Aminiya:
2025-05-16@23:02:47 GMT

An kama wasu da haramtaccen buhunan takin zamani 20 a Borno

Published: 16th, May 2025 GMT

Rundunar ’yan sandan Jihar Borno ta kama wasu mutane uku da ake zargi ɗauke da buhuna 20 na haramtattun takin zamani samfurin “Urea”.

An bayyana hakan ne a wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Borno DSP, Nahum Kenneth Daso ya fitar a ranar 15 ga Mayu, 2025.

Cikin makonni kaɗan Obasanjo ya murƙushe Boko Haram — Atiku Gwamnatin Katsina za ta gina birnin dawakai na farko a Afirka

Rundunar kai ɗaukin gaggawar (RRS), ƙarƙashin jagorancin Kwamishin ‘Yan sandan jihar CP Yusufu Mohammed Lawal ne ta kama waɗanda ake zargin a ranar 13 ga Mayu, 2025, da misalin ƙarfe 11:30 na safe a unguwar Tashan Journey, Maiduguri.

Waɗanda ake zargin sun haɗa da, Shamsuddeen Rabiu mai kimanin shekara 35, Malam Yau mai shekara 29, da Ibrahim Mohammed Sani mai shekara 30, suna jigilar takin zamanin da aka haramta samfurin urea ne, a cikin buhun taki na NPK a cikin keke NAPEP mai lamba GZA 17 ƁH Borno.

Rundunar ’yan sandan ta jaddada cewa, an haramta amfani da sinadarin urea a jihohi da dama ciki har da Jihar Borno, saboda yadda ‘yan ta’adda ke amfani da su wajen ƙera ababen fashewa.

Yanzu haka dai waɗanda ake zargin suna hannunsu, kuma ana ci gaba da gudanar da bincike mai zurfi akan su.

Rundunar ’yan sandan jihar ta jaddada ƙudirinta na tabbatar da tsaro da tsaron al’ummar Jihar Borno, sannan ta buƙaci jama’a da su guji yin mu’amala da haramtattun abubuwa.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Yan Sanda yan sandan Jihar Jihar Borno

এছাড়াও পড়ুন:

Mutum 10 sun rasu sakamakon rikicin gona da dabbobi a Filato

Aƙalla mutum 10 ne suka rasu, yayin da aka sace shanu da dama a wani sabon rikici da ya ɓarke a Ƙaramar Hukumar Riyom da ke Jihar Filato.

Sabon rikicin ya samo asali ne daga lalata gonaki, sace shanu, da kuma kai wa dabbobi hari, wanda mutane daga ɓangaren Fulani da Berom ke zargin juna da aikatawa.

Ce-ce-ku-ce ya ɓarke kan bayyanar Sheikh Alƙali a shirin ‘Gabon talkshow’  Hauhawar farashi ya ragu zuwa kashi 23.71 — NBS

A cewar sanarwar da rundunar Operation Safe Haven ta fitar, matsalar ta fara ne a ranar Litinin, 12 ga watan Mayu, 2025, bayan wasu matasa da ake zargi sun kashe shanu da suka shiga gonakinsu a ƙauyen Dayan, da ke Ƙaramar Hukumar Riyom.

Wasu da ake zargin makiyaya ne sun kai harin ramuwar gayya ƙauyen Danchindo da yammacin a ranar 13 ga watan Mayu, inda suka kashe mutane huɗu.

A ranar 14 ga watan Mayu, an kashe shanu 26, wasu kuma sun jikkata a ƙauyen Darwat, lamarin da ake zargin ramuwar gayya ce saboda kashe mutane da aka yi.

Daga bisani wasu da ake zargin ‘yan bindigar Fulani ne sun kai hari wani ƙauye da ke kusa da al’ummar Wereng Kam, inda suka kashe mutane shida.

Bayan samun rahoton tashin hankali a Riyom, jami’an haɗin gwiwar tsaro sun shiga tsakani tare da ganawa da wakilan jama’a domin kwantar da tarzoma, da kuma gargaɗin jama’a kan ɗaukar doka a hannunsu.

A bisa zargin sace shanu da kisa, an kama mutum ɗaya wanda ake ci gaba da bincike a kansa, tare da ƙwato shanu 130 a hannunsa.

Sanarwar ta kuma ce, tsayin dakan da sojoji suka yi ne ya hana maharan ƙone ƙauyen Wereng gaba ɗaya.

An fara sintiri domin kama waɗanda suka gudu, yayin da jami’an tsaro ke ci gaba da kasancewa a yankin domin wanzar da zaman lafiya.

Manjo Janar Folusho Oyinlola, kwamandan Operation Safe Haven kuma shugaban runduna ta 3, ya kai ziyara yankin inda ya gana da shugabanni da wakilan al’umma.

Yanzu haka an fara samun zaman lafiya yayin da jami’an tsaro ke ci gaba da tabbatar da tsaro a yankin.

Wannan lamarin ya faru ne kwanaki huɗu bayan wasu ’yan bindiga sun kai hari kasuwa a Ƙaramar Hukumar Wase, inda suka sace ’yan kasuwa biyar kuma suka kwashe kayayyaki.

Har ila yau, an ruwaito cewar maharan sun isa kasuwar ne a babura a ranar Litinin, lokacin da kasuwa ta cika da ’yan kasuwa da masu sayayya daga sassa daban-daban.

Sun fara harbe-harbe wanda ya sa mutane suka tsere domin tsira da rayukansu.

A baya-bayan nan, ɗaruruwan mutane sun rasa rayukansu, yayin da wasu da dama suka rasa muhallansu sakamakon hare-haren da ake yawan kai wa wasu sassan Jihar Filato.

Gwamna Caleb Muftwang na Jihar Filato, ya bayyana waɗannan hare-hare a matsayin yunƙurin kisan ƙare dangi.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamna Lawal Ya Jaddada Aniyar Inganta Kiwon Lafiya A Jihar Zamfara
  • Sojoji sun kashe ’yan bindiga da ƙwato shanun sata 1000 a Taraba 
  • Xi Jinping Ya Jaddada Wajibcin Koyi Da Nagartattun Halayen Wasu Mutane Masu Bukata Ta Musamman
  • Mutum 10 sun rasu kan rikicin gona da dabbobi a Filato
  • Mutum 10 sun rasu sakamakon rikicin gona da dabbobi a Filato
  • An kama wata mata kan zargin safarar makamai zuwa Katsina
  • Mutum 2 sun shiga hannu zargin yi wa ƙananan yara fyaɗe a Gombe
  • Gwamnati Kaduna Tace Zuba Jarin Da Ta Yi Na Euro Miliyan Dari Da Shadaya Zai Maganin Sufuri A Jihar
  • ‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi 239, Sun Ƙwato Makamai Da Alburusai A Kogi