Fiye Da Falasdinawa 300 Ne Su Ka Yi Shahada Da Jikkata Daga Safiyar Yau Juma’a
Published: 16th, May 2025 GMT
HKI tana ci gaba da yi wa Falasdinawa kisan kiyashi a Gaza wanda ya ci rayukan Falasdiniwa kusan 300 da su ka hada kananan yara da mata.
Tashar talabijin din ‘almayadin’ ta ambaci cewa;Tun da asubahin yau ne dai sojojin mamayar su ka fara kai wadannan munanan hare-haren wanda ba komai ba ne, sai kisan kiyashi akan Falasdinawada suke fama da matsananciyar yunwa saboda rashin abinci.
Bugu da kari, mafi yawancin Falasdinawan da HKI take kai wa hare-haren suna rayuwa ne a cikin hemomi bayan da ta rushe musu gidajensu.
Ma’aikatar kiwon lafiya ta Falasdinu ta sanar a cewa; A cikin sa’oi 24 da su ka gabata, adadin wadanda su ka yi shahada sun kai 109, kuma tuni an fito da gawawwakinsu daga gine-gine da hemomin da su ka fada a kansu, yayin da wasu 216 su ka jikkata.
A jiya kadai, adadin Falasdinawan da su ka yi shahada sun haura 100. Baya ga wadanda su ka yi shahadar, da akwai kuma wani adadi na falasdinawa da ya kai 100 da sun bace.
Daga 7 ga watan Oktoba na 2023 zuwa yanzu, adadin Falasdinawan da su ka yi shahada sun kai dubu 53, da 119, sai kuma wadanda su ka jikkata da sun kai 120,114.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Iran Ta Bawo Mayakan Huthi Fasahar Kera Makamai Masu Linzami Daga Cikin Ruwa
JMI ta bawa kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen makamai masu linzami wadanda ake iya cillasu daga cikin tekuna mai suna Ghadr.
Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya ce makamai mai linzami samfurin Ghadir wanda ake iya cilla shi daga cikin teku ya shiga hannun sojojin kasar Yemen sannan bisa bayanan wasu kasashen yamma hakan wani hatsari ne ga kasashen Amurka da kawayenta a yankin, musamman HKI.
Makamin wanda ake iya cillashi daga tekun red sea yana yin barna mai yawa ga makaman makiya. Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran bata yi wani karin bayani dangane da wannan labarin ba, majiyar ofishin daraktan tsaron kasa na Amurka ta bayyana cewa, JMI tana ta fi ko wace kasa a yankin mallakan makamai masu linzami kuma sune a gaba a duniya wajen kera jiragen yaki wadanda ake sarrafasu daga Nesa.