Wakilin VOA Haruna Dauda Ya Rasu A Maiduguri
Published: 19th, May 2025 GMT
Allah ya yiwa fitaccen ɗan jarida kuma wakilin Gidan Rediyon Muryar Amurika (VOA) a jihohin Borno da Yobe, Haruna Dauda Biu rasuwa a ranar Lahadi a Maiduguri.
Marigayin, wanda ya kuma kasance tsohon shugaban ƙungiyar ‘yan jarida (Correspondents Chapel) na jihar Borno, ya rasu ne bayan doguwar jinya.
Na Dauki Karramawar Jaridar LEADERSHIP Da Matukar Muhimmanci – Gwamna Abba Babu Wani Dan Jarida Da Aka Hana Shiga Taron Gwamnonin Arewa – CPS Ibrahim MusaAn shirya gudanar da sallar jana’izarsa yau Litinin a ƙofar gidansa da ke unguwar State Low-Cost, Maiduguri.
Abokan aiki da ‘yan uwa sun bayyana baƙin ciki game da rasuwar, suna yaba masa da halayensa na kirki da ƙwarewarsa a fannin jarida.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Jarida
এছাড়াও পড়ুন:
De Bruyne Ya Kammala Komawa Napoli Bayan Barin Man City
An sanar da tashin shi daga City kafin karshen kakar wasa ta bana, kuma De Bruyne ya yi bankwana da magoya baya a filin wasa na Etihad bayan wasansa na karshe a gida da suka buga da Bournemouth a watan Mayu, City ta yi kokarin cike gibin da De Bruyne ya bari, yayinda ta dauki yan wasan tsakiya Tijjani Reijnders daga AC Milan da Rayan Cherki daga Lyon.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp