Mashawarci tsohon shugaban Ƙasa kan Sufuri Jiragen Sama ya rasu
Published: 16th, May 2025 GMT
Kyaftin Shehu Iyali, tsohon mataimaki na musamman kan sufurin jiragen sama a zamanin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo da Goodluck Jonathan, ya rasu.
Kyaftin Shehu Iyal ya rasu ne a ranar Alhamis bayan ya yi fama da jinya.
Kafin rasuwarsa shi ne shugaban kamfani jiragen sama mai suna Afri Air.
Marigayin yakasance jigo a harkar sufurin jiragen sama a Najeriya kuma ya tuka shugabannin ƙasa.
A shekarar 1977 Kyafin Shehu Iyal ya kammala karatun digiri ɗinsa a Jami’ar Ahmadu Bello kafin daga bisani ya shiga Kwalejin Koyon Tuƙin Jiragen Sama (NCAT) da ke Zariya.
Kafin rasuwarsa ya riƙe muƙamai da dama a fannin sufurin jiragen sama har da Hukumar Aikin Hajji ta Ƙasa a matsayin mai kula da sashin zirga-zirgar jirage na hukumar.
Bayanai daga iyalan marigayin na nuni da cewa za ayi jana’izar Kyaftin Shehu Iyal a yau Juma’a da yamma a unguwar Ƙwarbai cikin birnin Zariya.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Jiragen sama Shehu Iyali jiragen sama
এছাড়াও পড়ুন:
Dalibai 29 Suka Rasu A Turmutsitsin Tserewa Ga Fashewar Taransifoma A Jamhuriyar Afirka Ta Tsakiya
Dalibai 29 ne suka rasa rayukansu sakamakon turmutsitsin a Jamhuriyar Afrika ta tsakiya yayin tserewa fashewar taransifoma
Akalla dalibai 29 ne suka mutu a birnin Bangui na kasar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya a wani turmutsutsu sakamakon fashewar tiranfomar lantarki a lokacin jarrabawar sakandare, a cewar ma’aikatar lafiya ta Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.
Wata takarda daga ma’aikatar lafiya ta ce: “Mutane 29 ne suka rasa rayukansu bayan an kai su asibitocin birnin Bangui.”
Ba a samu ingantattun bayanan yawan wadanda suka mutu ba har zuwa yammacin ranar Larabar da ta gabata, a lokacin da fashewar ta faru, sama da dalibai 5,300 ne ke zana jarrabawar kwana na biyu na jarabawar sakandare.