2025-12-01@12:38:34 GMT
إجمالي نتائج البحث: 4831

«Yan sa Kai»:

    Daga Ali Muhammad Rabi’u  ’Yan bindiga kimanin guda huɗu dauke da makamai sun kai hari a garin Eruku da ke ƙaramar hukumar Ekiti a jihar Kwara, inda suka sace wani manomi mai suna Mista Aasaru. Rediyon Najeriya ya ruwaito  cewa wannan hari shi ne na biyu da aka kai wa garin Eruku cikin wata guda,...
    ’Yan bindiga sun yi garkuwa da wani fasto da matarsa da mabiyansa a yayin da suke tsaka da ibada a coci da ke a  Jihar Kogi. Wani ganau da ke cikin cocin a lokacin da aka kai harin, Adegboyega Ogun, ya ce misalin ƙarfe 9.30 na safe ’yan bindigar suka kai harin suna bude wuta....
    Rahotanni sun bayyana cewa ministan harkokin wajen kasar Turkiya ya iso birnin Tehran a jiya lahadi kuma  ya samu kyakkyawar tarba daga takwaransa na kasar iran Abbas Araqchi. Ziyarar tasa ana saran za ta kara fadada dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, ganin cewa dukkan kasashen biyu suna taka rawa a batutun da suka shafi yanki...
    Nicolas Maduro shugaban kasar Venzuwela yayi tir da barazanar da Washington ke ta nanatawa na yin amfani da karfin soji kan karakas, kuma yayi gargadi game da shirin Amurka na kwace ikon kila da rijiyoyin mai na kasar a hanyar amfani da karfin soji. Maduro yayi wannan bayanin ne a cikin wata wasika da ya...
    A wani bangare na huldar duplomasiya tsakanin iran da saudiya , mataimakin ministan harkokin wajen kasar saudiya Saud bin mohammad Al-sati ya gana da ministan harkokin wajen kasar iran Abbas Araqchi a nan birnin tehran inda suka tattauna kan batutuwan da suka shafin alakokin dake tsakani da kuma ci gaban yankin. Ganawar wani bangare ne...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A mafi yawan ƙasashen duniya, ana ɗaukar jakadu a matsayin fuskar ƙasa kuma ginshiƙan hulɗar diflomasiyya. Saboda haka, akwai muhimman halaye da suke tilas jakadan ƙwarai ya mallaka domin ya wakilci ƙasarsa cikin mutunci, da nagarta da kwarewa.   Tun bayan da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya...
    Ma’aikatar kiwon lafiya ta Falasdinu a Gaza ta sanar da cewa; An sami shahidai 3 da aka kai su asibitin a cikin sa’o’i 24 da su ka gabata.  Shi kuwa ofishin gwamnati dake Gaza ya sanar da cewa, daga tsagaita wutar yaki zuwa wannan lokacin, sau 591 Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta keta wutar yaki. Ofishin...
    Jaridar Washington Post ta buga rahoto akan Shirin Donald Trump na aikewa da sojoji zuwa Gaza, tare da cewa tana fuskantar matsala, domin har yanzu ana Magana akan yadda za a raba ‘yan gwgawarmaya da makamansu. Jaridar ta ci gaba da cewa; Da akwai damuwa a cikin manyan biranen kasashen duniya danagne da yiyuwar a...
    Hukumar Agaji ta MDD ta sanar da cewa, kasar Somaliya ta shiga cikin wani mawuyacin yanaki saboda fari, da yanki mai yawa na kasar ya bushe bayan da aka dauki shekaru hudu a jere babu ruwan sama. Hukumar ta MDD ta kuma ce, da akwai miliyoyin mutanen kasar da suke fuskantar yunwa mai tsanani, yayin...
    ’Yan bindiga sun shiga garin Chaco da ke Ƙaramar Hukumar Wurno a Jihar Sakkwato, inda suka sace amarya da ƙawayenta guda 14. Yayin da mutane ke tsaka shagalin bikin auren, sai ’yan bindigar suka afka musu tare da tarwatsa komai. Mutum 6 sun jikkata a rikici manoma da makiyaya a Jigawa Sojoji sun ceto mutum...
    ’Yan bindiga sun harbe wata tsohuwa har lahira a wani sabon hari da suka kai ƙauyen Yankamaye da ke Ƙaramar Hukumar Tsanyawa a Jihar Kano. Sun kai harin ne a daren ranar Asabar, a lokacin da mutanen ƙauyen ke kwance. Likitoci sun gindaya sabon sharaɗi bayan janye yajin aiki Tinubu ya sake aike wa majalisa...
    Cinikin kasashen waje na kasar Iran a cikin watanni takwas na farko na bana ya kai tan 131,540, wanda darajarsa ta kai dala biliyan 76.5. kwatankwacin tagomashi na kashi 1.53% idan aka kwatanta da bara warhaka. Bayanin da aka samu daga hukumar kwastam ta Iran ya ce: “A wannan lokacin, an fitar da tan 105,231,000...
    Rahotanni sun bayyana cewa shugaban kasar najeriya Bola Ahmad tunubu ya mika sunayen mutane 32 ciki har da tsohon shugaban hukumar zabe ta kasa mahamud yakubu da tsohon ministan sufurin jiragen sama femi kayode ga majalisar dokokin kasar domin a tantancesu kwanaki bayan tura sunayen mutane 3 a fara da su. Mai magana da yawun...
    Rahotanni sun bayyana cewa iran ta yi tir da sanarwar da shugaban Amurka ta fitar na rufe sararin samaniyar kasar venuzuwela kuma ta bayyana shi a matsayin keta dokokin kasa da kasa, da kuma dokokin kula da zirga –zirgar jiragen sama. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar iran Isma’ila Baghae ne ya fitar da wannan sanarwa...
    A ranar nuna goyon baya ga alummar falasdinu shugaban kasar Pakistan Asif Ali zardari ya jinjinawa Alummar falasdinu game da juriya da tsayin Dakar da suka nuna, yace jarumtar da suka nuna ta bude sabon shafin tarihi, don haka gudanar da bincike kan laifukan yaki da HKI ta tafka yana da muhimmanci sosai. Kasar Pakistan...
    Antonio Guterres babban sakataren majalisar dinkin duniya yayi kira da a kawo karshen mamayar yankunan falasdinawa da isra’ila ke yi da ya sabama doka, kuma yace babu ja da baya game da kudurin kafa kasashe biyu masu cin gashin kai Sakataren ya sake yin kira ne saboda ya nuna irin bukatar da ake da ita...
    Gwamnatin kasar Iran ta bada sanarwan cewa ta kakkabo jiragen yakin HKI fiye da 196 a cikin yakin kwanaki 12 da aka dora mata a cikin watan Yunin da ya gabata. Daga ciki har da jiragen yaki samfurin Heron da Hermes -900 wadanda ke aiki da kayakin zamani. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran...
    Shugaban kasar Amurka Donal Trump ya bada sanarwan rufe zirga zirgan jiragen sama kwata-kwata a kan sararin samaniyar kasar Venezuel daga yau, a cikin shirinsa na fara mamayar kasar. Tashar talabijan ta Al-Mayadeen ta kasar Lebanon ta nakalto Trump yana fadar haka a shafinsa na sadarwa True Social. Ya kuma bayyana cewa wannan sako ne...
    Kamfanin kera jiragen sama na ‘Airbus’ ya bukaci duk wadanda suka sayi jiragen sama samfurin A320 ya dawo da shi saboda aiwatar da wata gyra a tsarin tuka jiragen. Kamfanin dillancin Labaran AFP na kasar Faransa ya nakalto kamfanin yana bada wannan sanarwan a jiya Jumma’a ya kuma kara da cewa, Wannan shine karon farko...
    Cibiyar HANs Centre for Social Justice and Development tare da Kanady Academy, sun kammala horon kwana uku domin koya wa yara marasa galihu da matasa mata sana’o’in dogaro da kai a Jihar Gombe. Shugabar HANs, Barista Hannatu Dauda Simon, ta ce an shirya horon ne domin ƙarfafa gwiwar mahalarta, tare da koya musu yadda za...
