Yadda ’ya’yan shugabanni ke musu yaƙi da ’yan adawa
Published: 18th, May 2025 GMT
Yanayin da ’ya’yan shugabanni suke yin fito-na-fito da masu ƙalubalanta ko yin tambaya a kan abubuwa ko matakan da iyayensu suka ɗauka, sai ƙara muni yake yi a fagen siyasar Najeriya.
Abin da da ke ƙara zama ruwan dare a Najeriya shi ne yadda a duk lokacin da mutane suka tambayi shugabanni ko suka ƙalubalanci wani aiki ko mataki da suka ɗauka ko abin da suka faɗa, ’ya’yan shugabannin ke fito su yi ɓaɓatu, wani lokaci ma har da cin mutunci.
Yaran suna zargin masu neman bayanin, kamar saɓo suka yi, sun manta cewa a matsayin iyayensu na shugabanni, haƙƙi ne a kansu su yi wa jama’a bayani kuma a riƙa bibiyar ayyukansu tare da tambayar su.
Yadda ’ya’yan shugabanni ke ci gaba da yin hakan abin damuwa ne, kamar sun kasa fahimtar cewa iyayensu na da mataimaka da ake biyan su albashi, waɗanda aikinsu shi ne yin bayanin abubuwan da gwamnati ta yi.
Yadda shugabannin ba sa kwaɓar ’ya’an nasu ta sa an wayi gari yaran sun shiga kusan cikin komai, suna ƙoƙarin canza abin da mutane ke tunani, wani lokacin ma har da zagi da cin mutuncin abokan hamayyar siyasar iyayensu.
Suna kuma amfani da kafofin sada zumunta wajen wallafa ra’ayoyinsu, suna zafafawa a martaninsu tare da yin fito-na-fito, maimakon tattaunawa kan batutuwa.
Da sanin iyayensu suke yi’ Abin mamaki shi ne iyayensu ba sa kwaɓar su, wanda ake ganin shi ya sa dabi’ar take kara yaɗuwa.
Wani tsohon hadimi ga wani shugaba da ’ya’yansa ke da wannan ɓabi’a ya ce, iyayen suna goyon bayansu.
Ya ce, “Daga abin da na gani zan iya cewa iyayensu suna goyon bayan hakan. Da iyayensu sun hana su, da sun daina, amma tun da suka ci gaba, hakan yana nuna cewa, iyayensu ba goyon bayansu kawai suke yi ba, har ma karfafa su suke yi a fakaice.”
Wani sanannen marubuci, Sam Omatseye, ya taɓa yin jayayya da ’ya’yan tsohon Gwamna Jihar Kaduna, Nasir El-rufai.
Ya rubuta cewa, abin taikaici ne shugaba ba zai iya shawo kan al’amura a cikin iyalinsa ba.
Sam Omatseye ya rubuta ce: “Matarsa, Hadiza ta yi wa ɗansa, Bashir magana, saboda kalamansa na rashin ɗa’a ga Shugaba Tinubu a shaguɓen da ya yi wa Obasanjo. Cikin fushi Hadiza ta yi wa Bashir tambaya cewa, “Da mahaifinka na cikin gwamnatin za ka faɗi haka?”
A da ba haka abin yake ba A da, ’ya’yan shugabannin kasa — da gwamnonin da ministoci da sauran waɗanda aka naɗa, a bayan fage suke, ba a jin muryoyinsu, kuma an fi ganin su ne a wuraren bukukuwan ɗaurin aure da sauransu, amma ba sa magana a kan gwamnatin iyayensu.
An ruwaito cewa a lokacin da ’yan jarida suka tambayi wani tsohon shugaba ƙasa tambaya kan soke zaɓen 12 ga watan Yunin, 1993, ɗansa ya yi ƙoƙarin kare shi, amma ya galla wa ɗan wani mugun harara, dun daga lokacin bai sake yin magana a madadin mahaifinsa ba.
’Ya’yan tsohon shugaban ƙasa na mulkin soja Janar Sani Abacha, musamman Ibrahim wanda ya rasu a hatsarin jirgin sama, sun yi fice a lokacin mulkin mahaifinsu, amma da ƙyar su fito suna bayyana ko kare manufofinsa, duk da cewa Abacha yana ɗaya daga cikin shugabannin da aka fi sukar su.
