Guguwar raba Masarautar Katsina ta kunno kai
Published: 18th, May 2025 GMT
A farkon wannan sati ne wata takardar neman raba Masarautar Katsina ta bayyana, wadda take neman a ƙirƙiro ƙarin masarautu uku da suka haɗa da ƙarin sarki mai daraja ta ɗaya da mai daraja ta biyu da kuma mai daraja ta uku.
Takardar wadda aka gani da tambarin da ke nuna alamar an miƙa ta ga Majalisar Dokokin Jihar Katsina ta tayar da ƙura, inda ake ta musayar yawu kan abin da ta ƙunsa da kuma abin da zai iya biyo baya.
Wakilinmu ya gano cewa takardar, wadda kafar yaɗa labarai ta Katsina Times ta fara wallafa wa a kafofin sada zumunta, ta fito ne daga wata ƙungiya mai fadi-tashin ganin an ɗaga darajar wasu garuruwa da hakimansu.
Rashin ganin sunayen waɗanda suka sanya wa takardar hannu shi ma ya sa an yi ta tambayoyi game ainihin manufar waɗanda suka rubuta ta da kuma hakikanin manufarsu.
Dalilin neman raba masarautar KatsinaMasu neman a raba Masarautar Katsina sun kafa hujja ad wasu dalilai na tarihi a matsayin misalan da suke ganin sun wadatar a naɗa sabbin sarakuna masu daraja ta ɗaya da masu daraja ta biyu da masu daraja ta uku, mai maimakon Sarkin Katsina da a halin yanzu shi ne kaɗai sarkin yanak.
Sun kawo misali da yankin Kurfi wanda yanzu karamar hukuma ce amma ba ta da sarki mai daraja ta biyu ko ta uku.
A cewarsu a da can Kurfi kasa ko yanki ne mai zaman kansa da ke karbar umarni daga Shehu Danfodiya.
Kazalika, sun ce, a lokacin turawan mulkin mallaka, Gwamna Lugga ya nada Kaura Amah Sarauta a matsayin mayakin da ya tsare sashen Dankama daga maharan da ke fitowa nan sashen, amma Kaura Amah ya ki amsar tayi ya ce, a bar shi a matsayin shi na mayaki.
Saboda haka suke ganin a sake bayar da wannan sarauta ko da a matsayin mai daraja ta uku ce.
Masu neman sabbin masarautun sun ce, hatta yankin Maska yana buƙatar a yi masa sarki mai daraja ta ɗaya, duba da irin rawar da Sarkin Maska ya taka, wanda ya yi zamani da Sarkin Katsina Muhammadu Korau, wanda shi ne sarki Bahaushe Musulmi na farko da ya yi sarautar ta Katsina.
Ta ci gaba da cewa hatta da Malunfashi da Kafur sun cancanci a ba su sarki mai daraja daya, idan aka yi la’akari da matsayi da kuma tarihin yankunan musamman abubuwan da Malan Dudi Zuri’ar Danejawa ya taka wajen kafa Malumfashi da Kafur.
Ƙungiyar ta kuma waiwayi ita kanta Masarautar Katsina a matsayinta na masarauta tilo da ake da ita mai sarki mai daraja ta ɗaya.
Ta tuno tarihin mutanen nan uku da suka je karbo tuta a hannun Shehu Danfodiyo — Ummarun Dallaje da Malam Na Alhaji da da Ummarun Duniyawa — wadanda a cewar kungiyar, kowanne daga cikinsu yana mulkin yankinsa, kuma suna karbar umarni ne daga wajen shi Shehun Danfodiyo.
Wato, suna mulkin haɗaka wanda daga baya turawan mulkin mallaka suka tilasta masu zama karkashin sarki guda, kamar yadda masu neman wannan bukata suka ce tarihi ya nuna.
Akan haka suke ganin yana da kyau a fitar da sarki mai daraja ta ɗaya a cikinsu yayin da sauran biyun za su zamo sarakuna masu daraja ta biyu, wato, yankin ’Yandakawa da kuma Ummarun Duniyawa wanda ya fara zama a garin Zandam.
