2025-08-13@08:54:24 GMT
إجمالي نتائج البحث: 6392

«da Gwamnonin»:

    Shugaban EFCC, Ola Olukoyede, ya ce, “Idan ba a zarge ni wajen binciken gwamnoni da ministocin jam’iyyar da ke mulki ba, bai kamata a zarge ni idan na binciki ’yan hamayya ba.” Duk da haka, mutane da dama a kafafen sada zumunta sun nuna shakku, tare da tambayar dalilin da ya sa EFCC ba ta ɗauki mataki kan manyan ’yan siyasa na jam’iyyar APC kamar tsohon Gwamnan Delta Ifeanyi Okowa, tsohon Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje, da tsohon Gwamnan Kogi Yahaya Bello ba. Wasu sun zargi EFCC da yin aiki ƙarƙashin ikon gwamnatin da ke mulki, yayin da wasu suka yi tsokaci ta hanyar buƙtar shugaban EFCC ya bayyana bayanan asusun bankinsa na yanzu. Daga kanmu, magana ta ƙare....
    Babban kwamandan sojojin kasar Iran Manjo Janar Amir Hatami ya tabbatar da cewa, Isra’ila da Amurka ne suka bukaci  a tsagaita bude wuta cikin gaggawa bayan da suka fuskanci martani mai tsanani a lokacin da suka kaddamr da hare-hare kan kasar Iran. A yayin da yake karbar bakuncin babban kwamandan rundunar tsaron kasar a Afirka ta Kudu, Janar Hatami ya ce, hukumomin Isra’ila da Amurka sun yi amfani da dukkan karfinsu wajen kai wa Iran hari, amma sun kasa cimma burinsu. Har ila yau, ya bayyana matakin da Afirka ta Kudu ta dauka  na shigar da kara kan Haramtacciyar Kasar Isra’ila a kotun kasa da kasa a matsayin wata babbar Jarunta, yana mai jaddada cewa tarihi zai tabbatar da wannan...
    Ministan Ruwa na Habasha Habtamu Etfa ya jaddada cewa, babbar madatsar ruwa ta kasarsa amfanin dukkanin kasashen yankin ne. Etfa ya bayyana hakan ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook, kamar yadda shafin yanar gizo na Ethiopian Monitor ya bayyana cewa, ” kwararar kogin Blue Nile ya karu a lokacin noman rani, yayin da muka ga raguwar ambaliya da kuma jinkiri fiye da wata guda.” Ya jaddada cewa abin da muke hasashe kuma muke bayyanawa  yau da kullun ya tabata a aikace.” Ya kara da cewa, “Grantin Renaissance Dam na Habasha ba kawai ya kara yawan filayen noma da ake nomawa a kasashen da ke gabar kogin Blue Nile ba, har ma ya taimaka wajen kare...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Bankin Duniya ya amince da bayar da dala miliyan 300 domin aiwatar da wani sabon shiri da zai inganta rayuwar ’yan gudun hijira da kuma al’ummomin da suka ba su matsugunni a Arewacin Nijeriya. Bankin ya bayyana cewa a ƙarƙashin shirin mai suna Solutions for the Internally Displaced and Host Communities Project wato SOLID, wanda aka amince da shi a ranar 7 ga Agusta, za a lalubo hanyoyin da za a bi wajen taimakon ’yan gudun hijira, da ma garuruwan da suke rayuwa a ciki. Ya bayyana cewa shirin SOLID zai ruɓanya ƙoƙarin da gwamnati ke yi da ma wanda sauran abokan hulɗa suka riga suka gudanar, ciki har da Shirin Farfado da Yankunan Da Rikici Ya Shafa (MCRP). Haka...
    Gwamnan jihar Anambra, Farfesa Charles Soludo, ya ce ranar Litinin ya ziyarci Shugaban Kasa Bola Tinubu, kuma sabanin yadda ake ta rade-radi, shugaban na nan cikin koshin lafiya kuma babu abin da ke damun shi. A ’yan kwanakin nan dai ana ta samun jita-jitar cewa shugaba Tinubu na can kwance magashiyyan yana fama da rashin lafiya a daidai lokacin da aka shafe sama da mako guda ba a ji motsin shi ko an gan shi a wajen wani taro ba. DAGA LARABA: Yadda sinadaran dandanon abinci ke yin illa ga lafiya Fursunoni 16 sun tsere daga gidan yarin Keffi Sai dai da yake zantawa da ’yan jaridar Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja bayan ya gana da shi, Gwamnan ya...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A yau, yawancin mutane suna amfani da sinadaran dandano wajen girki domin ƙara wa abinci ɗanɗano da ƙamshi. Amma, binciken masana ya nuna cewa ana yawan amfani da su fiye da yadda ake bukata, musamman irin waɗanda aka sarrafa a masana’antu. Wannan rashin kiyaye ƙa’ida yana iya jawo matsaloli ga lafiya. Sau da yawa mutane kan manta cewa a cikin waɗannan sinadarai akwai gishiri mai yawa da wasu ƙarin abubuwan da idan aka tara su a jiki na dogon lokaci, suna iya haifar da illa. NAJERIYA A YAU: Yadda matasa ke bayar da gudunmawa ga ci-gaban al’umma DAGA LARABA: Me Ke Sa Matasa Zama Karnukan Farautar ‘Yan Siyasa A Kafafen Sadarwa Na Zamani?...
    Da yake tabbatar da faruwar lamarin ga LEADERSHIP a ranar Talata, Kakakin Rundunar ’Yansandan Jihar Bauchi, CSP Ahmed Wakil, ya ce rundunar ‘yansandan ta samu kiran waya da misalin karfe 9:20 na safe daga CLO, inda ya ce Chukwuebuka mai lambar jiha BA/25A/2069 bai farka ba daga barcinsa, yayin da sauran ’yan uwansa Kiristocin ke shirin tafiya wurin bauta a ranar Lahadi.   “CLO ya je don ya tayar da shi daga barci amma sai ya gano cewa, ba ya numfashi, nan take ya kai rahoton lamarin ga hedikwatar ‘yansanda ta Dambam,” in ji Wakil.   Biyo bayan umarnin kwamishinan ‘yansandan jihar Bauchi, CP Sani Omolori-Aliyu, jami’in ‘yansanda na sashen ya jagoranci tawagarsa zuwa wurin.   An garzaya da Chukwuebuka...
      A halin da ake ciki, EFCC ta yi Allah wadai da jam’iyyar ADC bisa zargin sanya siyasa a binciken da ta gudanar kan Tambuwal. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ana fargabar cewa wasu fursunoni 16 sun tsere daga gidan yarin Keffi da ke Jihar Nasarawa bayan wani kwantan bauna da suka yi wa gandirebobi. Wata sanarwa da mai magana da yawun Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali a Nijeriya, Umar Abubakar, ta ce fursunonin da ke gidan sun yi wa ma’aikatan da ke tsaronsu rubdugu, lamarin da ya bai wa mutane 16 damar guduwa a safiyar wannan Talatar. An kama ɗan shekara 18 kan zargin fashi da makami a Gombe An kama basarake kan zargin yi wa ’yar shekara 12 fyaɗe a Gombe Sanarwar ta ce biyu daga cikin jami’ai biyar da suka ji rauni a yayin harin na cikin mawuyacin hali, kuma yanzu haka ana duba lafiyarsu a...
    Da aka tambaye shi dalilin da ya sa ya fito ƙarara ya goyi bayan shugaban ƙasa wanda ba a cikin jam’iyyarsu yake, Soludo ya ce goyon bayansa ga Tinubu ba sabon abu ba ne.   “An samar da waɗannan huluna tun lokacin da Shugaban Ƙasa ya ziyarci Jihar Anambra kuma kun ga allunan talla da sauran abubuwa da ke bayyana cewa masu ra’ayin kowa ci gaba suna aiki tare ne da juna,” in ji Soludo.   “Bayan haka, wannan wata babbar manufa ce da na yi imani da ita sosai, cewa ya kamata dukkan jam’iyyun siyasa da ke ikirarin ra’ayin ci gaba su haɗu a ƙarƙashin wata babbar ƙawance don zurfafa tunani da kawo ci gaba ba kawai a tafarkin...
    Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe ta cafke wani matashi mai shekaru 18, Hassan Aminu Sadiq, bisa zargin aikata fashi da makami a lokuta daban-daban, bayan wani samame da aka kai unguwar unguwar Yelwa da ke garin Kwadon a Karamar Hukumar Yemaltu Deba. Mai magana da yawun rundunar, DSP Buhari Abdullahi, ya ce an kama wanda ake zargin ne a ranar 9 ga Agusta, 2025, da misalin ƙarfe 2:30 na rana, yana ɗauke da kunshin ganyen da ake zargin tabar wiwi ne. An kama basarake kan zargin yi wa ’yar shekara 12 fyaɗe a Gombe EFCC ta saki Tambuwal Binciken da aka soma gudanarwa ya nuna cewa Hassan yana cikin jerin mutanen da ake nema ruwa-a-jallo, bisa zarginsa da hannu a...
    Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe ta cafke wani basarake, Mohammed Tukur mai shekaru 55, a kauyen Sabon Gari da ke yankin Zambuk na Ƙaramar Hukumar Yamaltu Deba, bisa zargin yi wa wata yarinya ’yar shekara 12 fyaɗe. Mai magana da yawun rundunar, DSP Buhari Abdullahi, ya tabbatar da faruwar lamarin cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata. EFCC ta saki Tambuwal Bankin Duniya zai kashe $300m domin inganta rayuwar ’yan gudun hijira a Arewacin Nijeriya Ya ce abin ya faru ne da misalin ƙarfe 9:00 na daren ranar 9 ga Agusta, 2025, lokacin da ake zargin ya yaudari yarinyar wadda ya kaita wani wuri da babu idon jama’a ya aikata ta’asar. Bayan samun rahoton faruwar lamarin ne, jami’an...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Tsohon Gwamnan Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal, ya shaki iskar ’yanci bayan sakinsa da Hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin Nijeriya ta’annati ta yi a yammacin wannan Talatar. A jiya Litinin ce aka ruwaito cewa EFCC ta tsare Tambuwal a hedikwatarta da ke Abuja, inda take zargin ya fitar da wasu kuɗaɗe ba bisa ka’ida ba har naira biliyan 189 a lokacin da yake rike da madafan iko.