    Ma’aikatar Harkokin Wajen Lebanon ta sanar a ranar Juma’a cewa ta shigar da kara a kan Isra’ila gaban kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya dangane da gina katanga biyu na siminti a cikin yankin Lebanon da ke kudu da garin Yaroun (yankin Bint Jbeil). A cikin wata sanarwa da ta fitar, Ma’aikatar ta ce tawagar Jakadancin...
    A baya, samun fara da yawa a shekara abin tsoro ne ga kowa, dalilin ɗab’arta ta lalata amfanin gona, sai dai a yanzu ta zamo hanyar samun abincin mutanen da dama, musamman ma mata a Jihar Kano. Duk da cewa a baya ma akwai tsirarun mutane da ke cin fara dace kuma halaccin cin...
    A baya, samun fara da yawa a shekara abin tsoro ne ga kowa, dalilin ɗab’arta ta lalata amfanin gona, sai dai a yanzu ta zamo hanyar samun abincin mutanen da dama, musamman ma mata a Jihar Kano. Duk da cewa a baya ma akwai tsirarun mutane da ke cin fara dace kuma halaccin cin...
    Babban Bankin Nijeriya CBN, ya sake bayar da wani dauki a Kasuwar hada-hadar musayar kudade, da nufin samar da sauki wajen samun kudade a cikin kasar. Hakan ya sanya Bankin, ya sayar da dala miliyan hamsin, ga dilolin da aka yarjewa yin hada-hadar musayar kudade a cikin kasar. Kazalika, Bankin ya yi hakan ne, domin...
    Ma’aikatar harkokin wajen kasar Pakistan ta bayyana ziyara da babban sakatare tsaron kasar Iran Dr Ali Larijani ya kai kasar a matsayin babban ginshiki a alakar dake tsakanin Tehran da kuma Islam Abad , domin ya kara karfafa danganatar dake tsakanin a bangarorin siyasa, tattalin arziki, da kuma tsaro dake tsakanin kasashen makwabtan juna. Kasashen...
    Shaikh Naim Qasim babban sakatare janar din kungiyar hizbullah ta kasar labanon ya bayyana cewa kisan babban kwamanda Haitham Ali tabataba’I da isra’ila ta yi bai zai sa ta cimma manufofinta ba, don haka hizbulla za ta mayar da martani a lokacin da ya dace, Wadanan kalaman suna zuwa ne a lokacin da ake zaman...
    Mai Magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar China ta bayyana cewa: Beijing ba ta lamunta da duk wani kokarin tsoma bakin kasashen waje a harkokin cikin gidan wannan kasar.” Mao Ning wacce ta gabatar da taron manema labaru a brinin Beijing a kasar China ta yi kira ga kasar Amurka da ta fasa Shirin...
    Rundunar “Sarayal-Quds” ta kungiyar Jihadul-Islami ta sanar da shahadar  mayakanta biyu a yammacin kogin Jordan sanadiyyar harin da sojojin mamaya na Haramtacciyar Kasar Isra’ila su ka kai. Daya daga cikin shahidan shi ne Yusuf Ali Asa-Asa, dan shekaru 37, da kuma Mahmud Abdullah dan shekaru 26, sun kuma yi shahadar ne a jiya Alhamis.  Sanarwar...
    Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya bayar da umarnin a fara tsara yadda za a shigar da kungiyar “Muslim Brotherhood” a cikin jerin kungiyoyin ta’addanci na waje. Kungiyar ta ce, babu wani dalili da Amurkan za ta iya samu da zai tabbatar mata da cewa kungiyar tana ayyukan ta’addanci. Haka nan kuma kungiyar ta ce,...
    Ma’aikatar harkokin wajen kasar  Senegal ta sanar da cewa hambararren shugaban kasar Guinea Bissau UOumar Sissoko Embalo ya isa kasar a cikin wani jirgin sama na musamman. Sanarwar ta ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Senegal ta fitar a jiya Alhamis ta ce an dauko shi ne a cikin jirgin sama na musamman bayan da kungiyar...