Sai bayan shekaru da rasuwarsa ne ’ya’yansa, musamman Gumsu, take fitowa tana rubuta kyawawan abubuwa a kasna a shafinta na X, kuma jefi-jefi ta kan yi amfani da shafin wajen fayyace batutuwan da take ganin an danganta su da shi ba daidai ba.
A kwanankin baya ta wallafa a cewa, “Maza har ma bayan mutuwa, ku ne babban abokin hamayyarsu.”
Hakazalika iyalan Abacha sun fitar da wata sanarwa lokacin da tsohon shugaban ƙasa na mulkin soja, Janar Ibrahim Babangida, ya ƙaddamar da littafinsa, wanda a ciki ya zargi Marigayi Abacha da soke zaɓen 12 ga watan Yuni, 1993.
Ɗaya daga cikin jikokin Abacha, Raees, ya shiga wannan tankiyar, inda wallafa wani rubutu a shafinsa na X mai taken “Kakana ya ceci rayuwar rago” ya ƙara da cewa, “da Janar Abacha ne a awnnan matsayi, da ba zai taɓa yi wa Babangida irin butulci ba.”
A lokacin mulkin Olusegun Obasanjo daga 1999 zuwa 2007, ɗansa, Gbenga, ya kasance sananne sosai, amma ba a san shi da mayar da martani ga masu sukar ayyukan mahaifinsa ko kalamansa ba.
Wani abin mamaki shi ne, ’yar Obansajo mai suna Iyabo, bayan ta shiga siyasa ta hanyar zama kwamishina a Jihar Ogun sannan kuma Sanata, ba ta kare mahaifinta ba, hasali ma, har zargin sa ta yi a miyagun abubuwa iri-iri a bainar jama’a.
A zamanin Buhari, ’yarsa Zarah ta kasance mai sha’awar yaba masa a farkon mulkinsa, amma daga baya ta yi shiru, watakila ta sauya tunani game da wannan hanyar, ko an taka mata burki.
Halin da ake ciki yanzu Tun bayan rantsar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu, biyu daga cikin ’ya’yansa, Alhaja Folashade Tinubu-Ojo da ɗansa, Seyi, suke aiki kai da fata wajen ƙoƙarin tallata shi.
’Ya’yan sauran masu riƙe da muƙaman gwamnati kamar gwamnoni, ministoci masu ci da tsofaffi su ma sun bi sahu a wannan ɗabi’a da ta zama ruwan dare.
Alhaja Folashade Tinubu-Ojo Alhaja Folashade TinubuOjo, wacce aka fi sani da Iyaloja Janar ta Jihar Legas, ta yi ta aiki kai da fata wajen tallata kyawawan ayyukan mahaifinta.
Ta taɓa fitowa ta a roƙi ’yan Najeriya su yi haƙuri da mahaifinta game da matsin tattalin arziƙi a ƙasar, da cewa su kasance masu kyakkyawan fata saboda matsalar al’amari ne da ya shafi duniya baki ɗaya, ba Najeriya kaɗai ba.
Ta yi kiran ne a hirarta da ’yan jarida a taron Maulidin Annabi na 2024 na reshen Jihar Legas na Ɗarikar Ƙadiriyya, inda aka naɗa ta Iya Adinni ta Ƙadiriyya a Najeriya da Afirka.
Ta ce, “Saƙona ga duk ’yan Najeriya shi ne su ƙara haƙuri kaɗan. Komai zai daidaita; lokaci ne kawai. Muna buƙatar mu ci gaba da kasancewa masu kyakkyawan fata. Koma-bayan tattalin arziƙi a duk faɗin duniya ne, ba a Najeriya kadai ba.
“Amma muna roƙon Allah Ya taimake mu.”
Seyi Tinubu ɗan Shugaban Tinubu, Seyi mutum ne mai magana sosai wajen kare gwamnatin mahaifinsa da sukar ’yan adawansa.
A wani taron matasa a Yola, Jihar Adamawa, Seyi ya bayyana mahaifinsa a matsayin shugaba na gari da Najeriya ba ta taɓa samun irinsa ba.
Kalamansa: “Ba siyasa ba ce ko kaɗan, amma suna ci gaba da nema na, da iyalina, da mahaifina, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, shugaba mafi girma a tarihin Najeriya.”
