2025-05-20@21:42:50 GMT
إجمالي نتائج البحث: 532

«Mawaƙiya»:

    Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da fitar da kudi sama da naira miliyan 279 ga  Ƙungiyar Direbobin Motocin Haya ta Najeriya (NURTW reshen jihar Jigawa karkashin shirinta na tallafawa masu sana’o’i. Kwamishinan Muhalli, Sabunta Makamashi da Sauyin Yanayi na jihar, Dr. Nura Ibrahim ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai bayan...
    Da safiyar yau Talata mazauna yankin “al-Daraj’dake Gaza su ka  farka daga cikin sanadiyyar  harin da jiragen yakin HKI su ka kai wa makarantar ” Musa Bin Nusair” dake karkashin hukumar agaji ta UNRWA” wacce take kunshe da daruruwan ‘yan hijira. Dama dai wannan ba shi ne karon farko da wannan yankin yake fuskantar hare-hare...
    Wani harin kwanton bauna da rundunar sojin al-Qassam suka kai kan sojojin mamayar Isra’ila a Beit Lahiya ya yi sanadiyar halaka tare da jikkatan sojojin mamaya masu yawa Rundunar Izzuddeen al-Qassam bangaren sojin kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas, ta sanar da cewa: Mayakanta sun kai wani kazamin harin kwantan bauna a yankin al-Atatra da ke...
    An dauke kashin farko na maniyyata 550 daga jihar jigawa zuwa Saudiyya a filin jirgin Nuhu Muhammadu Sunusi domin gudanar da aikin hajjin shekarar 2025.   Babban Daraktan hukumar Alhaji Ahmed Umar Labbo ya bayyana hakan jim kadan bayan tashinsu zuwa kasa mai tsarki.   Ya bayyana cewa maniyyatan sun fito ne daga kananan hukumomi...
    Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya bayyana cewa, tattaunawar dake tsakanin Iran da Amurka za ta iya taka rawar gani wajen samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin. A yayin da yake zantawa da manema labarai a gefen dandalin tattaunawa na Tehran, Araghchi ya ce kasashen yankin suna goyon bayan tattaunawar da...
    Shugaban Amurka Donald Trump ya ce yayi tattaunawa ta wayar tarho mai aramashi da takwaransa na kasar Rasha Vladimir Putin, inda suka tattauna kan batutuwa da dama ciki har da yunkurin fara tattaunawar tsagaita bude wuta nan da nan tsakanin Rasha da Ukraine. Kamfanin dillancin labaran Rasha na RIA shi ma ya ambato, shugaban Kremlin...
    Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka, sharhin bayan labarummu zai yi magana dangane da taron tattaunawa ta Tehran wanda aka bude a ranar Lahadi 18 ga watan mayu a nan Tehran. A ranar Lahadi 18 ga watan Mayu da muke ciki ne aka bude taron tattaunawa da ta Tehran ta farko a nan Iran,...
    Ma’aikatar lafiya ta jihar Kano ta ce ta samu gagarumar nasara wajen shiga sahun kasashen duniya a ranar cutar hawan jini ta duniya. Kwamishinan lafiya Dr Abubakar Labaran ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a taron tunawa da ranar hawan jini ta duniya, wanda aka gudanar a Kano.  ...
    Manyan jami’ai daga kasashe da dama da ke halartar taron tattaunawa na Tehran sun yi kira da a tattauna domin tunkarar manyan al’amura a yankin. Manyan jami’ai daga kasashe 53 da suka hada da ministoci da masana da ne ke halartar taron na kwanaki biyu. Ministan harkokin wajen Oman Badr bin Hamad Al Busaidi ya...
    Wani jami’in Hukumar Sibil Difens, Abubakar Abdulkadir Mayos, ya mayar da kuɗin wata maniyyaciya Naira 822,038 da suka ɓata a sansanin alhazai na Yola da ke Jihar Adamawa. Kuɗin da aka samu sun haɗa da dala $505 da Riyal 30 na ƙasar Saudiyya, wanda ya kai kimanin Naira 822,038. An kama ƙasurgumin ɗan bindiga yayin...
