar Majalisar Dinkin Duniya da ke New York cewa “Zan iya cewa babu wani shirin makamin nukiliya domin mun dade muna duba shi. Wannan ya zo ne yayin da Iran ta yi gargadin cewa aiwatar da abin da ake kira “snapback” da sake sanya takunkumin Majalisar Dinkin Duniya da kasashen Turai uku za su soke yarjejeniyar da ta yi da IAEA kan sake fara hadin gwiwa da aka sanya wa hannu a birnin Alkahira a ranar...
Sakataren Ma’aikatar Yaki na Amurka, Pete Hegseth, ya ce ma’aikatarsa na shirin daukar matakin soja idan gwamnatin Najeriya ta gaza kawo karshen “kashe-kashen Kiristoci marasa laifi” a kasar. Hegseth, yana mayar da martani ga wani sako da Shugaban Amurka Donald Trump ya wallafa a Truth Social, inda ya zargi gwamnatin Najeriya da yin shiru kan hare-haren da ake kai wa Kiristoci. Gwamnatin Najeriya ta mayar da martani kan jawabin da shugaban Amurka Donald Trump ya yi inda yake zargin kashe kiristoci a Najeriyar. A martanin da ta mayar, ma’aikatar harkokin wajen Najeriya, ta ce lamarin ba haka ba ne. Sanarwar da kakakin ma’aikatar Kimiebi Imomotimi Ebienfa ya sanya wa hannu, ta ce, “duk da cewa Najeriya na godiya da kulawar...
Ofishin yada labarai na gwamnati a Gaza ya musanta zargin da y ace karce ce ” da rundunar sojin Amurka (CENTCOM) ta yi cewa Hamas ta sace wata babbar mota dauke da kayan agaji. “Mun tabbatar da cewa wannan zargin karya ne, kuma wani bangare ne na manufar kafofin watsa labarai da nufin bata sunan rundunar ‘yan sandan Falasdinu, wadanda ke aikinsu na kasa da na jin kai na neman taimako da kare ayarin motocin agaji,” in ji Ismail Al-Thawabta, darektan ofishin yada labarai na gwamnatin Gaza. Yakara da cewa ba a fayyace ainihin rana, lokaci, da wurin da lamarin ya faru ba, Al-Thawabta ya bayyana bidiyon a matsayin “yunkuri bayyananne na yada bayanai marasa tushe.” Sanarwar ta karyata ikirarin...
Fadar Gwamnatin Nijeriya ta bayyana cewa nan da wasu kwanaki Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai gana da takwaransa na Amurka, Donald Trump, domin tattaunawa kan zargin kisan Kiristoci a Nijeriya. Mai ba wa Shugaba Tinubu shawara na musamman kan yaɗa manufofi, Daniel Bwala, ne ya tabbatar da hakan a cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X. Kisan Kiristoci: Za mu kai hari Najeriya — Trump Jamus ta shiga sahun ƙasashen da ke neman kawo ƙarshen yaƙin Sudan A cewar Daniel Bwala, shugabannin biyu — Tinubu da Trump — sun yi tarayya da juna kan fahimta ta haɗin kai wajen yaƙi da ta’addanci da duk wata barazana ga bil’adama. “A bayan nan Shugaba Trump ya taimaka wajen ba...
Jamus ta shiga sahun ƙasashen duniya da ke kiran a gaggauta tsagaita wuta a yaƙin da ke ci gaba da salwantar rayuka a ƙasar Sudan. Sama da shekaru biyu ke nan Sudan na fama da yaƙin da ya ɗaiɗaita fararen hula baya ga asarar rayuka. Rikicin PDP: Tsagin Wike ya dakatar da Damagum Kisan Kiristoci: Za mu kai hari Najeriya — Trump Ministan Harkokin Wajen Jamus, Johann Wadephul, ya bayyana halin da Sudan ke ciki a matsayin “mummunan bala’i,” yana mai cewa babbar matsalar jinkai ta duniya a yanzu ta tattara ne a Sudan ɗin. A taron da aka gudanar a Bahrain, ƙasashen Birtaniya da Jordan su ma sun yi magana kan rikicin, suna kiran da a kawo ƙarshen...
Majiyar ta kara da cewa, bayan yunkurinsu bai yi nasara ba a Tsanyawa, maharan sun sake wani sabon shiri, inda suka kai hari a kauyen Yar Tsamiya da ke gundumar Faruruwa, karamar hukumar Shanono, da misalin karfe 1:30 na dare, inda suka kashe mutane uku suka, tare da sace wasu uku. Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, hukumomin tsaro ba su fitar da wata sanarwa a hukumance kan lamarin ba. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Yadda Ƴan Mata Ke Kashe Kuɗaɗe Wajen Yi Wa Samarinsu Hidima November 1, 2025 Manyan Labarai Tinubu Ya Kaddamar Da Ayyuka Bakwai A Jami’ar Ilori November 1, 2025 Manyan Labarai Rikicin PDP Ya Ƙara Ta’azzara Yayin Da Ɓangarori Ke Dakatar Da...
Shugaban Amurka Donald Trump ya yi barazanar amfani da ƙarfin soji kan Najeriya matuƙar gwamnatin ƙasar ba ta dakatar da kisan da ’yan ta’adda masu iƙirarin jihadi ke yi wa Kiristoci ba. A yammacin jiya Asabar ne Trump ya umarci Ma’aikatar Yaƙin Amurka ta Pentagon da ta soma tsara yadda za a kai hari Nijeriya bayan da ya yi zargin cewa ana yi wa Kiristoci kisan gilla a ƙasar. Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Truth Social, Trump ya ce Amurka a shirye ta ke ta aike da sojoji da manyan makamai cikin Najeriya don bai wa Kiristocin kariya. Barazanar shugaban na Amurka na zuwa ne kwana guda bayan ya yi iƙirarin cewa an kashe Kiristoci aƙalla...
Rahotanni da muka samu sun nuna cew wasu yan ta’adda sun kashe wasu dakarun sa kai guda biyu a kudu masu gabashin iran a yankin sisitan Baluchistan. Jami’In huda da jama’a na dakarun kare juyi yayi karin harke game da harin da aka kai, yace an kashe mutane ne yayin da suke kokarin ketare da jami’an tsaro suna tafiya akan babbar hanyar da ta hada birnin kashsh dake lardin da kuma babban birnin zahidan An bayyana cewa wanda abin ya shafa sun hada da Esma’il shavarzi da kuma mukhtar shahouze da kuma wadanda suka samu mummuan rauni a lokacin kai harin Lardin sistan baluchestan na da iyaka da kasar Pakistan da ya dade yana fuskantar tashe tashen hankula kan fararen...
Taron kaddamar da rabar da taraktocin noman, ya gudana ne a Shalkwatar Ma’aikatar Kula da Aikin noma da kuma yin Noman Rani da ke garin Kalaba. Kazalika, taron ya samu halartar ‘yan Majalisa da Sarakunan Gargajiya da kungiyoyin manoma mata da masu ruwa da tsaki a fannin aikin noma da ke jihar da abokan hadaka. Daukacinsu, sun jinjina wa wannan kokari na gwamna Bassey, kan wannan hangen nesa da gwamnatinsa ta yi, na kaddamar da taraktocin noman, musamman domin ciyar da fannin aikin noman jihar gaba, duba da cewa; fannin ne kinshikin tattalin arzikin jihar. Har ila yau, gwamna Bassey, ya nanata kudurin gwamnatinsa wajen ci gaba da bai wa fannin aikin noma muhimmanci a matsayin fannin...
Naurorin tauraron dan adam sun nuna hoton yadda sojojin Amurka suke kara kusantar kasar venuzuwela ciki har da jiragen yaki masu kai hare-hare duk da yake cewa shugaban Amurka Dolad trump ya karyata batun da ake yi na yunkurin kai mata harin soji, Wannan matakin yana daya daga cikin yadda sojojin ruwan Amurka suka mayar da hankali a yankin karebiya, wanda hakan ya haifar da damuwa a latin Amurka game da yiyuwar daukar matakin soji na bangare daya kan kasar Venuzuwela ba tare da izinin majalisar dinkin duniya ko kuma kasashen duniya ba, Washington ta yi ikirarin cewa za ta kai hari kan masu fataucin miyagun kwayoyi ne sai dai masu sa ido kan alamuran yankin sun bayyana cewa yanayin...
