Wata takardar bayani da aka wallafa a yau Lahadi 18 ga watan Mayun shekarar 2024, ta nuna cewa, jimillar kudin da aka samu a masana’antar harkokin sadarwar tauraron dan Adam na kasar Sin ta kai yuan biliyan 575.8, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 79.9, a shekarar 2024, adadin da ya karu da kaso 7.39 cikin dari bisa na makamancin lokacin bara.

Takardar game da bunkasar masana’antar harkokin sadarwar tauraron dan Adam ta kasar Sin, ta yi nuni da cewa, a karshen shekarar 2024, yawan adadin manhajojin fasahar sadarwar tauraron dan Adam a kasar Sin ya zarce 129,000, kuma an sanya wa kusan wayoyin salula miliyan 288 a kasar tsarin da suke iya amfani da sadarwar daga tsarin amfani da tauraron dan Adam na BeiDou.

A matsayin tsarin sadarwa ta tauraron dan Adam na duniya da MDD ta amince da shi, tsarin BeiDou na kasar Sin ya shiga tsarin kungiyoyin kasa da kasa guda 11 ciki har da zirga-zirgar jiragen sama, da jiragen ruwa, da sadarwar wayar salula da sauransu, kana yana ci gaba da fadada yawan kasashe da yankuna masu amfani da shi a duniya.

A halin yanzu, kasashen Afirka fiye da 30 ciki har da Najeriya, da Tunisia, da Senegal da sauransu sun riga sun gina tasoshin CORS masu amfani da tsarin BeiDou.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: tauraron dan Adam a kasar Sin

এছাড়াও পড়ুন:

Kafofin Yada Labarai Na Amurka Sun Bayyana Kuzari Da Ci Gaban Da Fina-finan Kasar Sin Ke Samu A Bikin Cannes 

Kamar yadda mujallar ta bayar da rahoto a kai, rumfar fina-finai ta kasar Sin ta zama wata alama da ke nuna yadda kasar Sin ke ci gaba da kyautata cudanyar al’adu da hadin gwiwar kasa da kasa a harkar fina-finai. Kana, bisa samun karuwar jawo hankulan kasashen duniya da kuma kafa kwakkwarar turbar fasahar kirkira ta gwaninta da iya tsara labarin fim, sashen fina-finan na kasar Sin ya mike haikan wajen taka rawa sosai a duniya. (Abdulrazaq Yahuza Jere)

 

 

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Ciwon Mara Lokacin Al’ada
  • MDD: Yunwa Ta Kara Tsanani A Duniya Daga Shekarar 2024
  • Kafofin Yada Labarai Na Amurka Sun Bayyana Kuzari Da Ci Gaban Da Fina-finan Kasar Sin Ke Samu A Bikin Cannes 
  • An Ziyarci Gidajen Tarihin Kasar Sin Sau Biliyan 1.49 A Shekarar 2024
  • Masana Kimiyya Na Kasar Sin Sun Gano Wata Sabuwar Hallita A Tashar Sararin Samaniya Ta Kasar 
  • Rokar Kasuwanci Ta Kasar Sin Ta Harba Taurarin Dan Adam 6 Zuwa Sararin Samaniya
  • Bude Kofar Kasar Sin Dama Ce Ga Duniya Har Abada
  • Kudaden da sojojin Afirka suka kashe a bara ya karu da dala biliyan 52 a shekarar 2024
  • NAJERIYA A YAU: Shin Jam’iyyar NNPP Za Ta Kai Labari A 2027?