    Gwamnatin jihar Kano ta gana da shugabannin ‘yan bangar siyasa da suka tuba a jihar tare da yi musu alkawarin tallafa musu ta hanyar sauya tunaninsu da horar da su sana’o’i da kuma kayan aikin fara sana’ar. Taron wanda ya gudana a ranar Talata a Kano ya samu halartar tubabbun ‘yan barandan siyasa da masu satar waya kusan 718. Gwamnatin Kano Ta Bayar Da Kwangilar Hanyoyi 17 Akan Naira Biliyan 40.8 Sin Ta Gabatar Da Sanarwar Hadin Gwiwa Kan Taron Tattalin Arziki Da Cinikayya Tsakaninta Da Amurka A Stockholm Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida, Ibrahim Waiya ya yi kira ga mahalarta taron da su rungumi tuba da gaskiya tare da bayar da hadin kai ga shirin gwamnati na...
    Bankin Duniya ya amince da bayar da dala miliyan 300 domin aiwatar da wani sabon shiri da zai inganta rayuwar ’yan gudun hijira da kuma al’ummomin da suka ba su matsugunni a Arewacin Nijeriya.  Bankin ya bayyana cewa a ƙarƙashin shirin mai suna Solutions for the Internally Displaced and Host Communities Project wato SOLID, wanda aka amince da shi a ranar 7 ga Agusta, za a lalubo hanyoyin da za a bi wajen taimakon ’yan gudun hijira, da ma garuruwan da suke rayuwa a ciki. Dasuki: Kotu ta bai wa Gwamnatin Tarayya wa’adin kammala shari’ar kuɗin makamai Nijeriya ta sake ƙulla alaƙar tsaro da Isra’ila Ya bayyana cewa shirin SOLID zai ruɓanya ƙoƙarin da gwamnati ke yi da ma wanda...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Mai magana da yawun ma’aikatar cinikayya ta kasar Sin ya bayyana a yau Talata 12 ga wata cewa, bisa dokoki ko ka’idojin da suka shafi saka wasu sassa cikin wadanda aka sanyawa takunkumin sayar musu da kayayyaki, ma’aikatar ta fitar da sanarwa mai lamba 21 da ta 22 a ranar 4 da kuma ranar 9 ga watan Afrilun bana, inda ta saka wasu sassa 28 na Amurka cikin wadanda ta sanyawa takunkumin sayar musu da kayayyaki, wato hana sayar musu kayayyakin amfanin jama’a da ake iya amfani da su a bangaren soja. Har wa yau, domin tabbatar da matsayar da aka cimma a wajen shawarwarin manyan jami’an Sin da Amurka a bangaren tattalin arziki da cinikayya, an yanke shawarar cewa,...
    Sun fara soyayya ba da jimawa ba, inda suka fito fili suka bayyana alakar dake tsakaninsu a shekarar 2017, masoyan sun haifi yarsu ta farko, Alana, a watan Nuwamba na shekarar 2017, daga nan suka haifi tagwaye, Bella da Angel, a watan Afrilun 2022, amma jim kadan da haihuwarsu Angel ya rasu, Georgina ta kuma taimaka wajen renon wasu ‘ya’yan Ronaldo guda uku – Cristiano Jr., wanda aka haifa a watan Yuni 2010, da tagwaye Eva da Mateo wadanda aka haifa ta hanyar dashen kwayoyin halittta a watan Yunin 2017.   Ronaldo, mai shekaru 40, ya na cikin kakar wasa ta hudu tun bayan komawarsa kungiyar Al-Nassr ta kasar Saudi Arabia, tsohon dan wasan Real Madrid, Manchester United da Juventus...
    Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta bai wa Gwamnatin Tarayya ranakun 24, 25 da 26 ga watan Satumba domin ta kammala shari’ar da ta shafe shekaru goma tana yi wa tsohon mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Kanal Sambo Dasuki mai ritaya, kan zargin mallakar makamai ba bisa ƙa’ida ba da kuma halasta kuɗin haram. Mai shari’a Peter Lifu ya bayar da wannan umarnin a ranar Talata, bayan amincewa da buƙatar gwamnati ta ɗage zaman domin kawo ƙarin shaidu da kuma ba wa Dasuki damar fara kare kansa. Nijeriya ta sake ƙulla alaƙar tsaro da Isra’ila Tinubu na amfani da EFCC ya muzguna wa ’yan adawa — Atiku Ya kuma umurci gwamnati ta kira sauran shaidunta domin...
    Biyo bayan sanarwar hadin gwiwa bayan taro kan tattalin arziki da cinikayya da aka yi tsakanin Sin da Amurka a birnin Geneva a ranar 12 ga watan Mayun 2025 wato sanarwar Geneva, da tarukan da aka yi a birnin London a ranekun 9 da 10 ga watan Yunin 2025, da wanda aka yi a Stockholm a ranekun 28 da 29 ga watan Yulin 2025, gwamnatin jamhuriyar jama’ar kasar Sin da gwamnatin Amurka, sun waiwayi alkawuran da suka dauka karkashin sanarwar hadin gwiwa ta Geneva, kuma sun amince cewa daga ranar 12 ga watan nan na Agusta, za su fara aiwatar da matakai kamar haka: Amurka za ta ci gaba da gyara matakan karin haraji kan kayayyakin kasar Sin, ciki har...
    Hukumar Kwastam Najeriya ta kama kwantainoni 16 ɗauke da makamai da miyagun ƙwayoyi da magungunan da wa’adin aikinsu ya ƙare da wasu haramtattun kaya na kimanin Naira 10 a Tashar Jiragen Ruwa ta Apapa da ke Jihar Legas a ranar Litinin. Hukumar ta bayyana cewa ta kama mutane shida dangane da wannan haramtattun kaya da aka yi fasa-ƙwaurin su zuwa Najeriya. Kwanturola Janar na Kwastam, Adewale Adeniyi, ya sanar da cewa an yi ƙarya wajen bayyana kayan da  kwantainonin suke ɗauke da su, inda aka ɓoye makamai, harsasai da magungunan da ba su da rajista. “A yau, muna sanar da kama kwantainoni 16 da shigowarsu ke karya dokokinmu kuma suna barazana ga tsaron ƙasa. Darajar harajin da za a biya...
    Babban sakataren Majalisar Kolin Tsaron kasar Iran Ya bayyana cewa: Kungiyar gwagwarmaya ta Hizbullah ba ta bukatar juya akalarta Babban sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran Ali Larijani ya bayyana cewa: Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah tana da cikakken ilimin siyasar da zata gudanar da al’amuranta bisa dacewa, kuma gwagwarmaya ba ta bukatar horo. Larijani ya kara da cewa a wani taron manema labarai a birnin Bagadaza na kasar Iraki; “Dukkansu sun damu da tsaron yankin baki daya, kuma al’ummar Iraki ba sa bukatar wani takunkumi.” Larijani ya jaddada cewa: Rattaba hannu kan yarjejeniyar tsaro da kasar Iraki na da nufin hana duk wata barazana ga tsaron kasashen biyu. A yayin da yake mayar da martani ga wasu nazari...
    Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya zargi gwamnatin Bola Tinubu da amfani da Hukumar EFCC wajen yi wa masu adawa da ita barazana. Saƙon da ɗan takarar shugaban ƙasa a Zaɓen 2023 ya wallafa wannan Talatar a shafinsa na X, na zuwa ne bayan tsare tsohon Gwamnan Sakkwato, Sanata Aminu Waziri Tambuwal da EFCCn ta yi. Amurka da China sun dakatar da harajin da suka ƙaƙaba wa juna Harin ’yan fashi: An rufe Federal Poly Bauchi Bauchi A cewar Wazirin Adamawa, “dalilin da EFCC ta tsare tsohon Gwamnan Sakkwato, Sanata Aminu Waziri Tambuwal, shi ne saboda yana cikin jam’iyyar adawa ta haɗaka. “Wannan yana ƙara nuna yadda gwamnatin Tinubu ke ci gaba da yaɗa manufofinta na musgunawa, tsoratarwa, da...
    Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa ya rattaba hannu kan wata yarjejeniyar da za ta tsawaita dakatar da harajin da ya ƙaƙaba wa ƙasar China na tsawon kwanaki 90. Trump ya sanar da hakan ne cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta na Truth Social, sa’o’i kaɗan kafin wa’adin farko da ya tsara ya ƙare. Harin ’yan fashi: An rufe Federal Poly Bauchi Bauchi Mastering diverse trading strategies for market success A ɗaya hannun, ma’aikatar kasuwanci ta ƙasar China ta kuma tabbatar da cewa ita ma ta dakatar da ƙarin haraji kan kayayyakin Amurka daga yanzu zuwa tsawon kwanaki 90, a matsayin martani. Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters ya ruwaito cewa tun a watan Mayun...
