NAJERIYA A YAU: Mece ce Makomar Dimokuraɗiyya Idan Aka Wajabta Kada Kuri’a?
Published: 19th, May 2025 GMT
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
Ɗaya daga cikin ginshiƙan tsarin dimokuradiyya shi ne zaɓi – bai wa jama’a dama su zaɓi abin da suke so, ko kuma wanda suke so ya shugabance su.
Wannan ne ya sa ɗaya daga cikin muhimman matakai a kafuwar tsarin shi ne zaɓe.
Sai dai kuma abin tambaya shi ne, zaɓin ya haɗa har da na yin zaɓe ko ƙaurace masa?
Mene ne matsayin tsarin dimokuraɗiyya idan aka wajabta wa al’umma kaɗa ƙuri’a?
NAJERIYA A YAU: Shin Jam’iyyar NNPP Za Ta Kai Labari A 2027? DAGA LARABA: Tasirin Mulkin Karɓa-Karɓa A NajeriyaWannan shi ne batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai duba.
Domin sauke shirin latsa nan
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Dimokuraɗiyya Zaɓe zaɓi
এছাড়াও পড়ুন:
Maryam Sanda na cikin waɗanda Tinubu ya yi wa afuwa
Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya yi wa Maryam Sanda afuwa, wadda aka yanke wa hukuncin kisa a shekarar 2020 bisa laifin kashe mijinta, Bilyaminu Bello, ɗan tsohon shugaban jam’iyyar PDP, Alhaji Haliru Bello.
Maryam,’ mai shekara 37, ta shafe shekaru shida da watanni takwas a gidan yarin Suleja kafin yi mata afuwa.
Talauci da tsangwama na hana yara mata karatu a Gombe — Kwamishina Gwamnan Kebbi ya bai wa sojoji kyautar motoci 6 da babura 30 don inganta tsaroRahotanni sun nuna cewar an yi mata afuwar ne bayan yin nadama da aikata kyakkyawan halaye.
Iyayen Maryam sun roƙi gwamnati da ta sake ta saboda ’ya’yanta biyu da ta ke da alhakin kula da su, tare da alƙawarin sauya halayenta.
Shugaba Tinubu, ya kuma yi wa wasu mutane afuwa da suka haɗa da Manjo Janar Mamman Vatsa, Ken Saro-Wiwa, da kuma Sir Herbert Macaulay.
Gaba ɗaya mutane 175 ne shugaban ya yi musu afuwa, ciki har da masu manyan laifuka, tsoffin fursunoni, da waɗanda suka yi kyakkyawan tuba.
Wannan shi ne karon farko da Shugaba Tinubu ya yi amfani da ikon yafe laifi don tausaya wa waɗanda suka aikata laifuka tun bayan hawansa mulki.