    Rundunar ’Yan Sandan Jihar Jigawa, ta ceto wata tsohuwa mai shekaru 80 da aka sace a Jihar Kano, bayan wani samame da suka kai Ƙaramar Hukumar Garki. A yayin samamen, sun kashe mutane biyar da ake zargi masu garkuwa da mutane ne, sannan sun kama wasu biyar. Yadda ’ya’yan shugabanni ke musu yaƙi da ’yan...
    Yanayin da ’ya’yan shugabanni suke yin fito-na-fito da masu ƙalubalanta ko yin tambaya a kan abubuwa ko matakan da iyayensu suka ɗauka, sai ƙara muni yake yi a fagen siyasar Najeriya. Abin da da ke ƙara zama ruwan dare a Najeriya shi ne yadda a duk lokacin da mutane suka tambayi shugabanni ko suka ƙalubalanci...
    Yanayin da ’ya’yan shugabanni suke yin fito-na-fito da masu ƙalubalanta ko yin tambaya a kan abubuwa ko matakan da iyayensu suka ɗauka, sai ƙara muni yake yi a fagen siyasar Najeriya. Abin da da ke ƙara zama ruwan dare a Najeriya shi ne yadda a duk lokacin da mutane suka tambayi shugabanni ko suka ƙalubalanci...
    Dare da aka zubar da jini mafi muni a Gaza: Sama da Falasdinawa 80 ne suka yi shahada a sassa daban-daban na Zirin Sojojin mamayar Isra’ila suna ci gaba da aiwatar da kisan kiyashi kan fararen hula a yankuna daban-daban na zirin Gaza, inda suka yi sanadiyyar shahadan sama da Falasdinawa 80, kuma mafi yawansu...
    Sauran sassan da aka gyara da kuma saka kayan aiki sun haɗa da sashen Kulawa da Mata (ANC), ɗakin tiyata, ɗakin X-ray, sabon ginin hukunta asibiti, masallaci, gidan Babban Daraktan Lafiya (gidaje mai ɗakuna 3), da kuma sashen kula da yara, da dai sauransu.   A yayin jawabinsa a wajen ƙaddamar da aikin, Gwamna Lawal...
    Bayan da wani matashi ɗan shekara 33 ɗan kasar Japan mai suna Honkon ya yi tarin kuɗi na tsawon shekaru 10 don siyan motar da yake mafarki — na wata sabuwar mota ƙirar Ferrari 458 Spider — sai ya zauna yana kallon yadda motar take ƙonewa cikin sa’a ɗaya da tuƙa ta a karon farko....
    Farfesa Radda ya ce an cire ‘yan takara masu yawa da suka cencenta saboda rashin adalci, duba da cewa sun cika dukkan sharadan da ya dace wajen neman mukamin shugabancin makarantar.  Haka kuma, Farfesa Bichi ya ce zargin da ake masa ba gaskiya ba ne, yana mai cewa an gudanar da zaben cikin gaskiya da...
    Farfesa Radda ya ce an cire ‘yan takara masu yawa da suka cencenta saboda rashin adalci, duba da cewa sun cika dukkan sharadan da ya dace wajen neman mukamin shugabancin makarantar.  Haka kuma, Farfesa Bichi ya ce zargin da ake masa ba gaskiya ba ne, yana mai cewa an gudanar da zaben cikin gaskiya da...
    Jagoran juyin juya halin musulunci a nan Iran Imam Sayyid Aliyul Khaminae ya yi watsi da wasu kalaman shugaban kasar Amurka Donal Trump a ziyar da ya kammala a wasu kasashen larabawa na yankin Tekun farisa, ya kuma bayyana wasu kalamansa a matsayin kungiya ga kansa da kuma mutanen Amurka. Har’ila yau Jagoran ya kara...
    Tsohon fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ya ce: Fira ministan Netanyahu ya yi sakaci da rayuwar yahudawa a cikin aikinsa don haka hambarar da gwamnatinsa ita ce mafita Tsohon Fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila Ehud Barak ya yi kira da a hambarar da Benjamin Netanyahu da gwamnatinsa, yana mai zarginsa da yin sakaci...