Wata majiya ta shaida wa wakilinmu cewa takardar ta fito ne daga wata kungiya da ke da hedikwata a Funtuwa, karkashin jagorancin wani mai suna Salisu Idris Funtuwa.
Wakilinmu ya yi kokarin jin ta bakin kungiyar da ake zargi amma abin ya ci tura.
‘Mun dade muna neman a ba mu masarauta’Game da yadda jama’ar jihar ke kallon wannan lamari, Malam Ibrahim wani mazaunin garin Funtuwa da wakilinmu ya tuntuba ya ce, “ai mu tuni muka so a yi mana sarki a wannan yanki duba da irin tarihin yankin.
“Mun so a ce an yi mana Sarkin Kudu mai daraja ta daya ko kuma ita wannan hakimci da ake kira da Sarkin Maska ta koma sarki ne mai wukar yanka, ba wannan suna ba hakimi ba.”
Abin da ya faru ya Kano ya ishe mu darasiAmma Alhaji Usman, ya bayyana cewa “Wannan neman raba kan al’umma ne kawai ba hadin kai ba.
“Su masu wannan tunani ba su duba halin da makwabciyarmu Jihar Kano take ciki a yanzu kan maganar rikicin masarautun?
“A matsayin jiha baki daya fa ke nan da aka samu wannan matsala, to ina ga wani sashe daga cikin jihar?”
Alhaji Usman ya kara da cewa, “idan har suna maganar tarihi ne, sai mu ce a mayar wa da Hausawa sarautarsu domin Hausawa ne suka fara yin sarauta a Katsinar kafin Fulani su shigo.
“Kuma tun wancan lokacin akwai wurare da yawa inda aka haɗe su suka zama daya da kuma inda aka yi musaya.
“Misali, ’Yandoto da Kankara, ai da can ’Yandoto a karkashin Katsina take ita kuma Kankara tana karkashin Zamfara. Lokacin Sarki Dikko aka yi wannan musayar. Su ma sai a ce kowa ya kama gabansa.
“Idan kuma muka koma can Kudancin Katsinar, ita kanta Funtuwar yaya aka same ta? Garin Sabuwa wa ya samar da shi? Sannan mu dawo shiyyar Daura, sai a ce, a mayar da sarautar a garin Zango tunda can ne tushe kuma daga can ake nado sarki,” in ji Alhaji Usman.
Ana zargin gwamnatiShi kuma wani da ya nemi a sakaya sunansa ya ce, “gaskiya ina zargin akwai wata balulluba daga wasu mukarraban gwamnati ko ita kanta gwamnatin.
“Dalili, wannan batun bai fito ba sai bayan da shugaban kasa ya zo kuma aka samu akasin da aka samu na zuwan sarkin wajen daurin auren ’yar gwamna.
“Kowa ya ga yadda wani ya rubuta takarda yana neman a hukunta sarki saboda karya kofa da dogarawansa suka yi don ya shiga masallacin da ake taron bayan da jami’an tsaron shugaban kasa suka yi yunkurin hana sarki shiga bisa hujjar shugaban kasa ya riga ya shigo masallacin an rufe kofa.
“Sannan akwai batun karin hakimai da gwamnatin jihar za ta yi a masarautun biyu na Katsina da Daura, amma a masarautar ta Katsina suka fi yawa.
“Wadannan duk wasu alamu ne da nake ganin cewa, gwamnati na da sha’awar ganin an farfasa masarautar.
“Wata hujja da muka gani ta cewar, wai sarki tun bayan hawansa bai yi rangadin da sarakunan baya suka rika yi ba, sai ya manta kullum cigaba ake samu.
“Kuma ana sara ana duban bakin gatari. Sarkin nan mutun ne mai tausayin talakawa baya son aza masu wani nauyi.