    Hakan ya gudana a ƙarƙashin jagorancin hukumomin da ke lura da yadda ake tafiyar da gasar da kuma kare haƙƙin masu amfani da kaya (FCCPC), hukumar kula da tallace-tallace ta Nijeriya (ARCON), da hukumar kula da harkokin caca da wasanni ta Jihar Legas (LSLGA). Zaɓen ya kasance cikin gaskiya da adalci, inda waɗanda yi nasara suka bar Naira 10,000 a cikin asusun ajiyarsu na Stanbic IBTC ko @ease Wallet har tsawon kwanaki 30. Daga mata ‘yan kasuwa, zuwa ɗalibai, har zuwa ma’aikatan da suka yi ritaya, waɗanda suka yi nasara yanzu suna iya biyan kuɗin makaranta, fara ƙananan sana’o’i, ko kuma tafiyar da buƙatun gidajensu cikin sauƙi. An ƙara sanya wasu mutane takwas cikin farin ciki a zaɓen babbar garaɓasar...
    Hukumomin Kwalejin Kimiyya da Kere-kere ta Gwamnatin Tarayya sun ufe makarantar a sakamakon zanga-zangar da dalibai suka gudanar domin nuna fushinsu kan harin da ’yan fashi suka kai dakunan kwanansu. Daliban sun tayar da tarzoma ne da sanyin safiyar Talata bayan harin ’yan fashin ya ya yi sanadiyyar jikkatar wasu dalaibai da dama, suna mazu zargin hukumomin kwalejin da kasa kare su daga abin da ya faru cikin dare. Rahotanni since ’yan fashin sun kwace wa daliban kayayyakinsu, tare da jikkata mutum tara. An dai ga fusatattun daliban suna gudanar da zanga-zanga a kan hanyar Bauchi zuwa Dass, inda suka daura shingen hana zirga-zirga a kofar shiga kwalejin. ’Yan sanda sun harba barkonon tsohuwa domin tarwatsa jama’a, lamarin da ya sa...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Babban abin kunya ne shirun da gwamnatocin yammacin Turai suka yi game da muggan laifukan ‘yan sahayoniyya Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya dauki kisan gillar da yahudawan sahayoniyya suka yi wa ‘yan jaridun Falasdinawa a matsayin wata shaida ta ta’addancin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila da take gab da rugujewa. A yayin da yake tsokaci game da kisan gilla da yahudawan sahayoniyya suke yi kan ‘yan jaridan Falasdinawa, Araqchi ya rubuta a dandalin sada zumunta na “X” a jiya litinin cewa: “Sojojin mamayar Isra’ila sun kai hari kan wasu fitattun ‘yan jarida na Falasdinu. Shin wannan wata alama ce ta nuna karfi? Ko kuwa shaida ce ta ta’addancin gwamnatin da...
    Babban sakataren Majalisar Kolin Tsaron kasar Iran Ya bayyana cewa: Kungiyar gwagwarmaya ta Hizbullah ba ta bukatar juya akalarta Babban sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran Ali Larijani ya bayyana cewa: Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah tana da cikakken ilimin siyasar da zata gudanar da al’amuranta bisa dacewa, kuma gwagwarmaya ba ta bukatar horo. Larijani ya kara da cewa a wani taron manema labarai a birnin Bagadaza na kasar Iraki; “Dukkansu sun damu da tsaron yankin baki daya, kuma al’ummar Iraki ba sa bukatar wani takunkumi.” Larijani ya jaddada cewa: Rattaba hannu kan yarjejeniyar tsaro da kasar Iraki na da nufin hana duk wata barazana ga tsaron kasashen biyu. A yayin da yake mayar da martani ga wasu nazari...
    Kasar Italiya ta janye jirgin ruwanta daga tekun Bahar Maliya bayan gazawarta a fage kwamawa da kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen Kasashen Turai sun ci gaba da janye jiragen ruwa da jiragen yaki daga tekun Bahar Maliya, lamarin da ke tabbatar da hukuncin da kasashen nahiyar suka dauka na cewa ci gaba da zamansu a cikin tekun ba shi da amfani bayan da Dakarun ‘yan gwagwarmyar Yemen suka yi gargadin cewa; Duk masu alaka da haramtacciyar kasar Isra’ila zasu fuskanci  hare-haren makamai masu linzami da na jiragen saman yaki. Kwanaki biyu bayan sanar da janye jirgin ruwan Faransa daya tilo, da rundunar Turai ta kafa don kare jigilar jiragen haramtacciyar kasar Isra’ila, “Aspedes,” ta sanar da janye jirgin ruwan Italiya...
    Majalisar Dinkin Duniya ta sanar da cewa: Mutane 60 ne suka rasa rayukansu sakamakon yunwa a birnin El Fasher na Sudan Ofishin kula da ayyukan jin kai na Majalisar Dinkin Duniya, OCHA, ya bayyana damuwarsa kan rahotannin da ke fitowa daga birnin El Fasher da ke arewacin Darfur, da ke cewa sama da mutane 60 sun mutu sakamakon yunwa da rashin abinci mai gina jiki cikin mako guda. Ofishin Majalisar Dinkin Duniya ya tabbatar da cewa ya fara tattara bayanan yunwa a sansanin Zamzam na ‘yan gudun hijira a Arewacin Darfur kimanin shekara guda da ta wuce, kuma ya jaddada cewa yana sa ran za a iya yada yunwa a wasu yankuna. A wani labarin kuma, Majalisar Dinkin Duniya ta...
    Rijistaran makarantar, Alhaji Kasimu Salihu, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana cewa an rufe makaranta kuma an umarci ɗalibai su bar harabar makarantar har sai an bayar da sanarwa ta gaba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    ‘Yan Democrats a Amurka sun zargi Donald Trump da mutumin da giyar mulki ke ruɗawa, bayan ya ce zai tura jami’an rundunar tsaro ta ƙasar birnin Washington don yaƙi da laifukan da ake ganin sun gagari ƴansandan birnin. Magajiyar birnin Muriel Bowser, ta ce matakin bai dace ba, sannan ta musanta batun da shugaban ke yi cewa an gaggara daƙile masu aikata laifi. ‘Yan Democrats a majalisa, sun ce wannan mataki babu wani abin da zai haifar face ‘tsoro da hargitsi, kuma wannan yunƙuri ne kama hanyar kama-karya. Shugaban masu rinjaye a majilsar wakilai ya ce Mista Trump ya mayar da mulki kamar wata sarauta. Shi dai Trump ɗin ya ce birnin washington a cike yake da masu gararamba a...
    Rundunar ‘yan sandan jihar Kwara ta kama wasu mutane biyu da ake zargin ’yan kungiyar asiri ne tare da kwato musu wasu abubuwa na bata gari a Ilorin.   A cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan, Adetoun Ejinre-Adeyemi ya fitar, ya ce, ‘yan sandan da ke aiki bisa sahihiyar bayanan sirri daga majiyoyin tsaron al’umma, sun dauki wami mataki kan wani harin fashi da makami da ya afku a wani dakin kwanan dalibai da ke unguwar Eleko, Ilorin. Sanarwar ta ce ba tare da bata lokaci ba jami’an ‘yan sanda da ‘yan banga, sun kai ga kama wasu maza biyu da ake zargi.   Ta ce wadanda ake zargin sun hada da Ishola Adeyemi,...
    Dakarun Operation FANSAN Yamma (OPFY) sun yi nasarar fatattakar ‘yan ta’adda da dama a wani hari da suka kai ta sama da kasa a yankin Makakkari da ke dajin Gando a karamar hukumar Bukkuyum a jihar Zamfara.   Wannan farmakin wanda ya gudana a ranar 10 ga watan Agustan shekarar 2025, ya biyo bayan wasu bayanan sirri da suka samu cewa dimbin ‘yan ta’addan da ke biyayya ga marigayi Halilu Buzu da Alhaji Beti sun taru a cikin dajin inda suka shirya kai harin ramuwar gayya kan al’ummomin Addabka da Nasarawan Burkullu a garin Bukkuyum.   Jami’in yada labarai na rundunar ‘Operation Fansan Yamma OPFY’ Kyaftin David Adewusi, ya ce bayanan sirri sun nuna cewa, harin da suka shirya kai...
    Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya sake nada Dr. Muheeba Dankaka a matsayin shugaban hukumar kula da da’a ta tarayya (FCC) a wa’adi na biyu na shekaru biyar.   Mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan yada labarai, Bayo Onanuga, ya ce nadin na daya daga cikin alkawurran da shugaban kasar ya yi na “karfafa hukumar don tabbatar da adalci, daidaito da kuma hada kai a nade-naden na tarayya bisa tanadin tsarin mulki.”   Shugaban ya kuma nada Mohammed Musa a matsayin sakataren hukumar sannan Kayode Oladele daga jihar Ogun a matsayin kwamishina. An nada Oladele, wanda tsohon dan majalisar wakilai ne a hukumar a shekarar 2024 kuma ya rike mukamin shugaban riko bayan kammala wa’adin farko na Dankaka....
    Yajin aikin sai baba-ta-gani da kungiyar kwadago ta Najeriya NLC reshen jihar Taraba, da kungiyar Kwadago (TUC) reshen jihar Taraba suka kaddamar a ranar Litinin da ta gabata, ya gurgunta ayyukan gwamnati a ma’aikatu da hukumomin gwamnati a jihar.   Matakin wanda ya fara da tsakar daren litinin, ya kasance tare da hadin gwiwar shugabannin kungiyoyin biyu bayan taron majalisar zartaswar jihar da aka gudanar a ranar Lahadi a sakatariyar kungiyar NLC ta jihar.   Taron ya yi nazari ne kan wa’adin da aka bayar tun da farko kan wasu kura-kuran da ake zargin an tafka a cikin ayyukan kwamitin tantance bayanan da gwamnatin jihar ta kafa.   A cikin wata sanarwar hadin gwiwa da sakataren kungiyar NLC na jihar,...
