Isra’ila ta yi barazanar kashe shugaban kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen
Published: 17th, May 2025 GMT
Gwamnatin Isra’ila ta yi barazanar kashe jagoran kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen, Abdul-Malik al-Houthi, idan har Sana’a ta ci gaba da kai hare-hare da makami mai linzami kan Isra’ilar don goyon bayan Falasdinu.
Ministan harkokin soji na gwamnatin, Isra’ila Katz ya ce idan har Yemen ta ci gaba da ayyukanta “za su sha azaba mai radadi.
Katz ya ce kisan da gwamnatin za ta wa al-Houthi zai yi kama da kisan gilla kan “Deif da Sinwars a Gaza.”
Ministan na Isra’ila yana magana ne a kan tsohon kwamandan kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas da ke Zirin Gaza, Mohammed Deif, wanda gwamnatin kasar ta sanar da kashe shi a watan Janairu.
Katz ya kuma ce yuwuwar nasarar kisan gillar da gwamnati ta yi kan al-Houthi zai iya tunawa da kisan gillar da Tel Aviv ta yi wa tsohon babban sakataren kungiyar Hizbullah Sayyed Hassan Nasrallah, da kuma kisan Ismail Haniyeh, wanda shi ne shugaban ofishin siyasa na Hamas da Yahya Sinwar.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Jiragen Yakin HKI Sun Kai Hare-hare A Kasar Yemen
Majiyar tsaron kasar Yemen ta ce; Jragen HKI sun kai wasu jerin hare-hare akan tasoshin jiragen ruwa na Hudaidah, da Salif a gudunar Hudaidah dake yammacin kasar.
Majiyar tsaron ta Yemen ta ci gaba da cewa; An yi amfani da bama-bamai masu yawa da aka jefa akan wadannan tasoshin jiragen ruwan,kuma fiye da jiragen sama na yaki 10 ne su ka kai harin.
Wata majiyar HKI ta fada wa tashar talabijin din “Kan” cewa; manufar kai wadannan hare-haren su ne kakaba wa Yemen takunkumi ta ruwa.”
A ranar 6 ga watan nan na Mayu da ake ciki, ma HKI ta kai wani harin akan filin saukar jiragen saman a Sana’a tare da kona jirgen saman kasar da dama.
Ita dai kungiyar “Ansarullah” ta kasar Yemen ta sha bayyana cewa ba za ta daina kai wa HKI hare-hare ba har sai idan ta daina kai wa Gaza hari.
Jagoran kungiyar ta “Ansarullah” Sayyid Abdulmalik Al-Husi ya bayyana cewa; Matsayar da Yemen ta dauka na taimakawa Gaza, ba zai fuskanci tawaya ba ko ya ja da baya, zai ci gaba.