A ci gaba da keta yarjejeniyar dakatar da bude wuta da HKI ke yi a kasar labanon a jiya ma ta kai hari a kudancin kasar kuma ta yi sanadiyar mutuwar mauta 4 tare da jikkata wasu guda 3, Isra’ila ta kai hari da jirgin sama mara matuki kan wata mota a kauyen kafr rumman , kana kuma ta sake kai wani harin a garin kafr sir kamar yadda rahotanni suka bayyana, kuma wadannan hare haren suna zuwa ne kwanaki 3 bayan da sojojin israila suka kai samame ta kasa a kudancin labanon a yankin Nabatiya inda suka kai hari a jiya, A ranar jumaa da ta gabata ne shugaban kasar ta labanon joseph Aun ya nuna damuwarsa game da...
Ministan harkokin wajen kasar iran Abbas Araqchi a wata hira da yayi da gidan talabijin din Aljazeera ya gargadi isra’ila kuma yayi cikakkan bayani kan shirin nukiliyar iran na zaman lafiya , da kuma halin da yankin ke ciki da yi yuwar sake komawa teburin tattaunawa da kasar Amurka. Wannan bayani yazo ne adaidai lokacin da lamura ke kara zafi a yankin bayan yakin da aka yi tsakanin iran da kuma Israila, don haka bayanan na Araqchi wata sanarwa ce dake nuna shirin iran na mayar da martani amma kuma tabar kofar tattaunawar diplomasiya a bude. Har ila yau ministan ya bayyana cewa iran a shirye take ta tunkari duk wani kalu-bale, kuma za ta mayar da martani mai karfi...
Shugaba Trump ya yi barazanar daukar matakin soji kan Najeriya, yana mai zargin gwamnatin kasar da kyalewa ana kashe kiristoci. A wani sako da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, Trump ya ce Washington na iya shiga Najeriya da ƙarfin soji don kakkabe abin da ya kira ƴanta’adda masu kishin Islama da ke aikata ta’asa. Ya kuma yi barazanar dakatar da duk wani taimakon da Amurka ke bawa Najeriya. Tuni Najeriya ta yi watsi da ikirarin cewa ana kashe kiristoci ba gaira ba dalili a yankin arewacin inda galibi musulmi suka fi yawa. A bayanin da Trump ya wallafa a kafar sadar zumuntarsa ta Truth a ranar Asabar ya ce ya ba wa ma’aikatar tsaron Amurka damar ta fara...
Rikicin jam’iyyar PDP ya ƙara tsananta bayan sakataren jam’iyyar na ƙasa, Sanata Samuel Anyanwu, ya sanar da dakatar da shugaban jam’iyyar na ƙasa, Ambasada Illiya Damagum. Yayin da yake yi wa manema labarai jawabi a Abuja, Anyanwu, wanda yake ɗan tsagin Nyesom Wike, ya ce an dakatar da Damagum da wasu manyan jami’an jam’iyyar guda biyar saboda zargin rashin ƙwarewa, almundahana, da ƙin bin hukuncin kotu. Kiristoci: Najeriya ba ta yadda da cin zarafin addini ba — Tinubu PDP ta dakatar da Anyanwu da wasu ’yan tsagin Wike “Mun yanke shawarar dakatar da shugaban jam’iyyar na ƙasa, Ambasada Ilya Damagum, saboda rashin ƙwarewa, almundahana, da ƙin mutunta hukuncin kotu,” in ji Anyanwu. “An dakatar da shi na tsawon wata guda,...
Bug da kari Tinubu ya jinjina wa Shugaban jami’ar, Farfesa Wahab Olasupo Egbewole (SAN)da ‘yan tawagarsa wajen maida hankalin da suka yi na bunkasa Jami’ar da kumna kudurinta na muradun ci gaban da ake bukata. Shi ma anashi jawabin Shugaban Jami’ar Sarkin Katsina, Alhaji. Abdulmumin Kabir Usman, wanda Wazirin Katsina, Sanata Ibrahim Idah ya wakilta, ya nuna jin dadinsa kan irin kokarin da UNILORIN saboda bunkasar ilimi da kumasamar wuraren koyon kaaratu masu kyau da kuma suka dace. Ya yi ma kallon ayyukan da ak kaddamar a matsayin“ irin abubuwan da ake bukatar gani ke nan”da za su taimakawa lamarin koyarwa, koyo,da kuma bincike, inda ya kara da cewa yadda Jami’ar ta maida hankalinta wajen bunkasa dabarar koyon yin abubuwa...
Wannan mataki ne awanni kaɗan bayan ɓangaren Damagum ya dakatar da Anyanwu da wasu mutane uku, lamarin da ya ƙara ta’azzaea rikicin shugabanci a cikin jam’iyyar PDP. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Dalibin Jami’ar Jos Ya Kashe Abokinsa Ya Binne Gawar A Rami November 1, 2025 Manyan Labarai Sojoji Sun Kama Ƴan Ta’adda 20, Sun Ceto Mutane 17 Da Aka Yi Garkuwa Da Su November 1, 2025 Manyan Labarai Gwamnatin Tarayya Ta Mayar Da Martani Kan Iƙirarin Trump Na Kisan Ƙare Dangi Ga Kiristoci November 1, 2025
Sin: Katsalandan Cikin Harkokin Kamfani Da Netherlands Ta Yi Ya Kawo Tsaiko Ga Tsarin Masana’antu Da Samar Da Kayayyaki Na Duniya
Ya ce Sin tana maraba da kamfanonin dake fuskantar kalubale su tuntubi ma’aikatar ko hukumomi masu ruwa da tsaki, yana cewa, ma’aikatar za ta nazarci ainihin abubuwan dake faruwa da kuma bayar da damar fitar da kayayyaki ga wadanda suka cancanta. (Mai fassara: FMM) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin An Gudanar Da Taron Tattaunawa Na Duniya Kan Kirkire-Kirkire Da Bude Kofa Da Ci Gaba Na Bai Daya A Nijeriya November 1, 2025 Daga Birnin Sin Sabbin ‘Yan Saman Jannatin Kasar Sin Sun Shiga Tashar Sararin Samaniya Ta Kasar November 1, 2025 Daga Birnin Sin Xi Jinping Ya Tattauna Da Shugaban Koriya Ta Kudu Lee Jae-myung November 1, 2025
Shugaba Bola Tinubu ya mayar wa da Shugaban Amurka, Donald Trump martani cewa Najeriya ba ta yadda da duk wani nau’in zarafin addini. Tinubu, ya yi wannan bayani ne bayan Trump ya sake sanya Najeriya cikin jerin ƙasashen da ake kiran “Ƙasashen da ke da Babbar Matsala wajen ’Yancin Addini.” PDP ta dakatar da Anyanwu da wasu ’yan tsagin Wike Sharrin son auren Mai Wushirya aka yi min — Mansura Isa Trump ya yi iƙirarin cewa Kiristoci a Najeriya na fuskantar barazana, amma ya sha alwashin cewa Amurka za ta kare su. A cikin wani saƙo da ya wallafa a kafafen sada zumunta, Trump ya rubuta cewa: “Addinin Kirista yana fuskantar babbar barazana a Najeriya. Ana kashe dubban Kiristoci.” A...
Jagoran ‘yan hamayyar siyasar kasar Kamaru Issa Chiroma Bakary ya kira yi magoya bayansa da su dakatar da dukkanin harkoki domin a tsayar da kasar wuri a matsayin ci gab da nuna kin amincewa da sakamamon zabe. A can garin Marwa dake a matsayin babban birnin Arewacain kasar,dukkanin harkokin yau da kullum sun tsaya kacokau. Wani dan kasuwa ya bayyana cewa, rufe kasuwa a wurinsu abu ne mai wahala,amma za su yi ne saboda tsoron kar a kona musu shaguna. Haka nan kuma ya ce, kasuwar ma ta tsaya cak saboda babu masu saye da suke zuwa. Da akwai garuruwa da dama da su ka zama kango, saboda kaurewa harkokin yau da kullum da mutane su ka yi a ci...
Hukumar kare hakkin bil’adam dake karkashin MDD ya sanar da cewa tana sa ido akan kashe-kashe da rashin adalcin da ake yi a karkashin zaben shugaban kas ana kasar Tanzania. Tun a ranar Larabar da ta gabata ne dai da ake zaben rikici ya barke a kasar sabod kin amincewar ‘yan hamayya akan yadda zaben zai gudana ba tare da manyan ‘yan takara ba. Shugabar kasar Samia Suluhu Hassan ce dai babbar ‘yar takara. Babbar jam’iyyar adawa ta sanar da cewa fiye da mutane 700 ne aka kashe a fadin kasar da ake Zanga-zanga. Shugaban ofishin hukumar kare hakkin bil’adama na MDD Seif Magango ya sanar da cewa; Sun karbi rahoranni daga majiya mai tush akan cewa a kalla...
