Tsohuwar mawaƙiyar Hausa Hip-hop za ta yi aure
Published: 20th, May 2025 GMT
Tshouwar Mawakiyar Hausa Hip-Hop, Zainab Ishaq Muhammad, wadda aka fi sani da ‘Queen Zeeshaq’ za ta shiga daga ciki a ranar Lahadi mai zuwa.
Duk da cewa ba a yayata batun auren ba, Aminiya ta tabbatar da ganin katin gayyata da ke nuna za a ɗaura auren nata da angonta, Hussain Muhammad Koya, a ranar 25 ga watan Mayu, 2025.
Rahotanni sun nuna cewar a ranar Laraba za a fara bidirin bikin har zuwa ranar Asabar.
An shirya gudanar da walima, ƙwallon ƙafa, saukar karatun Alƙur’ani da sauransu har zuwa ranar ɗaurin aure.
A shekarun baya, Queen Zeeshaq, ta yi suna wajen yin waƙoƙin Hausa Hip-Hop duk da cewar an ji ta shiru a baya-bayan nan.
A yanzu mawaƙiyar ta fi mayar da hankali wajen ayyukan jin-ƙan marayu da kuma aikin jarida.
Aminiya ta tuntuɓi makusantan mawaƙiyar don jin dalilin ɓoye bikin, amma sun ce wasu dalilai ne ya sa suka ɗauki wannan mataki.
A lokacin da Queen Zeehsaq ta ke tashe ta yi wakoki da dama tare da fitattun mawaƙa irin su Billy O da sauransu.
Daga cikin waƙoƙinta da suka yi shura akwai Mahaifiyata, Gari Ya Waye, Lokaci da sauransu.
Ga katin bikin a ƙasa:
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Matashiya Mawaƙiya Waƙoƙi
এছাড়াও পড়ুন:
Borno ta fara fitar da kayan robobi zuwa ƙasashen waje – Zulum
Gwamnan Jihar Borno, Umara Zulum ya sanar da fara fitar da kayayyakin robobi zuwa ƙasashen duniya wanda hakan ke nuna wani gagarumin ci gaba a wani ɓangare na ƙoƙarin farfaɗo da tattalin arzikin Jihar.
Gwamnan ya jaddada cewa, wannan matakin wani ɓangare ne na babbar ajanda na bunƙasa masana’antu da kuma kawar da dogaro da jihar kan yi na kason da gwamnatin tarayya ke bayarwa duk wata.
Ƙwallo ta kashe ɗan wasan Cricket Za a rataye wanda ya kashe ɗan uwansa a EkitiZulum ya sanar da hakan ne a ranar Alhamis yayin rangadin duba masana’antar robobi ta Borno da ke cikin yankin masana’antu na Maiduguri.
“Ina farin cikin lura cewa mutanen Jihar Borno ba za su sake sayen kayan robobi daga wasu wurare ba, kun ga an sayar da kayayyakin ga ƙasashen maƙwabta da sauran jihohi a cikin Najeriya.”
“Za mu zuba jari sosai a masana’antunmu, don haka nan gaba kaɗan, gwamnatin Jihar Borno ba za ta sake dogara da asusun tarayya ba don ayyukanta na yau da kullum,” in ji Zulum.
Gwamnan ya bayyana cewa masana’antar ta fara fitar da kayayyakinta ga ƙasashen waje, tare da jigilar kayayyakin filastik da aka gama zuwa ƙasashe maƙwabta kamar Chadi da Jamhuriyar Kamaru.
Zulum ya lura cewa an fara gina cibiyar ne a lokacin gwamnatin tsohon Gwamna Kashim Shettima, amma an farfaɗo da ita a matsayin wani ɓangare na shirin murmurewa da ci gaban gwamnatinsa.