HKI Ta Kashe Falasdinawa Akalla 143 A Ranar Tunawa Da Musibar Nakba
Published: 16th, May 2025 GMT
Majiyar kiwon lafiya a zirin Gaza ta bayyana cewa daga safiyar jiya Alhamis zuwa karfe 12 dare HKI ta kashe falasdinawa 143 tare da amfani da jiragen saman yaki tankunan yaki ta kasa da kuma jiragen ruwa yaki.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa bayan tsakiyar dare ma sojojin yahudawan sun kashe wasu karin mutane 21 wato a safiyar yau Jumma’a, a sansanin yan gudun hijira na Jabaliya.
Labarin ya kara da cewa a wasu hare haren guda biyu a Khan Yunus sojojin yahudawan sun kashe falasdinawa 5 wasu daga cikinsu yara.
Gwamnatin Hamas a Gaza, ta bayyana cewa, tun lokacinda sojojin yahudawan suka sake komawa yaki a ranar 18 ga watan Maris da ya gabata sun kashe Falasdinawa 2,876.
Sannan tun daga ranar 7 ga watan Octoban shekara ta 2023 kuma ya kai mutane 56,000.
Jiya Alhamis ce ranar Nakba ga falasdinawa sabo ranarce aka kori falasdinawa daga kasarsu aka kuma kafa HKI.
A bangaren yahudawan sahyoniyya kuma wannan rana ce ta farinciki a tsakaninsu don aranar ce aka kafa HKI.
Mai yuwa shi ya sa sojojin yahudawan suka kara yawan kashe falasdinawa don kara masu bakinciki a wannan ranar.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: kashe falasdinawa sojojin yahudawan
এছাড়াও পড়ুন:
Kananan Yara 2 Falasdinawa Masu Shan Nono Sun Yi Shahada Saboda Yunwa
Tashar talabijin din Aljazira ta bayar da rahoton da yake cewa; Rashin abinci mai gina jiki da karewar madarar jarirai a yankin Gaza, ya sa jarirai biyu sun yi shahada.
Majiyar asibitin Nasar ta a birnin Khan –Yunus dake kudancin Gaza, ta ambaci cewa jariran biyu sun rasa ransu ne saboda rashin abinci mai gina jiki da kuma madarar jarirai.