Bashir El-Rufa’i Bashir, ɗan tsohon Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa’i, da ɗan uwansa Bello sun yi fice wajen kare mahaifinsu, inda suke kausasawa tare da amfani da miyagun kalamai a martaninsu ga kalaman da suke ganin an yi su ne don cutar da mahaifinsu.
A kwanakin baya, Bashir ya soki Gwamna Uba Sani, kan binciken da Majalisar Dokokin Jihar Kaduna, ke yi kan zargin gwamnatin mahaifinsa da karkatar da kusan Naira biliyan 423.
Bashir ya bayyana matakin a matsayin tsoratarwa ta siyasa, tare da zargi cewa wasu nasu faɗa-a-ji da daga waje ne ke tunzura binciken.
Bashir El-Rufai ya sha sukar Shugaba Tinubu da cewa IMF da Bankin Duniya ba za su iya ceton shugaban ba, kuma dabarun da ya yi amfanin da su wajen jagorantar Jihar Legas a lokacin da yake gwamna ba za su yi aiki a matakin kasa, har ma ya kwatanta wani mutum mai matuƙar ƙarfin faɗa-a-ji a gwamnatin da wani sanannen ɗan ta’adda a ƙasar Kolombia, Pablo Escobar.
Lokacin da Gwamna Uba Sani ya sanar ceaw ya gaji bashin dalar Amurka miliyan 587, Naira biliyan 85 da kuma kuɗaɗen ’yan kwangila na biliyan 115 daga gwamnatin El-Rufai, Bashir ya mayar masa martani da cewa gwamnatinsa tana fama da rashin ƙwarewa da rashin sanin makamar aiki.
Ya rubuta a shafinsa na X cewa, “Gwamnatin Jihar Kaduna tana gina zauren taro na Naira biliyan 7 amma tana kukan bashin da gwamnatin baya ta bari. Waɗannan mutanen sun san cewa ba su da ƙwarewa ko kaɗan, kuma hanya ɗaya tilo da za su ɓoye wannan wauta ita ce su karkatar da hankalin jama’a.”
Ya ci gaba da cewa: “Gwamnan da kullum yake kwana a Abuja da taron mataimaka marasa ƙwarewa waɗanda aka ba su muƙamai saboda dalilai na siyasa na wauta.”
Bello El-Rufa’i ƙaninsa, Bello El-Rufai, wanda yanzu ɗan Majalisar Wakilai ne, shi ma ba kanwar lasa ba ne a wannan fage.
Shi ya yi wa Majalisar Dokokin Jihar Kaduna kaca-kaca bayan ta kafa kwamitin binciken harkokin kuɗi, lamuni, tallafi, da aiwatar da ayyuka daga a zamanin mulkin mahaifinsa daga 2015-2023.
A wani saƙo da ya aike wa Majalisar, wanda daga baya ya goge, ya yi wa Shugaban Majalisar, Yusuf Liman, kakkausan magana, wanda Majalisar ta bayyana a matsayin abin takaici.
Majalisar ta ce: “Abin takaici ne yadda ɗan Majalisar Tarayya, wanda aka amince da shi ya wakilci mutane, zai yi irin wannan halayyar yana ƙoƙarin hana ayyukan doka na Majalisar Dokokin Jihar Kaduna wadda ke son ta sake tabbatar wa al’ummar jihar cewa ta ci gaba da yin tsayuwar daka wajen hidimta musu ba tare da tsoro ko nuna son kai ba.”
Ƙoƙarin da aka yi don yin magana da Bashir El-Rufai bai yi nasara ba, saboda bai amsa kiran wayarsa ba da rubutaccen saƙon da aka aika masa.
Bai kuma mayar da kiran da aka yi masa ba.
Shamsudeen Bala Mohammed Shi ma Shamsudeen, ɗan Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, kwanan nan ya fito ya kare mahaifinsa, inda ya zargi tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, da yin aiki don ganin mahaifinsa bai sake cin zaɓe ba a 2023.
Akwai kuma zargin cewa bayan bikin naɗin sarautar da aka yi wa tsohon Gwamnan Jihar Bauchi, Mohammed Abubakar, a Fadar Mai Martaba Sarkin Bauchi, mataimakin gwamnan jihar, Auwal Jatau, ya mari Ministan Harkokin Waje, Yusuf Tuggar.
A kan haka ne Shamsudeen ya wallafa wani rubutu a shafinsa na Facebook inda yake ba’a ga ministan.