An Gudanar Da Taron Tattaunawa Na Duniya Kan Kirkire-Kirkire Da Bude Kofa Da Ci Gaba Na Bai Daya A Nijeriya
An gudanar da taron tattaunawa na duniya kan kirkire-kirkire da bude kofa da ci gaba na bai daya, jiya Juma’a a birnin Lagos na Nijeriya. Yayin taron wanda babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na Sin CMG da karamin ofishin jakadancin Sin dake Lagos suka shirya, ministan kula da harkokin matasa na Nijeriya Ayodele Olawande da shugaban CMG Shen Haixiong, sun gabatar da jawabai ta kafar bidiyo. A cewar ministan na Nijeriya, cikin shekaru 5 da suka gabata, dubban matasan kasar sun ci gajiyar tallafin karatu da shirye-shiryen horo da na musaya da Sin ta samar, kuma wannan hadin gwiwa da ake yi a aikace ya kara fahimta da aminci tsakanin kasashen biyu. Ya kara da cewa, a shirye ma’aikatarsa...
Shugaban kasar Nigeria Bola Ahmad Tinubu ya fada wa Shugaban Amurka Donald Trump cewa; a Nigeria ba a lamunta da duk wani rikicin addini. Shugaban na kasar Najeriya ta mayar wa da Tinubu martani ne saboda yadda ya bayyana Najeriya a matsayin kasa mai jawo damuwa ta musamman”, bisa zargin cewa Mabiya addinin kiristanci suna fuskantar barazanar karewa, ya kuma yi alkawalin cewa Amurkan za ta ba su kariya. Donald Trump ya ce; Kiristoci suna fuskantar barazanar karar da su a Nigeria, an kuma kashe dubban kiristoci a kasar.” A yau Asabar, kwana daya daga wancan zancen na Tinibu ne dai shugaban kasar ta Nigeria Bola Ahamd Tinubu mayar da martanin da ya kunshi cewa: Nageria kasa ce ta Demokradiyya,...
Ofishin kula da zirga-zirgar kumbuna masu dauke da mutane na kasar Sin ya ce, an harba kumbon Shenzhou-21 mai dauke da ‘yan sama jannatin kasar Sin 3 cikin nasara, a daren jiya Juma’a, agogon Beijing. Daga baya kumbon ya sarrafa kansa wajen hade jikinsa da na tashar binciken sararin samaniya ta kasar Sin, ta yadda ‘yan saman jannatin suka shiga tashar, inda tsoffin ‘yan saman jannati 3 da suka dade a cikin tashar, suka yi musu maraba. Hakan ya shaida haduwar sabbi da tsoffin ‘yan sama jannatin kasar Sin karo na 7 a tashar binciken sararin samaniya ta kasar. Bisa shirin da aka yi, wadannan ‘yan sama jannati 6 za su kwashe kimanin kwanaki 5 suna aiki tare a cikin...
Rikici a babbar jam’iyyar adawa ta PDP, na ƙara ƙamari, bayan da jam’iyyar ta dakatar da sakatarenta na ƙasa, Sanata Samuel Anyanwu, da wasu da ake ganin ’yan tsagin Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike ne. Mai magana da yawun jam’iyyar na ƙasa, Debo Ologunagba ne, ya sanar da dakatarwar bayan wani taro da Kwamitin Ayyuka na Ƙasa (NWC), ya gudanar a hedikwatar jam’iyyar da ke Abuja. Zargin Kisan Kiristoci: Maganar Trump a kan Najeriya tsagwaron ƙarya ce — Shehu Sani Zaɓen Tanzania: Shugaba Samia ta yi tazarce da kashi 97 an ƙuri’u Sauran da aka dakatar sun haɗa da Mai Bai wa jam’iyyar Shawara kan Harkokin Shari’a, Kamaldeen Ajibade (SAN); Sakataren Tsara Harkokin Jam’iyya, Umar Bature; da Mataimakin...
Rikici a babbar jam’iyyar adawa ta PDP, na ƙara ƙamari, bayan da jam’iyyar ta dakatar da sakatarenta na ƙasa, Sanata Samuel Anyanwu, da wasu da ake ganin ’yan tsagin Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike ne. Mai magana da yawun jam’iyyar na ƙasa, Debo Ologunagba ne, ya sanar da dakatarwar bayan wani taro da Kwamitin Ayyuka na Ƙasa (NWC), ya gudanar a hedikwatar jam’iyyar da ke Abuja. Zargin Kisan Kiristoci: Maganar Trump a kan Najeriya tsagwaron ƙarya ce — Shehu Sani Zaɓen Tanzania: Shugaba Samia ta yi tazarce da kashi 97 an ƙuri’u Sauran da aka dakatar sun haɗa da Mai Bai wa jam’iyyar Shawara kan Harkokin Shari’a, Kamaldeen Ajibade (SAN); Sakataren Tsara Harkokin Jam’iyya, Umar Bature; da Mataimakin...
A wannan rana, a gun taron manema labarai da aka gudanar bayan kwarya-kwaryar taron shugabannin kungiyar APEC, Lee Jae-myung ya ce hadin gwiwar tattalin arziki tsakanin Sin da Koriya ta Kudu yana da matukar muhimmanci, ya kuma yi imanin cewa birnin Shenzhen na kasar Sin zai karbi bakuncin kwarya-kwaryar taron shugabannin kungiyar APEC cikin nasara a shekara mai zuwa.(Safiyah Ma) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Xi: A Hada Kai Wajen Gina Al’ummar Bai Daya Ta Asiya-Pasifik November 1, 2025 Daga Birnin Sin CMG Ta Kammala Gabatar Da Rahoto Kan Ganawar Shugabannin Sin Da Amurka October 31, 2025 Daga Birnin Sin Ministan Wajen Malawi: Tsarin Ci Gaban Kasar Sin Ya Samar Da Darussa Ga Kasashe Masu...
Ko za ki fadawa masu karatu dan takaitaccen tarihinki? An haife ni a a ‘Delta state’, na yi makarantar firamare da sakandare a Delta, sannan nayi aure a can. Yara na uku, Allah ya kawo rabuwa tsakani na da mijina. Babana dan ‘Nasarawa State’ ne, Mama ta kuma ‘yar Jihar Kano ce. Shekaruna Talatin da hudu, na tsinci kaina a masana’antar Kannywood ne shekara shida da suka wuce baya. Me ya ja hankalinki har ki ka tsunduma cikin masana’antar Kannywood? Saboda fim yana daya daga cikin abin da ya fara burge ni bayan aure na ya mutu, shi fim abu ne wanda yake kamar wa’azantarwa da kuma tunatarwa. Ya gwagwarmayar farawar ta kasance? Yadda gwagwarmayar ya kasace shi...
Ban da haka, shugaban na Sin ya ce, kasarsa na son yin kokari tare da bangarori daban daban, wajen aiwatar da ra’ayin raya kasa na kirkiro sabbin fasahohi, da tabbatar da daidaito, da kare muhalli, da bude kofa, gami da haifar da alfanu ga kowa, ta yadda za a kafa wata al’ummar bai daya ta yankin Asiya da na tekun Pasifik. Duk a wajen taron, yayin wani bikin mika damar karbar bakuncin taron kungiyar APEC, shugaba Xi Jinping ya sanar da cewa, kasar Sin za ta karbi bakuncin kwarya-kwaryar taron shugabannin kungiyar APEC karo na 33, wanda ake sa ran gudanar da shi a birnin Shenzhen na kasar Sin a watan Nuwamba na shekarar 2026. (Bello Wang) ShareTweetSendShare...
Tsohon Sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya soki Shugaban Amurka, Donald Trump, bisa kiran Najeriya “ƙasa mai matsala ta musamman” kan zargin yi wa Kiristoci kisan ƙare dangi. Sani, ya ce kalaman Trump sun samo asali ne daga bayanan da ba su da tushe, da wasu mutane suka ba shi domin su tayar da fitina a Najeriya. Sharrin son auren Mai Wushirya aka yi min — Mansura Isa Zaɓen Tanzania: Shugaba Samia ta yi tazarce da kashi 97 an ƙuri’u A ranar Juma’a ne, Trump ya wallafa rubutu a shafinsa na sada zumunta cewar Kiristanci yana cikin hatasri a Najeriya. Ya yi iƙirarin cewa ’yan ta’adda sun kashe dubban Kiristoci, amma ya ce Amurka za ta yi duk mai...