    Hukumar Kwastam Najeriya ta kama kwantainoni 16 ɗauke da makamai da miyagun ƙwayoyi da magungunan da wa’adin aikinsu ya ƙare da wasu haramtattun kaya na kimanin Naira 10 a Tashar Jiragen Ruwa ta Apapa da ke Jihar Legas a ranar Litinin. Hukumar ta bayyana cewa ta kama mutane shida dangane da wannan haramtattun kaya da aka yi fasa-ƙwaurin su zuwa Najeriya. Kwanturola Janar na Kwastam, Adewale Adeniyi, ya sanar da cewa an yi ƙarya wajen bayyana kayan da  kwantainonin suke ɗauke da su, inda aka ɓoye makamai, harsasai da magungunan da ba su da rajista. “A yau, muna sanar da kama kwantainoni 16 da shigowarsu ke karya dokokinmu kuma suna barazana ga tsaron ƙasa. Darajar harajin da za a biya...
    Ya ƙara da cewa gwamnati ta ƙara kuɗi zuwa Naira miliyan 1,000 (wato miliyan 500 da aka ware a baya da ƙarin miliyan 500) domin magance matsalar yunwa a jihar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Hukumar Yaki da Masu Karya Tattalin Arziki (EFCC) ta tsare tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato, Sanata Aminu Waziri Tambuwal kan zargin almundahana. A ranar Litinin ce EFCC ta tsare Tambuwal bayan da ya masa gayyatar da ta yi masa zuwa Ofishinta domin amsa tambayoyin kan badaƙalar Naira biliyan 189. Majiyoyi sun shaida wa wakilinmu cewa Hukumar EFCC ta tsare tsohon Shugaban Majalisar Wakilan ne kan zargin cirar Naira biliyan 189. Wata majiya a EFCC ta bayyana cewa, “Ba kama shi aka yi ba, zuwa ya yi domin amsa tambayoyi kan yadda ya yi amfani da Naira biliyan 189. Amma da ya kasa bayani sai aka tsare shi. Ina ganin shi ya sa mutane ke cewa an kama shi. “Zai ci gaba...
    Ministan harkokin wajen kasar Masar Badr Abdelatty ya yi gargadin cewa a shirye take ta dauki duk wani mataki na kare muradunta na iyakokin teku. Da yake magana a wani taron manema labarai na hadin gwiwa a birnin Alkahira tare da ministan harkokin wajen kasar Ivory Coast, Léon Kacou Adom, wanda aka gudanar a wani bangare na shawarwarin siyasa karo na uku tsakanin Masar da Cote d’Ivoire, Abdelatty ya ce tattaunawar ta yi tsokaci kan kalubalen ci gaban kasashen Sahel da yammacin Afirka. Ya kuma kara da cewa, an tattauna hadin gwiwa kan yaki da ta’addanci, inda ya yaba wa Cote d’Ivoire bisa kokarin da take yi a wannan fanni. Abdelatty ya jaddada cewa, “Masar na mai da hankali matuka...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araghchi ya yi Allah wadai da kisan da aka yi wa ‘yan jarida  biyar a wani harin da Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta kai a zirin Gaza, yana mai bayyana wannan laifi a matsayin shaida ta yanke kauna daga  gwamnatin da duniya ta juya mata baya saboda munanan laifukanta. A wani sakon da ya wallafa a shafin sada zumunta a yammacin wannan Litinin, Araghchi ya bayyana cewa kisan gillar da aka yi wa wasu manyan ‘yan jarida na Falasdinu ba alama ce ta karfin gwamnatin sahyuniya ba, hakan alama ce ta gazawa da yanke kauna. Ya kuma kara jaddada cewa hadin kan da wasu gwamnatocin kasashen Yamma suke baiwa Isra’ila yana mai ishara da kasashe...
    Ma’aikatar lafiya a Gaza ta sanar da isar shahidai 69 da wadanda suka jikkata su 362 zuwa asibitoci a cikin kasa da sa’o’i 24 da suka gabata. Daga cikin shahidan akwai wadanda yunwa ce ta kashe su, da kuam wadanda suka yi shahada a wajen neman samun agajin abinci, ida Isra’ila take kai hari kansu abbu kakkautawa. A cikin rahotonta na kididdiga na yau da kullun, ma’aikatar ta gano mutuwar mutane biyar da suka hada da yaro daya sakamakon yunwa a cikin sa’o’i 24 da suka gabata, wanda adadin wadanda suka yi shahada sakamakon yunwa ya kai 222, ciki har da yara 101. Ma’aikatar ta tabbatar da cewa adadin wadanda suka mutu a harin ta’addancin Isra’ila ya karu zuwa shahidai...
    Ministan tsaron kasar Italiya Guido Crosetto ya bayyana cewa gwamnatin Isra’ila ta fita hayyacinta a yakin da ake ci gaba da yi a zirin Gaza, yayin da kuma yake nuni da cewa Italiya a shirye take ta bi sahun kasashen duniya wajen kakaba wa Isra’ila takunkumi. A cikin wata hira da jaridar La Stampa ta Italiya, Crosetto ya bayyana cewa, abin da ke faruwa a Gaza ba abu ne da za a amince da shi ba. Crosetto ya kuma jaddada cewa Italiya ta ci gaba da jajircewa wajen bayar da agajin jin kai, amma ya kara da cewa, “Yanzu dole ne mu nemo hanyar da za mu tilasta wa Netanyahu sake yin tunani.” Dangane da yuwuwar kakaba takunkumi, Crosetto ya...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Samun matasan da ke bayar da gudunmawa ga ci-gaban al’ummominsu abu ne da ba kasafai ake samu ba a wannan zamani. Amma duk da haka, wasu matasa sun sadaukar da rayuwarsu wajen bayar da gudunmawarsu wajen ci-gaban al’ummarsu. NAJERIYA A YAU: Yadda Damina Ke Shafar Masu Ƙananan Sana’o’i DAGA LARABA: Me Ke Sa Matasa Zama Karnukan Farautar ‘Yan Siyasa A Kafafen Sadarwa Na Zamani? Shirin Najeriya  A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan irin gudunmawar da matasa ke bayarwa wajen ci-gaban al’ummarsu. Domin sauke shirin, latsa nan
    Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Ƙasa (NAFDAC) murna bisa ci gaba da riƙe matsayin Maturity Level 3 (ML3) na Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) wajen kula da magunguna da rigakafi. Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara na Musamman kan Harkokin Bayani da Tsare-tsare, Bayo Onanuga, a cikin wata sanarwa, ya bayyana cewa, an gudanar da binciken sake tantance matsayin WHO daga 28 zuwa 30 ga Mayu, 2025, inda aka kimanta NAFDAC bisa ka’idojin ƙasa da ƙasa. Hukumar ta fara samun wannan matsayi na ML3 ne a 2022, inda ta zama hukumar farko a Afrika mai kula da ƙasashen da ba sa samar da magunguna da ta cimma wannan nasara. Wannan sabon...
    Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ƙasa (EFCC) ta yi wa tsohon gwamnan Jihar Sokoto, Sanata Aminu Tambuwal, tambayoyi kan zargin fitar da wasu kuɗi har Naira biliyan ₦189 ta hanyar cire kuɗin daga banki. Rahotanni sun nuna cewa, Tambuwal ya isa shalƙwatar EFCC a Abuja da misalin karfe 11:30 na safiyar yau Litinin, inda yake ci gaba da fuskantar tambayoyi daga jami’an bincike kan zargin. Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ba a tabbatar ko za a tsare shi ba na dogon lokaci ba. Ku Yaƙi Cin Hanci Ba Ƴan Adawa Ba – ADC GA EFCC EFCC Ta Kama Mutane 11 Kan Haƙar Ma’adinai Ba Bisa Ƙa’ida Ba A Akwa Ibom Majiyoyi daga EFCC sun tabbatar da...
    Gwamna Umar Namadi na Jihar Jigawa ya ce yaki da talauci muhimmin mataki ne na hanzarta ci gaban tattalin arziki da samar da ayyukan yi. Ya bayyana haka ne a lokacin shirin gwamnatin jihar mai taken “Gwamnati da Jama’a” wanda aka gudanar a karamar hukumar Ringim. Malam Umar Namadi ya jaddada muhimmancin horas da matasa sana’o’in hannu da samar da yanayin kasuwanci mai kyau domin cimma wadannan manufofi. Saboda haka, ya yi kira ga zababbun wakilai, masu rike da mukaman siyasa, shugabannin kasuwanci da sauran attajirai da su taimaka wa al’ummarsu domin kara bunkasa ci gaba da habaka tattalin arziki. A yayin taron, Kwamishinan jin kai da harkokin musamman na jihar, Auwal Danladi Sankara, ya raba naira miliyan 50...
    Yanzu haka mutane huɗu suna karɓar magani a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Shika, Zariya, bayan sun jikkata a wani mummunan haɗarin da ya haɗa da tankoki biyu a ƙauyen Kake, yankin Dan Magaji, kan hanyar Zariya–Kaduna. Haɗarin ya jawo mummunar gobara bayan haɗuwar motocin. Kwamandan hukumar kiyaye haɗɗura ta ƙasa (FRSC) reshen Zariya, Nasir Abdullahi Falgore, ya bayyana cewa ɗaya daga cikin tankokin na ɗauke da iskar gas (LNG), yayin da ɗayar kuma babu komai a cikinsa. Ya ce sakamakon binciken farko ya nuna tayar ɗaya daga cikin tankokin ce ta fashe, lamarin da ya sa tankar da ke biye ta bugi ta gaba, wanda ya haddasa fashewar gas da tayar da gobara. Kwalejin Digiri...