Ya kuma yada wasu rubuce-rubuce game da zargin marin da wasu masu amfani da Facebook da ake zaton magoya bayan mahaifinsa ne suka yi.
Wakilinmu ya yi ta ƙoƙarin yin magana da Shamsudeen, amma haƙarsa ba ta cimma ruwa ba.
Wani makusancin iyalin wanda ya yi alƙawarin yin magana da shi domin ya bayyana dalilin da ya sa yake sukar ’yan adawar mahaifinsa, bai yi nasara ba, kuma bai sake tuntuɓar wakilinmu ba har zuwa lokacin da akq kammala wannan rahoto.
Mohammed Atiku Lokacin da Shamsudeen ya zargi Atiku da yi wa mahaifinsa maƙarƙashiya, ba ofishin yaɗa labarai na tsohon mataimakin shugaban ƙasar ba ne ya mayar da martani, ɗansa, Mohammed, wanda kuma shi ne Shugaban Ƙungiyar Magoya Bayan Atiku (ASO), ne ya mayar da raddi.
Mohammed ya yi zargin cewa mahaifin Shamsudeen bai taɓa goyon bayan Atiku a harkokin siyasarsa ba.
Hasali ma, a wata sanarwa da ya fitar, ya bayyana kalaman Shamsudeen a matsaryin girman kai da zuzuta abin da bai dace ba.
Adam Tuggar Adam Tuggar, ɗan ministan da ake zargin an mara, shi ma ya sa kafar wando da Shamsudeen, inda ya zarge shi da yada karya.
Ya ce, “Ban yi mamaki ba, saboda ya taɓa zagi da sukar manyan mutane masu daraja kamar Atiku Abubakar, kawai saboda suna da saɓanin siyasa da mahaifinsa.”
Ya kuma wallafa a shafinsa na Facebook, cewa bai fiya magana a kan siyasa a intanet ba, amma, “Wannan abin kunya da sangartaccen ɗan gwamnan Jihar Bauchi da karnukan farautarsa a kafofin sada zumunta suka yi, su ne suka tilasta ni na yi wasu maganganu masu zafi.
Ya ƙara da cewa: “Mahaifinka yana da muhimman batutuwa da ya kamata ya magance. Ya kamata ya mayar da hankali kan abin da zai yi wa al’amuran Jihar Bauchi maimakon karkatar da hankalin jama’a ta hanyar ƙirƙirar da yaɗa irin waɗannan labarai a kafofin watsa labarai. Ba abin mamaki ba ne ganin kana yin irin wannan aikin wauta.”
’Yan jarida ba su samu damar jin ta bakin Shamsudeen Bala Mohamed da Adam Yusuf Maitama Tuggar ba don yin tsokaci ba.
Mataimakan mahaifansu sun ƙi amincewa su ba da lambobin wayarsu.
Wakilimmu a Bauchi ya yi ƙoƙarin tuntuɓar mutane da yawa, amma ba su samu lambobin ba.
Martanin ’yan Najeriya sun nuna damuwa bisa ƙaruwar yadda ’ya’yan shugabannin siyasa ke yin shisshigi ko fito-na-fito da masu ƙalubalantar shugabancin iyayensu.
Amma kuma ra’ayoyin masana sun bambanta a game da wannan lamari, inda wasunsu ke cewa yaran na da ’yancin yin tsokaci kan abin da ya shafi shugabancin iyayensu, wasu kuma ke zargin irin ƙarfin tasirin yaran, da kuma yadda suke mayar harkokin siyasa tamkar sha’anin iyali ko na gado, alhali ba zaɓensu aka yi ba.
Ana kuma ganin kafofin intanet sun taimaka wa yad5uwar wannan ɗabi’a, musamman ganin yadda batutuwan siyasa ke saurin yaɗuwa a kafofin sada zumunta.
Wani masanin Kimiyyar Siyaas, Farfesa Hassan Salisu, ya ce wannan ba sabon abu ba ne, saboda yaran suna da kusanci da shugabanci da kuma ƙarfin faɗa a ji.
Farfesa Hassan ya ƙalubalanci yadda “Wasu daga cikin yaran suka tara biliyoyin kuɗaɗen ƙasashen waje,” inda yake zargin da goyon bayan iyayensu suke yin abin da suke yi, saboda iyayen “na shirya su ne domin wasu manyan muƙaman siyasa, a nan gaba.”