Daga Abdullahi Shettima Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Uba Sani, ya wakilci Nijeriya a taron ƙoli na biranen Asiya da ya gudana a ƙasar Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), inda ya gabatar da kudirorin sauyin ci gaban Kaduna. Taron ya samu halartar manyan baki daga ƙasashe sama da 150, ciki har da gwamnoni, shugabannin birane da jagororin kasuwanci daga Asiya, Fasifik, Turai da Afirka. Taken taron shi ne “Haɗin Gwiwa. Ƙarfafawa. Sauyi.” A jawabinsa mai taken “Gina Haɗin Gwiwa Domin Ci Gaban Kowa,” Gwamna Uba Sani ya bayyana yadda Kaduna ke samun nasara a fannoni da dama kamar gyaran birane, bunƙasa noma da tallafawa jama’a. Ya ce tsarin ci gaban jihar yana dogara ne kan faɗaɗa damar tattalin arziki, kare marasa ƙarfi,...
A wani bidiyo daban da PUNCH Metro ta gani a Facebook, wanda Mc Pee ya wallafa, wani mutum da ake zargin dalibi ne na jami’ar ya bayyana abin da ya faru. A cewarsa, marigayin ya roki a bar shi ya rayu kafin daga bisani wanda ake zargin ya kashe shi. Ya ce: “Nanpon ya riga ya yanke Peter a kumatunsa yayin da yake rokon a bar shi. Lokacin da muka shiga tsakani muka ce ya daina, sai ya yi barazanar yanka duk wanda ya kusanto shi. “Da Peter ya ga ba ya sauraron rokonsa, sai ya rungume shi yana rokonsa da kuka. “Mun fita neman taimako amma babu wanda ya amsa mana. Da Peter ya yi kokarin tserewa sai ya...
Daga Usman Muhammad Zaria Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta yi kira ga mazauna jihar Jigawa da su kasance masu bin doka da oda, tare da yin aiki kafada da kafada da rundunar ‘yan sanda domin tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali a fadin jihar. Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar Jigawa, CP Dahiru Muhammad, ne ya bayyana haka lokacin da ya karɓi sabbin motoci 10 kirar Toyota Hilux da Gwamna Umar Namadi ya bai wa rundunar a Dutse, babban birnin jihar. A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, SP Lawan Shiisu Adam, ya fitar, CP Dahiru Muhammad ya yaba da jajircewar Gwamna Umar Namadi wajen tallafa wa hukumomin tsaro domin sauke nauyin da ke kansu a jihar....
Jami’an diflomasiyya a Tanzania sun ce akwai kwararan hujjoji da ke tabbatar da an kashe akalla mutum 500 a cikin kwana biyu da barkewar zanga-zangar kin amincewa da sakamakon zaben da aka gudanar a ranar Laraba. Sai dai a wani bangaren kuma, alkalumman Yan’adawa sun zarta haka. Wakiliyar BBC ta ce ministan harakokin wajen Tanzania Mahmoud Kombo Thabit ya musanta rahotannin, amma wani jagoran adawa John Kitoka ya ce ‘yansanda da wasu sojojin haya na kasashen waje ne suka aiwatar da kisan mutane cikin dare. Majalisar Dinkin Dauniya ta yi kiran gudanar da bincike kan zargin amfani da karfin da ya wuce kima a kan masu zanga-zangar. BBC
Daga Usman Muhammad Zaria Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta yi kira ga mazauna jihar Jigawa da su kasance masu bin doka da oda, tare da yin aiki kafada da kafada da rundunar ‘yan sanda domin tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali a fadin jihar. Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar Jigawa, CP Dahiru Muhammad, ne ya bayyana haka lokacin da ya karɓi sabbin motoci 10 kirar Toyota Hilux da Gwamna Umar Namadi ya bai wa rundunar a Dutse, babban birnin jihar. A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, SP Lawan Shiisu Adam, ya fitar, CP Dahiru Muhammad ya yaba da jajircewar Gwamna Umar Namadi wajen tallafa wa hukumomin tsaro domin sauke nauyin da ke kansu a jihar....
Dan wasan da ya lashe kyautar a bara, Ademola Lookman na Nijeriya ba ya cikin jerin ‘yan wasan da aka lissafo a bana, inda hukumar kwallon kafa ta Afirka (Caf) ta samar da kwamitin kwararru wanda ya zakulo masu horarwa da ‘yan wasan da suka “Taka rawar gani” a tsakanin 6 ga watan Janairu zuwa 15 ga watan Oktoban wannan shekara. An bayyana sunan mai horar da tawagar ‘yan kwallon kafa ta kasar Cape Berde, Bubista a matsayin mai neman lashe kyautar mai horarwa mafi kwazo bayan jagorantar tawagar kasar ta Blue Sharks wajen samnun gurbin gasar kofin duniya a karon farko a tarihi. Haka nan tawagar ta tsibirin Cape Berde na cikin masu gogayyar lashe kungiya mafi hazaka a...
Jamhuriyar Musulinci ta Iran, ta nuna damuwarta game da irin tashin hankali da ake ciki a Sudan musamman a yankin El Fasher. Iran ta sake jaddada goyon bayanta ga ‘yancin Sudan, da hadin kai, da kuma cikakken yankin kasar yayin da tashin hankali ya mamaye kasar dake Arewacin Afirka. Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araghchi ne ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa ta waray tarho da takwaransa na Sudan Mohiuddin Salem a ranar Juma’a. Na farko ya nuna damuwa musamman game da hare-hare da kisan gillar da aka yi wa fararen hula a birnin El Fasher da ke kudu maso yammacin Sudan. Duniya ta damu matuka a daidai lokacin da ake ci gaba da samun karuwar tashin...
Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya kada kuri’ar nuna goyan baya ga wani kudiri da ya jaddada cewa shirin da Morocco ta gabatar kan Yammacin Sahara shi ne mafita ‘’mafi dacewa” ga yankin da ake takaddama a kai. Kudirin ya nuna goyan bayan kasashe mambobin kwammitin ga shirin na Morocco, tare da bayyana cewa ikon masarautar kan yankin zai iya kasancewa mafita mafi dacewa. Kan hakan ne kwamitin yaya kira ga Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya António Guterres da wakilinsa na musamman kan wannan batu, Staffan de Mistura, da su gudanar da tattaunawa “bisa ga” wannan shirin don cimma yarjejeniya da kowa zai aminta da ita. Aljeriya wacce ta ke kaddama da Morocco kan yankin ta kaurace kada...
Hukumar zaben kasar Tanzaniya ta bayyana shugabar kasa mai ci Samia Suluhu Hassan a matsayin wadda ta lashe zaben shugaban kasar. Shugaban hukumar zaben ya ce Shugaba Samia ta yi nasara a zaben da kashi 98% na jimillar kuri’un da aka kada. Bayanai sun ce manyan ‘yan takarar adawa ba su shiga ba, wasu kuma an tsare su ko kuma an hana su tsayawa takara, wanda hakan ya haifar da tashin hankali. Jam’iyyar adawa ta kasar ta ce daruruwan mutane ne suka mutu sanadiyyar zanga-zangar da aka kwashe kwanaki ana yi tun bayan zaben na ranar Laraba. Wani mai magana da yawun jam’iyyar adawa ta Chadema ya shaida wa AFP cewa kimanin mutane 700 ne suka mutu, a alkalumman da...
Gwamnatin Najeriya ta mayar da martani kan jawabin da shugaban Amurka Donald Trump ya yi inda yake zargin kashe kiristoci a Najeriyar. A martanin da ta mayar, ma’aikatar harkokin wajen Najeriya, ta ce lamarin ba haka ba ne. Sanarwar da kakakin ma’aikatar Kimiebi Imomotimi Ebienfa ya sanya wa hannu, ta ce, “duk da cewa Najeriya na godiya da kulawar da kasashen duniya ke ba ta musamman kan batun hakkin dan’adam da hakkin addini, wannan batun na zargin kashe kiristoci a kasar ba haka ba ne. Duk yan Najeriya suna da yancin gudanar da addininsu yadda ya kamata, kuma suna gudanar da ibadarsu ba tare da tsangwama ba.” Inji sanarwar. Shi dai shugaban Amurka Donald Trump Ya ce kiristanci na fuskantar...