    Sojoji sun samu nasarar kai wani gagarumin farmaki kan maboyar ’yan ta’addan da suka addabi manoma da mazauna wasu ƙauyuka a Jihar Zamfara da ke Arewa maso Yammacin Nijeriya. Bayanai sun ce dakarun sojin na sama da ta ƙasa, waɗanda ke ƙarƙashin rundunar Operation Fasan Yamma da ke sintiri a Arewa maso Yamma domin kawar da masu tayar da ƙayar baya, sun hallaka sama da ’yan ta’adda 400 a yayin wannan samamen. Za a gyara tarbiyar tubabbun ’yan daban Kano Direba ɗaya ya tsira a hatsarin tankokin dakon iskar gas a Zariya Majiyoyi sun bayyana cewa ’yan ta’addan, waɗanda ke fakewa a dajin Makakkari tare da shugabanninsu daban-daban, sun dauki haramar kai hari kan wani ƙauye ne kafin sojojin su...
    Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya shawarci matasan da ake ribatarsu a matsayin ’yan daban siyasa da suka tuba da su guji tashin hankali, yana tabbatar musu da shirye-shiryen gwamnatinsa na gyara tarbiyarsu tare da mayar da su cikin al’umma. Gwamnan ya yi wannan alkawari ne a taron wuni ɗaya da aka gudanar tare da shugabannin rukunan ’yan daban da suka tuba a ƙarƙashin Shirin Safe Corridor. Direba ɗaya ya tsira a hatsarin tankokin dakon iskar gas a Zariya An kama mutumin da ake zargi da kashe jami’in sibil difens a Jigawa Gwamnan, wanda Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida, Ibrahim Waiya, ya wakilta, ya ce: “Ba za a sake ɗaukar makami da sunan fadan siyasa ko wasu munanan...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Fitaccen masanin tattalin arziki dan kasar Birtaniya John Ross, ya ce ma’aunin tattalin arziki na GDP na kasar Sin ya karu da kaso 5.3 bisa dari a mizanin shekara, cikin rabin farko na shekarar nan ta 2025, wanda hakan ke nuni ga ingancin tushen tattalin arzikin kasar. Ross, wanda ya bayyana hakan a baya-bayan nan, yayin zantawarsa da kamfanin dillancin labarai na kasar Sin Xinhua, ya ce Sin ta wanzar da managarcin yanayin zuba jari, tana kuma kara fadada jarin da ake shigarwa a fannin bincike da samar da ci gaba, tare da ingiza daga matsayin fasahohi, wanda hakan ya haifar da managarcin yanayi na bunkasa tattalin arzikin kasar. A cewar shaihun malamin, tattalin arzikin kasar Sin zai ci gaba...
    Jam’iyyar ADC ta zargi hukumar EFCC na yin son zuciya tare da yin aiki a matsayin kayan aikin siyasa ga jam’iyyar mai mulki APC. Jam’iyyar ta gargaɗin cewa irin wannan mataki yana rage ingancin yaƙin da ake da cin hanci da kuma rage amincewar jama’a. A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun jam’iyyar na ƙasa, Mallam Bolaji Abdullahi, ya fitar, ADC ta bayyana cewa ayyukan EFCC na baya-bayan nan, ciki har da buɗe tsofaffin shari’o’i da kuma maida hankali kan ƴan adawa, sun nuna halayyar kamar ta “mai aiwatar da umarnin siyasa” maimakon hukuma mai aiki da gaskiya. Ta kuma zargi hukumar da kiran wasu shugabannin adawa kan shari’o’in da suka dogara da tsoffin zarge-zarge na siyasa. UEFA...
    A safiyar wannan Litinin ɗin ce aka wayi gari da wani mummunan hatsarin tankoki biyu na dakon iskar gas a Zariya, inda direba ɗaya kacal ya tsira da rai, yayin da wasu da dama suka ƙone ƙurmus. Shaidun gani da ido sun ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe tara na safe, a kusa da shatale-talen Jirgin Sama Mota da ke titin Kaduna zuwa Zariya, daura da sabuwar Kasuwar Ɗan Magaji. An kama mutumin da ake zargi da kashe jami’in sibil difens a Jigawa Ya ba wa alaramma kyautar motarsa saboda daɗin karatun Alkur’ani Rahotanni sun nuna cewa motocin biyu sun gogi juna ne yayin da ɗaya ke ƙoƙarin wuce ɗaya, lamarin da ya haddasa kamawar wuta nan take....
    Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kaduna ta shawarci maniyyata aikin Hajjin shekarar 2026 da su fara shirin biyan kudaden ajiya. Kiran ya biyo bayan taron da Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Kasa (NAHCON) ta gudanar tare da hukumomin Alhazai na jihohi, inda aka bayar da shawarar ajiyar naira miliyan 8 da rabi ga masu niyyar zuwa aikin Hajji, kafin a sanar da hakikanin kudin aikin Hajjin shekarar 2026. A cikin wata sanarwa, mai magana da yawun hukumar, Yunusa Mohammed Abdullahi, ya shawarci wadanda ba su da fasfo da su gaggauta zuwa Hukumar Shige da Fice ta Kasa domin yin nasu, yana mai cewa shi ne ake amfani da shi wajen hada takardun tafiya. Najeriya ta sake samun kujeru...
    Chen Xiaoguang ya bayyana cewa, dabarun da aka saba amfani da su na yaki da sauro suna da tasgaro. Ya ce tarko da gidan sauro na kama sauro ne marasa shan jini, yayin da tsarin kama sauro cikin mazubi da ruwa, ke kama sauro masu jan jini da yin kwai.   Ya kara da cewa, abun da suka kirkiro na’ura ce dake gudanar da ayyuka biyu a lokacin da ake ciki, kuma tana da matukar inganci wajen sa ido da bibiyar sauro. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a...
    Hukumar tsaro ta sibil difens (NSCDC) ta sanar da cafke wani mutum, Salisu Muhammad, mai shekaru 45, bisa zargin kashe jami’inta, Bashir Adamu Jibrin, a kasuwar Shuwarin da ke Karamar Hukumar Kiyawa a Jihar Jigawa. A cewar wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Muhammed Badarudeen ya fitar a Dutse, babban birnin jihar, lamarin ya faru ne a ranar kasuwa lokacin da marigayin yake gudanar da aikinsa. Ya ba wa alaramma kyautar motarsa saboda daɗin karatun Alkur’ani Tankokin mai sun yi bindiga a Zariya Rahotanni sun nuna cewa, ana zargin Salisu ya buga wa jami’in dutse a kai, lamarin da ya yi sanadin mutuwarsa. Hukumar ta ce ta kama wanda ake zargin ne a gidansa da ke Shuwarin...
    Asusun Kula da Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) tare da haɗin gwiwar Gavi da ke taimakawa wajen samar da rigakafi, sun mika na’urorin samar da wutar lantarki ta hasken rana g Gwamnatin Jihar Kano domin amfani da su a cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko (PHCs) guda 28 da nufin ƙarfafa rigakafin yara da kuma kula da lafiyar jama’a. A yayin bikin mika kayayyakin ga gwamnatin jihar da Hukumar Kula da Lafiya a Matakin Farko ta Ƙasa (NPHCDA), Kwamishinan Lafiya na Kano, Dakta Abubakar Labaran Yusuf, ya ce wannan shiri na nufin taimaka wa yaran da ba a musu rigakafi, da mata masu juna biyu da ba su da damar samun rigakafin yau da kullum da kuma wasu ayyukan...
    Birnin Karbala mai tsarki na sa ran karbar bakwancin masu ziyara sama da miliyan 4 daga kasashen ketare domin gudanar da juyayin Arbaeen Jama’a masu dimbin yawa na tururuwa zuwa birnin Karbala mai tsarki daga Najaf domin halartar yuyayin ranar Arbaeen a cikin tsauraran matakan tsaro da na hidima. Wakilin Al-Alam da ke kan titin Karbala Mo’ataz Al-Aboudi ya ruwaito cewa: Ana ci gaba da zirga-zirgar masu ziyarar Arbaeen lami lafiya duk kuwa da tsananin zafi a kan hanyoyin da ke kan hanyar zuwa Karbala. Wakilin na Al-Alam ya bayyana cewa: Birnin Karbala mai tsarki yana sa ran halartar masu ziyara sama da miliyan 4 daga wajen kasar Iraki, a cewar gwamnan Karbala Jassim Al-Khattabi. Ya yi nuni da cewa...
    Kasashen Turai biyar na kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya sun ki amincewa da matakin mamaye Gaza Wakilin dindindin na Slovenia ya gabatar da wata sanarwa ga kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya a madadin Burtaniya, Faransa, Denmark, da Girka, yana mai cewa: “A matsayinsu na kasashen Birtaniya, Denmark, Faransa, Girka, da Slovenia, sun kira taron gaggawa na kwamitin tsaron Majalisar kan halin da ake ciki a Gaza. Suna Allah wadai da matakin da haramtacciyar kasar Isra’ila ta dauka na fadada ayyukanta na soji a Gaza. Ya kuma jaddada cewa: Hakan yana barazana tare da keta dokokin kasa da kasa, yana mai kiran gwamnatin mamayar Isra’ila da ta hanzarta janyewa daga wannan matsayi.  Ya jaddada cewa: Duk wani matakin mamaye yankunan Falasdinawa...
    Wani mutum ya ba da kyautar motarsa da ita kadai gare shi ga wani mai jan baki (alaramma) saboda ƙwarewarsa a haddar Al-kur’ani. Malam Yusuf Ɗan-Birni, ya kyautar da motar ce a taron wa’azin wata-wata da Ƙungiyar Jama’atu Izalatil Bid’a Wa Iƙamatis Sunna (JIBWIS) ta shirya a garin Kubwa da ke yankin Babban Birnin Tarayya. Malam Yusuf Ɗan-Birni wanda ke sana’ar gyaran waya, ya bai wa jama’a mamaki a yayin da ake tsaka da karatun da misalin ƙarfe 10 nan dare inda ya miƙa makullan motarsa ga mai gabatar da wa’azin, Sheikh Mahmud Assalafi, ya sanar da shi cewa ya kyautar da ita ga majabaƙinsa, Alaramma Usman Nasidi Gusau. Wani ganau mai suna Malam Nuhu Abu-Huzaifa ya shaida wa Aminiya...