    A lokacin da yake jawabi a wurin ƙaddamarwar, Gwamna Lawal ya bayyana cewa da hawansa mulki a watan Mayun 2023, ya ci karo da tsarin kiwon lafiya da ya tabarbare saboda rashin kulawa. Ya ce, “Gwamnatinmu, ƙarƙashin ginshiƙan shirye-shiryen ceto, nan da nan ta fara tantance abubuwan da asibitoci ke buƙata, inda sakamakon ya zama...
    Majiyar kiwon lafiya a zirin Gaza ta bayyana cewa daga safiyar jiya Alhamis zuwa karfe 12 dare HKI ta kashe falasdinawa 143 tare da amfani da jiragen saman yaki tankunan yaki ta kasa da kuma jiragen ruwa yaki. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa bayan tsakiyar dare ma sojojin yahudawan sun...
    Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Sun yi imani da tattaunawa da zaman lafiya ba tare da mika wuya ga barazana ba A yayin ganawarsa da masu fafutukar siyasa da zamantakewa a lardin Kermanshah da ke yammacin kasar Iran a jiya Alhamis, shugaban na Iran Masoud Perzeshkiyon ya ce za a gudanar da shawarwari kan...
    Ministan Harkokin Wajen Iran ya jaddada cewa: Ƙarfin tsaron Iran da makamanta masu linzami suna ba su ƙarfin gwiwa Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya bayyana cewa, da a ce Amurka za ta iya lalata cibiyoyin makamashin nukiliyar Iran, da ba za ta shiga zaman tattaunawa ba, yana mai jaddada cewa: Iran ta dogara...
    Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta shirya wata zanga-zanga da Falasdinawa ke jaddada cewa: babu halacci ga ‘yan mamaya kuma al’ummar Falastinu za su ci gaba da gwagwarmaya Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta jaddada cewa: Haramtacciyar kasar Isra’ila ba ta da halacci ko kuma wani ikon mallakar wani yanki na Falasdinu da ta mamaye,...
    A cewarsa, yanzu haka ana sayar da shinkafa kimanin naira 60,000 kan kowane buhu, buhun fulawa kan naira 55,000, da masara a kan Naira 30,000.   Ya yi bayanin cewa, kafin zartar da umarnin rage harajin kwastam kan kayayyakin abinci, ‘yan kasuwa kan sayen kayan abinci tun yana gona su boye, sannan su sayar da...
    Tashar talabijin din almayadin ta watsa labarin dake cewa, daga safiyar yau Alhamis zuwa yanzu, adadin Falasdinawan da su ka yi shahada sun haura 40,mafi yawancinsu daga yankin Khan-Yunus. Tun da safiyar yau Alhamis ne dai sojojin HKI su ka fara kai hare-hare a yankuna mabanbanta na Gaza da su ka hada da Khan-Yunus. ‘Yan...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Manyan Makarantu (JAMB) ta yi amai ta lashe. Bayan ta musanta duk zarge-zargen da aka yi cewa tana da hannu a rashin kyawun sakamakon jarabawar da ta shirya, shugaban hukumar ya fito ya amsa laifin. Yayin wata ganawa da ya yi da manema labarai,...
    Ya ƙaryata zargin cewa an ci zarafin waɗanda ake zargin, yana mai cewa an bi doka da ƙa’idoji na ƙasa da na duniya a duk matakan binciken da aka gudanar. Ya ƙara da cewa bidiyon da ke yawo a kafafen sada zumunta an shirya shi ne domin yaudarar jama’a da neman tausayi tare da ɓata...
    A hare-haren wuce gona da iri da sojojin mamayar Isra’ila kai kan yankunan Zirin Gaza a cikin dare daya sun kashe Falasdinawa 51 Adadin wadanda suka yi shahada sakamakon hare-haren wuce gona da iri da sojojin gwamnatin Isra’ila suka kai kan arewaci da kudancin zirin Gaza tun daga tsakiyar daren Laraba ya kai Falasdinawa 51,...
