Mutum ɗaya ya rasu a rikicin manoma da makiyaya a Yobe
Published: 16th, May 2025 GMT
Wani rikici da ya ɓarke tsakanin manoma da makiyaya a ƙauyen Chikuriwa da ke Ƙaramar Hukumar Nangere a Jihar Yobe, ya yi sanadin mutuwar mutum ɗaya tare da jikkata wasu.
Rahotanni sun nuna cewa rikicin ya faru ne da yammacin ranar Litinin, 13 ga watan Mayu, 2025 bayan da wani makiyayi ya shigar da shanunsa cikin gonar wani manomi, abin da ya tayar da rikici.
A lokacin da rigimar ta ɓarke, an harbi wani manomi mai suna Babayo Maina Osi da kibiya a goshinsa, wanda hakan ya jikkata shi.
Wata majiya daga ƙauyen ta ce rikicin ya ƙazanta sosai har ya rikiɗe zuwa faɗa tsakanin manoma da makiyaya.
A lokacin wannan faɗa ne aka harbi wani mutum mai suna Usman Mohammed, mai shekara 35 da kibiya, wanda daga bisani ya rasu a Babban Asibitin Nangere.
Jami’an tsaro sun isa wajen domin daƙile rikicin da kuma hana ya ƙara rincaɓewa.
Rahoton ya bayyana cewa an ƙwato shanu biyu, awaki 29 da raguna daga hannun manoman da ake zargi sun ƙwace daga hannun makiyaya.
A yanzu haka, an gayyaci shugabannin ɓangarorin biyu domin tattaunawa da kuma tabbatar da cewa irin wannan rikici bai sake faruwa ba a nan gaba.
Duk ƙoƙarin da wakilin Aminiya ya yi don jin ta bakin kakakin ‘yan sandan jihar, DSP Dungus Abdulkareem, ya ci tura, domin bai daga wayarsa ba.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Makiyaya
এছাড়াও পড়ুন:
Majalisar Dattawa ta buƙaci a tura ƙarin sojoji zuwa Borno da Yobe
Majalisar Dattawa ta buƙaci rundunar sojin Nijeriya ta tura ƙarin sojoji da manyan makaman yaƙi zuwa jihohin Borno da Yobe, bayan farfaɗowar hare-haren ‘yan ta’adda na Boko Haram a jihohin.
Ƙudurin ya biyo bayan ƙarin hare-haren ‘yan ta’addan ne a arewa maso gabashin ƙasar, ciki har da kashe kimanin sojoji goma a garin Marte da ke ƙaramar hukumar Monguno ranar Litinin, 12 ga watan Mayu, da kuma wani harin da suka kai Gajiram na Ƙaramar Hukumar Nganzai, da sanyin safiyar ranar Talata.
Zaɓen 1993: IBB ya wallafa ba daidai ba a littafinsa — Sule Lamiɗo Trump ya janye takunkumin da Amurka ta ƙaƙaba wa SyriaA wani ƙuduri da mai tsawatarwa majalisar, Sanata Tahir Munguno, ya gabatar a ranar Talata, ‘yan majalisar sun ce duk da cewa a baya kashi biyu cikin uku na ƙananan hukumomin Jihar Borno sun kasance ƙarƙashin ikon ‘yan Boko Haram — haɗin kai tsakanin sojoji da ‘yan sa-kai ya taimaka wajen ƙwato ƙananan hukumomin.
Amman zaman lafiyan da aka samu, ya sa hedikwatar yaƙi da ta’addancin ta koma Arewa maso yammacin ƙasar, inda sojin ƙasar ke yaƙi da ‘yan fashi da masu garkuwa da mutane.
Yayin da yake nuna damuwa game da yadda ‘yan ta’addan ke sauya dabarun yaƙin su, Monguno ya bayyana yadda ƙungiyar ke amfani da na’urorin zamani ciki har da jirage marasa matuƙa da kuma ƙarin amfani da abubuwan fashewa da suka ƙera da kansu, lamarin da ya janyo mace-macen fararen hula da sojoji da kuma katse harkokin sufuri.
Majalisar Dattawan, ta yi kira ga shugabannin sojin ƙasar su tura isassun sojoji zuwa arewa maso gabashin ƙasar su kuma tabbatar da cewa an ba su na’urorin zamani domin su daƙile sabuwar barazanar.
Kazalika, majalisar ta nemi kwamitinta kan sojin ƙasa da na sama ya sa ido tare da tabbatar da cewa sojojin sun bi umarnin.