    Kungiyar Kwadago da ta ‘yan kasuwa ta Nijeriya (NLC da TUC) reshen jihar Taraba sun bayyana shirin fara yajin aiki tun daga karfe 12 na daren Litinin 11 ga watan Agusta, 2025. Wannan mataki ya biyo bayan sakamakon taron majalisar zartarwa ta jihar da kungiyoyin biyu suka yi a ranar Lahadi a Jalingo, babban birnin jihar Taraba. A cikin sanarwar da LEADERSHIP ta samu a daren Lahadi mai dauke da sa hannun sakataren kungiyar NLC, Adamu-Buba, da sakatariyar kungiyar TUC, Polina Gani, sun yi kira ga mambobinsu da su ba da hadin kai ga matakin da kungiyoyin suka dauka domin neman hakkokinsu a wurin gwamnatin jihar ta Taraba. Kungiyar kwadagon ta ce, taron ya sake duba wa’adin da aka bayar...
    Rundunar sojin Isra’ila ta ce ta kashe wani fitaccen dan jarida na kafar yada labarai ta Al Jazeera Anas al-Sharif tare da abokan aikinsa hudu a wani hari da ta kai Gaza. Isra’ila ta zarge shi da kasancewa wani jagora na Hamas sannan ta ce ta hallaka shi saboda irin rahotannin da yake bayarwa masu tsanani daga arewacin Gaza. Isra’ila ta hari ‘yan jaridar biyar – Anas al-Sharif wanda shi ne fitacce tare da Mohammed Qreiqeh masu aikawa da rahotanni ne sai kuma masu daukar musu hoto Ibrahim Zaher da Mohammed Noufal da kuma Moamen Aliwa wadanda dukkanin su suna aiki ne da kafar ta Al Jazeera. A lokacin da Isra’ila ta kai musu harin ta sama suna cikin wani...
    ’Yan ta’adda sun kashe mutum 24 tare da sace wasu akalla 144 a cikin mako guda a sassan Jihar Zamfara. Kungiyar Al’ummar Zamfara mai suna Zamfara Zamfara Circle Community Initiative ta bayyana cewa ’yan ta’addan sun kai hare-haren da suka kai kan kauyuka 15 inda suka jikkata mutane 16 a kananan hukumomi daban-daban. Ta bayyana cewa daga ranar 4 zuwa 10 ga watan nan na Agusta, 2025 ’yan ta’adda suka kai hare haren; kauyukan da aka kai wa farmakin sun hada da Sabe, Tungar Yamma, Sauru, Lambasu, Dogon Madacci, Dankalgo, da Kwanar Kalgo a ƙaramar hukumar Bakura. A Karamar Hukumar Tsafe, hare-haren sun shafi Chediya, Kucheri, Yankuzo, da Katangar Gabas Bilbils. A Karamar hukumar Mafara, an samu rahoton hare-hare a...
    A ci gaba da gudanar da bukukuwan makon shayarwa da nonon uwa na duniya, asusun kula da kananan yara na majalisar dinkin duniya UNICEF ya shirya tarurruka a Kano tare da hadin gwiwar U-Reporters da sauran kungiyoyin matasa domin wayar da kan al’umma kan amfanin shayarwa.   An gudanar da gangamin a lokaci guda a wurare daban-daban a fadin jihar, wadanda suka hada da Dangi Roundabout, KSIP Roundabout dake kan titin Ahmadu Bello, Central Road, Triumph Roundabout, Legas Street, Hotoro Roundabout dake Gabashin Bypass, Gidan Gwamnati dake kan titin Jiha, da Kasuwar Abubakar Rimi.   Sauran wuraren sun hada da Kofar Gadon Kaya, Kofar Nasarawa, Gadar Lado dake kan titin Zaria, da Unguwar Kasuwar Yankaba dake kan titin Hadejia.  ...
    Gwamna Oyebanji ya godewa ‘yan majalisar zartarwar jihar da abin ya shafa tare da yi musu fatan samun nasara a ayyukansu na gaba.   Sai dai, umarnin bai shafi babban Lauyan jihar da kwamishinan shari’a ba.   Har ila yau, daga cikin wadanda sallamar ba ta shafa ba, akwai Kwamishinonin Lafiya da Ayyukan Jama’a, Noma da Tattalin Abinci da Ayyuka.   Bugu da kari, kwamishinan ciniki, saka hannun jari, masana’antu da kungiyoyin hadin gwiwa; Mai ba da shawara na musamman kan Ilimin masu bukata ta Musamman; da mai ba da shawara na musamman kan tsare-tsaren kasa, duk suna nan kan mukamansu.   Haka kuma, duk Daraktocin da ke cikin majalisar zartarwa ta Jihar, za su ci gaba da rike mukamansu....
    Gwamna Mohammed Umar Bago na jihar Neja, ya kaddamar da aikin sarrafa man kade tan dubu talatin a karamar hukumar Mokwa ta jihar tare da alkawarin samar da muhallin kasuwanci don bunkasa.   Wani wuri mai daraja na duniya, wanda Salid Agriculture Nigeria Ltd ya gina kuma bankin NEXIM PLC zai samar da shi zai kawo sauyi ga tattalin arzikin matan karkara, kananan manoma, da kuma tattalin arzikin jihar Neja.   Gwamna Mohammed Umar Bago ya samu rakiyar Dr. Aliyu Sabi Abdullahi, Ministan Noma, Abba Bello, MD/Shugaban Bankin NEXIM, Alhaji Ali Sa’idu, MD/Shugaba na Salid Agriculture Nigeria Ltd da tsohon Gwamnan Bayelsa da kuma fitattun iyayen gidan sarauta da suka hada da mai martaba Etsu Nupe, Alhaji Yahaya Abubakar da...
    Rundunar ‘yan sandan jihar Nasarawa ta cafke wasu mutane shida da ake zargin ‘yan fashi da makami da masu garkuwa da mutane ne a karamar hukumar Doma da ke jihar.   Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar SP Ramhan Nansel ya bayyana haka a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a lafiya, ya ce jami’an sun kuma kama wani makiyayi dauke da makamai a karamar hukumar Keana ta jihar.   Sanarwar ta ce, jami’an sashin Doma da ke aiki da sahihan bayanan sirri daga wani dan kasa mai kishin kasa, karkashin jagorancin jami’in ‘yan sandan shiyya, sun kai samame a wata maboyar ‘yan ta’adda da ke Yelwa Ediya inda aka kama wadanda ake zargin.  ...
    Kungiyar Muslim Media Watch Group ta Najeriya ta yi Allah-wadai da wata sanarwa da ake zargin Bishop David Oyedepo kan amfani da hijabi da daliban Musulman Jami’ar Landmark ta Omu-Aran ta Jihar Kwara suka yi.   A cikin wata sanarwa dauke da sa hannun wakilinta na kasa Sheikh Abu Sheriff, kungiyar ta yi Allah wadai da Bishop David Oyedepo da take hakkin dalibai musulmi da ma’aikatan cibiyar da ke da hakkin dan Adam kamar yadda sashe na 38 na kundin tsarin mulkin Najeriya ya tabbatar.   A cewarsa a cikin wani faifan bidiyo da aka yada sosai, Oyedepo ya yi kira ga iyaye da masu kula da Musulmai da su janye ‘ya’yansu mata idan suka dage ba za ayi amfani...
    Mahalarta taron masu ruwa da tsaki na yini daya don tabbatar da sakamakon bincike kan al’amuran zamantakewa da suka shafi ilimin ‘ya’ya mata a jihar Zamfara, sun bukaci iyaye, shugabannin al’umma, da gwamnati a dukkan matakai da su magance matsalolin da ke hana yara mata zuwa kammala karatun sakandare.   Kungiyar AGILE da ke Jihar Zamfara tare da hadin gwiwar Media and Publicity Consult ta shirya taron masu ruwa da tsaki na rana daya domin tabbatar da sakamakon binciken da aka yi kan ka’idojin zamantakewa da ke kawo cikas ga ’yan mata matasa da ke hana shiga makarantun gaba da sakandare a jihar Zamfara.   Da yake jawabi a wajen taron, Farfesa Abubakar Aliyu Liman na Jami’ar Ahmadu Bello da...
    Rundunar ‘yan sandan jihar Kwara ta ce ta karfafa matakan tsaro a yankin Babanla biyo bayan harin da wasu da ake zargin mahara ne suka kai musu, inda suka kashe mutane 5 ciki har da dan sanda Adejumo Wasiu.   A cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda, SP Adetoun Ejinre-Adeyemi ya fitar, ya ce ‘yan fashi da makami da yawansu ya kai daruruwa, a kan babura, sun mamaye al’ummar Babanla a karamar hukumar Ifelodun.   A cewarsa wadanda ake zargin sun kai hari ne a hedikwatar ‘yan sanda inda suka kai farmaki cikin kasuwar.   Ya bayyana cewa maharan sun yi ta harbe-harbe kai-tsaye, inda suka kashe mutane 5 ciki har da dan sanda...
    Gwamnatin Tarayya ta yi hasashen ruwan sama mai karfi da zai iya haifar da ambaliya a jihohi 15 na Arewacin Najeriya da wasu wurare 68, a cikin kwanaki biyar masu zuwa. Wannan gargadi ya fito ne daga Cibiyar Lura da Gargadin Ambaliya ta Kasa, karkashin Ma’aikatar Muhalli ta Tarayya, inda aka bukaci hukumomi da al’umma su dauki matakan gaggawa don kare rayuka da dukiyoyi. Cibiyar ta bayyana jerin jihohi da wuraren da ambaliyar za ta iya shafa sun hada da: Adamawa: Jimeta, Mubi, Mayo-Belwa, Wuro-Bokki, Yola, Farkumo Bauchi: Jama’a Nasarawa: Keffi Kaduna: Jaji, Kafanchan, Zaria, Birnin-Gwari Katsina: Katsina, Bindawa, Kaita Kebbi: Kamba, Kangiwa, Kalgo, Ribah, Sakaba, Saminaka, Gwandu, Jega, Bunza, Birnin Kebbi, Bagudo, Argungu Kano: Bebeji, Gwarzo, Karaye, Sumaila, Tundun-wada...
    Sanarwar ta zayyana wasu fitattun garuruwa da al’ummomin da ka iya fuskantar mummunar ambaliyar ruwa da suka hada da Jimeta, Mubi, Keffi, Kafanchan, Birnin Kebbi, Minna, Gusau da Sakkwato.   A cikin jihohin da aka lissafa, Kebbi ce ta fi kowacce yawan garuruwa da aka fi tsammanin ambaliyar za ta yi kamari, ga su guda 10 kamar yadda ta bayyana: Kamba, Kangiwa, Kalgo, Ribah, Sakaba, Saminaka, Gwandu, Jega, da Birnin Kebbi.   Bokani ya bukaci mazauna yankin da hukumomin jihar da su dauki matakan kare rayuka da dukiyoyi cikin gaggawa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Damina lokaci ne da ɗan Adam yake matuƙar bukata. Da za ta yi jinkiri, sai a ga hankalin kowa ya tashi. A lokaci guda kuma, yadda damina kan hana wasu harkoki gudana kan jefa wasu mutane cikin wani irin yanayi. NAJERIYA A YAU: Shekara nawa shugabanni ke bukata don cika alkawuran zabe? DAGA LARABA: Me Ke Sa Matasa Zama Karnukan Farautar ‘Yan Siyasa A Kafafen Sadarwa Na Zamani? Shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne a kan yadda damina kan shafi rayuwar ƙananan ’yan kasuwa da masu ƙananan sana’oi. Domin sauke shirin, latsa nan
    Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya tabbatar da cewa “babu wani abu da aka yanke ya  yanzu game da tattaunawa da Amurka,” ya kara da cewa “babu wani tabbci kan zabar wata kasa da za ta karbi bakuncin tattaunawar.” A jawabin da ya yi a gefen taron majalisar ministocin a jiya Lahadi, Araqchi ya yi jawabi kan  ziyarar mataimakin babban daraktan hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA wanda ke shirin isa birnin Tehran a yau litinin. Araqchi ya bayyana cewa “babu wani shiri na ziyartar wata tashar nukiliya kafin a cimma wata matsaya kan hakan,” ya kara da cewa wannan tsarin “zai dogara ne kan dokar majalisar dokokin kasar Iran kawa,” kuma “ba za a fara wasu...
    Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya gudanar da zaman gaggawa a hedikwatar MDD da ke birnin New York a jiya Lahadi, bayan matakin da majalisar ministocin Isra’ila ta dauka na fadada ayyukan soji da kuma mamaye yankin zirin Gaza. Mataimakiyar  Sakatare-Janar mai kula da harkokin Turai, Tsakiyar Asiya da Amurka, Miroslav Jenča, ta jaddada a yayin zaman  cewa, “ba za a iya dakatar da dimbin wahalhalun jin kai da ake fama da su a Gaza ba, sai ta hanyar tsagaita bude wuta nan take kuma mai dorewa,” tana mai kira da a gaggauta sakin dukkan fursunoni ba tare da wani sharadi ba. Jenča ta yi kira ga Isra’ila da ta bi abin da ya rataya a wuyanta a karkashin...
    Jami’an tsaron kasar Iraki sun sanar da gano wata kungiyar ‘yan ta’adda da ta yi niyyar kai wa masu ziyarar Arbaeen hare-hare, wanda aka shirya gudanarwa a kwanaki masu zuwa. Ma’aikatar tsaron ta bayyana cewa, “tsarin da ‘yan ta’addan ke da shi sun hada da dasa ababen fashewa a kan hanyoyin da masu tattaki ke bi a yankin kudancin kasar da kuma saka guba a cikin kayan abinci da ake ba wa masu tattaki. Har ila yau, bincike ya nuna cewa kungiyar ta’addanci ta ISIS ta yi amfani da hanyoyi daban-daban wajen daukar wadannan mambobi nata da aka wanke wa kwakwalwa domin aiwatar da wadannan ayyuka. Ma’aikatar ta bayyana cewa, kungiyar na yin hakan ne ta hanyar yin amfani littafai...
    “Na taɓa zama abar kwatance, musamman a ɓangaren da shafi kuɗi, suna, girmamawa, amma kuskuren da na yi ya zama dalilin da yasa masana’antar ta juya min baya, sakamakon babu abin da na iya ko na sani face; harkar ta fim. Halin da ake ciki yanzu, babu wani tallafi, babu aikin yi, akwai lokacin da ina da ɗimbin masoya da suke son aurena da kuma nuna min soyayya, amma sai na kasa zaɓen wanda zan ci gaba da rayuwata da shi a wancan lokaci. Babban dalilin da ya jawo min koma-baya a harkar fim shi ne, hatsarin da na samu na mota, wanda Allah ya jarrabce ni da shi, na yi hatsarin mota da har sai da na samu karaya...
    Rahotanni daga sojojin da ke mulki a Mali, sun ce sun kama wasu sojoji kusan 30 da ake zargin suna shirin kifar da gwamnati ƙasar. Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa cikin waɗanda aka kama akwai Janar Abass Dembele, tsohon gwamnan yankin Mopti da ke tsakiyar ƙasar. Ma’aikatan shari’a 97 sun samu ƙarin girma a Borno EFCC ta kama ’yan damfara a ɗakin karatun Obasanjo  Har yanzu gwamnatin ƙasar ba ta fitar da sanarwa a hukumance ba game da lamarin. Ita ma gwamnatin da ke mulki yanzu ta karɓi mulki ne ta hanyar juyin mulki a shekarar 2021. Wannan zargi ya ƙara nuna cewa akwai rashin kwanciyar hankali a tsakanin gwamnatin sojin. Yanzu haka dai gwamnatin na fuskantar matsalar hare-haren masu...
    Sunana Comr, Nr. Ibrahim Lawan Stk Lokaci wani abu ne da yake nuna yanayi a kodayaushe, sannan yake bada damar aiwatar da abubuwa masu kyau da mararsa kyau a rayuwa. Haka kuma yanayi ne da yake bada damar rayuwa a cikin daƙiƙu, mintuna, da kuma, awowi, ranaku, makonni dakuma shekaru. Ana amfani da lokaci ne ta hanyar da ya kamata kamar gudanar da rayuwa maikyau da zamantakewar yau da gobe, da kuma hanyoyin da ya dace na gudanar da rayuwa. Lokaci na yana da matuƙar muhimmanci wajen gudanar da rayuwa. Amfanin lokaci na nufin amfani da lokaci ko kuma yadda ake amfani da shi wajen cimma burin mutum ko gudanar da ayyuka. Ga wasu daga cikin amfanin lokaci; inganta...
    Sojojin HKI sun shiga yankuna da dama a lardin Qunaitara na kasar Siriya a Jiya Asabar. Inda ta kafa shingaye a kan tituna a wasu garuruwa a lardin suka yi ta binciken ababen hawa, kafin su janye daga baya. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa, HKI tana shirin mamayar wadan nan yankunan na kasar Siriya shi ya sa bata son ganin an sami zaman lafiya a kasar ta Syriya gaba daya, har zuwa lokacinda zata mamaye yankin. Gwamnatin kasar Siriya mai ci ta tabbatar da cewa samuwar sojojin HKI a duk lokacinda suka ga dama a wadannan yankuna alamace ta rashin zaman lafiya a kasar. Kowa ya san cewa HKI ba zata taba barin kasar Siriya...
    Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ta bada sanarwan cewa alkalan wasan kwallon kafa ta mata kuma ta Salon guda biyu ne ta zama a kasar Iran don alkalanci a gasar FIFA ta kwallon Saloon ta masa na wannan shekara ta 2025, wanda za’a gudanar a kasar Philipine. Zaben Zari Fathi da kuma Gelareh Nazemi a matsayin alkalai a wannan gasar mai muhimmanci ya nuna irin matsayinda Iran take da shi a hukumar ta FIFA. A ranar 21 ga watan Nuwamba mai zuwa ne, zuwa 2 ga watan Decemban shekara ta 2025 ne za’a gudanar da gasar kwallon salon ta mata da kuma duniya a biranen Manila da Negros,na kasar Philipine. Inda kungiyoyin kwallon kafa ta mata 16 daga kasashen...
    Amma saboda yanzu yanayin rayuwa ya canza, ba ni da mota ko ɗaya; ya sa idan na yi waccan maganar sai wasu su riƙa nuna rashin amincewarsu, wannan kuma rashin sani ne kawai, domin kuwa da a ce sun san wane ne Mai Dawayya a shekarun da suka gabata, da ba su yi wannan magana ba, koda kuwa da wasa, in ji shi. Mai Dawayya ya buƙaci matasan mawaƙa masu tasowa a masana’antar ta Kannywood, da su tabbatar sun yi amfani da wannan lokaci da suke kan ganiyarsu, duniya kuma take yi da su; wajen gina gobensu, ba wai su dinga hawan motoci da sauran sharholiyar rayuwa ba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu...