    A jawabinsa na maraba, sakataren zartaswa na asusun tallafawa ‘yansandan Nijeriya, Mista Mohammed Sheidu, ya gode wa shugaban kasa Bola Tinubu bisa jajircewarsa, sadaukar da kai ga bangaren tsaro, kawo sauyi, karfafa cibiyoyi, da goyon bayan da yake bai wa asusun tallafawa ‘yansandan Nijeriya wanda ya yi tasiri sosai, har ya iya gina ofishin ‘yansanda...
    Masana sun ce wannan mataki zai iya sauya tsarin kasuwanci da ci gaban fasaha a duniya, musamman a yankin Larabawa. Bayan kammala taron a Saudiyya, ana sa ran zai wuce Qatar da kuma Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE) domin ci gaba da tattaunawa da shugabannin yankin kan batutuwan tsaro da haɗin gwiwar tattalin arziƙi. Yarjejeniyar ta...
    Majalisar Dattawa ta buƙaci rundunar sojin Nijeriya ta tura ƙarin sojoji da manyan makaman yaƙi zuwa jihohin Borno da Yobe, bayan farfaɗowar hare-haren ‘yan ta’adda na Boko Haram a jihohin. Ƙudurin ya biyo bayan ƙarin hare-haren ‘yan ta’addan ne a arewa maso gabashin ƙasar, ciki har da kashe kimanin sojoji goma a garin Marte da...
    Majalisar dattawa a ranar Talata ta yi kira ga rundunar sojin Nijeriya da ta gaggauta tura jami’anta da sabbin kayan yaki na zamani zuwa jihohin Borno da Yobe sakamakon sabon hare-haren da mayakan Boko Haram suka kai a yankin. An yi wannan kiran ne biyo bayan sabbin hare-haren ta’addanci a yankin Arewa maso Gabas, ciki...
    A yau Talata ne shugaban kasar Amurka Donald Trump ya isa kasar Saudiyya domin fara ziyarar aiki a karon farko tun da ya zama shugaban kasa. Baya ga kasar Saudiyya shugaban kasar ta Amurka zai kuma kai Ziyara zuwa kasashen Qatar da Hadaddiyar Daular Larabawa da zummar bunkasa alaka  da larabawan yankin tekun Pasha kamar...
    Gwamnatin kasar Iran ta yi kakkausar suka ga gwamnatin HKI kan hare-haren da ta kaiwa wani sansanin yan gudun hijira a gaza inda ta kashe ko takai mutanen da dama ga shahada, daga ciki har da mata da yara jarirai. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran...
    Kasar Sin ta harba wani rukunin taurarin dan adam daga cibiyar harba tauraron na Taiyuan dake lardin Shanxi na arewacin kasar. An harba taurarin ne jiya Lahadi da misalin karfe 9:27pm agogon Beijing, bisa amfani da samfurin rokar Long March-6 da aka yi wa ‘yan gyare-gyare. A cewar cibiyar ta Taiyuan, rukunin taurarin mai suna...
    Mataimakin firaminsitan kasar Sin He Lifeng, ya gana da babbar jami’ar hukumar kula da cinikayya ta duniya (WTO) Ngozi Okonjo-Iweala, a daren jiya Lahadi a Geneva. Yayin ganawar tasu, He ya ce, kamata ya yi mabambantan bangarori su daidaita bambancin ra’ayi da takaddama bisa shawarwari, kuma cikin adalci karkashin ka’idar WTO. Haka kuma, a hada...
    Sojojin mamayar Isra’ila sun aiwatar da mummunan kisan kiyashi a garin Jabaliya, tare da janyo shahada da jikkatan wasu a Khan Yunis A rana ta 56 da sake komawa yaki ta hanyar kai hare-haren wuce gona da iri kan Gaza, sojojin mamayar Isra’ila sun ci gaba da yin luguden wuta kan wasu wuraren zama, da...