“Amma duk inda aka yi wani abu muddin aka gaya masa, yana zuwa shi da kansako ya tura wakili.”
Muna bincike kan takardar —MajalisaDuk da cewa gwamnatin jihar ba ta ce koomai game da wannan batu ba, amma dangane da batun miƙa wannan takadar majalisar dokokin jahar wadda a aka ga tambarinta a kai, mai magana yawun Kakakin majalisar dokokin jihar ta Katsina, Honarabil Nasiru, Aminu Magaji, ya ce, har zuwa lokacin da wakilinmu ya tuntube shi, babu wata takarda mai kama da irin wannan, ba ma ita ba da aka kawo majalisar.
Ya bayyana cewa, majalisar ta kaddamar da binciken yadda aka buga wa takardar da ke yawo a gari tambari da sunanta.
“Yanzu in aka tuna, ana satar sanya hannun mutun a takarda, yin amfani da tambarin karya da sauran irinnsu.
“Sannan a wannan takarda, babu sunan wanda ko wadanda suka rubuta, ta balle sunaye da sa hannu.
“Yadda ka gan ta a soshiyal midiya haka mu ma muka gani,” in ji Aminu Magaji, mai magana da yawon kakakin majalisar dokokin jihar Katsina.
Duk wani kokari na ji daga Masarautar Katsina ya ci tura, kuma har zuwa lokacni da muka kamamla hada wannan labari babu wani abu da ya fito daga gareta a hukumance.
Sai dai wasu na kusa da ita sun ce babu mamakin ji ko ganin irin wannan batu musamman ga masarauta.
“Idan har za a dubi tarihi da kuma yanayi, ai an san Masarautar Katsina haka ya kamace ta ta tsaya. Duk wuraren da ake magana wa ya haifar ko ya raya su?
“Kada mu ɗauka da nisa, abin da Marigayi Sarki Muhammadu Dikko ya yi a wannan masarauta duk arewa babu sarkin da ya yi. Mu kawai dai muna kallon wadanda suke neman kawo wannan matsalar walau sun yi don neman suna ko wani abu can na biyan bukata, musamman a siyasance”, inji wani da ya nemi a sakaya sunansa a yayin da wakilinmu ya tuntube shi a wayar salula
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Masarautar Katsina sarki mai daraja ta ɗaya raba Masarautar Katsina daraja ta biyu masu daraja ta wakilinmu ya wa takardar
এছাড়াও পড়ুন:
Iran ta ce babu wata rubutaciyar shawara da ta samu daga Amurka
Jamhuriyar Musulinci ta Iran, ta bayyana cewa babu wata rubutaciyar shawara data samu daga Amurka.
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya musanta ikirarin samun rubutaccen sako daga Amurka kan yarjejeniyar nukiliya.
“Iran ba ta sami wata rubutacciyar shawara daga Amurka ba, kai tsaye ko a kaikaice,” in ji Araghchi a cikin wani sakon da ya wallafa a shafinsa na X ranar Juma’a.
Wannan matsayi na zuwa ne bayan da shugaban Amurka Donald Trump ya yi ikirarin cewa Iran ta samu wata shawara daga kasarsa.
Ya kara da cewa sakonnin da muke samu, kamar wanda duniya ke samu, suna cike da rudadi da kace-nace.
Amma matsayin Iran, na daram kuma babu ja da baya, ‘’ ku amince da hakkinmu ku kum akawo karshen takunkumai, idan hakan ya samu to za’a iya cimma matsaya.
Ministan hakokin wajen kasar ta Iran, ya kuma kara da cewa babu wani abu da zai sa Iran ta dakatar da hakkinta na inganta sanadarin uranium na zaman lafiya ba wanda yake kunshe a cikin ‘yancin da aka baiwa dukkan kasashen da suka sanya hannun kan yarjejeniyar hana yaduwar makamman nukiliya.
A koyaushe muna maraba da tattaunawa bisa mutunta juna, sannan muna watsi da duk wani yunkuri na tilastawa ko matsin lamba. »