Tsohon fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ya ce: Fira ministan Netanyahu ya yi sakaci da rayuwar yahudawa a cikin aikinsa don haka hambarar da gwamnatinsa ita ce mafita

Tsohon Fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila Ehud Barak ya yi kira da a hambarar da Benjamin Netanyahu da gwamnatinsa, yana mai zarginsa da yin sakaci wajen kubutar da fursunonin yahudawa da suke hannu ‘yan gwagwarmaya a Zirin Gaza.

Barak ya ce: Netanyahu yana sakaci da rayuwar fursunonin yahudawa da ake tsare da su a Gaza domin faranta wa masu tsattsauran ra’ayi a gwamnatinsa rai.” Ya bayyana shi a matsayin mai sakaci wajen gudanar da ayyukansa, da kuma ci gaba da kisan kiyashi a Zirin Gaza domin karecmanufofin siyasa saboda neman ci gaba da mulki.

A wata hira da yayi da tashar talabijin mai zaman kanta ta Isra’ila ta 12, Barak ya bayyana cewa: Netanyahu “yana sakaci da rayukan mutanen da ake tsare da su a Gaza domin farantawa masu tsatsauran ra’ayi a gwamnatinsa rai. Don haka ya jaddada yin kira ga ‘yan adawa da su dauki matakin ruguza gwamnatin Netanyahu maimakon ceto shi.

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: a gwamnatinsa

এছাড়াও পড়ুন:

Riƙaƙƙen Ɗan Ta’adda, Bello Turji, Yana Neman Ayi Sulhu Bayan An Kashe Yaronsa

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Bayyana Cewa: Ba Za A Iya Kawar Da Fasahar Nukiliya Da Karfi Ba
  • Isra’ila na bincike kan harin dakarunta da ya kashe fararen hula a Gaza
  • Sabani Tsakanin Bin Gafir, Smotresh Da Zamir Kan Makomar Fursinonin Yahudawa A Gaza
  • Riƙaƙƙen Ɗan Ta’adda, Bello Turji, Yana Neman Ayi Sulhu Bayan An Kashe Yaronsa
  • Iran Ta Bukaci Gudanar Da Bincike Kan Dalilin Isra’ila Na Kai Harin Kan Gidan Yarin Tehran
  • An ɗage jana’izar Aminu Ɗantata zuwa Talata
  • Tawagar Gwamnatin Tarayya Ta Isa Saudiyya Don Halartar Jana’izar Ɗantata
  • Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Jaddada Cewa: Al’ummar Iran Masu Juriya Za Su Tsaya Tsayin Daka Waje Kare Hakkinsu
  • Kafar Labaran Amurka Ta Ce: Isra’ila Ta Yi Mummunar Hasara A Yakinta Da Kasar Iran
  • Madarar Shanu Da Nijeriya Ke Samarwa Ta Karu Da Tan Miliyan 1.4 A Shekara Biyar