Babban Kwamishinan Kare Hakkin Dan Adam na Majalisar Dinkin Duniya ya soki hare-haren sama da Amurka ta kai wa jiragen ruwa a yankin Caribbean da Pacific, wanda ya kasance keta dokokin kare hakkin dan adam na duniya. “An ruwaito cewa an kashe mutane sama da 60 a jerin hare-haren da sojojin Amurka ke kai wa jiragen ruwa a Caribbean da Pacific tun farkon watan Satumba, wadanda ake zargin suna da hannu a safarar miyagun kwayoyi, a cikin wani yanayi da ba su da hujja a karkashin dokokin kasa da kasa,” in ji Volker Turk a cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Juma’a. Babban jami’in Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana hare-haren a matsayin “abin da ba za a yarda...
Tsohuwar jarumar Kannywood, Mansurah Isa, ta ƙaryata labarin da wata jaridar intanet ta yaɗa cewa wai tana son ta auri shahararren dan TikTok, Ashiru Mai Wushirya, wanda ya yi tashe a kafafen sada zumunta a ’yan kwanakin nan. A wani saƙo da ta wallafa, Mansurah ta ce labarin ƙarya ne kuma ya jefa ta da iyalinta cikin ruɗani da damuwa. Ta ce, “Na shiga firgici bayan na ga wannan labarin. Ba ni da wata alaka da Mai Wushirya. Wannan sharri ne tsagwaron karya.” Rahoton da aka yada a jaridar AMC Hausa ya yi iƙirarin cewa wai Mansurah ta ce ta shirya auren Mai Wushirya idan har yana son ta da gaske. Kofin kofi mafi tsada a duniya ya shiga kasuwa...
Harkokin siyasa na Kudancin Kaduna ya dauki wani salo yayin da dan majalisar da ke wakiltar mazabar Jema’a/Sanga a majalisar tarayya, Hon. Dan Amos, ya sanar da komawarsa jam’iyyar APC mai mulki zuwa jam’iyyar PDP, yana mai cewa ya dauki wannan mataki ne domin ya hada kai da gwamnatocin jiha da na tarayya don cigaban yankin. Yayin da yake jawabi ga manema labarai a Kafanchan kafin karbar sa a hukumance tare da Sanata Marshall Katung, Amos ya bayyana cewa wannan mataki ya biyo bayan dogon shawarwari da aka yi da shugabannin al’umma, kungiyoyin addini, kwararru da kuma sarakunan gargajiya a fadin mazabarsa. Ya ce jam’iyyar PDP, wacce a da take da karfi sosai a Kaduna, ta ragu saboda rikice-rikicen cikin...
Shugaba Samia Suluhu Hassan, wadda ke neman wa’adin ta na farko a hukumance bayan ta gaji marigayi John Pombe Magufuli a 2021, ta tsaya takara ƙarƙashin jam’iyyar CCM mai mulki. Sai dai rashin shigar manyan ‘yan adawa da aka hana tsayawa ko aka daure ya jefa shakku kan ingancin zaɓen da aka gudanar, inda masu zanga-zanga suka yi kira da a kafa gwamnatin riƙon ƙwarya da zai shirya sahihin zaɓe a gaba. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai An Cafke Ma’aikatan Gidan Marayu Da Suka Sayar Da Yara 4 A Kan Naira Miliyan 3 November 1, 2025 Manyan Labarai Yadda Gwamnatin Tarayya Ta Dakile Yaɗuwar Ɓarkewar Cutar Dabbobi A Jihar Jigawa November 1, 2025 Manyan Labarai Jerin Gwarazan...
Sanata Sunday Marshall Katung, wanda ke wakiltar mazabar Kaduna ta Kudu a majalisar dattawa, ya sanar da hukuncin da ya yanke na komawa jam’iyyar All Progressives Congress (APC), yana mai cewa wannan mataki ne da ya dace domin inganta aikin wakilci da kuma tabbatar da ƙarin haɗin kai ga al’ummar mazabarsa. A cikin wata sanarwa mai taken “Sabon Babin Rayuwa: Saƙon Haɗin Kai da Manufa Ɗaya,” Sanata Katung ya bayyana cewa wannan shawara ta biyo bayan dogon shawarwari da aka yi da mazauna mazabarsa, jagororin siyasa, iyalansa da abokan aikinsa. Ya ce, “Wannan sauyin matsayi yana fitowa ne daga niyyar gaskiya ta yin wa mutanenmu hidima cikin inganci, da tabbatar da cewa muryarmu tana da ƙarfi kuma ana jin ta...
Shugaba Samia Suluhu Hassan ta kasar Tanzania ta sake lashe zaɓen shugaban ƙasar mai cike da ruɗani. Hukumomin zaɓen ƙasar sun sanar da cewa Shugaba Samia Suluhu ta lashe zaɓen ne da kashi 97 na kuri’un da aka jefa. Hukamar zaɓen ƙasar ta bayyana cewa mutum 31,913,866 ne suka kaɗa kuri’a a zaɓen, wanda ya gudana a yayin da kasar ke fama da ƙazamar zanga-zanga.
“Haka kuma an kama wata mata mai shekaru 34 da ake zargi da hannu a lamarin, tare da wasu masu gidan marayu guda biyu da ke Abuja da Jihar Nasarawa, inda aka gano wasu yaran da ake kyautata zaton an yi safarar su. Wasu daga cikin gidajen marayun da aka gano ana amfani da su ne a matsayin cibiyoyin ajiye yara, inda ake jiran ‘kwace’ ko sayar da su da sunan daukar nauyin marayu.” Ya ce, “An gano gidajen marayu guda hudu da ke Kaigini, Kubwa Edpressway Abuja; Masaka Area 1, Mararaba kusa da Abaca Road; da kuma Mararaba bayan Kasuwar Duniya suna da alaka da wannan kungiya, kuma ana ci gaba da bincike a kansu.” Ya kara da cewa,...
Rahotanni sun bayyana cewa gwamnatin isra’ila na fuskantar suka game da matakin da ta dauka na kai hari kan kungiyar unicef ta majalisar dinkin duniya a gaza, matakin da falasdinawa da masu sa ido ke gani a matsayin wata dabara ta murukushe kungiyoyin agaji da kuma fitar da kungiyoyin majalisar dinkin duniya daga yankin gaza Rahoton da wani jami’in majalisar dinkin duniya ya fitar a jiya jumaa ya nuna cewa sojojin isra’ila sun kama wani ma’aikacin UNICEF mai suna Raed Afif mai shekaru 45 da haihuwa a kerem shalom alokacin da yake gudanar da ayyukansa. Yazu wa yanzu isra’ila bata bayyana dalilan da suka sanya ta kama shi ba kuma take ci gaba da tsare shi. Kwana daya kafin tayi...
A wani rahoto da miami herald ya wallafa a jiya jumaa ya nuna cewa kasar Amurka na shirin kaiwa kasar Venuzuwela hare hare, yayin da Donald trump shugaban kasar Amurka yake musantawa cewa babu wani shiri na daukar matakin soji a kasar ta latin Amurka. Yace gwamnatin trump ta yanke shawarar kai hari kan wasu wuraren soji a kasar, a kowanne lokaci. Yace duk da yakin da washington ke yi kan miyagun kwayoyoi gwamnatinsa ba ta la’akari da kai hare-haren sojin kan venuzuwela yana nuna a akwai karo da juna a kalamansa na makon da ya gabata Da manema labarai suka tambayeshi ko hare-haren da Amurka takai a yan kwanakin nan kan jiragen ruwa a yankin karebiya da aka ce...
’Yan bindiga sun sace Mataimakin Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kebbi, Honarabul Samaila Bagudu, a garinsu da ke Ƙaramar Hukumar Bagudu. Rahotanni sun bayyana cewa ’yan bindigar sun mamaye garin Bagudu ne da yammacin ranar Juma’a tare da yin harbe-harbe don tsorata al’umma. Maharan sun yi awon gaba da ɗan majalisar ne a kan hanyarsa ta dawowa daga masallaci bayan ya an idar da sallah masallaci a garin na Bagudu. Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Babban Sakataren Yaɗa Labarai na Gwamnatin Jihar Kebbi, Ahmed Idris, ya ce an sanar da hukumomin tsaro, kuma ana ci gaba da ƙoƙarin tabbatar da kuɓutar da Mataimakin Shugaban Majalisar.