    Yayin da a wannan Litinin ake bikin ranar jami’an jinya ta Duniya ta shekarar 2025, hukumar lafiya ta Duniya WHO ta ce akwai kashi 42 cikin 100 na ma’aikatan jinya a Afirka, dake cike da burin ficewa daga nahiyar saboda rashin cikakkiyar kulawa da kuma albashi mara tsoka. A jawabin da ya gabatar akan ranar...
     Kungiyar Kurdawan Turkiya PKK ta sanar da cewa za ta ajiye makamanta ta kuma rusa kanta. Kamfanin dillancin labarum “Furat” mai kusanci da kungiyar ta PKK, ya nakalto cewa; Kungiyar ta yanke zartar da wannan matakin ne a yayin taron da ta yi kaso na 12 da ta yi kwanaki kadan da su ka gabata....
    Kungiyar Hamas wacce take iko da yankin Gaza, ta bada sanarwan cewa a shirye take ta saki fursina mai suna Edan Alexander wanda yake da jinsiyar Amurka da HKI don bude kofa ga tattaunawar tsagaaita wuta a gaza da kuma bude kofar rafa don samar da kayakin abicni a gaza. Kamfanin dillancin labaran IP na...
    Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya ba da shawarar yin  tattaunawa “kai tsaye” ba tare da sharadi ba” tsakanin kasarsa da Ukraine a ranar 15 ga Mayu a Istanbul. A martanin da ya mayar, shugaban na Ukraine ya ce a shirye ya ke don tattaunawa kai tsaye, amma ya zama dole a tsagaita bude wuta...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Da safiyar yau Asabar Falasdinawa 7 sun yi shahada sanadiyyar harin da HKI ta kai a yankin Gaza. Sojojin HKI sun kai harin ne a kan sansanin ‘yan hijira na unguwar ” al-Sabrah” a cikin birnin Gaza, da hakan ya yi sanadiyyar shahadar Falasdinawa 5 a iyalai daya na Dulaibh. Shahidan su nel Saqar Ahmad...
    Fira ministan kasar Pakistan Shahbaz Sharif ya kira yi Majalisar kasa wacce take kula da makaman Nukiliyar kasar  da su yi taro. Wannan matakin da ake yi wa Kallon mai hatsari yana faruwa ne a daidai lokacin da kasar ta Pakistan take yaki da Indiya. Ita  dai Majalisar  kasar Pakistan dake kula da makaman Nukiliya...
    Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni a ranar Alhamis ya ziyarci sojojin Hedikwatar Task Force Brigade ta 27 Buni Gari, domin jajantawa waɗanda aka kashe kan harin da ’yan tada ƙayar baya suka kai.  A cikin jawabinsa Gwamna Buni ya bayyana cewa, abin takaici ne ga sake ɓarkewar tashe-tashen hankula da kuma hare-haren da ake...
    Fira ministan kasar Siriya ya bayyana cewa: Kasar Siriya zata gudanar da tattaunawa ba na kai tsaye ba da haramtacciyar kasar Isra’ila! Shugaban gwamnatin rikon kwarya na kasar Siriya Abu Mohammed al-Julani ya sanar a jiya Laraba cewa: Kasar Siriya zata gudanar da zaman tattaunawa ba na kai tsaye ba da gwamnatin mamayar haramtacciyar kasar...
    A yau Laraba kungiyar kare hakkin bil’adama ta “Amnesty Interantional” ta fitar da rahoto da a ciki ta yi kira ga HKI da ta kawo karshen shirinta na korar Falasdinawa daga Gaza da karfi, tare da cewa; Har yanzu Isra’ilan tana ci gaba da tafka laifukan yaki a Gaza da yi wa mutane kisan kiyashi.”...
    Wani rahoto na musamman da HKI ta gudanar akan asarar da ta fuskanta sanadiyyar yaki da Hizbullah, ya bayyana cewa, a fagen aikin gona kawai sun yi asarar dalar Amurka miliyan 108 wacce ta fara daga 8 ga watan Oktoba 2023. Kungiyar ReGrow Israel” ta ce, yakin da aka yi da Hizbullah ya yi barna...