‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 3, Sun Sace 26 A Zamfara
Published: 19th, May 2025 GMT
Akalla mutane uku ne aka ce an kashe tare da yin garkuwa da wasu 26 a wani sabon harin da wasu ‘yan bindiga suka kai a karamar hukumar Kauran Namoda da ke jihar Zamfara. Daily trust ta bankado cewa, hare-haren na tun ranakun Alhamis zuwa Asabar, sun shafi al’ummomi da dama a yankin. Tattalin Arzikin Sin Ya Bunkasa Bisa Daidaito A Afirilu Yanzu-Yanzu: Ana Zargin Makiyaya Sun Kashe Mutane 15 A Benuwe Shaidun gani da ido sun bayyana cewa, lamarin ya fi kamari akauyen Sabon Gari, inda aka kashe mace guda tare da yin garkuwa da mazauna yankin kusan 20.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Mummunan Hatsarin Mota Ya Kashe Mutane 7, Wasu 11 Sun Raunato
Aƙalla mutane bakwai sun mutu yayin da wasu 11 suka jikkata a wani hatsarin mota da ya faru a ƙauyen Essa da ke kan hanyar Agaie-Badeggi, ƙaramar hukumar Katcha, jihar Neja.
Binciken LEADERSHIP ya nuna cewa motar ɗauke da hatsi ta gwamnatin tarayya ce, kuma fasinjojinta maza ne kimanin 36, daga Legas zuwa Kano.
Sojoji Sun Harbe Mutane Biyu Har Lahira Da Ake Zargi Ɓarayin Mota Ne A Filato An Tsinci Gawarwakin Yara Biyar Cikin Tsohuwar Mota A NasarawaHatsarin ya faru ne da ƙarfe 3 na daren ranar Lahadi, lokacin da direban ya yi ƙoƙarin ƙetare wani ɓangare mara kyau na hanyar da ake ginawa.
Daraktan hukumar kula da sufuri na Jihar Neja (NSEMA), Abdullahi Baba Arah, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa ana kan aikin ceto da binciken kan iftila’in.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp