Masan sun ƙalubalanci sojoji kan maharan ƙasashen waje
Published: 9th, May 2025 GMT
Masana harkokin masana tsaro sun nuna rashin amincewarsu da iƙirarin sojojin Najeriya cewa baƙi daga ƙasashen waje ne ke kai yawancin hare-haren da ake kaiwa al’ummomin ƙasar, musamman a jihohin Filato da Benue.
Wannan ƙalubalen ya fito ne bayan wata sanarwa da Hedikwatar Tsaro ta yi a ranar Alhamis, cewa yawancin hare-haren da ake kai wa manoma da kashe-kashe a sassan kasar, makiyaya ne ’yan kasashen waje suka fi aikatawa.
Daraktan Ayyukan Yada Labarai na Tsaro, Manjo-Janar Markus Kangye, ya bayyana haka ne lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai game da hare-haren a kan manoman.
An kashe mutane da yawa tare da raba wasu dubbai da gidajensu a jihohin Filato da Benue a sakamakon hare-hare da makiyaya ɗauke da makamai suka kai a kwanakin baya.
Manjo-Janar Kangye ya ce duk da cewa ana magana da Hausa a sassa daban-daban na Afirka, amma abu mai sauƙi ne a gane waɗanda ba ’yan Najeriya ba ne. Ya ce, “idan aka ji su suna magana, za a iya gane ’yan ƙasa ne ko baƙi.”
Ya bayyana cewa sun kama wasu daga cikin ’yan ta’addan, kuma yadda suke magana da kamanninsu da ma gashin kansu, yana nuna cewa ba ’yan Najeriya ba ne.
Y amince cewa yawancin masu aikata ta’addanci a Najeriya baƙi ne, duk da cewa akwai ’yan ƙasar a cikinsu. Ya ƙara da cewa yawancin tashin hankalin da ake ji a wasu sassan ƙasar nan, galibi waɗanda suka shigo ƙasar ta bayan fage ne ke aikata su.
Ya yi kira ga hadin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro don tabbatar da an yi ɗauki bayanan duk wanda ya shigo Najeriya.
Masana sun ɗiga ayar tambayaSai dai, wasu masana tsaro sun nuna shakku game da wannan iƙirarin.
Dakta Kabiru Adamu, Shugaban Kamfanin Beacon Consult, ya amince cewa sojojin Najeriya suna fuskantar matsin lamba sosai saboda ƙaruwar hare-hare da kuma yadda ake bibiyar su daga kafafen yada labarai da manyan jami’an gwamnati.
Ya ce wannan matsin lamba zai iya shafar ƙarfin guiwar sojoji da kuma yadda suke gudanar da ayyukansu, wanda zai iya kai su ga bayar da irin wannan sanarwa don nuna cewa suna samun ci gaba tare da ɗora alhakin ga wasu.
Ya yi nuni da yarjejeniyar ECOWAS kan zirga-zirgar dabbobi da makiyaya, yana mai cewa duk da manufarta ta sauƙaƙa zirga-zirga, ana ganin ta a matsayin hanyar da ’yan bindiga za su iya shigowa kasar ba tare da an san su ba.
Kabiru Adamu ya yi kira da a sake duba yadda ake aiwatar da wannan yarjejeniya tare da samar da hanyoyin da za a iya bibiyar masu shigowa ƙasar.
Ya kuma jaddada matsalar iyakar Najeriya da ba ta da tsaro, yana mai kira da a inganta haɗin gwiwa da ƙasashe makwabta tare da saka hannun jari a yankunan kan iyaka.
Wani tsohon kwamandan sojin sama, Dakta Musa Salmanu, ya ce zai ɗauki maganar kakakin hedikwatar tsaro da muhimmanci, amma ya nuna damuwa cewa idan ’yan kasashen waje ne ke kai hare-haren, hakan na nufin Najeriya na fuskantar wani nau’i na mamayewa.
Ya yi tambayoyi game da ko waɗannan mutane ne suka zo da kansu ko kuma wasu ƙasashe ne ke ɗaukar nauyinsu.
Ya jaddada cewa ko ’yan Najeriya ne ko baƙi, babban abin da ya kamata a fi mayar da hankali a kai shi ne yadda za a dakatar da barnar da suke yi.
Ya kuma yi kira da a magance tushen matsalar rikicin makiyaya da manoma da sauran matsalolin tsaro a sassan Najeriya.
Wani tsohon ɗan majalisa, Destiny Enabulele, ya zargi shugabannin Najeriya da rashin jajircewar magance matsalar rashin tsaro.
Ya yi tambaya game da yadda ake kashe kuɗaɗen da aka ware don tsaro, yana mai cewa har sai an samu jajircewar yaƙar rashin tsaro, ba za a samu mafita ba.
Ya kuma yi kira ga jami’an shige da fice da na kwastam da su koma kan iyakokin kasar don gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.
Wani masanin tsaro, Jackson Lekan Ojo, ya musanta iƙirarin sojojin, yana mai cewa hakan ya nuna gazawar hukumomin iyaka da na leƙen asiri na ƙasar.
Ya ce ya kamata a hukunta waɗanda ke da alhakin tsaron iyakokin Najeriya, yana mai bayyana ikirarin a matsayin “uzuri maras tushe,” da ke nuna halin ko-in-kula na sojoji da sauran jami’an tsaro.
Ya yi kira da a fatattaki waɗannan mutane, a kama su ko kuma a mayar da su kasashensu.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: yan ta adda hare hare Makiyaya Tsaro
এছাড়াও পড়ুন:
Barau ya nemi Trump ya janye kalamansa, ya nemi afuwar Najeriya
Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Jibrin Barau, ya nemi Shugaban Amurka, Donald Trump, ya janye barazanar da ya yi wa Najeriya kan zargin yi wa Kiristoci kisan ƙare dangi.
Trump, ya yi barazanar ɗaukar matakin soji a kan Najeriya saboda zargin ana zaluntar Kiristoci.
Barazanar Trump: Ya kamata shugabannin Najeriya su farka daga bacci — Bishop Kukah Tinubu ya gana da Sarkin Musulmi a Aso RockBarau ya ce maganar da Trump ya yi ba ta dace ba, kuma ta saɓa wa dokokin ƙasa da ƙasa.
A cikin wani bidiyo da aka fitar a ranar Juma’a, Mataimakin Shugaban Majalisar, ya ce Najeriya, a matsayinta na ƙasa mai cin gashin kanta, ba za ta yadda a ci zarafinta ko a tsangwame ta ba.
“Shugaban Amurka ya fito ya ce, ‘Najeriya wulaƙantaciyyar ƙasa ce, za mu kai muku hari,’ wannan bai dace ba.
“Ya kamata ya janye wannan maganar ya kuma nemi afuwar Najeriya,” in ji Barau.
Ya ƙara da cewa maganganun Trump sun karya dokokin diflomasiyya da na ƙasa da ƙasa.
“Idan kuna da ƙorafi a kan ƙasarmu, ku bi hanyoyin shari’a. Ku je Majalisar Ɗinkin Duniya, ku nemi izini, sannan ku aiwatar da shi yadda ya dace. Tsallake wannan hanya ba abin da ya dace ba ne,” in ji shi.
Barau, ya jaddada cewa kalaman Trump ba za su firgita Najeriya ba, kuma ya kamata shugaban Amurka ya girmama ƙasa mai cin gashin kanta.
“Ba za mu ji tsoron faɗin gaskiya ba. Da Trump yana nan, da na faɗa masa kai-tsaye cewa abin da yake yi ya saɓa wa dokokin ƙasa da ƙasa kuma ba daidai ba ne,” in ji shi.