3. A Hangen Nesansa wajen jagorancin al’umma, ya mayar da hankali kan masana’antu, sabunta ababen more rayuwa da kuma gina Dan’adam; domin mayar da Jihar Nasarawa matsayin wata babbar cibiyar zuba jari a Nijeriya da horar da aikin injiniya tare da kyautata jin dadin al’ummar jihar; an zabi Injiniya Abdullahi A. Sule a matsayin Gwarzon Gwamnan Shekarar 2025. Injiniya Abdullahi Sule: Wanda Ya Fi Yin Fice Kan Harkokin Masana’antu A Duk Fadin Arewa 4. Shugabancinsa ya yi matukar kawo sauye-sauye a Jihar Ekiti, musamman ta hanyar gudanar da mulki na adalci, sabunta ayyukan more rayuwa, karfafa matasa da fadada aikin gona; sakamakon tawali’un da yake da shi da horon da ya samu wajen tafiyar harkokin kudi da gina jama’a tare...
Babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na Sin CMG, ya gabatar da labarin ganawar da aka yi jiya Alhamis tsakanin shugabannin Sin da Amurka a Busan na Korea ta Kudu, cikin harsuna 85. Kuma zuwa yau Juma’a, mutanen da suka karanta rahotanni masu alaka da ganawar ta hanyoyin watsa labarai na dandalin CMG sun kai miliyan 712. Haka kuma, kafafen watsa labarai na kasa da kasa 1678, sun wallafa tare da tura rahotanni da bidiyon labaran CMG na harsuna daban daban game da ganawar, har sau 4431. Har ila yau a wannan rana, an gudanar taron tattaunawa na kasa da kasa kan bude kofa da kirkire kirkire da ci gaba na bai daya a kasar Uruguay, wanda CMG da...
Gwamnatin Amurka ƙarƙashin Donald Trump ta sake sanya Najeriya cikin jerin “Ƙasashe Masu Matsala ta Musamman” saboda zargin yi wa Kiristoci kisan ƙare dangi. Wannan zargi ya biyo bayan jawabin da Mataimakin Shugaban Najeriya, Kashim Shettima, ya yi a taron Majalisar Ɗinkin Duniya a kwanan baya. Barcelona ta shiga zarwacin Victor Osimhen Za mu ci gaba da shirye-shiryen babban taronmu — PDP A lokacin taron Shettima ya bayyana halin da ake ciki a Gaza a matsayin abin tausayawa, inda ya hi kira da a tabbatar da zaman lafiya ta hanyar kafa ƙasashe biyu masu zaman kansu. Bayan jawabin nasa, wasu ƙungiyoyi suka fara yaɗa labarin cewa ana yi wa Kiristoci kisan ƙare dangi a Najeriya, duk da cewa mutane da...
Daga Ali Muhammad Rabi’u Gwamnatin Jihar Kwara ta kafa kwamitoci biyu domin tantance bayanan wadanda suka yi ritaya a matakin jiha da kananan hukumomi. A cikin wata sanarwa da Kwamishinar Kudi ta jihar, Dakta Hauwa Nuru ta fitar, ta bayyana cewa kwamitocin za su tantance tare da tabbatar da sahihancin bayanan wadanda suka yi ritaya, domin a biya su bisa lokacin da suka bar aikin gwamnati. A cewarta, kwamitin mutum takwas da aka kafa don kula da kudaden ritaya na matakin jiha zai kasance karkashin jagorancin Mai Duba Asusun Jiha, wato (Auditor General), yayin da wanda ke kula da matakin kananan hukumomi zai kasance karkashin Mai Duba Asusun Kananan Hukumomi. Sanarwar ta bayyana cewa babban burin kwamitocin shi ne...
A cewarsa, ta hanyar wadannan shirye-shirye, kasar Sin ta nuna goyon baya mai dorewa ga kasashe masu tasowa kuma tana ba da gudummawa mai ma’ana ga ci gaban duniya a karkashin tsarin hadin gwiwar kasashe masu tasowa. (Abdulrazaq Yahuza Jere) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Xi: A Shirye Sin Take Ta Hada Hannu Da Canada Wajen Mayar Da Dangantakarsu Bisa Turbar Da Ta Dace October 31, 2025 Daga Birnin Sin Xi Ya Gabatar Da Rubutaccen Jawabi Ga Taron Kolin Shugabannin Masana’antu Da Kasuwanci Na APEC October 31, 2025 Daga Birnin Sin Sin Da Amurka Suna Taimaka Wa Juna Da Samun Wadata Tare October 31, 2025
Yayin ganawarsa da firaministan Thailand, Shugaba Xi Jinping ya ce a shirye kasarsa take ta karfafa hadin gwiwa da Thailand kan dabarun samun ci gaba, tare kuma da gabatar da gogewarta na samun ci gaba a sabon zamani, kuma ya yi kira da a gaggauta gina layin dogo tsakanin Sin da Thailand da bunkasa hadin gwiwa a bangaren cinikin amfanin gona da tattalin arziki mai kiyaye muhalli da kuma kirkire kirkiren fasaha. (Mai fassara: FMM) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Xi Ya Gabatar Da Rubutaccen Jawabi Ga Taron Kolin Shugabannin Masana’antu Da Kasuwanci Na APEC October 31, 2025 Daga Birnin Sin Sin Da Amurka Suna Taimaka Wa Juna Da Samun Wadata Tare October 31, 2025 ...
“Amurka ba za ta tsaya kawai tana kallo ba yayin da irin waɗannan ta’addancin ke faruwa a Nijeriya da sauran ƙasashe. “Mun shirya, muna da ƙarfi da niyyar kare Kiristoci a faɗin duniya,” in ji Trump. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai An Tsare Wani Mutum A Gidan Yari Kan Zargin Kashe Matarsa Saboda Ƙuli-Ƙuli A Kano October 31, 2025 Manyan Labarai Makarantar Kogi Poly Ta Bankaɗo Masu Ƙirƙirar Takardun Kammala Karatu na Bogi October 31, 2025 Manyan Labarai Kifewar Kwalekwale: Gwamnan Gombe Ya Jajanta Wa Al’ummar Nafada Kan Mutuwar Matasa Biyar October 31, 2025
Mai shari’a Dahiru ya amince da buƙatar, ya kuma ɗage shari’ar zuwa ranar 12 ga watan Disamba, 2025, domin ci gaba da sauraron shari’ar. Ƙuli-ƙuli dai nau’in abin ci ne mai taushi da ake yi da gyaɗa, ana soyawa har sai ya zama ƙura-ƙura ta yadda za a ci cikin nishaɗi. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Makarantar Kogi Poly Ta Bankaɗo Masu Ƙirƙirar Takardun Kammala Karatu na Bogi October 31, 2025 Manyan Labarai Kifewar Kwalekwale: Gwamnan Gombe Ya Jajanta Wa Al’ummar Nafada Kan Mutuwar Matasa Biyar October 31, 2025 Manyan Labarai NPA Da Ƙungiyar Injiniyoyi Ta Yi Haɗaka Don Bunƙasa Tashoshin Jiragen Ruwa October 31, 2025
Kungiyar ƙwallon ƙafa ta Barcelona da ke Sipaniya na ƙoƙarin ɗauko Victor Osimhen a matsayin wanda zai maye gurbin Robert Lewandowski wanda ke fama da matsalar raunuka Ɗan jaridar ƙasar Sifaniya, Gabriel Sans na Mundo Deportivo ya bayyana cewar, Barcelona na neman wanda zai maye gurbin Robert Lewandowski a matsayin mai jefa ƙwallo a raga, hakan ne ya sa ƙungiyyar ta amince da ɗaukar Osimhen. ’Yan bindiga sun sace fasinjoji a cikin motocin bas a Kogi Real Madrid zata nemi diyyar Dala bilyan 4 daga UEFA A ƙarshen kakar bana ne ake tunanin up Lewandowski zai bar Barca, wanda zai tilasta wa ƙungiyyar neman wani zaƙaƙurin ɗan wasan gaba mai ciyo ƙwallo. Victor Osimhen dai a bazarar nan ne ya...
Jam’iyyar PDP ta bayyana cewa za ta ci gaba da shirin gudanar da babban taronta wanda za a yi a ranar 15 da 16 ga watan Nuwamba a Ibadan da ke Jihar Oyo. Tun da farko, Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ta hana jam’iyyar gudanar da taron, inda ta ce PDP ta karya dokokinta na cikin gida. ’Yan bindiga sun sace fasinjoji a cikin motocin bas a Kogi Kotu ta dakatar da gudanar da babban taron PDP Mai shari’a James Omotosho, wanda ya jagoranci shari’ar, ya umarci Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), da kada ta karɓi ko ta wallafa sakamakon taron har sai PDP ta cika dukkanin sharuɗan da doka ta tanada. Sai dai a cikin wata sanarwa da...
Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta dakatar da jam’iyyar PDP daga gudanar babban taronta na ƙasa da aka shirya yi a Ibadan, Babban Birnin Jihar Oyo, a watan gobe. Mai shari’a James Omotosho ne, ya bayar da wannan umarni, yayin da yake yanke hukunci kan wata ƙara da aka shigar domin sanin ko jam’iyyar PDP na da ikon ci gaba da shirya taron da aka tsara gudanarwa a ranakun 15 da 16 ga Nuwamba. Real Madrid zata nemi diyyar Dala bilyan 4 daga UEFA An raba wa iyalan jami’an ’yan sandan da suka rasu a bakin aiki a Borno N63.4m Waɗanda suka shigar da ƙarar sun haɗa da Austine Nwachukwu, shugaban PDP na Jihar Imo; Amah Abraham Nnanna, shugaban...
Ya kuma bayyana cewa kasar Sin wuri ne mai kyau ga harkokin zuba jari ga ‘yan kasuwa na duniya. Ya ce hadin gwiwa da kasar Sin yana nufin hadin gwiwa da damammaki, imani da kasar Sin yana nufin imani da kyakkyawar makoma, zuba jari a kasar Sin yana nufin zuba jari mai riba ta dogon zango.(Safiyah Ma) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Sin Da Amurka Suna Taimaka Wa Juna Da Samun Wadata Tare October 31, 2025 Daga Birnin Sin Xi Jinping Ya Halarci Kwarya-Kwaryan Taron Shugabannin APEC Na 32 Tare Da Gabatar Da Jawabi October 31, 2025 Daga Birnin Sin An Gudanar Da Taron Kasa Da Kasa Na Tattaunawa Kan Kirkire-kirkire Da Bude Kofa Da...
Daga Usman Muhammad Zaria Majalisar Zartarwa ta Jihar Jigawa ta amince da bayar da rancen kudi ga hukumar gidaje ta jihar domin gina gidaje 52 a Dutse. A cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labarai na jihar, Alhaji Sagir Musa Ahmed ya fitar, ya bayyana cewa gidajen za su kunshi masu dakuna uku da kuma dakuna biyu kowanne. Ya ce aikin zai kasance a gaban tsohuwar unguwar majalisar dokoki, kusa da hanyar wucewa ta Jami’ar Tarayya da je Dutse, a matsayin wani shiri na asusun gina gidaje karkashin ma’aikatar gidaje, ci gaban birane da tsare-tsaren yankuna, ta hannun hukumar gidaje ta jihar. Alhaji Sagir ya bayyana cewa, wannan mataki na nuna kudirin gwamnati wajen magance matsalar gidaje a babban...
Wasu ’yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun yi garkuwa da fasinjoji a cikin wasu motocin bas Toyota guda biyu a titin Itobe zuwa Ajegwu-Anyigba a Ƙaramar hukumar Ofu ta jihar Kogi. An samu rahoton cewa, lamarin ya faru ne a ranar Alhamis da misalin ƙarfe 5 na asubahi a tsakanin ƙauyukan Ojiwo’-Ajengo da Mamereboh da ke kan babbar hanyar. Gwamnatin Yobe ta ƙaddamar da shirin amfani da ma’adanai Kotu ta dakatar da babban taron PDP na ƙasa An ce masu garkuwa da mutanen sun yi amfani da wata tirela da aka kama wajen tare hanyar bayan shingen binciken jami’an tsaro, da ke kusa da wurin da lamarin ya faru. Shedun gani da ido sun ce...
Gwamnatin kasar Iran ta sanar da ranar 30 ga watan nuwambar kowacce shekara a matsayin ranar kasa ta tsibirin Abu Musa tumbu babba da tumbu karami da ta karbo daga hannu birtaniya a shekaru da suka gabata, wanda yayi daidai da 9 ga watan Azar na kalandar iraniyawa . Tsibiran guda 3 da ake takaddama akansu Abu musa da tunbu babba da karami suna yankin tekun fasha ne tsakanin mailand na iran da kuma hadaddiyar daular larabawa, tsibbiran wani bangare ne na kasar iran tun karnoni da suka gabata da ke cike da abubuwa da suka safi doka da tarihi a iran da kuma kasa da kasa. Iran ta jaddada cewa dukkan wadannan tsibirai guda 3 wani bangare na kasarta...
Rahotanni sun bayyana cewa Isra’ila ta kashe wasu falasdinawa guda 5 yankin gaza a ci gaba da keta yarjejeniyar dakatar da bude wuta da suka cimma tsakaninta da kungiyar Hamas a farkon watan oktoba, A yau juma’a kafar yada labarai ta falasdinu ta bayyana cewa sojojin Isra’ila sun harbe wani bafalasdine a yankin jabaliya dake arewacin yankin Gaza, haka zalika wani bafalasdine mai suna Mahmud suleman al- wadiya sojojin isaraila sun kashe shi a gabashin shuja’iyya dake makwabtaka da gabashin gaza, gari mafi girma a gaza kuma an jikkata wani dan uwansa, Har ila yau hamdi al-barim da mohamma salem qadi sun ji mummunan rauni sakamakon harin da sojojin Isra’ila suka kai musu a khan yunus dake yammacin gaza a...
Bayan kwashe shekaru ana taƙaddama kan abubuwan kunya da ake zargin shi da aikatawa, a yanzu an tube shi, kacokan, duk wata alfarma ko sarauta ko mukami daga tsohon yariman Birtaniya Andrew, wanda da ne ga marigayiya Sarauniya Elizabeth II. Fadar masarautar Birtaniya ta Buckingham Palace ce da kanta ta fitar da sanarwa game da hakan. A yanzu “za a rika kiransa da tsuran sunansa, wato Andrew Mountbatten Windsor,” in ji sanarwar. Masarautar na fatan wannan mataki nata zai kawo karshen muhawara kan jerin abin kunyar da ake zargin yariman ya aikata wadanda ake alakantawa da masarautar. Yanzu an tube shi karfi da yaji, duk wasu sarautu da ke kansa, kamar yariman York da sauran su. Share 0 0 votes...
Bayan duguwar tattaunawa a birnin Istanbul na kasar turkiya kasashen pakisatan da Afghanistan sun amince da batun tsawaita dakatar da bude wuta a tsakanin iyakokin kasashen, bayan da kasashen turkiya da Qatar suka shiga tsakanin domin samun daidaito. Gwabzawa a iyakokin kasashen biyu dake mukwabtaka a yan makwannin nan yana barazana sosai ga zaman lafiyar yankin, sai dai wannan yarjejeniyar za ta hana yaduwar fadan da kuma kara samun hadin guiwa kan tsaron iyakokin. Zabiullah mujahid kakakin kungiyar Taliban ya tabbatar da kulla yarjejeniyar, kuma yace Kabul tana son samun kyakkyawar dangantaa da dukkan kasashen dake makwabtaka da ita, musamman kasar Pakistan bisa mutunta juna da kuma rashin tsoma baki a harkokin cikin gidan kasashen. Share 0 0 votes Article...
Rahotanni sun bayyana cewa majalisar dinkin duniya ta yi gargadin game da barazanar hadarin gwajin makamanin nunkiliya bayan da shugaban Amurka Trump ya bada umarnin a fara gwajin makaman nukiliya, Tace wannan matakin barazana ne ga tsaro da zaman lafiyar duniya. Farhan Haq mataimakin kakakin majalisar dinkin duniya ya shaidawa manema labarai a birnin New York cewa sakataren janar din majalisar Antunio Guteress ya jaddada cewa hatsarin da makamin nukiliyar yake da she a halin yanzu yana ishara game da muhimmancin rashin daukar mataki akanshi don kaucewa babbar matsalar da zai haifar Har ila yau Guterres ya gaya wa duniya irin bala’in da gwajin da makamin nukiliyar ya jawo wanda aka yi na nukiliya 2000 a shekaru 80 da suka...
