Masana Kimiyya Na Kasar Sin Sun Gano Wata Sabuwar Hallita A Tashar Sararin Samaniya Ta Kasar
Published: 18th, May 2025 GMT
Hukumar kula da ayyukan sama jannati ta kasar Sin ta ce masu bincike sun tabbatar da wata sabuwar halitta da aka samu a cikin tashar binciken sararin samaniya ta kasar Sin, wanda aka yi wa lakabi da Niallia Tiangongensis
A watan Mayun 2023 ne, tawagar ‘yan sama jannati ta kumbon Shenzhou-15 ta gano wani samfurin halitta a cikin tashar binciken sararin samaniya ta kasar Sin yayin da take cikin da’irarta.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Kafar Labaran Amurka Ta Ce: Isra’ila Ta Yi Mummunar Hasara A Yakinta Da Kasar Iran
Hasarar da gwamnatin mamayar Isra’ila ta yi a hare-haren da ta kai wa kasar Iran ya kai dala biliyan uku
Kafar watsa labaran Bloomberg ta Amurka ta yi kiyasin cewa: Hasarar da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta yi a yakin da ta yi da Iran ya kai kusan dala biliyan 3, saboda gyaran gine-gine da suka lalace da kuma biyan diyya ga kamfanoni.
Kafar ta Bloomberg ta bayyana a cikin wani rahoto cewa: Hasarar da gwamnatin mamayar Isra’ila ta yi na nuni da irin yadda Iran ta kutsa kai cikin tsaron Isra’ila a cikin kimanin makonni biyu da harba makaman masu linzami kan yankunan kasar.
Jaridar Amurka ta rawaito wani jami’in gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila yana cewa: “Wannan shi ne kalubale mafi girma da suka fuskanta, wanda ba a taba samun irin wannan barna a tarihin haramtacciyar kasar Isra’ila ba.”
Bayanai na hukuma da ma’aikatar kudi ta haramtacciyar kasar Isra’ila ta fitar a cikin wannan yanayi na nuni da cewa: Irin barnar da aka yi na nuna irin yadda makamai masu linzami na Iran suka kutsa cikin tsarin tsaron haramtacciyar kasar Isra’ila a cikin kimanin makonni biyu da harba makaman.