Ma’aikatar kula da harkokin cinikayya ta kasar Sin, ta ce sabuwar gwamnatin Amurka ta dauki jerin matakan kakaba haraji na ba gaira ba dalili, lamarin da ya kawo tsaiko ga dangantakar cinikayya da tattalin arziki tsakanin kasashen biyu da ma tsarin cinikayya da tattalin arziki na duniya, tare da kawo kalubale mai tsanani ga farfadowar tattalin arzikin duniya.

Kuma domin kare hakkoki da muradunta, Sin ta dauki matakan mayar da martani.

A cewar kakakin ma’aikatar, a baya bayan nan, bangaren Amurka ya bayyana shirinsa na tattaunawa kan batun harajin da sauran batutuwa masu nasaba da shi ta hanyoyi da dama. Kuma bayan nazartar sakonnin Amurka, kasar Sin ta yanke shawarar tattaunawa da ita, bisa la’akari da burin al’ummun duniya da muradun kasa, da kuma kiraye kiraye daga masana’antun Amurka da masu sayayya na kasar. Kuma a matsayinsa na jagoran tawagar Sin a tattaunawar harkokin tattalin arziki da cinikayya tsakaninta da Amurka, mataimakin firaministan kasar He Lifeng zai gana da sakataren Baitul malin Amurka Scott Bessent.

Tattalin Arzikin Sin Tamkar Teku Ne Ba Karamin Tabki Ba Korar Ma’aikata: Likitocin Birnin Tarayya Sun Tsunduma Yajin Aikin Gargadi Na Kwanaki 3 

Kakakin ya ce matsayar kasar Sin bata sauya ba, idan aka tilasta mata shiga fada, to a shirye take, idan kuma tattaunawa ake son yi, kofarta a bude take.

Ya kuma yi gargadin cewa, duk wani yunkuri na fakewa da tattaunawar a matsayin wata dama ta matsin lamba ko barazana, toh, kasar Sin ba za ta cimma wata yarjejeniyar da za ta kai ga sadaukar da ka’idojinta, ko lalata tsarin adalci da tsare gaskiya a duniya ba. (Fa’iza Mustapha)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Xi Jinping Ya Mika Gaisuwar “Bikin Girbi Na Manoman Kasar Sin” Na Takwas

Yayin da “bikin girbi na manoman kasar Sin” na takwas ke karatowa, babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin wato JKS, shugaban kasar, kuma shugaban kwamitin kolin soja Xi Jinping, a madadin kwamitin kolin JKS, ya mika gaisuwar bikin, da fatan alheri ga manoma da ma’aikatan dake gudanar da ayyukan da suka shafi harkokin noma, da kauyuka da kuma manoma a fadin kasar.

Xi Jinping ya yi nuni da cewa, a bana, mun shawo kan illar bala’o’i kamar fari, da ambaliyar ruwa, da samun daidaiton noman hatsin rani, da karuwar noman shinkafa mai nuna da wuri, ana kuma sa ran samun karin girbin hatsi.

Xi Jinping, ya jaddada cewa, zamanantarwa irin ta kasar Sin ba za a iya raba ta da zamanantar da aikin gona da kauyuka. Don haka dole ne kwamitocin JKS, da gwamnatoci na sassan kasar su aiwatar da shawarwari da tsare-tsare na kwamitin kolin JKS, da tsayawa tsayin daka wajen raya aikin gona da kauyuka, da kyautata manufofi don karfafawa, da amfana, da wadatar da manoma, da karfafa goyon bayan kayayyakin aikin gona na kimiyya da fasaha, da mayar da hankali kan inganta cikakken karfin samar da amfanin gona, da aiwatar da matakai da dama don inganta ayyukan yi, da kara samun kudin shiga na manoma, da kuma sa kaimi ga farfadowar kauyuka a dukkan fannoni. (Safiyah Ma)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Araqchi; Tattaunawa Tsakanin Iran Da Norway Kan Kyakkyawar Alakar Da Ke Tsakaninsu
  • Firaministan Sin Ya Isa New York Don Halartar Babban Taron Mahawara Na MDD Karo Na 80
  • Kuri’ar Jin Ra’ayoyi Ta CGTN: Guguwar Amincewa Da Kasar Falasdinu Ta Nuna Yadda Amurka Da Isra’ila Suka Zama Saniyar Waren Da Ba A Taba Gani Ba
  •   Nato Na Yin Taron Tattaunawa Keta Hurumin Samaniyar Kasar Estonia Da Rasha Ta Yi
  • He Lifeng: Ya Kamata Sin Da Amurka Su Karfafa Dangantakar Tattalin Arziki Da Cinikayya Mai Dorewa Cikin Lumana
  • Tattalin arzikin Najeriya ya ƙara haɓaka — NBS
  • Xi Jinping Ya Mika Gaisuwar “Bikin Girbi Na Manoman Kasar Sin” Na Takwas
  • Li Qiang Ya Gana Da Tawagar Membobin Majalisar Wakilai Ta Amurka
  • Ya Kamata Sin Da Amurka Su Hau Turbar Hadin Gwiwa Da Samun Moriyar Juna A Sabon Lokaci
  • Shugaban Kasar Iran Ya Yi Kira Ga Samar Da Tattalin Arziki Da Shugabancin Kwararru