    Ƴan bindiga sun kashe mutane biyar, ciki har da wani Ɗansanda, a sabon harin da suka kai garin Babanla a ƙaramar hukumar Ifelodun ta jihar Kwara. Lamarin ya faru ne a ranar Juma’a, kwanaki ƙalilan bayan kisan wasu matafiya uku da garkuwa da wasu biyu a yankin. Mai magana da yawun rundunar ƴansandan jihar, Toun Ejire-Adeyemi, ta ce maharan sun kai ɗaruruwa akan babura ne suka farmaki garin, kuma suka kai hari ofishin Ƴansanda na yankin, sannan suka yi ɓarna a kasuwar garin. An kashe Kofural Adejumo Wasiu tare da wasu fararen hula huɗu. NDLEA Ta Kama Fasto Bisa Laifin Safarar Miyagun Kwayoyi A Legas  Jirgin Shugaban Ƙasa Ya Laƙume Naira Biliyan 26.38 Cikin Wata 18 Ƙarƙashin Tinubu Ta bayyana...
    Hukumar Shari’a ta Jihar Borno ta ƙara wa ma’aikatanta 97 girma bayan wani taro na kwanaki huɗu da ta gudanar a Maiduguri. Muƙaddashin sakataren hukumar, Saleh Khala Jidda ne, ya bayyana hakan a wata sanarwa cewa ma’aikatan sun samu ƙarin girma ne saboda ƙwazonsu. EFCC ta kama ’yan damfara a ɗakin karatun Obasanjo  ’Yan bindiga sun kashe gomman mutane a ƙauyukan Sakkwato Waɗanda abin ya shafa sun hada da Majistare 10 daga matakin Majistare mataki na ɗaya zuwa Babban Majistare mataki na biyu. Sai Majistare daga matakin farko zuwa Babban Majistare na biyu. Sauran sun haɗa manyan Magatakarda daga mataki na ɗaya zuwa na biyu. Sai dai a gefe guda, hukumar ta ɗauki mataki kan wani alƙalin Babban Kotun Majistare...
    Wakilan LEADERSHIP sun lura cewa yanzu ana amfani da wasu daga cikin waɗannan ofisoshin hulɗa da jama’a na Jihar Legas a matsayin matsugunin ‘yan kasuwa na da masu safarar barasa. Binciken da aka yi ya kuma nuna cewa jami’an tsaro da masu kula da waɗannan gidaje suna hayar wasu sassan gine-ginen da daddare don yin haramtattun ayyuka, inda suka mayar da su gidajen karuwai. Lamarin dai ya haifar da fargaba a tsakanin mazauna yankin da kuma ‘yan kasuwa a yankunan da ke maƙwabtaka da su, inda suka ce ayyukan na da matuƙar haɗari ga tsaro, suna jawo masu aikata laifuka, da kuma zubar da mutuncin wakilan Jihar a Legas. Lamarin dai ya haifar da fargaba a tsakanin mazauna yankin da...
    Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi Allah wadai da matakin da haramtacciyar kasar Isra’ila ta dauka na mamaye zirin Gaza Ma’aikatar harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi Allah wadai da matakin baya-bayan nan da majalisar ministocin gwamnatin ‘yan sahayoniyya ta dauka na mamaye yankin zirin Gaza da korar al’ummarta, tare da la’akari da hakan a matsayin wani mataki na kammala shirin kisan gillar ga Falasdinawa da suke yi da kawar da asalin wanzuwar Falastinu. A cikin bayanin da ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta fitar dangane da abubuwan da suke faruwa a zirin Gaza da yankunan Falastinu da aka mamaye, ma’aikatar harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta bayyana matukar damuwarta da takaicin yadda ake ci gaba da...
    Jami’in ma’aikatar harkokin wajen Iran ya jaddada cewa; Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta cimma babban matsayi a yakin kwanaki 12 Ali Baqiri Kani mamba a majalisar tsare-tsaren a ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta cimma babban matsayi a yakin kwanaki 12 da aka kwashe ana gwabzawa da yahudawan sahayoniyya. Baqiri ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi ta gidan talabijin a yammacin jiya Asabar cewa: Tabbas Iran ta cimma matsayi sosai a yakin kwanaki 12 da aka kwashe ana gwabzawa, yana mai jaddada muhimmancin diflomasiyya wajen tunkarar hare-haren da ake kai wa kasar, yana mai jaddada cewa: “Dole ne Iran ta mayar da martanin wuce gona da iri...
    Ya bayyana cewa, gwamnatin da ta gabata ce ta rufe cibiyoyin da aka kafa a gwamnatin Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, amma gwamnatinsa ta yanke shawarar farfado da su domin magance matsalar rashin aikin yi. “Don haka ne a yau, kowane Dalibi wanda ya kammala karatun, ba kawai takardar shaida za a bashi ba har ma da kayan aikin sana’ar da ya koya” in ji Yusuf. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Jami’an Hukumar Yaƙi da Yi Wa Tattalin Arziƙi Zagon Ƙasa (EFCC), sun kai samame a Ɗakin Karatun Olusegun Obasanjo da ke Abeokuta, a Jihar Ogun, inda suka kama wasu matasa da ake zargin ’yan damfara ne. Samamen ya faru ne da safiyar ranar Lahadi a sashen otal na ɗakin karatun. ’Yan bindiga sun kashe gomman mutane a ƙauyukan Sakkwato An ɗaure tsohon Firaminista Succes Masra shekaru 20 a Chadi Gidan Obasanjo na musamman yana cikin harabar ɗakin karatun. Wani faifan bidiyo da ya karaɗe kafafen sada zumunta, ya nuna yadda wasu matasa ke gudu domin ka da EFCC ta kama su. Rahotanni sun ce jami’an EFCC sun ƙwace sama da motoci 20 tare da wasu kayayyaki masu daraja. Wani jami’in...
    An sake shiga tashin hankali a Jihar Sakkwato bayan wani sabon mummunan hari da ’yan bindiga suka kai a wasu kauyuka, lamarin da ke ƙara tsananta matsalar tsaro a faɗin jihar. Rahotanni sun nuna cewa duk shekara musamman a lokacin damina, ’yan bindiga sukan ƙara ƙaimi wajen kai hare-haren da ke tarwatsa jama’a a garuruwansu da hana manoma zuwa gona ko kuma ƙaƙaba musu harajin zuwa gonakin. An ɗaure tsohon Firaminista Succes Masra shekaru 20 a Chadi Dan wasan Barcelona Inigo Martinez ya koma Al-Nassr Aminiya ta ruwaito cewa, a bana ma, maharan sun ci gaba da addabar mazauna ƙananan hukumomi 20 daga cikin 23 na Jihar Sakkwato. Majiyoyi sun tabbatar cewa a harin baya-bayan nan, ’yan ta’addan sun hallaka...
    Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) ta kama wanda ya kafa kuma yake kula da cocin ‘The Turn of Mercy’, Adefolusho Olasele, wanda aka fi sani da Abbas Ajakaiye, bisa zarginsa da hannu wajen safarar miyagun kwayoyi da dama daga Ghana zuwa Nijeriya. Fasto Olasele, wanda ya shafe watanni ba a san inda yake ba, an kama shi ne a ranar Lahadi, 3 ga watan Agusta, 2025, a cocinsa da ke Okun Ajah, yankin Lekki, a Legas. NDLEA Ta Cafke Masu Baburan Da Ke Kai Saƙon Muggan Ƙwayoyi A Abuja Dole Ne Afrika Ta Mayar Da Hankali Wajen Amfana Da Damarmakin Da Ke Tekunanta – Ɗantsoho Wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar, Femi...
    Wata kotu a N’Djamena, babban birnin Chadi, ta yanke wa tsohon firaminista kuma madugun adawa, Succes Masra, hukuncin ɗaurin shekaru 20 a gidan yari. Kamfanin Dillancin Labaran Faransa AFP ya ruwaito kotun ta samu tsohon firaministan da laifin kalaman ƙiyayya, nuna wariyar ƙabilanci da kuma tayar da tarzomar da ta rikiɗe zuwa kisan kiyashi. Dan wasan Barcelona Inigo Martinez ya koma Al-Nassr MDD za ta yi zaman gaggawa kan yunƙurin ƙwace Gaza Kotun a ranar Asabar ta ce ta sami Mista Masra da laifi kan rawar da ya taka wajen tayar da rikicin ƙabilanci wanda ya yi sanadin mutuwar mutane 42 a ranar 14 ga Mayu — waɗanda galibi mata da yara ne a yankin Mandakao da ke kudu maso...
    A ranar Asabar kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta sanar da cewa dan wasan bayanta, Inigo Martinez zai bar kungiyar, kuma jaridun Sifaniya sun ruwaito cewa zai koma kungiyar Al-Nassr da ke gasar Saudi Pro League. Tafiyar Martinez za ta taimaka wajen rage nauyin biyan albashin ’yan wasa a Barcelona, kungiyar da a bayan nan ke fama matsalar rashin kudi. MDD za ta yi zaman gaggawa kan yunƙurin ƙwace Gaza Dubban mutane sun yi zanga-zangar goyon bayan Falasɗinu a Isra’ila da Pakistan Martinez mai shekara 34 ya buga wasa a wasanni 71 a dukkan gasanni tun bayan komawarsa kungiyar daga Athletic Bilbao a shekarar 2023, inda ya taimaka wa Barcelona ta lashe kofin La Liga a kakar bara. Kafin haka,...
    Gwamnan ya kuma umurci jami’an tsaro da su rufe gidan rediyon tare da nemo bayanan mai gidan rediyon, inda ya zarge ta da haddasa tashin hankali.   Sai dai a kara mai lamba FHC/L/CS/1587/2025 da aka shigar a ranar Juma’ar da ta gabata a babban kotun tarayya da ke Legas da SERAP da kuma NGE suna neman sani “ko a sashe na 22 na kundin tsarin mulkin Nijeriya na 1999 (wanda aka yi wa kwaskwarima) da sashe na 2(1) (t) na dokar NBC, NBC na da hakkin kare ‘yancin Badeggi FM da gwamnan Neja ya rufe.” Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga...