Raya Kasa Na Bukatar Bin Daidaitacciyar Hanya
Published: 20th, May 2025 GMT
A ganin mista Akanbi, manufofin kasashen yamma ne dalilin da ya haifar da tafiyar hawainiyar tattalin arzikin Najeriya da na sauran kasashe dake nahiyar Afirka. Misali, kamfanonin kasashen yamma sun samu damar mamaye bangaren hakar ma’adinai na Najeriya, kana sun takaitawa kasar damar sarrafa ma’adinai, da ta raya masana’antu.
Ta yaya za a iya daidaita matsalolin da ake fuskanta? Mista Akanbi ya ba da shawarar daina dogaro da kasashen yamma, da tabbatar da bangarorin tattalin arzikin kasa da za a ba muhimmanci, bisa ra’ayin kasar, kamar yadda kasar Sin ta yi a baya. Ya ce, abokan hulda da Najeriya take bukata, su ne wadanda za su iya taimaka mata raya masana’antu, da zama mai zaman kai ta fuskar tattalin arziki. Saboda haka, karfafa hulda da kasashen BRICS, musamman ma kasar Sin, za su sanya Najeriya kama hanyar zama kasa mai karfin masana’antu, da na cinikayya.
Ci gaban kasa tamkar tafiyar da wani mutum yake yi. Idan wata hanyar da ake bi ba ta kai mutum inda ya nufa ba, to, sai a canza zuwa wata da daban. Wannan dabara ce da ta nuna hikima da sanin ya kamata. (Bello Wang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci Ta Iran Ya Ce: Haramtacciyar Kasar Isra’ila Ba Ta Da Alkiblar Siyasa
Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran ya bayyana cewa: Haramtacciyar kasar Isra’ila ba ta da wani yanki na siyasa mai zaman kansa
Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran Muhammad Baqir Qalibaf ya bayyana cewa: Yahudawan sahayoniya ba su da wata kafa ta siyasa mai cin gashin kanta, a maimakon haka dole ne a fahimci matsayinsu geopolitical bisa tsarin mulkin Amurka.
A jawabin da ya gabatar a wajen rufe taron tattaunawa na Tehran a jiya litinin, Qalibaf ya kara da cewa: A fagen siyasar kasa, siyasa ba ita ce kullin nauyi ba, a maimakon haka, labarin kasa shi ne ginshikin da siyasa ta ginu a kansa a matsayin wani mataki mai girma.
Ya bayyana cewa: Idan ana magana game da ababen more rayuwa da labarin ƙasa ke wakilta a zahiri, ana nufin nazarin abubuwa uku: Wuri, mutane da lokaci. Wato fahimtar nazarin al’amuran ɗan adam a lokuta daban-daban yana samuwa ne ta hanyar nazarin fifikon wuri. Don haka, a cikin binciken a fagen siyasa, za a dogara da wuri a matsayin tushen abubuwan more rayuwa.