A jawabinsa yayin taron, Gwamna Sani ya gabatar da kasida mai taken: “Gina Haɗin Gwiwa Domin Ci Gaban Kowa”, inda ya bayyana yadda Jihar Kaduna ke ci gaba da samun nasara a fannoni da dama kamar gyaran birane, bunƙasa noma, da tsarin tallafiwa jama’a. Gwamnan Ya ce tsarin ci gaban jihar yana dogara ne kan faɗaɗa damar tattalin arziki da kare marasa ƙarfi, da ƙarfafa jama’a su samu nasara a rayuwarsu. Gwamna Uba Sani, ya kuma halarci shirin baje koli na birnin Dubai mai taken : “Sauya Arewa a Nijeriya: Jagoranci, Ƙirƙira, da Tasirin Zamantakewa”, inda nan ma ya jaddada cewa jagoranci mai nagarta da amfani da fasaha a mulki suna da matuƙar muhimmanci wajen buɗe damarmaki ga...
Sai dai don neman cimma burinta na “sake mayar da kasar Amurka zakaran gwajin dafi”, kasar Amurka ta sha daukar matakai na dakile ci gaban kasar Sin, ciki har da katse huldar tattalin arziki da ita da ma sanya takunkumai ga kamfanoninta masu ci gaban kimiyya da sauransu, duk da hakan, kasar Sin ta kiyaye bunkasar tattalin arzikinta yadda ya kamata, har ma karuwar tattalin arzikinta ta kai kaso 5.2% a cikin watanni tara na farkon bana, lamarin da ya shaida inganci da juriya na tattalin arzikin kasar. A kwanan nan, kasar Sin ta zartas da shawarwarin da aka gabatar game da tsara shirin raya tattalin arziki da zaman al’umma cikin shekaru biyar masu zuwa, kuma bisa ga shawarwarin, za...
“Ana kiransa da suna dokar binciken tntanet ta tsoratarwa, wadda kasashen da suka ci gaba da dama suka dade da yin watsi da ita. A karni na 21, ba za a iya tunanin cewa gwamnatin Nijeriya za ta tauye ‘yancin fadin albarkacin baki, wanda shi ne ginshikin mulkin dimokuradiyya.” Atiku ya ce duk wata doka da ke take ‘yancin ‘yan kasa na yin tsokaci mai muhimmanci game da shugabanninsu ko a hanyoyin sadarwar zamani ko ta hanyar magana ba dimokuradiyya ba ce kuma kai tsaye take hakkokin Dan’adam ne. “A cikin shekaru biyu da rabi da suka gabata tun bayan da gwamnatin Tinubu ta fara daukan matakan da ke janyo kuncin tattalin arziki da yunwa da bakin ciki ga mutanen...
Gwamnatin Jihar Yobe ta ƙaddamar da shirin fara amfani da ma’adinan ƙarƙashin ƙasa da Allah SWT ya hore ma ta da nufin haɓaka tattalin arzikinta tare da samarwa al’umma aikin yi. A yayin ƙaddamar da taron masu ruwa da tsaki na Jihar da aka yi a babban ɗakin taron gidan gwamnatin Jihar da ke Damaturu, Gwamnan Jihar Mai Mala Buni ya ce kamfanin haɓaka ma’adanai ta Yobe Limited ita ce kawai hukumar da aka bai wa izini don gudanar da duk ayyukan bincike da haƙar ma’adinai a faɗin jihar. Kotu ta dakatar da babban taron PDP na ƙasa Real Madrid zata nemi diyyar Dala bilyan 4 daga UEFA Yana mai cewa, kamfanin haƙar ma’adinai na Yobe a halin yanzu shi...
Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta dakatar da jam’iyyar PDP daga gudanar babban taronta na ƙasa da aka shirya yi a Ibadan, Babban Birnin Jihar Oyo, a watan gobe. Mai shari’a James Omotosho ne, ya bayar da wannan umarni, yayin da yake yanke hukunci kan wata ƙara da aka shigar domin sanin ko jam’iyyar PDP na da ikon ci gaba da shirya taron da aka tsara gudanarwa a ranakun 15 da 16 ga Nuwamba. Real Madrid zata nemi diyyar Dala bilyan 4 daga UEFA An raba wa iyalan jami’an ’yan sandan da suka rasu a bakin aiki a Borno N63.4m Waɗanda suka shigar da ƙarar sun haɗa da Austine Nwachukwu, shugaban PDP na Jihar Imo; Amah Abraham Nnanna, shugaban...
Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta dakatar da jam’iyyar PDP daga gudanar babban taronta na ƙasa da aka shirya yi a Ibadan, Babban Birnin Jihar Oyo, a watan gobe. Mai shari’a James Omotosho ne, ya bayar da wannan umarni, yayin da yake yanke hukunci kan wata ƙara da aka shigar domin sanin ko jam’iyyar PDP na da ikon ci gaba da shirya taron da aka tsara gudanarwa a ranakun 15 da 16 ga Nuwamba. Real Madrid zata nemi diyyar Dala bilyan 4 daga UEFA An raba wa iyalan jami’an ’yan sandan da suka rasu a bakin aiki a Borno N63.4m Waɗanda suka shigar da ƙarar sun haɗa da Austine Nwachukwu, shugaban PDP na Jihar Imo; Amah Abraham Nnanna, shugaban...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Kifewar Kwalekwale: Gwamnan Gombe Ya Jajanta Wa Al’ummar Nafada Kan Mutuwar Matasa Biyar October 31, 2025 Manyan Labarai NPA Da Ƙungiyar Injiniyoyi Ta Yi Haɗaka Don Bunƙasa Tashoshin Jiragen Ruwa October 31, 2025 Manyan Labarai Yan Nijeriya Na Ɗanɗana Kuɗarsu Kan Jinkirta Cire Tallafin Mai – Sarki Sanusi October 31, 2025
Ya Kamata Shugaba Tinubu Ya Ƙulla Alaƙa Ta Kut-da-kut Tsakanin Hukumar Shige Da Fice Da Kwastam – Babandede
“Iyakar kasa ba wai kawai yanki ne na tsaro ba. Yanki ne na al’adu; yanki ne na tarihi; haka nan ma yanki ne na tattalin arziki. Kula da shige da fice na da matukar amfani ga ci gabanmu. Wajibi ne Nijeriya ta zuba jari a kan kula da nau’in mutanen da take tacewa wajen shiga kasa da kuma irin mutanen da muke tacewa wajen fita daga kasa. “Dole ne mu yi nazarin nau’in ayyukan da bakin-haure ke yi da kuma yadda suke shafar tattalin arzikinmu. Muna bukatar tsame mutanen da ke kawo cikas ga ci gabanmu”, in ji Babandede. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Rundunar Sojin Nijeriya Ta Shirya Wa Janar Musa Faretin Gama Aiki October 31, 2025 Labarai...
Wata kotu da ke birnin Madrid ta yi watsi da ƙarar da Hukumar ƙwallon ƙafa ta Nahiyyar Turai UEFA, LaLiga da Hukumar Kwallon Kafa ta Sipaniya suka shigar kan ƙin amincewa da gasar Super League. Wannan yana nufin yanzu Real Madrid da sauran ƙungiyyoyin za su iya neman diyyar kudi Euro Milyan 4. Kotu ta tsige dan majalisar da ya sauya sheka zuwa APC Shugabannin Kudancin Kaduna za su karrama Janar Christopher Musa Real Madrid ta ce, wannan hukuncin ya tabbatar da cewa UEFA ta karya dokokin gasa, kuma ƙungiyyoyi sun rasa maƙuden kuɗaɗe tun daga lokacin da aka dakatar da gasar. Gasar wacce aka shirya farawa a shekarar 2021 tare da manyan ƙungiyoyin Turai, an yi hasashen zata samar...
Daga Usman Muhammad Zaria Kananan manoma a jihar Jigawa sun yabawa kungiyar Sasakawa Africa dangane da tallafin da take samarwa a fannin inganta noma. Yayin tattaunawa da wasu daga cikin wadanda suka ci moriyar shirin musamman manoman shinkafa a garin Chandam dake karamar hukumar Birnin Kudu, sun bayyana cewa tallafin Sasakawa ya habaka noman shinkafar su tare da samun karin kudade. Manoman sun bayyana cewar shirin ya taimaka masu wajen bunkasa harkokin noma tare da tallafawa al’ummomin su. Daya daga cikin wadanda suka amfana da shirin a yankin Chandam dake karamar hukumar Birnin Kudu, Buhari Nafi’u, yace Sassakawa Africa ta samar masu da tallafin noma daban daban. A cewar sa tallafin sun hada da horo wanda ya...