Xi Ya Jaddada Kwarin Gwiwa Kan Ci Gaba Mai Inganci A Kasar Yayin Ziyararsa A Henan
Published: 21st, May 2025 GMT
A ziyarar da ya kai jerin kogon Longmen, mai shekaru sama da 1,500 wanda UNESCO ta sanya cikin jerin wuraren tarihi da aka gada na duniya, wanda kuma shi ne ke wakiltar matsayin koli na fasahar sassaka kan dutse ta kasar Sin, shugaban ya bayyana muhimmancin karewa da gado da ma yayata al’adun gargajiya na kasar Sin masu daraja.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
MDD: Yunwa Ta Kara Tsanani A Duniya Daga Shekarar 2024
A wani rahoton da MDD ta fitar a cikin kwanakin nan, ya bayyana cewa, tun daga 2024 ne yunwar da ake fuskanta a duniya ta kara tsanani domin ta shafi mutanen da sun kai miliyan 295.
Rahoton ya kara da cewa; wannan adadin na mutanen dake fama da yunwa mai tsanani suna warwatse a cikin kasashe 53 na duniya.
A Juma’ar da ta gabata aka fitar da wannan rahoton. Haka nan kuma an bayyana cewa idan aka kwatanta da yunwar da aka yi fama da ita a shekarar 2023, to da aka shiga 2024 an sami karuwar masu fama da matsananciyar yunwar da adadinsu ya karu da miliyan 13.7. Shekaru shida kenan a jere da ake samun karuwar yawan mutanen da suke fama da yunwa.
An kaddamar da wannan rahoton ne a karkashin kawancen kasa da kasa na fada da karancin abinci a duniya wanda ake kira da ( GNAFC) wanda ya kunshi hukumar Abinci ta duniya ( FAO), da kuma ( WFP) da sauran kungiyoyin da ba na gwamnati ba.
Babban magatakardar MDD Antonio Guterres ya bayyana alkaluman da aka fitar na adadin masu fama da matsananciyar yuwa da cewa; Wani adadi ne wanda bai girgiza duniya ba, domin tana tafiya ne a karkace.”
Wani sashe na rahoton ya yi ishara da cewa da akwai dalilai masu yawa da su ka haddasa karancin abinci; sun kuwa hada da talauci, koma bayan tattalin arziki, sauyin yanayi mai tsanani, sai dai kuma duk da haka rikice-rikice da fadace-fadace a cikin wasu yankuna, su ne ummul-haba’isin karancin abincin.