Ya yi gargaɗin cewa irin haka na iya mayar da siyasar ƙasar tamkar ta gado, saɓanin yadda a baya ko shugabannin mulkin soji ’ya’yansu ba sa tsoma baki a kan shugabancinsu.
“Shi ya sa yanzu ministoci da kwamishinoni da manyan jami’an gwamnati ke durƙusa musu,” in ji shi.
Farfesa Hassan ya ce rashin taka kwaɓar yaran zai yi wa gurgunta dimokuraɗiyyar ƙasar nan na tsawon lokaci, musamman lura da yadda siyasa ta zama wani fage da kowanne irin mutane ke tururuwar shiga.
Sai dai ya ce da wuya a yi saurin kawo ƙarshen wannan matsala siyarar Najeriya, ganin yadda ake fifita dukiya da kusanci, kuma yaran sun hada duka biyun.
Don haka ya yi hasashen yiwuwar komawar shugabancin siyasa kamar na gado, saboda talaucin ƙasar da ke mayar da mutane masu rauni da saukin juya ra’ayinsu a lokacin zaɓe.
Wani lauya, Salman Jawondo, ya bayyana wannan ɗabi’a a matsayin mummuna hatta ga iyalan yaran.
Ya ce abin da ’ya’yan shugabannin siyasan ke yi alama ce ta tsantsar yarinta da rashin tarbiyya kuma zai iya haifar da rikici.
Wani malamin Kimiyyar Siyasa, Seyid Hassan Cisse, ya bayyana abin da ke faruwa a matsayin alamar raunin dimokuraɗiyya.
Ya ce ko da yake yaran suna da ’yancin faɗin albarkacin bakinsu, amma tasirin da suke yi na fitowa ne daga matsayin iyayensu.
Ya bayyana cewa dokar ƙasa ba ta ba da wani matsayi ga ’ya’yan shugabannini siyasa ba, kuma akwai buƙatar su kasance masu kyawawan ɗabi’u da mutunta jama’a.
Ya kuma ja hankali da a guji take hakkokin bil Adama a ƙoƙarin magance wannan matsalar.
Sai dai ya ƙara da cewa tana iya yiwuwa wata dabarar siyasa ce, ba lallai da nufin muttsike ’yan adawa ba, kuma ya ja hankalin shugabannin da su taka wa ’ya’yansu burki a matsayinsu na iyaye.
Masanan sun yi ittifaƙin cewa muddin wannan ɗabi’a ta ci gaba, to za ta kawar da damar naɗa shugabanni da suka cancanta, ta damƙa shugabanci a hannun masu ƙarfin iko domin tabbatar su a kan shugabanci.
Mohammed Yaba, Kaduna, Ibrahim Yushau, Bauchi; Fassara: Sagir Kano Sale
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Siyasa ya yan shugabannin ya yan shugabanni wannan ɗabi a Gwamnan Jihar Jihar Bauchi a a matsayin Jihar Kaduna a gwamnatin a ƙoƙarin ya mayar da goyon bayan
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Katsina za ta gina birnin dawakai na farko a Afirka
Gwamnatin Jihar Katsina ta samu sahalewar Hukumar Wasanni ta Kasa domin gina Birnin Dawakai na farko a nahiyar Afirka.
Wannan amincewa ta biyo bayan wata ganawa ta musammam tsakanin Gwamna Dikko Umaru Radda — wanda Daraktan Hukumar Tarihi da Al’adun Gargajiya ta Jihar Katsina Dokta Kabir Ali Masanawa ya wakilta — da Shugaban Hukumar Wasanni ta Kasa, Malam Shehu Dikko da Ministar Al’adu, Yawon Bude da kuma Tattalin Arziqin Kirkire-kirkire Barista Hannatu Musa Musawa.
Gwamna Radda wanda ya bayyana cewa, gagarumin aikin Birnin Dawakan zai lakume biliyoyin Naira kuma zai kara inganta qokarin gwamnatin jihar na raya al’adun jihar tare da samar da hanyoyin tattalin arziki mai dorewa ga al’ummar jihar da arewacin Najeriya gaba daya.
Sabon birnin Dawakan na zamani zai qunshi manyan wuraren gudanar da bikin Daba, filayen tseren dawaki, makarantar horar da wasannin dawaki da sauransu.
Mutum ɗaya ya rasu a rikicin manoma da makiyaya a Yobe BUA ya yi alkawarin karya farashin shinkafa