Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Zamfara ta yi kakkausar suka ga gwamna Dauda Lawal kan kalaman da ta bayyana a matsayin bata gari dangane da kokarin gwamnatinsa na magance ‘yan fashi da makami da kuma bayar da tallafi ga wadanda ‘yan fashin suka kashe.

 

Hakan ya biyo bayan wani faifan bidiyo ne da aka ga gwamnan yana magana da manema labarai kan yadda gwamnatinsa ke tafiyar da harkokin tsaro da kuma jin dadin wadanda matsalar tsaro ta shafa.

 

A wata sanarwa da sakataren yada labaran jam’iyyar APC, Yusuf Idris Gusau ya fitar, ya bayyana kalaman gwamnan a matsayin rashin gaskiya da yaudara.

 

Malam Idris Yusuf Gusau ya yi zargin cewa, gwamnatin ta gaza cika wasu muhimman alkawuran yakin neman zabe, musamman alkawarin kawo karshen ‘yan fashi da makami a cikin watanni biyun farko da fara aiki.

 

Sanarwar ta kara da cewa “Gwamna Lawal da alama yana shirin cika shekara biyu a kan karagar mulki ba tare da samun wani ci gaba mai ma’ana ba kan babban alkawarin da ya yi a yakin neman zabe, maimakon a samu ci gaba, matsalar tsaro ta ta’azzara a Zamfara.”

 

A cewar Yusuf Idris, kalaman gwamna Lawal na baya-bayan nan a babban asibitin Gusau sun nuna rashin tausayi da jin kai.

 

“Jam’iyyar ta kuma zargi gwamnan da yin watsi da wadanda harin ya rutsa da su. “Maimakon ya ziyarci al’ummomin da ‘yan bindiga suka lalata ko aika sahihan tawaga don jajantawa da bayar da goyon baya, Gwamna Lawal ya zabi tafiya daga wata jiha ko kasa zuwa wata, yana jin dadin abokansa da ‘yan uwa yayin da mutanensa ke shan wahala.”

 

Ya yi nuni da cewa, babban abin da ya jawo cece-kuce shi ne ikirarin da gwamnan ya yi na cewa wadanda suka samu raunukan harbin bindiga suna karbar magani kyauta a asibitin kwararru na Yariman Bakura da cibiyar kula da lafiya ta tarayya da ke Gusau.

 

“Wannan karya ce kawai,” in ji Idris. “A makonnin da suka gabata ni da kaina na ga wadanda lamarin ya rutsa da su an mayar da su asibitin Yariman Bakura saboda rashin kudi, abin takaici wasun su sun mutu sakamakon haka, ba tare da taimakon gwamnati ba.”

 

Jam’iyyar APC ta yi kira ga gwamnan da ya fito fili ya bayyana sunaye, al’ummomi, da bayanan kula da wadanda suka ci gajiyar da aka ce sun samu kulawa kyauta, ciki har da kudaden da aka kashe da kuma kudaden da suka dace ko kuma bayanan biyan su.

 

Kakakin jam’iyyar APC ya kuma bukaci Gwamnan da mahukuntan asibitocin biyu da su buga cikakkun bayanai na jinya kyauta da aka yi a karkashin gwamnatinsa.”

 

Jam’iyyar ta kuma bukaci ‘yan jaridan da suka gudanar da hirar da su tabbatar da ikirarin gwamnan tare da zurfafa bincike kan al’amuran da abin ya shafa a lunguna da sako na jihar, kamar karamar hukumar Tsafe, wadanda ba za su iya samun kayan aiki a Gusau ba.

 

REL/AMINU DALHATU.

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: Zamfara

এছাড়াও পড়ুন:

Dan Majalisar Tarayyar Kaduna ya bar Jam’iyyar PDP

Ɗan Majalisar Tarayya mai Wakiltar Sabon Gari Daga Jihar Kaduna, Sadiq Ango Abdullahi, ya fice daga Jam’iyyarsa ta PDP.

Honorabul Abdullahi wanda shi ne Mataimakin Shugaban Kwamishinan Hukumar Kula da Hanyoyi (FERMA) ya alaƙanta ficewarsa da rikicin cikin gida da rabuwar kai da ya ki ci ya ƙi cinyewa a jam’iyyar.

A ranar Litinin ya aike da wasikar ta ficewa ga Shugaban PDP na Mazabar Hanwa da ke Ƙaramar Hukumar Sabon Gari, yana mai cewa rikicin ya hana shi taɓukawa matsayin zaɓaɓɓen ɗan Majalisar Tarayya.

Ya cewa saboda haka yana dacewar ficewarsa daga jam’iyyar ba tare da la’akari da siyasa ba, domin amfanin ɗauƙacin al’ummar mazabar.

Majalisar Shura ta fara ganawar sirri da Malam Triumph Zaben Kamaru: Issa Tchiroma Bakary ya lashe yankunan da Biya ke da rinjaye

Ya yaba wa jam’iyyar bisa damar da kuma gudummawar da ta ba shi domin hidimta wa al’umma.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kotu ta aike da mutumin da ake zargi da satar yaran Kano yana kaiwa Delta zuwa gidan gyaran hali
  • Gwamnan Enugu Peter Mbah da kwamishinoninsa sun koma APC
  • Dan Majalisar Tarayyar Kaduna ya bar Jam’iyyar PDP
  • Zaben Kamaru: Issa Tchiroma Bakary ya lashe yankunan da Biya ke da rinjaye
  • Hukumar Hisbah Ta Kama Wasu Matasa Da Suka Yi Aure Ba Bisa Ƙa’ida Ba A Kano
  • Sojoji sun kashe ’yan ta’adda 9, sun kwato kudin fansa a Borno
  • Ahmed Musa Ya Nemi Afuwar Ƙungiyar 3SC Akan Abinda Ya Faru Da ‘Yan Wasansu A Kano
  • Yemen Ta Gargadi Isra’ila Kan Fuskantar Hare-Hare Idan Ta Karya Yarjejeniyar Tsagaita Bude Wuta
  • Afuwar Tinubu za ta buɗe hanyar ci gaba da aikata miyagun laifuka — Atiku
  • Macron Na Ci Gaba Da Shan Matsin Lamba Daga ‘Yan Adawa Da Tsofaffin Na Hannun Damansa