    Dubban mutane sun taru a Jihar Bauchi, don halartar jana’izar fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, wanda ya rasu a ranar Alhamis a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa. Gwamnatin Jihar Bauchi, ta ayyana ranar Juma’a a matsayin ranar hutu domin ba jama’a damar halartar jana’izar malamin. Trump zai haramta wa ’yan...
    Rahotanni sun bayyana cewa kasar Yamen ta yi tir da matakin da kasashen birtaniya da Amurka suka dauka na sukar hukumcin kisa da aka yanke wa wasu yan leken asiri bayan kama su da laifi, tace bata amince da wannan mataki ba kuma tsoma baki ne a harkokin cikin gidanta. Ma’aikatar harkokin wajen kasar yamen...
    Jagoran juyin musulunci na kar iran Ayatullah sayyid Ali Khamna’i ya bayyana cewa kasar Amurka bata ji da dadi ba a yakin kwanaki 12 da ta kaddamar a kan kasar iran a watan yuni, duk da amafani da ta yi da manyan makaman yaki na zamani da suka hada da jiragen yaki da kuma makaman...
    Gammayar ministocin harokin wajen kungiyar tarayyar Turai sun fitar da wata sanarwa da aciki suka soki hare haren da yahudawa yan share wuri zauna suke kai wa falasdinawa a gabar yammacin kogin Jodan da isra’ila ta mamaye kuma yake kara ci gaba fiye da kowanne lokaci a baya, Sanarwar ta fito ne daga minsitocin kasashen...
    Sanatan Borno ta Kudu, Ali Ndume, ya ce Najeriya na iya ajiye biliyoyin naira a duk shekara idan aka rungumi tsarin majalisa ta wucin gadi. Yayin da yake magana a gidan talabijin na Channels ranar Alhamis, Ndume ya ce kuɗin da ake kashewa wajen kula da Majalisar Dokoki a tsarin zama kodayaushe ba zai dore...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Sheikh Dahiru Usman Bauchi, fitaccen malamin addinin Musulunci, masanin tafsiri, kuma jagoran darikar Tijjaniyya, shahararre ne saboda iliminsa mai zurfi da tasirin da ya yi a fagen addini da tarbiyya a Najeriya da ma ƙasashen Yammacin Afirka.   Sheikh Dahiru Bauci ya shafe sama da shekaru saba’in yana...
    Ministan yakin Isra’ila ya yi barazanar kai wa kasar Lebanon hari gadan-gadan, inda ya bukaci kungiyar Hizbullah ta kwace damarar makamai. Ministan yakin Isra’ila, Isra’ila Katz, ya yi gargadin cewa Tel Aviv a shirye take ta kaddamar da wani sabon yaki kan kasar Labanon matukar kungiyar gwagwarmayar Hizbullah ta ki mika makamanta zuwa  karshen shekarar...
    Daga Sani Sulaiman   Gwamnan Jihar Taraba, Dr. Agbu Kefas, ya yi jimami kan rasuwar fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, wanda ya rasu a ranar Alhamis 27 ga watan Nuwamban 2025, yana da shekaru 102. Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai bai wa gwamnan shawara na musamman kan...
    Ma’aikatar kiwon lafiya a Gaza ta sanar da karbar gawawwakin shahidai 15 a jiya Laraba a karkashin yarjejeniyar musayar fursunoni, da kungiyar agaji ta “Red Cross” ta shiga tsakani. Sanarwar ma’aikatar kiwon lafiyar ta Palasdinu ta kuma ce, daga lokacin da aka fara musayar zuwa yanzu,adadin gawawwakin shahidan da su ka karba sun kai 345,...
    Daya daga cikin ‘ya’yan babban malamin addinin musulunci a Najeriya Sayyid Ali Dhahiru Usman Bauchi ne ya tabbatar wa da jaridar “Daily Trust” rasuwar malamin. Sayyadi Ali ya furta cewa: ” Tabbas Shehi ya koma ga mahaliccinsa, mu duka daga Allah muke, kuma zuwa gare shi za mu koma.” Haka nan kuma ya kara da...
    Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna, ta gano harsasai 210 da aka jefar a kan babbar hanyar Zariya zuwa Funtuwa, a unguwar Dogo Itace da ke Samaru, Zariya. Lamarin ya faru ne lokacin da DPO na Samaru tare da tawagarsa suke sintiri a kan hanyar. Allah Ya yi wa Sheikh Dahiru Bauchi rasuwa Juyin mulki ya...
    Fitaccen malamin addinin Musulunci nan daga Jihar Bauchi, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ya rasu. Ɗansa, Sayyadi Ali Dahiru Usman Bauchi ne,  ya tabbatar wa Aminiya rasuwar malamin. Juyin mulki ya rutsa da Jonathan a Guinea-Bissau Ɗan bindiga ya harbe sojoji 2 a fadar shugaban Amurka Ya ce sun karɓi wannan ƙaddara tare da gode wa...
    Bayan an zabi kasar Iran a matsayin mamba a kwamitin zartarwa na hukumar yaki da makaman guba ta duniya, wato ‘ the Chemical Weapons Convention (CWC)’ da kuriun jimillar yan majalisar, ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa Iran zata yi amfani da damar da ta samu na bin hakkin mutanen kasar...
    Wata cibiyar bincike mai suna “Frensic Architecture’ ta bada sanarwan cewa, HKI tana fakewa da tsagaita budewa juna wuta a Gaza a matsayin dama ta sake shata kan iyakoki a zirin gaza. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ta nakalto cibiyar tana cewa a halin yanzu HKI ta maida ‘koren layin da Trump ya...
    Ma’aikatar Ma’adinai da wutan lantarki a yankin Kurdistan na kasar Iraki ta bada sanarwan cewa an dakatar da tura iskar gas zuwa cibiyoyin samar da wutan lantarki a yankin saboda hare-haren da aka kai kan wata cibiyar hakar iskar gas a yankin. Tashar talabijan ta Almayadeentv ta kasar Lebanon ta bayyana cewa wani jirgin yaki...
    Daga Isma’il Adamu  Gwamna Dikko Radda na Jihar Katsina ya sanya hannu kan kudirin kasafin kudin jihar na 2026 na Naira Biliyan 897, makonni uku bayan gabatar da shi a gaban majalisar dokokin jihar. Yayin rattaba hannu a Fadar Gwamnati da ke Katsina, a gaban ‘yan majalisar dokokin jihar, gwamnan ya jinjinawa majalisar bisa gaggawar amincewa...
    Daga Bello Wakili Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ayyana dokar ta-baci kan harkar tsaro a duk fadin kasar, sakamakon karuwar kalubalen tsaro da ake fuskanta. Shugaban ya ce za a dauki sabbin jami’an tsaro nan ba da jimawa ba, wadanda suka hada da na sojiin, ‘yan sanda da sauran hukumomin tsaro — domin karfafa...
    Rahotanni sun bayyana cewa kididdigar da ma’aikatar harkokin wajen yankin falasdinu ta fitar ya nuna cewa sojojin Isra’ila sun kashe akalla yan mata 33000 a ci gaba da yakin kare dangi da take yi kan alummar Gaza. Ma’aikatar fa fitar da wannan sanarwar ce a wajen taron ranar kawo karshen hare-hare kan mata ta duniya...
    Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya dawo Abuja daga birnin Luanda na Angola, inda ya halarci taron AU–EU karo na 7 a madadin Shugaba Bola Tinubu. Ya wakilci shugaban kasa a taron G20 na 2025 da aka yi a Johannesburg, Afirka Ta Kudu. A Angola, Shettima ya karanta sakon Shugaba Tinubu wanda ya sake...
    Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna, ta bayyana sabbin nasarorin da ta samu wajen yaƙi da laifuka a jihar, ta hanyar holen mutum 34 da ta kama da aikata laifuka daban-daban. Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, Rabi’u Muhammad, ya ce wannan ci gaba ya samu ne saboda sabbin dabarun aiki da kuma bayanan sirri da aka samu...