Aminiya:
2025-07-04@10:00:55 GMT

Mataimakiyar shugaban majalisar dokokin Edo ta yi murabus

Published: 19th, May 2025 GMT

Mataimakiyar Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Edo, Misis Maria Oligbi-Edeko, ta ajiye muƙaminta.

Ta bayyana murabus ɗinta ne a zaman majalisar da aka yi a ranar Litinin a Birnin Benin, babban birnin jihar.

Zulum ya roƙi Gwamnatin Tarayya ta kai wa Marte ɗauki Hajji: Gwamnan Gombe ya yi bankwana da maniyyata 966, ya bai wa kowa kyautar Riyal 200

Oligbi-Edeko, wadda ke wakiltar mazaɓar Esan ta Arewa Maso Gabas II, ta ce ta yi murabus ne, saboda jam’iyyarta ta PDP ta rasa rinjaye a majalisar bayan wasu ’yan jam’iyyar ciki har da Shugaban Majalisar sun koma jam’iyyar APC.

An zaɓe ta a matsayin Mataimakiyar Shugaban Majalisar karo na takwas a ranar 16 ga watan Yunin 2023, kafin ta yi murabus.

Bayan ta yi murabus, majalisar ta zaɓi Mista Osamwonyi Atu daga jam’iyyar APC (Orhionmwon ta Gabas) a matsayin sabon mataimakin shugaban majalisar.

Jagoran Majalisar, Hon. Jonathan Aigbokhan, ya gabatar da ƙuduri cewa a ci gaba da biyanta dukkanin haƙƙoƙinta da ke tattare da kujerar mataimakiyar shugaban majalisar.

Wannan ƙuduri ya samu goyon bayan shugaban ’yan adawa, Hon. Charity Airobarueghian, kuma dukkanin ‘yan majalisar sun amince da shi.

A cikin wasiƙar murabus ɗinta, Oligbi-Edeko ta ce ta yi hakan ne domin tabbatar da adalci, gaskiya da daidaito ga dukkanin mazaɓu.

Ta kuma gode wa shugabanni da mambobin jam’iyyar PDP saboda damar da suka bata ta wakilci mazaɓarta.

’Yan majalisar sun yaba da ƙoƙarinta da jajircewarta wajen yi wa jama’a hidima.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Majalisar Dokoki Mataimakiyar Shugaban Majalisa Murabus Siyasa shugaban majalisar ta yi murabus

এছাড়াও পড়ুন:

Ɗantata: Majalisar Dattawa Ta Ɗage Taron Jin Ra’ayin Jama’a A Arewa maso Yamma

A yayin zaman, ana sa ran tattauna batutuwa da dama da suka haɗa da ’yancin ƙananan hukumomi, ƙirƙiro hukumar zaɓe ta ƙasa don kula da zaɓen ƙananan hukumomi, kafa ƴansanda na jihohi, da ƙara yawan kujerun mata a majalisun dokoki domin samun wakiltar jinsin mata. Haka kuma, za a duba ƙuduri guda shida da suka shafi inganta gaskiya da rikon amana a harkokin kuɗi.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Majalisar Jigawa Ta Isa Roni A Ci Gaba Da Rangadin Kananan Hukumomi
  • Majalisar Mali ta ƙara wa Goita wa’adin mulkin shekara biyar
  • Majalisar Dinkin Duniya Ta Fitar Da Rahoton Wadanda Suke Taimakawa ‘Yan Sahayoniyya Wajen Murkushe Falasdinawa
  • Majalisar Dinkin Duniya Ta Fitar Da Rahoton Wadanda Suke Taimakawa Yahudawan Sahayoniyya Wajen Murkushe Falasdinawa
  • ’Yan Majalisar Wakilai bakwai na Akwa Ibom sun koma APC
  • ‘Mutum 600 da suka bace a ambaliyar Mokwa sun mutu’
  • 2027: David Mark zai kai mu ga nasara — ADC
  • Majalisar Dokokin Filato ta zaɓi sabon shugaba
  • An Dakatar Da Shugaban APC Na Jihar Nasarawa
  • Ɗantata: Majalisar Dattawa Ta Ɗage Taron Jin Ra’ayin Jama’a A Arewa maso Yamma