’Yan sanda sun ceto tsohuwa mai shekara 80 a hannun ’yan bindiga a Jigawa
Published: 18th, May 2025 GMT
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Jigawa, ta ceto wata tsohuwa mai shekaru 80 da aka sace a Jihar Kano, bayan wani samame da suka kai Ƙaramar Hukumar Garki.
A yayin samamen, sun kashe mutane biyar da ake zargi masu garkuwa da mutane ne, sannan sun kama wasu biyar.
Yadda ’ya’yan shugabanni ke musu yaƙi da ’yan adawa Abba ya dakatar da hadiminsa saboda furta kalamai a kan KwankwasoRahoton ya ce samamen ya faru ne da misalin ƙarfe 1:30 na daren ranar 16 ga watan Mayu, 2025 bayan samun sahihan bayanan sirri.
Waɗanda suka sace tsohuwar, Hajiya Hajara daga Ƙaramar Hukumar Minjibir, a Jihar Kano, su 12 ne ɗauke da bindigogi, kuma sun zo ne a kan babura.
Rundunar ta haɗa kai da jami’an ’yan sanda daga Gagarawa, Gumel, Garki, da Sule-Tankarkar tare da ‘yan banga da mafarauta, ƙarƙashin jagorancin ACP Bala Umar, kwamandan ’yan sandan yankin Gumel.
Sun kai farmaki maɓoyar ’yan ta’addan da ke Wadi Fulani, GGW Tagwayen Fage, Wusada Fulani da Katoro Fulani duka a Garki.
A nan ne suka kashe mutum biyar da ake zargi, sannan suka kama wasu biyar ciki har da sarkin Fulanin Katoro mai suna Yahaya mai shekara 35.
Sun ceto Hajiya Hajara cikin ƙoshin lafiya, sannan sun ƙwato bindigogi guda uku (AK-47 biyu da LAR daya), harsashi 14, babura biyu da wayoyin hannu biyu.
Gawarwakin waɗanda aka kashe an kai su asibitin Gumel don gudanar da bincike, kuma babu jami’in tsaron da ya rasa ransa.
Majiyoyi sun ce ba a biya kuɗin fansa ba kafin ceto tsohuwar.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Bindiga Yan Sanda Jigawa Tsohuwa
এছাড়াও পড়ুন:
Iran: Aiwatarda Yarjeniyar Zaman Lafiya Tsakanin Armenia Da Arzerbaijan Zai Tabbatar Da Zaman Lafiya A Tsakanin Kasashen Biyu
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa aiwatar da yarjeniyar zaman zaman lafiya wadanda aka cimma tsakanin kasashen Armenia da kuma Azerbaijan da gaggawa zai tabbatar da zaman lafiya mai dorewa a tsakanin kasashen biyu.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ta nakalto Aragchi yana fadar haka a lokacin ganawarsa da sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Armenia, Armen Grigoryan wanda yake ziyarar aiki a nan Tehran a yau Asabar.
Ministan ya kara da cewa JMI zata tabbatar da cewa an aiwatar da sulhu tsakanin kasashen biyu da gaggawa saboda tana dasawa da kasashen biyu makobta gareta.
A cikin watan Maris da ya gabata ne kasashen Armenia da Arzerbaijan suka amince a rubuta yarjeniyar sulhu a tsakaninsu a tsakaninsu don kawo karshen rikici a tsakaninsu wanda ya kusan shekaru 40 suna fafatawa a tsakaninsu.
Kasashen biyu sun yi yaki na karshe a tsakaninsu kan mallakar yankin Karabakh a shekara ta 2020 haka ma sun tabka yake-yake a kan malakar yankin a shekaru 1990 da bayansa, har zuwa lokacinda Azerbaijan ta kwace yankin a cikin sa,o,ii a yankin 2020. Sannan Armenia ta sallama mata yankin. Kasashen duniya dai sun amince da cewa yankin na Azerbaijan ne.