Hajji: Gwamnatin Katsina ta biya wa maniyyata 2000 kuɗin hadaya
Published: 19th, May 2025 GMT
Gwamnatin Jihar Katsina ƙarƙashin jagorancin Gwamna Malam Dikko Umar Radda, ta biya wa maniyyatan jihar 2,047 kuɗin hadaya domin sauƙaƙa musu wajen hidimomin aikin Hajji na shekarar 2025.
Amirul Hajji kuma Mataimakin gwamnan jihar, Malam Faruk Lawal Jobe, ne ya bayyana haka a ranar Lahadi yayin da yake yi wa mahajjatan jirgin farko bankwana kafin tashin zuwa ƙasa mai tsarki.
Ya ce an biya wa kowane maniyyaci Riyal 600.
Mahajjatan da za su fara tafiya sun fito ne daga ƙananan hukumomin kudancin jihar, kuma za su tashi a jirgin kamfanin Max Air.
Gwamna Radda ya ja hankalin maniyyata da su kiyaye dokoki da ƙa’idojin aikin Hajji.
Haka kuma ya roƙe su da su yi addu’a don samun zaman lafiya da ci gaban Jihar Katsina da ma Najeriya baki ɗaya.
A shekarar da ta gabata ma, Gwamna Radda ya biya wa maniyyatan jihar kuɗin hadaya domin rage musu kashe kuɗi a aikin Hajji.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: gwamnati Hadaya maniyyata
এছাড়াও পড়ুন:
SULEJA – An Ci Moriyar Ganga (I)
A wancan lokacin, Sarkin Abuja shi ne Marigayi Sulemanu Barau, wanda ya rasu a shekarar 1979. Saboda hikimarsa da hangen nesa, ya ga cewa zai fi dacewa mutanensa su samu ‘yanci da asali ta hanyar kasancewa cikin wata jiha a kasar tarayya, fiye da su kasance a cikin wani yanki da ake kira kasar kowa ba tasa ba, kamar yadda ake kallon FCT a yanzu.
A sakamakon haka, kashi 80 cikin dari na kasar da ke karkashin Masarautar Abuja da sunanta gaba-daya, aka mika wa gwamnatin tarayya domin gina FCT. Wannan kaso ya yi daidai da 80 cikin dari na jimillar fadin FCT a yanzu. Sauran kashi 20 cikin dari kuwa, an samo su ne daga tsohuwar Jihar Filato da tsohuwar Jihar Kwara, wato Nasarawa da Kogi a halin yanzu.
Daga baya kuma, an sauya sunan garin zuwa Suleja a shekarar 1979, a girmama Marigayi Sulemanu Barau. sauran kasar 20 cikin dari yanzu su ne suka zama Kananan Hukumomin Suleja, Gurara da Tafa a Jihar Neja.
A karshe dai, yau dukkanin asalin mutanen Masarautar Suleja kafin kirkiro FCT, wato wadanda ke wajen FCT; amma cikin Jihar Neja da kuma ‘yan’uwansu daga kabilun Gbagyi, Koro da wasu da ke cikin FCT, sun zama tamkar marasa tushe ko makoma, suna kallon zuwan FCT a matsayin masifa maimakon albarka. Asalin mazauna FCT, na fafatawa da sauran ‘yan Nijeriya wajen mallakar kasa, wadanda ke da karfi na kudi da tasiri fiye da su.
‘Yan Nijeriya na da fa’ida biyu, zai iya zama dan asalin jiharsa kuma ya nemi mukami ko kujerar siyasa a nan da kuma FCT. Amma dan asalin FCT, ba zai iya samun irin wannan dama a wasu jihohi ba, saboda za a dauke shi a matsayin bako.
Haka kuma, dukkanin mutanen Jihar Neja da ma sauran ‘yan Nijeriya na gasa da mutanen Suleja wajen mallakar kasa a Suleja, saboda kusancinta da babban birnin tarayya, muddin suna da karfin kudi da goyon bayan gwamnati daga Minna. Duk da haka, ta halin da ake ciki da dabi’ar mutane, kowa ya fi jin dadin zama a kasarsa fiye da kasar da ba tasa ba.
Asalin mazauna Abuja ko da suna cikin Suleja ko FCT, sun takaita ne kawai a yankunansu, suna cikin gasa mai tsauri da sauran ‘yan Nijeriya. Hanyarsu mafi rinjaye ta samun abinci, ita ce noma, amma mallakar gonaki da gidaje a kauyukansu yanzu ya zama tarihi. Yawancin matasa ba su da karfin saye, sai dai su kama haya a garuruwansu, domin zama da iyalinsu; abin da yawancin al’umma ke kallo tamkar sabo da al’ada. Abin da ake tsoro da yake faruwa a FCT yanzu, ya fara bayyana har ma a makwabciyarta, Suleja.
Halin da suka ci gaba da shiga ya karu ne sakamakon jahilci da kin neman ilimi daga wasu, wadanda ke yada karya ga jama’a. Wani tsohon dan jarida ya rubuta a jaridar Sunday Tribune ta 28 ga Janairu 2024 cewa, gwamnatin tarayya ta biya diyyar asalin mazauna FCT, kuma ta gina musu Suleja. Wannan na nufin cewa; har ma tsofaffin ‘yan jarida da dattawan kasa suna da fahimta maras tushe cewa, Suleja ginin gwamnatin tarayya ne bayan kirkiro FCT.
Tambayoyin da suka dace a yi su ne; ko an biya Suleja diyya ne dangane da kafa FCT? Ko kuwa ana ba mazaunanta kulawa daidai da sauran al’ummomin Jihar Neja, wajen samar da ababen more rayuwa da ayyuka? Idan FCT na da fa’idodi, wa ke amfana da su, Suleja ko jihar?
Za mu ci gaba a mako mai zuwa
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp