MDD: Yunwa Ta Kara Tsanani A Duniya Daga Shekarar 2024
Published: 18th, May 2025 GMT
A wani rahoton da MDD ta fitar a cikin kwanakin nan, ya bayyana cewa, tun daga 2024 ne yunwar da ake fuskanta a duniya ta kara tsanani domin ta shafi mutanen da sun kai miliyan 295.
Rahoton ya kara da cewa; wannan adadin na mutanen dake fama da yunwa mai tsanani suna warwatse a cikin kasashe 53 na duniya.
A Juma’ar da ta gabata aka fitar da wannan rahoton. Haka nan kuma an bayyana cewa idan aka kwatanta da yunwar da aka yi fama da ita a shekarar 2023, to da aka shiga 2024 an sami karuwar masu fama da matsananciyar yunwar da adadinsu ya karu da miliyan 13.7. Shekaru shida kenan a jere da ake samun karuwar yawan mutanen da suke fama da yunwa.
An kaddamar da wannan rahoton ne a karkashin kawancen kasa da kasa na fada da karancin abinci a duniya wanda ake kira da ( GNAFC) wanda ya kunshi hukumar Abinci ta duniya ( FAO), da kuma ( WFP) da sauran kungiyoyin da ba na gwamnati ba.
Babban magatakardar MDD Antonio Guterres ya bayyana alkaluman da aka fitar na adadin masu fama da matsananciyar yuwa da cewa; Wani adadi ne wanda bai girgiza duniya ba, domin tana tafiya ne a karkace.”
Wani sashe na rahoton ya yi ishara da cewa da akwai dalilai masu yawa da su ka haddasa karancin abinci; sun kuwa hada da talauci, koma bayan tattalin arziki, sauyin yanayi mai tsanani, sai dai kuma duk da haka rikice-rikice da fadace-fadace a cikin wasu yankuna, su ne ummul-haba’isin karancin abincin.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
An yi zanga-zanga zagayowar ranar ‘’Nakba’’ a sassan duniya da dama
An gudanar da zanga-zangar nuna goyon baya ga al’ummar Falasdinu a sassa daban-daban na duniya, a yayin zagayowar cika shekaru 77 da ranar ‘’Nakba’’ cewa da masifa.
A Faransa da Ingila duk an gudanar da wannan zanga zanga a wasu sassan kasar.
A cikin jerin gwanon, an daga allunan da ke dauke da sakonni irin su “Falasdinu za ta rayu!” » ko “Dakatar da kisan kiyashi a Gaza”.
“Nakba ba wani lamari ne da ya faru a baya ba, yana ci gaba da faruwa ta hanyar korar jama’a, da amfani da bama-bamai,” kan al’ummar Gaza.
Masu zanga-zangar sun yi Allah wadai da tabarbarewar al’amuran jin kai a zirin Gaza tun bayan barkewar yakin kisan kiyashi da Isra’ila ta kaddamar a watan Oktoban 2023 bayan harin ba-zata da Hamas ta kai.
Masu zanga zangar dake dauke da tutocin Falasdinu a Paris, sun zargi hukumomin Faransa, da yin hadin gwiwa da Isra’ila ta hanyar yin gum da bakinsu.”
A Zirin Gaza tun daga ranar 18 ga watan Maris din 2025, lokacin da gwamnatin Sahayoniya ta ci gaba da kai hare-hare, tare da karya yarjejeniyar tsagaita bude wuta da Hamas da ta fara aiki a ranar 19 ga watan Janairu, an kashe Falasdinawa sama da 3,000, lamarin da ya kawo adadin wadanda suka mutu a Gaza tun farkon yakin zuwa akalla mutane 53,272, galibi mata da kananan yara, sannan Fiye da mutane 120,673 kuma sun jikkata.